← Book details Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 94

Sashe 42

Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su Abba suna dawowa daga masjid suka koma palace, obj na zaune yayi relaxing kaman gidanshi sai shan wine yake, su Abba zama sukayi oba ya fara dacewa
"To alhamdulillah Mun gama stage one...meye na biyun?...kuma ina fatan ba abinda ya fikarfina bane..." Dariya sukayi OBJ ya mike zaune yana ajiye glass cup dake hannun shi,
"Gaskiya na biyu ba abu bane mai wahala kaman na farko...amma awajen mu yafi na farkon important..."
"OK..." Oba yafada yana gyada mashi kai, Ahankali OBJ ya fara cewa
"Danmu Salem ne yaga wani flower acikin jikokinka...kuma by the grace of God zamuso mu tsinke wannan flower daga gidanka..." Oba daria jin dadi yayi
"You Salem dan Yusuf?" Ya tambaya
"Yes..." Wani sabon dariyan yayi da ka ganshi kasan ya ji dadin abinda yaji
"Alhamdulillah... Wannan abune mai kyau...hakan zai kara zumunci tsakanin mu...sannan yan bayan mu zasu gane cewa indai mutum yaga wacce yakeso koina take yana Iya aurenta, ba sai anyi tribalism ko nuna banbanshiba...alhamdulillah.. Am very excited.. But wacece?" Dariya sukayi OBJ yace
"No...kasan aladanmu...zamu zo da Salem sai ya nuna maka ko wacece"
"Hakane....so yaushe kuke ganin is convenient?" Da sauri Abba yace
"No your royal highness.. Duk sanda kake so we are free..."
"To alhamdulillah... Kaman yanda kuka sani da akwai wani bukin alada da zamu yiwa ameenatu da yarta..Wanda zai nunawa mutanen mu they are royalty.. Insha Allah zamuyi wannan shagalin coming Saturday...upper Saturday sai kuzo da shi Salem din ya nuna mana ko wacece" dukkan su kara zubewa kasa sukayi suna godiya. Sai bayan sallan ishai suka koma guest House din oba, saida suka isa masukinsu sannan Abba ya dauki wayanshi sai lokacin yaga jerin miss call din Salem daria yayi yana cewa
"Salem rigima" yana daukan wayan yafara ringing, picking yayi, ajiyan zuciya Salem yayi
"Finally.." Daria Abba yayi
"Son ya akayine?" Shima Salem Dan daria yayi yana shafa kanshi batare da yace komai ba, hankali kwance Abba yafadawa Salem yanda sukayi da oba, Salem ji yayi kaman anyi mashi albishir da gidan aljannah, kashe wayan yayi yana cewa
"I told you I will get you...tawa here I come" yafada yana shuumin dariya.

💙💚💛💜❤
ZAKISAN KONI WAYE
💛💙💜💚❤

®zuwairat(ummu maryam)

