← Book details Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 94

Sashe 29

Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tawa tana cikin aikin abincin lunch wayanta yafara ringing, kallon number tayi taga irin number yan Mtn, tsaki tayi ta katse wayan, bayan kaman second goma suka kara kira,
"Wai meye haka" tafada cikin fada mami kallon ta tayi
"Kini?" Cikin fada tawa tace
"Mami yan Mtn din banza nan ne" mami bata ce komaiba wayan ya cigaba da ringing harta tsinke, kara ringing yayi
"Pick mana" mami ta fada mata, tawa picking tayi ta saka wayan a speaker ta ajiye shi don tasan ba magana suke yiwa mutum ba, sai jitayi ana cewa
"Hello..miss Tawakaltu" da sauri ta kalli wayan batare data daukeshi, still cewa akayi
"Hello.. Miss Tawakaltu can you hear me" kallon mami tayi sannan tace
"Hello..please who is this?"
"Am I speaking to Tawakaltu Lukman?"
"Yes please who are you?"
"My name is Mr Michael.. I am calling from Mtn office in abuja..I want to congratulate you for you are among the lucky winners that win 25 million naira and a mansion in maitama ..." Da sauri tawa ta katseshi dacewa
"Please sir what sought of joke is?"
"Sorry miss but am not joking.. So please come to abuja before or on Thursday and collect your money and house" yana kaiwa nan ya katse wayan, tawa tsale tayi tana ihu ta fada jikin mami, mami mikar daita tayi tafara rawa
"Wayyo Allah na..alhamdulillah.. Alhamdulillah.. Alhamdulillah" tawa ta dinga maimaitawa,
"Mami..Allah yaamshi aduan mu..Allah yashare min hawaye na.." Tana fadan haka ta fara kuka, mami rungume ta tayi itama ta fara kuka
"Mami in karya ne fa?..mami in karyane sun dauki alhakina..." Girgiza mata kai mami tayi
"Insha Allah.. Babu karya cikin wannan maganan"
"Mami ya zanyi inje abuja..ban san kowa abuja ba..." Bata gama magana ba wayan ta yafara ringing tana dubawa taga Salem, da sauri ta dauka, zatayi magana Salem yayi saurin cewa
"Habibty abuja zani..Abdul zai shigaba da zuwa amsan abinci..." Tana exaggerating tace
"Me zakayi abuja?"
"Wani abokina ne Mtn sukayiwa kyauta shi...." Bai karasaba ta ce
"Sir nima yanzu aka kirani" tafada tana daka tsalle,da sauri Salem yace
"Me akayi naji kaman you are rejoicing?"
"Sir Mtn sunce sun bani 25m da...." Wani irin ihu Salem yayi kaman baisan abinda ke faruwa ba
"Habibty am happy for you..you are such a good person and Allah have reward you" har lokacin tawa bata bar tsalle ba
"So when are you redeeming your price?" Ya tambayeta, shuru tayi for a while sannan tace
"Kuma Mtn office sin zaku?"
"Yes..nan da hour daya zamu tafi da abokina don cewa sukayi yazo kafin su rufe"
"OK bari inyiwa mami magana zan kiraka"
"OK" yafada yana murmushi.
Tawa komawa tayi jikin mami tana cewa
"Mami wannan mutumin mai zuwa nan "
"Eh"
"Shima yanzu nan zai kai abokinshi abuja amso kyautan" mamaki ne ya kama mami
"Ashe suma sun samu"
"Eh..yanzu mami ya zaayi in he abuja?"
Mami shuru tayi
"Ko zaki bisu?" Mami ta tambayeta, ido ta zaro
"Mami yaufa zasu tafi"
"To ya kikeso?..so kike ke kadai kije?... Tunda chan zasu kawai ki bisu..and kinsan cewa bani da lafiya da zan bikI" tawa shuru tayi tana tunanin abinyi...don ko kadan batason ta kadaita da Salem ko kadan
"Mami sunce sai gobe zasu dawo...INA zan kwana?"
"Ki kirashi kiji inda zasu kwana mana" tawa kiran Salem tayi bayan yayi picking tace
"Sir inkuje abuja INA zaku kwana?" Mami ta kasa kunne don taji abinda Salem zaice
"Gidan brother na zamu kwana"
"Yana da family?"
"Eh mana..yana da yara da maranshi biyu" tawa kallon mami tayi, ahankali mami tace mata
"Tell him Zaki bisu" ahankali tawa tace
"Sir..In motan bai cika ba zanbiku" Salem runtse idanuwa yayi don dadi
"Mami zata amince?"
"Eh..ita tace in biku"
"OK..to ki shirya ..nan da 30 minutes zanzo daukan ki..kinsan abuja da akwai nisa.." Da sauri tawa ta kashe wayan ta shiga wanka, mami kuma na shirya mata bag sin dazatayi tafiya dashi.

