← Book details Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 94

Sashe 82

Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alhamdulillah yanzu an fara hidimomin bikin zeenat, komai da ameera akeyi, abinda yake bawa ameera mamaki yanzu shine yanda bata iya zaba tsakanin sultan da Khalid, da tana ganin tafison Khalid amma she was wrong, don yanzu tsohon son yarinta data yiwa sultan yafara lighting up, don tana jinshi har cikin jininta, yanzu in zaa tsareta da wuka ta zabe daya daga cikin su saidai a kashe ta cos bazata San Wanda zata zaba ba, bata taba tunanin zuciya daya na Iya kamuwa da son mutane biyu ba don har browsing tayi taga result din inda ake cewa is not possible wai dole Sai daya ya fi daya, itadai she loves them both, kuma tana shin saa basu kara tadda junansu ba, duk week end Khalid ke shigowa, Sai tayiwa sultan dubara kan zata gezawa cos kusan kullum yake zuwa gidansu, affan kam yana son sultan sosai don kullum inyazo Sai sunyi training, dama gashi da on football kuma ga international football har gida, abinda ke bawa ameera haushi shine wai har affan baison zuwan Khalid wai shima yana taya sultan kishi, last week da Khalid yazo ta fada mashi suna da biki kar yazo wannan week end don suna bikin zeenat, da kyar ta shawo kanshi don cewa yayi zaiyi attending, ranar kunshi, yan matan sunfi su talatin zaune, dukkan su sunsa ankon riga da skirt, black skirt da red top Sai Vail, yawancin yan Matan ameera ta taba wulakantawa mussanman lokacin aurenta da Salem,
"Ayiiiirrrrr...." Wata tayi guda Sannan tafara cewa
"Yanzu muka san ana biki...komai is well organized...." Kusan su biyar suka bushe da Dariya Sannan wata tace
"Hmmm wasu Sai wulakanci amma duk wulakancinsu saida bayerabiya ta koresu daga gidan miji..." Bata idaba ba wata ta katseta dacewa
"Gidan miji?.... Kin manta mutumin in questions cewa yayi bai taba aureba Sai lokacin auren shi da wannan bayerabiyar...." Ameera dake zaune kusa da zeenat ta mike, da sauri zeenat ta rike mata hannu ta maidata zaune Sannan ta kalli yanmatan tafara cewa
"Dan Allah banason haka...duk wacce tasan ba dan kunshi ta zoba kawai ta tafi...after all ko wacce nada matsalan ta amma Sai Ku ajiye gefe Ku hau na mutum...pls let's take care of our problem first before looking at others people's lives..." Zeenat ta fada hannun ta rike da hannun ameera da take kokarin kwacewa don barin wurin,
"Anya wannan itace wancan?...cos wancan is rude and arrogant...." Inji wata, ameera kallon zeenat tayi da idanuwanta da suka chanza kala
"Babe ki sakar min hannu in koma gida..." Tafada cikin whisper kaman zatayi kuka, itama cikin whisper zeenat tace
"Haba babe...saboda those nonentities zaki tafi?..."
"I need to go home now...I can't stay... Pls kiyi hakuri.."_tafada hawaye na faruwa idonta,
" OK...bari in kira yaya ya maidaki gida..." Zeenat ta fada tana dauko wayanta, text ta rubutawa sultan kaman haka
" _Yaya pls ka zo ka dauki ameera ga friends suna ta zolayanta kan abinda ya faru tsakanin ta da sir Salem"_ ta tura mashi, bayan kaman minti talatin sultan yazo cikin ranshi yana aduan Allah ya hada shi da Salem
"He will pay for making my ameera a laughing stock..," yafada yana shiga inda yanmatan suke, suna ganin shi ko wacce ta bude baki kaman sakara don dukda yana baki babu abinda farin mutum zai nuna bashi, fuskan
Babu faraa Ya nufosu, wasu da basu sanshi ba sai cewa suke
"Wannan kaman popular Dan kwalo sultan..."
"Eh mana....bakusan yayan zeenat bane shi?..$ wata ta amsa masu duk suna magana cikin whisper, zeenat na ganin shi ta Dan taba ameera data sadda kai kasa hawaye na zuba amma babu Wanda yasan kuka takeyi
" babe ga yaya...." Zeenat ta fada mata, da sauri ta goge hawayenta tare da mikewa, Vail dinta Sannan ta dauki bag dinta ta nufo sultan batare data daga kantaba cos batason ya gane tana kuka, shikuma yana ganinta ya San kuka take, ta taho shima ya taho Sannan ya fara cewa
"My jewel waya taba min ke!.." Yafada yanda duk wacceke wurin zaiji abinda yake cewa, yacigaba dacewa
"Sai ki zubda hawayenki saboda wata idiot..." Dukkan su kallon shi sukayi yafara nuna su da yatsa yana cewa
"Wallahi duk wacce ta kara sanadin hawayen my jewel Sai nayi maganinta... Ko yar wacece...." Yana kaiwa nan yakama hannun ameera data cigaba da hawaye suka bar wajen.
Suna fita waje ya bude mata kofan motan ta shiga, zagayowa yayi ya shiga, tsayawa yayi yana kallon ta, har lokacin hawayenta bai tsaya ba, daga kanta tayi ta kalleshi,
"Da baka fada masu komai ba..." Tafada cikin natsuwa, hannun shi yasa ya goge mata hawaye Sannan yace
" I have to warn them,..and shi kuma Salem I will deal with him..zan nuna mashi gaba da gabanta... Am just waiting for the right time... " kai ameera ta girgiza mashi
"No... Salem help my life... He changed me...taimaka min yayi..."
"I don't bloody care...what he did was barbaric...he have to learn his lessons...kawai just wait and see..." Kuka ta farayi tana cewa
"Wallahi babu ruwanka da sir Salem... He..." Katseta yayi dacewa
"Do you love him?... Why are you covering for him... Duk Wanda zaiji abinda yayi maki knows it is wrong..." Kuka ta farayi sosai tana cewa
"Bance ina sonshi na...kawai don't go near sir Salem or this relationship is over..." Tafada tana kokarin fita daga cikin motan, da sauri ya rike mata hannu
"Sorry for the accusations... Da nayi niyyan yi mashi rashin mutunci.. Amma na bari...since it is what you want..." Yafada cikin natsuwa, har lokacin yana rike da hannun ta, komawa tayi tare dayin relax tana goge hawayenta.

