← Book details Aimana Mami Yusuf Dabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 62

Sashe 52

Aimana Mami Yusuf Dabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Lumshe ido yayi tareda buÉ—esu lokaci É—aya ya saki murmushi, ya buÉ—e kofofin hancinsa yana jin kamshin kasar sa da ya kwashe shekaru biyar cif baya cikinta ahankali kamar baya so ya ce
"Nayi kewarki kasata, ina son kasata" zama yayi zaman jiran jirgin da zai kaisa tashi nan da minti arba'in da biyar zuwa kano
"Yaya Aimah" yafaɗa a hankali sake kallon agogon da ke ɗaure a tsintsiyar hannunsa yayi still dai yanada saura mintina arba'in da uku kafin tashin jirgin da zai kaisa kano, mikewa yayi ya saɓa jakarsa a baya ya gyara zaman sun glass ɗin dake idanunsa ya fito zuwa waje inda masu texzii suke,
"Barka da safiya Baba" Shaheed yafaÉ—a sanda yakarasa gaban wani tsoho mai texzii
"Barka dai É—ana an sauka lafiya, ina zan ajje ka" faÉ—a masa sunan unguwar da Mustapha da Aimanah ke zaune yayi kana bayan ya shiga gaban motar mutumin har ya fara tafiya Shaheed ya ce
"Baba zamu iya zuwa nan da minti talatin mu dawo airport jirgin kano zanbi na karasa gida"
"Zamu iya duk da akwai yar tazara amma inba daÉ—ewa zakiyi ba a wajan har ma dawo bari na kara gudun motar" kwantar da kansa yayi saman seat na motar kamar wani mai barci, haka kawai yaji gabansa na faÉ—uwa yayinda suka kusa zuwa unguwar ya buÉ—e idanunsa da suka soma canza kala
"Yaya Aimah" yafaÉ—a a hankali,
"Munzo ranka ya daÉ—e" Baice komai ba ya buÉ—e murfin motar ya fita yana kallon tangameman gidan dayake zaton nan ne inda yazo, jakar sa ya ajje a bayan motar yana kallon mutumin mai tasi ya ce
"Baba bari na shiga bazan jima ba yanzu zan fito gidan yayata ne gaisawa kawai zamuyi"
"Afito lafiya" sa kai yayi zai shiga get man ya tare basa kofa
"Daga ina"
"Daga gidan uwarka, dalla gyara ka bani waje na shige kasan koni waye a gidan nan zaka tare min hanya," hannu yasa ya wurgasa can gefe ya shiga ciki yana huci
Aimanah na rike da Islam wacce ke kukan yunwa yau yini biyu kenan basu saka komai a bakinsu ba, bata san ya akai ba Maman Hanif jiya da yau duka bata shigo ba gashi ita kuma ba waya a hannunta, sallamar da taji yasata É—ago da sauri ta kalli wanda ke shigowa
"Shaheed" ta faÉ—a a hankali yayinda idanunta ke kawo ruwan hawaye, da sauri ya karaso ya tsaya a kanta can kuma ya zube kan kafafunsa yana kallo Yayar tasa ba ko kiftawa
"Yaya Aimah kece kece kuwa lafiyarki kalau cuta kika yi da kikai wannan ramar ina Yah Musty"
"Shaheed abinci, yaran nan yunwa suke ji rabonsu da abinci tun jiya da safe" bai tsaya tambayar ba'asi ba ya mike ya juya ya fita mai motar daya kawosa ya bawa kuÉ—i ya ce yaje gidan abinci mafi kusa ya yo masa take away ya juya ya koma ciki
"Yaya Aimah wai ina yayanmu"
"Shaheed muna cikin matsala" karo na farko data buÉ—i baki ta iya gayawa wani halin datake ciki a gidan kuka sosai Shaheed keyi, kamar wani karamin yaro
