← Book details Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 94

Sashe 11

Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Wacegari tun gari bai wayeba dad ya tafi wurin da kB ke saida exotic car a sharada. Yana nan zaune har karfe tara kafin yaranshi su bude wajen, suna budewa kB yasa yaranahi suka karbi jeep din dad sannan suka bashi wani dunkullen jaguar, da agreement din cewan dad zai kawo million 2 inzai dawo.

KB ya taimaka mashi sukayi activating navigation din motan, cikin kankanin lokaci ya nuna mashi address din Salem, babu bata lokaci dad ya hau motan ya fara tahowa, yana tafiya motan na nuna mashi inda zaibi har ya iso wani makeken gida, horn yayi, mai gadin gidan ya dan bude, rufewa yayi yashiga cikin gidan , falo ya tarda Abdul nan ya fada ga wani mutum chan waje yanason shigowa, Abdul mikewa yayi yaje side din Salem, a lokacin Salem na zaune yana waya da first love dinshi , Salem dan kauda wayan yayi
"Alh Abdul ya akayi?"
"Sir wani mutum ne yake son shigowa..da alaman wurinka yazo..." Salem yasan alh umar ne don babu Wanda yasan address dinshi
"Go and tell him...bani da lokaci yanzu..." Yana kaiwa nan ya cigaba da waya da ummanshi.
Abdul komawa yayi ya fadawa maigadi sakon shikuma mai gadi ya fadawa dad ameera
"Ai kam ba inda zani...zan jirashi har sai ya sami time din" ya fada cikin ranshi.

Salem kam bai fitaba kuma baisa aka kiramashi dad ameera ba, har lokacin sallan zuhr sannan ya fita, shida Abdul, dad ameera na ganin an bude gate ya fito daga cikin mota da sauri ya nufeshi da sauri shima Abdul ya tare oganshi, Salem na daga kai ya ganeshi bata fuska yayi kaman baitaba dariyaba, cikin girmamawa dad ameera yace
"Good after noon s...."
"Who are you?" Salem ya watsa mashi tambaya batare da ya amsa gaisuwanshiba. Dan runtsunawa dad ameera yayi kafin yace
"Sir nine umar adam ..."
"And so?"
"Sir kaikace inzo..."
"Katafi gobe ka dawo am busy..." yana kaiwa nan ya juya ya barshi nan tsaye. Jikin ba kwari dad ameera ya juya yabar wurin, Salem dan juyawa yayi yaga yanda jikinshi yayi sanyi
"Don't give up...cos yanzu na fara treating dinku" ya fada ciki ranshi.

Haka dad ameera yaje ya biya million biyu bai samu biyan bukata ba.
Wacegari ma ya koma Amman da motan shi kasancewan ya riga yasan gidan, kaman jiya ma Salem cewa yayi bashi da time ya tafi gobe ya dawo.
Atakaice saida dad ameera yayi sati daya yana zuwa sannan Salem ya bashi daman shiga falo, yafi hour uku zaune kafin Salem yafito, fuskanshi Sam babu walwala. Zama yayi ya dora kafa daya kan daya yana kadasu ahankali
"What can I do for you.. Don yan kwana kin nan ka hanani sakewa.." Ahankali dad ameera ya dan rutsuna sannan yace
"Sir..aikina..."
"Please mister man...bani da time..talk fast" yafada babu alaman wasa amuryanshi
"Sir ban yi komai ba kuma an aikomin da emails wai anyi firing dina...."
"Bakayi komaiba...kana kirana mara adalci kenan..."
"No sir ba abinda nak...." Salem ya kara katseshi dacewa
"Yes mana...you are telling me ban san aikinaba tunda bakayi komaiba na koreka...anyway nazo garin nan kuma na duba ayyukanka sam batayiba...sannan abubuwan daya kamata abawa local hospitals kyauta saida masu akeyi..." Dasauri dad ameera yace
"Sir ba haka bane...."
"Mr umar are you by any means calling me a liar?..." Da sauri dad ameera ta girgiza kai
"No sir...am sorry.."
"Sorry for your self" yafada yana daria cikin ranshi don yanda mutumin ya zama abin tausayi cikin dan kankanin lokaci
"As I was saying before you interrupted... In na gayawa Bill Gates abinda akeyi azone dinka INA tabbatar maka da komai naka zaa amshe..." Da sauri dad ameera ya runtsuna
"Sir ka rufamin asiri kaman yanda Allah ya rufa maka asiri.."
"Zan rufa maka asiri on one condition..." Da sauri dad ameera ya kara cewa
"Anything sir..." Salem balance yayi kan sofa sannan ya fara cewa
"Na san kasani bani da mata...kuma daga ganinka kana kama da mutanen arziki..so inason acikin family dinka koma yanuwanka ka nema min yarinyan da zsan aura batare da bata lokaciba...and dana so auren yarka saidai bansan ko kanada yarinyan data isa aureba" tunda yafara magana dad ameera ke murnan cikin zuciyanshi.. Imagine ace sir Salem surukinshi ne
"Sir ina da yarinyan data isa aure mana.."
"Really?.." Yafada yana tunanin
"Nasan zaayi hakan" dad ameera yacigaba dacewa
"Yes sir..na baka ita...kuma bana bukatan sisinka..." Cikin ranshi yace
"Daman bani da niyyan kashe sisina kan lalatacciyan yarka..." Dariya karfin hali Salem yayi kafin yace
"That's wonderful of you...Amman wani hanzari ba guduba...bata da Wanda take so?...kar a samu matsala"
"Babu kowai..yanzu yaushe kake bukatan akawo maka mata?" Shuru Salem yayi for a moment sannan yace
"Zan gaya maka..ka amshi number ta wajen guard dina sai ka kirani"
"OK sir" dad ameera har ya mike sai kuma juyowa
"Sir yanzu ina iya komawa bakin aikina?"
"I will let you know" ya amsa mashi atakaice. Dad ameera fita yayi ranshi fal don anashi tunanin ko da bashi da aikinyi ba zaiyi talaushiba muddin yana da Salem amatsayin surukinshi. Sai Allah Allah yake yaje gida ya bawa angel dinshi labarin.

