← Book details Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 94

Sashe 34

Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wajen karfe one suka isa yola,har lokacin hawaye bai bar zubowa tawaba, nadaman abinda ya fidota kawai take, wani makeken gida suka shiga sukayi parking, waya taji sunayi
"Mun iso..." Shuru yayi for a moment sannan yace
"OK ma" fita sukayi suka bude mata, kin fitowa tayi, daya mai bakin fuska ya fixgota, ya rike mata hannu
"Dan Allah kar kuyimin komai.. Narokeku...ni kadaice wurin mamina... Please kuyi hakuri.." Ta dinga fada cikin muryan ta Mara fita don kuka, cikin wani katon falo suka wulla ta sannan suma suka shigo, falon ta fara kallo, gabanta ne yayi mugun faduwa data ga makeken hoton Salem, sanye yake da red fitted suit hannunshi cikin aljihunshi.. Fuskanshi kaman da models, kara kara juyawa tayi ta ga wani yana tsaye bayan wata beautiful mata da wani cool looking man, nan tasan gidansu Salem aka kawota, sabon kuka tafarayi, sun fi minti ashirin da zuwa sannan Umma ta fito, tafiyanta na kasaita tamkar ka tabata jini ya fito, tawa daga kumburarrun idanuwanta tayi ta kalleta, gani tayi da ita da Salem kaman an tsaga kara, tsawo kawai zai nuna mata, da sauri tawa tayi kneeling down kanta kasa hawaye na zuba tana fargaban abinda zai faru, Umma tsayawa tayi tana kallon tawa, mamaki ne kwance kan fuskanta don atunaninta wata gingimemeyin Yoruba zata gani, sannan kuma Sam babu alaman yarbancin jikin ta, kallon fuskanta tayi taga she is beyond wonderful.
"Please sit" ta fadawa tawa, Ahankali tawa ta girgiza kanta, gaidata tayi dukda muryan ta bata fita,amsawa tayi tana kara mamaki don Sam hausanta babu alaman yare cikin shi..kallon guys din tayi
"Are sure she's the one?"
"Yes ma..daga gidanshi muka daukota" daya daga cikin guys din ya amsa mata, kallon yanda tawa take shessheka tayi
"Kunyi mata wani abune?" Ta sake tambayan su, da sauri suka girgiza mata kai.
"Excuse us" ta fada masu, da sauri suka fita, kallon tawa tayi
"Come closer" ta umarceta, tawa bata mike ba tayi rarrafa zuwa gabanta, Umma kura mata ido tayi ta rasa abinda zata ce mata, Ahankali tace
"What is your name?" Cikin shessheka tace
"Tawakaltu Lukman"
"Wace yare ce ke?"
"Yoruba" ta amsa mata Ahankali,
"Koma ki zauna muyi wata magana" tawa kara girgiza mata kai tayi,
"Bari insa akawo maki abinci kafin muyi magana" tawa still girgiza kai tayi, Umma tsaya kallon ta tayi sai taga sam yarinyan ba irin yarinya marasa jin maganan nan bane...cikin zuciyanta sai tafara nadama daukota dayawa akayi,
"You can't let your only son marry Yoruba" wata zuciya ta fada mata,
"Kinsan Salem Yusuf sulaiman?" Umma ta tambayeta, Ahankali tawa ta gyada mata kai
"Meke tsakanin Ku?" Ta sake tambayan ta, shuru tawa tayi bata ce komaiba, Umma tacigaba dacewa
"Nice mahaifiyan Salem...kuma banason ki dauka cewa don inci maki mutunci yasa nasa adauko Mani ke...me kikeyi gidan ?" Gaban tawa faduwa ya farayi,still bata ce komaiba
"Zina kukeyi?" Da sauri tawa ta girgiza mata kai sabon hawaye na zubo mata,
