← Book details Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 94

Sashe 79

Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Sultan kam tunda ya shigo ya hangi ameera zaune da wani yaji kaman yajuya
"Yarinyan da bata fi one month da rabuwa da miji ba har ta fara Tara samari.." Yafada in a jealous tune. Zama yayi ya kasa fitowa, gani yayi har su ameera sun nufoshi, ahankali ya bude motan ya fito, duk yaso sakin fuskanshi don kar su gane wani Abu kasawa yayi.
"Yaya ina wuni..." Ta gaidashi,
"Lafiya...lau..." Ya amsa mata yana kallon eyeballs dinta, da sauri ameera ta dauke kanta don yanda taji gabanta yayi mugun faduwa.
"Ina su mommy..." Zeenat ta tambayeta
"Suna ciki... Ku shiga bari in dauki excuse wurin Khalid..." Maganan ta kara batawa sultan rai yayi ya kara daure fuska Sannan ya fara tafiya ya nufi hanyan falo, hannun Khalid ya daga mashi amma yayi kaman bai ganshi ba
💜💙💚❤💛
ZAKISAN KONI WAYE
💚❤💛💜💙

®zuwairat(ummu Maryam)

7⃣4⃣

Ya shige falo yana biye da zeenat, Khalid kura mashi ido yayi yana ganin kaman dan kwallon nan ne da ya Sani Sannan ya ganin shima saurayin ameera ne cos yaga yanda yayi behaving,
"I have a rival...and a footballer..." Ya fada cikin ranshi, ameera dawowa tayi gurin shi, murmushi yayi Sannan yace
"Hmmm ...dayake ni ba ayi trusting dinaba shine ba abari in shiga cikin falo gaida su mom..." Yafada yana marairace fuska, Dariya ameera tayi
"Not at all..." Dan hararanta yayi
"Wane irin not at all... Gashi wancan ya shiga...." Yafada kaman dan yaro, Dariya ameera tayi tana tunanin wannan mutumin is an ajebota daman haka ya nuna ajikinshi,
"Wancan is family... Ba saurayina bane...."
"Hmmm we have been hearing such things since 1857...." Itadai ameera Dariya take don he's sounding very funny
"Wallahi da gaske nake...ba saurayina bane..."
"Naji...ni zan tafi...kilan in dawo da dare ko kuma tomorrow morning kafin in koma kauyanmu..." Dan hararanshi tayi da vibrant eyes dinta
"Yola ke kauye?..."
Eh mana..." Ya amsa mata yana mikewa, takawa ya farayi tana biye dashi, har waje sukaje taga ya nufi wani Lamborghini, har bakin motan ta rakashi
"Da ka shigo da motanka ciki ai..."
"Nasani ko bazaki yarda ba?..."
"Why not..."
Yauma tare suke da Abdul don har yanzu bai iya zuwa gidan shi kadai cos bai iya gane hanya,
"Daman tare kuke da wani shine baku shigo tare ba?..." Tafada tana kallon Abdul dake zaune driver seat.
"Eh abokina ne..." Ameera Dan matsawa tayi kusa da inda yake zaune ta gaidashi, daga kai yayi yana amsawa, karaf sukayi ido hudu, kallon Khalid tayi ta kara kallon Abdul, confirm wannan shine Wanda sukazo tare da pilot ranar da aka za daukanta Sannan shine yayi mata karyan Salem na jiranta su tafi, tasan yanayiwa Salem aiki, he's bodyguard to be precise,
"To meye hadinshi da Khalid..." Ta tambayi kanta cikin ranta, murmushi ta saki Sannan sukayi sallama, komawa tayi cikin taga har sun zeenat sun fito.
"Kayyyy sis har kun fito?..." Ta tambayi zeenat, kawai ta kalli sultan Sai taga ya galla mata harara,
"Eh.... Wani wurin zamu...yau yaya zumunci yakesonyi,..."
"Ko ruwa bakushaba kilan..." Inji ameera data kasa kara kallon sultan,
"Ai baki zo kika bamuba...you were busy with your boyfriend..." Sukaji sultan ya fada, duk Wanda yaji yanda yayi magana yasan he's jealous, murmushi sukayi, ameera tace
"Yaya sorry.. Muje in Baku...."
"Kidaije ki dauko min insha tunda bansha Wanda aka bamuba...." Yafada sounding serious,
"Ok.." Ta fada Sannan ta shiga ciki, kallon ta yake babu blinking, kallon shi zeenat tayi tana tunanin ko yayanta na son ameera,
"Kilan" tafada cikin ranta cos tun last week yake damunta ta kaishi yawo sai su biya gidansu su ameera ya gaida abokin Abba, zeenat dai mamaki take don yayanta in ya zo Nigeria bai fita koina har ya koma. Kallon shi tayi suka hada ido
"What?..." Ya tambayeta, murmushi tayi
"Nothing.." Ta amsa mashi. Kurawa ameera ido yayi har ta karaso da juice da cup. Zubawa tayi ta bashi, amsa yayi ya hada da yatsanta na kasan cup amma yayi kaman bashi ya rike mata yatsan ba, da sauri ta zare hannun ta batare da zeenat ta ganeba, Dan shan juice din yayi
"Is too sugary..." Ya fada yana maida mata cup din. Mota ya shiga itama zeenat ta shiga, juyowa yayi ya kalleta ya kashe mata ido daya. Basarwa tayi amma cikin ranta tana tunanin kilan dan iskane
"Daman Wanda ya zauna kasan turawa dole yayi iskanci..." Ta fadawa kanta tana shiga falo.