Salem mikewa yayi yana cewa
"Lokaci yayi da ZAKISAN KONI WAYE" Abdul ya kira, yana zuwa yace
"Pack my things.. Yau zan bar Kano" Abdul zaiyi magana Salem yajuya ya koma dakin shi yana balla button din riganshi,Abdul dinshi yayi ya fiddo kayan dake cikin wardrobe, Salem kallon shi yayi
"Me zakayi dasu?"
"Sir cewa kayi I should pack your things"
"Banda kaya..just pack my shoes, wristwatches, perfumes da sauran important things"
"OK sir" cikin 10 minutes Abdul ya gama cika Nike traveling bag da Salem accessories, shima Salem designer polo shirt da jean ya saka, Abdul fitowa yayi da bag zai saka cikin jet Salem yayi mashi umarnin ya sakasu bayan taxi, babu musu ya sakasu
"Ka kulle koina ka fito mu tafi" yabawa Abdul umarni. Babu musu ya kulle ya dawo gefen Salem dake zaune a driver seat ya zauna, sai tunanin abinda ke faruwa yake, gashi babu dama yayi tambaya
"Sir what about the jet?"
"Zansa pilot yazo daukan shi" ya amsa mashi sannan ya tada motan suka bar gidan bayan Abdul ya kulle gate.

Da sauri tawa tafito daga bathroom, without wasting of time ta shirya cikin wrapper skirt and blouse, powder ta shafa sai kwali tare da wet lips,
"Tawa"
"Yes mami"
"Ki kula da kanki...don't let anything happen to you.. Kisan Allah yana kallon ki..kuma dakin dawo saina dubaki" Dan daria tawa tayi
"Mami don't worry...insha Allah nobody is going into my pant"

"Nadai fada maki..yanzu ya zamuyi da abincin mutumin?"
"Sir Salem yace zai aiki wani daukan abincin.. "
"Ga dubu goma cikin kudin jiya..ki rike in case zaki bukaci wani abu"
"Thank ma" tafada tareda amsan kudin, wayanta yafara ringing ta dauka
"Habibty ki fito mu tafi time is not on our side" yafada sannan ya katse wayan,
"Mami yazo" mikewa tayi ta dauki Vail dinta, itama mami bin bayan ta tayi da bag din da ta shirya mata. Suna fitowa waje Salem yayi sauri fitowa ya gaida mami, bayan ta amsa tace
"Please take care of my daughter.."
"Yes ma"
"Ka tuka motan ahankali"
"Insha Allah" jikkan hannun mami ya amsa, itakuma mami hugging tawa tayi tare dayimata kiss sannan tayi mata bye.
Tawa bayan motan ta bude ta zauna, Salem sai kallon lustrous lips dinta ta mirror yake. Suna Zuwa zoo road yayi parking
"Alh Abdul kazo ka amshi motan don hannuna ciwo yakeyi min"

💜💙💛❤💚
ZAKISAN KONI WAYE
💙💛❤💚💜

®zuwairat(ummu maryam)

3⃣2⃣

Baya ya dawo kusa da tawa ya Abdul gaba shi kadai, kallon shi tayi don shigan shi na yau ya sha different da sauran dressing da yakeyi, ita atunaninta don zaiyi tafiya ne, dan kallon shi takarayi, shima ya kalleta suka hada ido tare da sakarwa juna murmushi,
"Habibty sorry for boarding you with my personal problem.." Dan murmushi tayi batare data kalleshi ba
"Don't mind ...what are friends for" Dan harara ta yayi
"Ni friend dinki ne?..kodan yanzu kinzama millionaire kike..."
"Please.. I don't mean it that way"
"Apologies accepted" juya zamanshi yayi yana fuskantanta
"Miss..let me interview you..me zakiyi da 25m?" Tawa shuru tayi kaman mai tunani
"Gaskiya I don't want to get my hopes up..zan jira sai da gaske ne cos har yanzu ban yardaba" dan murmushi Salem yayi yana tunanin
"Come on..you are rich already" azahiri yace
"Just kiyi tunanin an baki kudin yanzu...me zakiyi dashi?" Lumshe idanuwa tayi sannan ta fara cewa
"First of all zan fara kai mami hospital.." Surprisedly Salem yace
"Is mami sick?" Ahankali tace
"Yeah..tana da chronic asthma...".
" oh sorry.. Then what next?"
"Then I will open a medium supermarket for mami da yaran da zasu dinga taimaka mata..." Kallon shi tayi tadan sakar mashi murmushi
"And zan baka 3m kafara business.." Baki Salem yabude kaman yana murna
"Are you kidding me?" Girgiza mashi kai tayi
"Am serious" Abdul dake sauraronsu yayi murmushi yana tunanin
"Nima kabani mai sona don Allah koda iyamurace" Salem yace
"Amman habibty I will be the happiest man on earth.. With 3m I can make it"
"Insha Allah"
"Then what next..."
"I will go to school"
"And"
"Shikenan" kallon mamaki Salem yayi mata
"Baki gamaba..continue"
"Shikenan nidai" tsaya kallon ta yayi
"Banji kinyi maganan auren mu ba" tawa murmushi tayi
"Aure a wannan stage din?..nifa adolescent ce.. Ba yanzu zanyi aureba"
"Waike meyasa da anyi maki maganan aure sai kice you are a child"
"Karya nayi?"
"Hmmm.. Habibty many of your age are married with a child or children"
"Hausawa kenan..mu bamu haka" Salem kauda kanshi gefe yayi tare da daure fuska kaman bai taba daria ba, kara kallon ta yayi
"Amman habibty baki sona kaman yanda nake sonki..if you love me you will want to be with me" tawa dai shuru tayi batace komaiba, haka suka cigaba da tafiya babu Wanda ya cewa Dan uwansa magana, Salem sai kallon ta yake, itakam relaxing tayi tana lumshe idanuwa, tunanin abubuwa da dama cikin ranta.
Chapter 29 · 0% Book details