"Then me ya mace kamanki takeyi gidan namiji mara aure?.." Tawa bata ce komaiba sai goge hawayenta take, Ahankali Umma tacigaba dacewa
" anyway.. Kome ke tsakanin Ku inason ta tsinke from this moment... Badan baki yimin ba..Aa..saidon aladan mu da naku ba daya bane ...but if you want...you can name your price... From 1m to 20m zan iya baki indai kin yimin alkawarin zaki rabu da Salem" tawa girgiza kanta tayi tafara cewa
"Please I don't want anything.. I want to go to my mami...kuma bazan kara kula Salem ba" tafada cikin muryan ta Mara fita, Umma duk sai taji haushin kanta
"Please kar ki kirani da muguwar mace...am just a woman that loves her son.." Ahankali tawa tace
"You are not ma..." Umma Dan murmushi tayi, tawa kuma goge hawayenta tayi,
"Yanzu ina baki shawaran kar ki Kara zuwa gidan saurayi..baa haka a aladanmu" Umma ta fada mata, Ahankali tawa tace
"First love wallahi bansan gidanshi bane..." Umma dadin sunan taji.. Don babu mai kiranta hakasai Salem
"Hope babu abinda yayi maki" da sauri tawa ta girgiza mata kai
"Ki gayamin in yayi maki wani abu.. Am he's mother..I know how to deal with him"
"Baiyi min komaiba "
"That's good to hear..hope baki ji haushin abinda na fada maki ba?"
"No ma" ta amsa mata Ahankali
"Tashi daga kneeling kici abinci sai insa a maida ki gida" bata tashi daga kan gwuiwowinta tace
"Thanks ma..na koshi"
"To shikenan.. Yanzu are we friends?" Da sauri tawa ta daga mata kai
"Then ki bani number ki..sai mu dinga gaisawa time to time" Ahankali tawa taba labarin yanda guys din suka yarda mata waya, mikewa Umma tayi ta shiga bedroom dinta, baa dadeba ta fito dauke da wani waya gionee m6 amma ba sabuwa ba, sai wata Leda mai dauke da kudi, tana zuwa ta mika mata wayan, kememe tawa taki mika hannu
"Ikon Allah.. Ki amsa mana" girgiza kai tayi
"To..kina fushi kan maganan danayi maki kenan"
"Aa..nagode" ledan ta mikewa tawa
"Gashi ki sayi duk abinda kike so.." Shima tawa girgiza mata kai tayi
"Gaskiya we are not friends.. Ya zaayi kiyi refusing dina..to amsa" ta kara mika mata wayan, Ahankali tawa ta amsa
"Thanks ma" Umma kara miko mata kudin tayi amma taki amsa, duk magiyan da Umma tayi bata amshi kudin ba
"Shikenan.. Amma ki huta zuwa yanma sai a tafi dake gida" kanta kasa tace
"Zan tafi yanzu"
"To shikenan.. Bari insa driver na ya maidaki gida" girgiza mata kai tayi
"Kawai su kaini park" Umma sawa tayi aka dauketa tana tunanin anya ta kyauta abinda tayi..don yarinyan ta kwanta mata
"She's Yoruba" tafada cikin ranta.
Tawa mancewa tayi bata dauki bag dinta daga cikin motan guys din da suka kawotaba, wani hummer ya kaita park. Kuka kawai take in ta tuna daga yanzu babu ita ba Salem.ji take kaman yau yafi kowane rana bakin ciki da muni a rayuwanta,.Ana sauketa ta duba taga babu bag dinta, wani shagon da ake saida waya ta shiga ta mika masu wayan da Umma ta bata, abanza suka sai wayan a 18k, bata tsaya ciniki dasuba ta amshi kudin, cikin shagon ta amshi wayan ta kira mami tayi mata karya cewa motan su ta lalace sannan kuma an dauke mata waya a park.
Cikin park ta shiga ta hau motan Ilorin , duk Wanda ya ganta yasan bata cikin hayyacinta.