Daga wannan ranar duk yanmatan basu kara gigin yi mata habaiciba, duk events da ita akeyi amma ba daita ake tashi ba don sultan daukan ta yakeyi su yita yawo cikin gari kafin ya maidata gida.

Yau akayi walima gidan amarya, ameera tayi mamakin gidan don sultan bai barta kai amarya ba, Mahmoud din data raina ashe shima yana da hali daidai kwarkwado don gidan ba karamin tsaruwa yayi ba, cikin bedroom ameera ta shiga lokacin tana shirin komawa gida kallon zeenat datayi tsuru2 tayi ta fashe da Dariya,
"Amarya ni zan tafi...yaya sultan yana jirana waje...." Ameera tafada mata, rike hannun ta zeenat tayi tana cewa
"Yanzu babe bakisan yanda first night yakeba?..." Ameera shuru tayi tana kallon zeenat, Sai Tawakaltu ta fado mata a rai,
"Hmmm...sis ya zaayi in Sani tunda ban taba ba...kawai get ready for the worst..." Idanuwa zeenat ta kwalo
"The worst fa kika ce..."
"Eh mana...baki ganin yanda Mahmud yake zumudi?..." Tafada tana dariya,
"Bakomai ai... Nasan duk wahala zuwa gobe nawuce wurin... Amma ke keda sauran wahala... Remember my bros is an athlete...." Baki Ameera ta tabe
"Ba Sai na zabeshiba..." Harara zeenat ta galla mata tana cewa
"Naga ta yanda zaki CI amanan yayana..." Ameera kwace hannun ta tayi tana cewa
"Babe Sai munyi waya..I will call you first thing in the morning..." Tafada tana fita daga dakin.

After three day which is Friday Ameera tana kwance tana tunanin zuwan Khalid gobe don basu dade da wayaba, juya kwanciyan ta tayi tare da kara daukan wayanta, YouTube ta shiga tana duba, latest wedding ta fara dubawa Sai taga the wedding of the year nasu Salem da tawa, murmushi tayi ta bude tana cewa
"Let me see your handsome face...." Relaxing tayi ta fara kallo, few minutes later taga kaman Khalid tsaye yana bada jawabi, da sauri ta maidashi baya tana cewa
"It can't be..." Kara kallo tayi taga confirm shine, ido ta kwalo
"Oh my Allah!....." Tafada tana mikewa da sauri.
Tun kafin ta shiga dakin mom ta fara kuka tana kwalawa mommy kira
"Mommy!...mommy!..." Ta dinga kwalawa mom kira,da sauri mom ta fito ta tare ta, fadawa tayi jikin mom
"Meye!.." Mom ta tambayeta cikin tension, Ameera bata samu bakin cewa komai ba sai kuka take, girgizata mom tayi da karfi
"Wai meye Dan ubanki kike neman tadamin hankali?.." Mom ta sake tambayeta, tana kuka ta mikawa mom wayan
"Mom ki kalla ki gani...Khalid friend din sir Salem ne..." Tafada cikin kuka, kin amsan wayan mom tayi
"Saboda wannan kike neman sa hawan jinina ya tashi?... AI shikenan ba sai kin aureshiba don bazaayi sakin wawa dakeba...." Ameera shuru tayi bata ce komai ba sai kuka
"Shima munafiki ne...AI Sai ya fada maki gaskiya amma ya boye maki..da niyyan shi sai kunyi aure ki gane gaskiya ko?... To alhamdulillah Sai ki godewa Allah da bai bar hakan ya faruba..." Ameera kuka ta cigaba dayi
"Dalla rufemin baki..." Da sauri taja bakinta ta tsuke
"Yanzu mom me zan fada mashi?... Inason..." Buge mata baki mom tayi
"Na anyi magana Sai kice kinason sonshi...Khalid... Kinason shi....sultan kinason... Bari ubanki ya dawo..." Tafada tana komawa dakinta, Ameera zama tayi nan kasan tiles tacigaba da kuka
"Ashe daman Salem yasan Khalid?..."
💛❤💜💚💙
ZAKISAN KONI WAYE
❤💛💜💚💙

®zuwairat(ummu Maryam)

7⃣7⃣

Tafada tana kuka,
"God have mercy on me..." Mikewa tayi ta koma dakinta ta cigaba da kuka atakaice aranan bata yi baccin kirki ba da tunanin yanda gobe zata kasance ta kwana don tasa ya zama dole ta rabu da Khalid, bazata iya auren best friend din Salem ba, she wants Salem ta be her past and not the best friend of her hubby, kashe wayan ta tayi gaba daya don batajin zata iya magana da mutum daya cikin su.
Chapter 82 · 0% Book details