← Book details Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 94

Sashe 88

Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Ba karamin party akayi wurin reception, dama ga Ameera sarauniyar rawa kuma Khalid sarkin rawa, rawa sukasha har na tashin hankali, Khalid komawa gefe yayi yana kallon yanda matarshi take dansewa, daga baya iyaye tafiya sukayi suka bar yanmata da samari suka shiga da party, wani crazy beat aka saka mai instrumental, fili yan mata suka bawa samari suka shiga da rawa kaman hauka har da kwantawa kasa don dadin dancing, suna cikin haka wata siririyar budurwa ta shigo mai shegen kyau kamar ita tayi kanta, da ka ganta ka ga Khalid saidai ita tafishi kyau kasancewan ta mace, ga hujen hanci rawa ta farayi ta nufo inda Khalid ke tsaye suna rawa, juyowa Khalid yayi ya wangalo idanuwa tare da rungume yarinyan
"Baby ya akayi kika dawo?...bana fada maki kar kizoba?..." Ya tambayeta, marairace fuska tayi tana cewa
"Kun hanani zuwa na yaya Salem Sannan kuma ashe kar inzo naka?...AI bani kadai ke karatu abroad ba..." Khalid girgiza kai kawai yayi ya kama hannun ta yayi introducing Ameera as his wife, yarinyan kissing Ameera tayi a cheeks dinta tana cewa
"Yaya dole ka mutu kanta... Wannan kyau haka?..." Ameera da Khalid Dariya suka, yarinyan wurin mc taje ta fada mashi ya fadawa mutane duka su zauna zata danse da yayan ta, aikam kowa komawa yayi ya zauna ya rage daga yarinyan Sai Khalid cikin katon filin, nan akasaka masu wani sabon waka suka fara rawa kaman mahaukata, banda Dariya babu abinda Ameera da sauran mutane suke, Ameera har da rike ciki saboda Dariya. Atakaice Sai twelve na dare aka tashi aka maida ameera gidansu cos the following day zaa kaita yola, adaren mom ta zaunar daita tayi mata nasiha ba kadan ba, har kuka Ameera ta farayi saboda yanda mom take magana. Sai wajen 3am ta kwanta, wacegari da wuri mom ta tadata tayi sallan Sannan takara yimata nasiha kan zamantakewa Daga nan ta koma dakinta Zainabu ta hada mata ruwan wanka mai dauke da turare, tayi wanka ta fito ta tadda anty Sadiya ta fiddo mata wasu blue lace masu shegen kyau da tsada, dinkin skirt da riga, skirt din har Jan kasa yake, ba karamin kyau tayiba, kwalliya wance aka biya donyi mata kwalliya tayi kyau sosai, mom ta kawo mata tea my kauri da kwai amma ta girgiza mata kai, zare mata ido mom tayi
"Mom na koshi..." Ta fada kaman zatayi kuka,
"Ubanme kike CI da safen nan zakice kin koshi?...come on amsa..." Ta daka mata tsawa, kuka ta farayi, anty Sadiya ta amshi tea din ta fara rarrashin ta tana bata da kanta tana sha har tasha rabi, lifaya aka sa mata mai shegen kyau aka rufe mata kai da hulan, wurin su dad aka kaita sukayi mata nasiha aka kaita wurin mom ta karayimata, kuka ta farayi sosai, hahhh su Ameera anyi hankali, ita kanta tasan Sai yanzu tayi aure. Motocin daukan amarya ne suka fara shigowa gidan, nan su anty Sadiya sukazo daukanta, kiri2 Ameera tace bata zuwa tana kuka kaman ba itace suke dirty dance da Khalid ba jiya. Da kyar aka banbareta daga jikin mom aka kaita kasa Sai ihu take kaman wacce zaa kai lahira, wayanta dake hannun Zainabu Sai ringing take, amma kuka ya hanata amsan wayan, har aka kaita bakin wani white range Rover bata bar kuka ba. Affan na gefen ta yana kuka shima kaman ranshi zai fita, anty Sadiya koreshi tayi yace shima zashi raka anty, dole anty Sadiya ta amince suka shiga cikin mota tare. Motoci 20 aka kawo daukan amarya, kowacce mota mutum biyu baya Sai daya gaba. A haka yanmatan suka shige motocin akayi hanyan Adamawa.
Chapter 88 · 0% Book details