💜💛💙❤💚

Tun cikin kauye ake tambayan hinde abinda ya faru cos kuka take kaman anyi mata albishir da jahannama, bata cewa kowa kala ba ta isa gidan ameera, da kuka ta iso Wanda hakan yayi sanadiyan mikewa ameera dake kudundune cikin zaninta,
"Wayyo sun kashe ni " tafada tana kuka
"Inna meyasameki?" Yarta ta tambayeta, hinde zama tayi nan kasa
"Zinarin da ameera ta bani aka amshe../" bata idaba ameera dake tsaye bakin kofa ta saki ashar
"Wallahi kinyi kadan...kawai ki kawo min zinari na..don wallahi sai ya sayi dukkanku.." Tafada tana rike kugunta
"Wallahi Aisha..wasune suka amshe..."
"Tell that to the birds..sai kin biyani kayana...kawai daga nace Dan saki da ku shine zaki cuceni?.. Aikam ban yarda sai kin biyani..." Hinde bata ce komai ba tacigaba da kuka
"Ki fidomin kayana..barauniya..." Gaskiya ki bar zaganmin uwar..." Inji diyar hinde, tafa hannu ameera tayi sannan ta nuna diyar
"Look at this creepy zombie.. Har kin isa kiyi magana inda nake magana?..ki gayawa barauniyan nan ta bani kayana..in ba hakaba in na fita daga gidan nan...sai na kulle duk zuriyanku..banza karamar bazawara..." Yarinya tsaka taja ta mikar da uwarta, aikam da sauri ameera ta karasa inda suke ta rike hinde da hannu daya sannan ta mika mata dayan hannunta
"Yanzu mikomin zinari na..." Bata karasa ba aka bude gate majed yashigo, ko kallonshi batayiba tacigaba da girgiza hinde tana cewa
"Ki bani yanzu ba sai gobe ba..." hinde sai kuka take ita kuma banzan diyarta sai kokarin kwace hinde take,
"Meke faruwa nan?" Majed ya tambayesu, cikin kuka hinde ta gaya mashi, ameera kam ko kallo bai isheta ba ,nace ko kin mance abinda ya taba yi maki
"Dalla malama ki saketa..."
"Ka biyamin zinari na mana..."
"Baki sakinta?..." Yafada yana karasowa inda suke, ameera na ganin ya karaso wajen su tayi saurin sakin hinde, Hinde najinta free ta bar gidan da gudu diyarta ta bi bayanta, ameera nuna majed tayi da dan yatsa
"Ban manta abinda ka yimin ba..kuma when the time is right zan rama..."" Tsaki ya ja zai shiga ciki ya dauki abinda akace ya dauko wayanshi yafara ringing, nan Abdul ke fada mashi tawa ta gudu, da sauri majed yaje ya dauki CCTV recorder ya kara gaba.

💙💜❤💛💚

Salem ya dawo abuja duk Ahankali shi tace, baisan ta inda zai fara Neman ta ba...baisan wane garin Yoruba zai fara zuwa ba, kaman ya hadiye zuciya ya mutu yakeji don zuciyanshi baki wulik take, yana sauka daga jet ya nufi inda ya sauke ameera, dakunan yadinga dubawa daya bayan daya kilan Allah yasa ya ganta ciki, amma nothing. Gaban wani kujera ya zauna ya hada kai da gwaiwa, gani yake in zai ganta yanzu babu abinda zai hanashi cin uwarta for playing with his heart
"Tawa..you can't run from me...Nigeria is too small for you to run.. Wallahi sonki bazai hanani maganinki ba..." Ya fadawa kanshi.

Around 2pm su Abdul suka dawo amma babu courage din da zasu shiga ciki, tsakar gidan Salem ya fito yana kale2, ajiyan zuciya kawai yake, baisan ana guduwa daga mutum don yawan arzikin shi ba. Tun safe baisha ko ruwaba, tap da bawa flowaer ruwa yaje yayi alwallah sannan ta ya fita waje don zuwa masjid, nan yaga su Abdul tsaye waje, ko kallonsu bai yiba ya wuce su, kan hanyan da zaibi ya hangi wani abu kaman waya tarwase a kasa, Ahankali ya karasa wajen, yana zuwa ya tsaya yana kallon wayan, nan take yaga kaman wayan tawa, Dan dukawa yayi ya dauki wayan yaga confirm wayan tawa ne, juyawa yayi yaga CCTV na kallon wurin, daukan sim card din yayi ya saka cikin aljihunshi ya kara gaba.

Yana dawowa yaje dakin da wasu mutane uku ke duba mai shiga da fita suke, yana shiga CCTV monitor takwas nagani, yana shiga yace
"I want to see what happened since in the morning"
❤💛💚💙💜
ZAKISAN KONI WAYE
💜❤💛💙💚
Chapter 34 · 0% Book details