← Book details Aimana Mami Yusuf Dabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 62

Sashe 36

Aimana Mami Yusuf Dabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Aimanah na kwance kan gado, yau gaba ɗaya batajin daɗi zazzaɓi take ji, Mustapha ya shigo ɗakin yatarar da ita kwance
"reina har yanzu baki tashi daga kwanciyar nan ba" ido kawai ta zuba masa ta kasa ce masa komai, hannu yasa ya taɓa jikinta yaji zafi zau
"reina bakida lafiya kizo na kaiki asibiti"
"Baby nifa lafiyata kalau, ina dai jin yunwa jikina kuma ba kwari bazan iya dafawa ba"
"Mai zaki ci to"
"Dambun shinkafa mai zogale da gyaÉ—a"
"Yanzu reina ina zan sami dambu dan Allah yanzu da ranar nan" turo baki tayi gaba kana ta juya masa baya ranta ɓace, dafe kai yayi shima baice mata komai ba yafita daga ɗakin, kai tsaye gidan Ammi ya shiga yayi sa'a dawowarta gidan kenan daga makaranta gaisawa sukayi yai tsaye ya kasa ce mata komai, shi kunyarta ma yakeji jiya haka Aimanah tasa ta mata awara yau kuma gashi tazo da mata maganar wai dambu
"Yadai babban Mutum kazo kamin tsaye anan" shafa kansa yayi kana ya ce
"Ammi reina ce da rigima wai dambu zata ci ni narasa wannan cin nata" mirmushi Ammi tayi kana ta ce
"Badamuwa zan bawa Surayya ta kawo mata" Mustapha ya juya ya fita bayan yayi mata godiya sanda ya koma gida yatarar Aimanah har tayi barci, bai tasheta ya zauna gefanta yana kallon yanda take barci ta wani taɓe fuska kamar mai shirin kuka ta cuno baki gaba, sumbatar kumatunta yayi ya fita daga ɗakin, Sumayya ta gama shaka ganin yanda yaketa zuruftu wajan Aimanah amma bata ce komai ba zura masa idanu kawai tayi, Aimanah sosai taci dambun nan, yau kuma gaba ɗaya sai taji nan duniya ba abinda takeson jin kamshi sama da turaran Mustapha ɗakinsa ta shiga ta rinka shan shana kayan sa harta gaji ta kira wayarsa
"Baby nidai kamshinka nakeson ji kadawo gida"
"Nadawo kuma ni bana ma kusa munje gwarzo nida Mas'ud"
"Baby kasan yanda nakeso naji kamshinka kuwa dan Allah kadawo"
"Ok gamu nan a hanya zanzo yanzu" shuru tayi nan barci ya kuma yin gaba da ita, sai farkawa tayi taga Mustapha a kusa da ita, jikinsa ta shige tana jin kamshin turaransa
"Baby ki yarda muje hospital na rantse bakida lafiya, abincin da kike ci yayi yawa ga yawan barci yau zaki iya kirga sau nawa kikai barci" tabuÉ—e baki zatai magana amai yazo mata hannu tasa ta danne bakinta da gudu ta shiga bathroom na cikin falon ta fara kwarara amai kamar zata amayar da yan hanjinta, sosai ta galabaita, Mustapha na tsaye gefanta sai sannu yake mata, taimaka mata yayi tai brush suka fito yana rike da ita, zubewa tayi saman tiles tana juyi rikeda cikinta
"Wayyo Yayanmu zan mutu, wayyo cikina" gaba É—aya hankalin Musty yatashi
"Baby kinga abinda nake gaya maki ko, zo muje hospital a...kafin ya rufe bakinsa wani aman ya kuma zuwar mata, wayarsa ya ɗauka ya kira Ammi yagaya mata Aimanah ba lafiya, kayan jikin Aimanah data ɓata ya cire mata ya taimaka mata tai wanka Ammi da Momy suka shigo lokacin Aimanah na kwance kan doguwar kujera tana murkusu su
"Mustapha mai kake jira baka ga yanda take ba akaita hospital" Ammi tafaÉ—a hankali tashe ganin idanun Aimanah sun canza kala
"Ammi taki yarda cewa take na barta ta mutu a É—akinta"
"To biye mata zakayi" Momy tafaÉ—a
"É—akko mata hijab" Momy tasa mata ta ruko ta suka fita, hankali tashe Mustapha ke tuki jefi jefi yana juyowa yana kallon Aimanah daketa kukan wayyo cikinta kirjinta kanta duk ta tashi hankalinsa har suka karasa É—aya daga cikin hospital É—in dake zoo road, nan da nan likitoci sukayi kanta aka É—aura mata drip sannan nurse ta É—ebi jininta zuwa lap, bayan mintuna aka dawo masu da sakamakon Aimanah na É—auke da cikin sati biyar
"Sati biyar" Mustapha ya maimaita yana dariya, Ammi tai kasa da kanta tana murmushi Momy na faÉ—in
"Alhamdulillah masha Allah, Allah abin godiya ubangiji ya raba lafiya"
"Amin" Mustapha yafaÉ—a a fili, Ammi ta É—ago ta kallesa
"Bakada kunya Musty a fili kake amsawa da Amin"
"Ammi taya zanki amsawa addu'a fa mai kyau Momy tayi"
"Zoka ajjeni a gida tunda ga Momy nan mai zanyi anan" ta fita bayan tayiwa Aimanah sannu, Momy tabi bayanta suna magana, Mustapha ya matso kusa da gadon da Aimanah ke kwance ya sumbaci cikinta, murmushi tayi tana kallonsa
"Daman wai duk cin nan Babynmu ne yaja"
"Baby na ce dai taja, nifa mace nakeson haifa"
"Ni kuma boy nakeso nasa masa sunan Daddyn daya haifa min mata ta" taɓe baki Aimanah tayi tace
"Allah ya kiyaye ni mace zan haifa Saudat" dariya yayi yana kallonta
"Zan maida Ammi gida maizan siyo maki a hanya"
"Apple" tafaÉ—a tana kautar da kai gefe, dawowar Momy É—akin yasa ya fita yana murmushi

Murjana gaba ɗaya abin duniya ya isheta tun jiya dataje chemist suka mata test suka tabbatar mata tana ɗauke da juna biyu tayi kuka sosai daran jiya ita kaɗai a ɗaki tayi nadamar da bata taɓa irinta ba, yau kwanan amarya uku bata gari tayita kiran wayarta bata ma shiga bare ta ɗauka hakanne yasa yanzu Murjana ta shiga wajan Sumayya, Sumayya da damuwa take cin ranta tana ganin Murjana ta fashe da kuka
"Murja ina cikin damuwa a gidan nan, son Mustapha zai kashe ni gaba É—aya bana gabansa, kina gani kwanaki fa mota ya saiwa Aimanah benz ni kuma ya sai min da toyota, komai zaiyi sai nata yafi nawa haka ake hakane adalci Murja?"
Chapter 36 · 0% Book details