"Sannu yaya sannu yaya Aimah insha Allah saina fitta ki daga wannan halin, yanzu bazaki iya fita daga gidan nan ba, muje ki ga ya mike shiya taimaka mata tasa hijab ya É—auki islam da jikinta ya saki sosai ga zafi da jikin yayi, ya ruko hannun Aslam da Tasnim cak taja ta tsaya lokacin da suka je bakin get
"Shaheed gasu nan za su kashe ni, Shaheed mage ce gata can a kofar fita bazan fita ba katafi da yaran kaje ka sanar da halin da nake ciki, ga wasu nan zasu hanaku tafiya shaheed fita da sauri" hannu tasa ta tura su waje ta mai da kofar ta rufe gam, tana jin sanda Shaheed ke faman kwaÉ—a mata kira, zama tayi jikin get É—in
"Shaheed ka kai yaran nan wajan Ammi ku maza ku tafi kafin Sumayya ta dawo bazata bari ka tafi da su ba" Shaheed jiki a sanyaye ya saka yaran cikin motar data kawo sa a ciki ya basu abincin sukaci sosai har mamakin abincin da sukaci yake, ya kalli agogon hannunsa yaga jirgi tuni ya tashi kusan da mintina biyar kenan
"Baba kaini tashar da zan sami motar da zata kaini kano" kai kurum baban ya gyaÉ—a yana cigaba da tukinsa har yakaisu ta sha kuÉ—i sosai Shaheed yabawa driver É—in ya sami wata motar su kaÉ—ai yabiya suka É—au hanya, yana rungume da Islam wacce yakejin kaunar yarinyar ta daban data yan uwanta, Tasnim na gefansa na dama yayin da Aslam ke gefansa na hagu sun kwantar da kansu a jikinsa sunata barci, gafda zasu shiga kano Islam ta fara kelaya amai kamar zata amayar da hanjin cikinta jikinta ya É—auki rawa idanunta na kafewa, gaba É—aya hankalin Shaheed yatashi sai cewa mai motar yake
"Dan Allah ka taka motar nan sosai mukai yarinyar nan hospital karta mace min" Aminu kano hospital suka je da wayar driver É—in yayi amfani ya kira wayar Ammi, Ammi dake tsaye gama wayarta kenan da Ahmad wanda ke sanar mata jirage biyu kenan na sauka daga Abuja amma ba shaheed a ciki zai taho gida, gaba É—aya hankalinta ya tashi tunani take maiya sami autan nata a yanda suka lissafa karfe sha É—ayan rana a kano zatai masa gashi yanzu magana ake ta huÉ—u harda kwata na yamma, jikinta ya kuma yin sanyi ta zurfafa cikin tunani har tsorata tayi sanda taji wayarta tayi kara, kamar bazata É—aga ba ganin lamba ba suna sai kuma ta É—aga sanda kira na biyu ya kuma shigowa wayar
"Ammi ina hospital kiyi maza ki zo dan Allah"
"Shaheed kana lafiya wanne asibitin maiya sameka yimin bayani"
"Ammi ina lafiya, kizo dai nan Aminu kano" cikin ruɗewa ta fito, tareda Momy suka tafi bayan ta mata bayanin Shaheed ya kirata, Ahmad ta kira tace su haɗu a can Ammi duk gudun da Momy keyi da mota gani take kamar sanɗa take ta kagu taje taga maiya sami ɗanta, yana tsaye sanda suka karasa a wata farfajiya ko gama dai daita motar batayi ba Ammi ta fito tana taɓa Shaheed
"Lafiya mai kake a hospital," baice komai ba yaja hannun Ammi suka shiga wani É—aki, gaba É—aya yaran suna kwance a gadajansu harsu Aslam yasa a binciki lafiyarsu
"Ammi kuna kasar nan amma yaya Aimah na cikin wani hali ba wanda ke bin ta kanta kun mata adalci kuwa?" Ammi kanta ne ya sara tai saurin dafa kan tareda dafa bango
Chapter 52 · 0% Book details