Tun five Tawakaltu bata farka ba sai 9pm, Ahankali ta bude idanuwanta, kallon Salem dake massaging kafanta tayi, yana ganin ta bude ido ya bar kafanta ya dawo wurin kanta,
"My angel.. Ya jikin?..." Ya tambayeta yana kissing hannun ta,
"Da sauki..." Tafada tana magana Ahankali,
"Me doc yace?..." Ta tambayeshi, murmushi yayi har lokacin yana kissing hannun ta
"Yace ki huta...kar kiyi komai...and you know what?..." Yafada yana kallon idanuwanta, Ahankali ta girgiza mashi kai Sannan yace
"Yace I should stop riding you for a while..." Idanuwa ta dan kwalo
"Really?..."
"Yes...har kinji dadi ko?..." Batace komaiba ta Dan saki murmushi,
"Ya akayi ya san abinda ke faruwa?..." Ta sake asking
"Because... You..,..are... Pregnant....." Yafada yana spelling out the word one after the other, idanuwa ta kara kwalowa ta kalli cikinta tare da tabashi
"Da gaske?..." Da sauri ya daga mata kai, murmushi ta saki
"So am becoming a mother?...." Bata idaba ya katseta dacewa
"And me a father..." Yafada yana dariya,
"Amma da wuri haka?...daman ana samu da wuri haka?.." Dariya Salem ya sakeyi cikin jindadi
"Kilan na first night dinmu ne..." Yafada in a funny way, ahankali ta Dan daga hannun ta ta dokeshi, hannun ta ya rike ya cigaba da Dariya,
"Yanzu tunda doc ya hanaka....ya kenan?..." Ta tambayeshi sounding very caring,
"Zan koma shan drugs dina,.." Da sauri ta girgiza mashi kai
"No...I don't want you to do that again... Problem fin na iya dawowa sabo... Kawai ka maido ameera..."
"Princess kin manta abinda wannan babban malami ya fada min last week bayan Mun gama waya da Aisha?..ai a gaban ki ya fadamin babu aure tsakanina daita bayan na fada mashi exactly abinda ya faru...kuma kinji yace dole Sai ta auri wani Sannan zan iya sake aurenta..." Tawakaltu shuru tayi tana kallon breathtaking face dinshi, ahankali tace
"But yace kana iya Neman wani ya aureta batare data saniba ...why not kayi trying hakan...wallahi banason problem dinka yayi worst..I know the hell I went through for the past week..."
"Kin manta abinda dayan malamin yace?... He said it is haram...yin hakan babu kyau", marairaice fuska tayi
" nidai gaskiya banason mu koma gidan jiya" Hancinta ya dan rike
"It will not continue like that... You will get use to it...every decent woman normally pass through such... So yanzu let's nurse our Fulani/Yoruba baby..." Yafada yana shafa cikinta, hannun ta ta dora kan nashi,
"Yanzu what will you eat?..." Ya tambayeta, shuru tayi for a while Sannan tace
"Wai bazasu sallameni ba ?...yanzu cikin ya bar ciwo sosai..."
"Bari inyiwa doc magana inji ya zata kaya..." Yafada yana mikewa, kiss yayiwa cikin ta Sannan ya fice daga dakin.
Chapter 79 · 0% Book details