Yana fita Salem ya kira agent dinshi, bayan sun gaisa Salem ya fara cewa
"Inason ka samomin fili a kauyen abuja.."
"Karami ko babba?"
"Girmanta yayi 100by100 sannan kasa afara ginashi right away...sannan ka tabbatar fence din yayi tsawo kaman na prison... Kuma ayi ginin ciki da pure kasa no cement.."
"Sir no cement kuma?"
"Are you deaf?...nace banda cement ko kadan..."
"OK sir...daki nawa?" Shuru Salem yayi kaman bai tunani sannan yace
"Daki biyu sai very small kitchen sannan bathroom da toilet waje daya"
"Alright sir" mutumin yafada sannan Salem ya katse wayanshi.
Dariya ya farayi yancewa
"This is going to be marvelous..."

💜💛💚💙❤
*ZAKISAN KONI WAYE
* 💙💚💛💜💛
®zuwairat(ummu maryam)

1⃣5⃣

Dad ameera sauri yake don ya isa gida, yana shiga gidan ko parking kirki baiyiba ya shiga ciki.

Direct dakin mom ya shiga, mom juyowa tayi ta kalleshi kafin tace
"Alh lafia? Ko yauma baka samu ganin shi ba?" Hulan kanshi ya cire yana cewa
"Hajiya.. Ameera ta tayi goshi..." Mom na jin ya kira sunan ameera ta dan bata fuska kaman ba ita ta haifetaba.
"Me akayi kuma?" Dad cire babban riganshi yayi yana cewa
" ameera ta tayi goshi wallahi... Saidai yan bakincik su mutu" dan tabe baki mom tayi
"Wai me yafaru?"
"Ai naga kin bata fuska daga kiran sunan ameera.. To albishirinki"
"Ni ka gayamin abinda ke faruwa" zama dad yayi kusa da mom tare da dora hannunshi kan kafadan mom sannan ya fara cewa
" sir Salem yace yanason ameera da aure kuma na bashi..." Zumbur ta mike
"Haba alh..yace yanasonta ko ka kaimashi tallanta...kuma yarinyan da ba ganin kowa da gashin arziki zaka bawa shugabanku gaba daya ta jawo mana zagi?" Ta danyi shuru ta hadiyi wani abu sannan ta cigaba dacewa
"Gaskiya alh ka sake shawara.." Shima mikewa yayi
"Daman nasan haka zakice...wallahi da ba gabana kika haifeta ba da sai ince bake kika haifetaba...to aure anyi angama...cewa yayi zai kirani..yana kirana yau zansa a daura masu aure a tafi da ita gidan Hutu...ban taba ganin inda uwa take bakin ciki da karuwan yarta ba sai a kanki...rubbish" mom baki ta tabe kafin tace
"Ni ina ruwana...daman tsutsun daya ja ruwa kanshi yake karewa....ayi lafiya" dad baice mata komai ba ya fice, direct dakin ameera ya tafi ,nan ya zaiyana mata yanda sukayi da Salem, dad bata gamaba tayi daka tsalle ta fada jikin dad dinta, shima rungumeta yayi.

Bayan dad yafita, kwantawa ameera tayi kan gado tana cewa
"Daman haka Allah yake biyawa bawanshi bukata? Daman duk abinda mutum ke in har kasa abun cikin ranka zaka samu?.. Imagine me as Salem wife , imagine me as surukin former President... Woowww" tafada da karfi tana tsalle kan gado, wayanta ta dauka tafara dailing number zeenat.

❤💜💙💚💛

Bangaren Salem kam hankalishi kwance don yanzu kwana uku da maganan shi da dad ameera, gini kam ana chan anayinta abinka da mai naira har an gama fence din kuma da aka turowa Salem hoton cewa yayi yayi kadan akara tsawon fence din, wani irin dogon fence mai kama da tower akayi sannan aka fara ginin ciki, shima har sunkai tsakiya aka turawa Salem hoton, shima cewa yayi dakunan sunyi girma a ragesu.

Yau yana kwance murmushi ne kwance a fuskanshi.. Kona meye oho, wayan shi ya dauka yasa Abdul ya kira Makeup artist dinshi.
Chapter 11 · 0% Book details