4⃣4⃣

Salem rawa ya dingayi da pillow dake hannun shi yana cewa
"I feel good.... Tarararara...I feel good...tarararara..feel good.. Pampam...feel good..." Waka kawai ya dingayi yana juya pillow kaman mutum, da sauri ya wurgar da pillow ya shiga bathroom yayi alwallah Sannan ya dawo yafara sallan nafila. Yana gamawa ya dauki wayanshi ya fara dailing number da tawa take kiranshi daita, ringing yafarayi, ya kusa tsinkewa sannan akayi picking,
"Good evening s.." Bata idaba yayi saurin cewa
"Habibty guest what?" Cikin sanyin murya tace
"Meye?..." Da sauri yace
"My wish is coming true..." Shuru tayi bata ce komai ba yacigaba dacewa
"Habibty am getting married..." Aikam na take gaban tawa yayi mugun faduwa, Dan dafe kirjinta tayi, sai nishi take akai2, Salem yasan batasan abinda ke faruwa ba so yasan she will be out of words
"Habibty kinyi shuru..please say something... Nasan baki damu daniba..." Tawa kuka ta farayi ahankali batare da sautiba, sai hawaye ke zuba ahankali,
"Honey please say something.." Kaman an fixgi kukan daga bakinta tafara kuka sosai, Salem rike baki yayi yana daria Mara fita, saida yayi mai isanshi sannan yace
"Haba godiam..meya faru?" Ahankali tace
"Zan fada maka inda nake..." Salem kara rike baki yayi yana daria
"Gaskiya Aa..na hakura...mubi maganan iyayenmu.." Cikin kuka sosai tace
"No...zan fada maka inda nake...wallahi ina ilo...." Bata idaba Salem ya katseta dacewa
"No...banaso...kawai ki bar wannan zancen..let's just be friends... And you can call me sir..just like you wanted to" tawa kuka tacigaba dayi
"Stop crying... It's not the end of the world..." Tawa bata saurareshiba tacigaba da kuka
"Tunda bazaki bar kuka ba..zai anjuma.." Da sauri ta goge hawayenta
"Na bari...am sorry.."
"For what?"
"For running away.."
"Wallahi ba komai...."
"Yanzu in fada maka inda nake?"
"Aa...muyi wani hiran...so tell me ya mami take..." Ahankali tace
"She's not around.. Tafita da yayarta"
"Wannan Daren?...ko inda kuke ranane?" Dan daria tayi
"Rana kuma?.."
"Eh..mana..It can ba possible"
"Hmmm..sai anjuma..." Da sauri Salem yace
"Haba friend har kin gaji da hira dani?" Ahankali tace
"No...amma sai anjuma..."
"Why please..."
"Don kar sabuwar matanka tayi fada..." Dariya Salem yayi
"Karki damu..zan aureki tabiyu...." Bai idaba ta katseshi dacewa
"Allah ya sauwake..."
"Why..."
"I can't share my husband with another woman.." Dariya Salem yayi
"Habibty is jealous... Har yanzu ban bar fushiba...cos you run away from me when I needed you the most..."
"Am sorry Ife..."
"Don't call me Ife...call me sir" batace komaiba Yacigaba dacewa
"No amount of sorry zaisa in yafe maki...har yau ban dawo normal ba saboda abinda kika yimin...amma kin nuna min cewa ba komai kudi zai Iya sayaba...so thanks for that.."
"Am sorry.." Ta sake fada cikin kuka
"Ki bar cemin sorry.. I don't like self pity..." Yanda yake maganan kasan cikin bacin rai yake,
"Nidai sai anjuma..."
"Kinga wata matsalanki...ni na kiraki..amma you are telling me sai anjuma...CE maki akayi na gaji da kiranki?...yanzu tell me ..what will you give as my wedding gift?" Ya tambayeta yana biting lower lip dinshi, tawa shuru tayi bata ce komaiba sai kuka take ahankali
"Habibty tell me mana..."
"What do you want?" Ta tambayeshi ahankali, gyara kwanciyan shi yayi sannan yace
"Will you do anything I want?" Cikin kuka tace
"Eh..." Dan murmushi yayi
"Will you let me make lo...."
"Please stop.."
"But you say you will do what ever I want..."
"Banda irin wannan maganan..."
"OK..naji...remember its my wedding..."
"Sai Anjuma... Zanyi bacci" Salem lumshe idanuwa yayi yana tunanin ta kwance next to him,
"To shikenan.. Let me call my wify...sai da safe"
"Na fasa baccin.." Tafada da sauri, dariya Salem yayi sosai.
"Jealousy....keda na dinga binki ina rokonki ki fadamin inda kike kinata jamin aji...to gashi yanzu ajin ya tsinke na samu wata...".
" wallahi ka bar cemin ajina ya tsinke... ".
" karya nayi?...wai kaman ni ki tsaya kina jamin aji... Nida mata suke kashe Kansu saboda..anyway kiyi murna da bake zan auraba..don na rantse inke na aura saina dauki mataki kanki for playing with my heart... "
"I said am sorry..."
"Is not enough..." Shuru sukayi Salem najin wani irin dadi cikin ranshi.
"Nidai ka yafemin...I will not run away again..." Dan murmushi yayi
"Kima gudu I will be right behind you.." Yafada cikin ranshi
"Wai habibty wannan number mami ce?"
"Eh..."
"Hmmm...ki turo account in sa maki kudi ki sayi waya...for the sake of friendship..."
"Banso...."
"To shikenan... Ai bazan kara rokonki kan komaiba cos you are stubborn..." Shuru tayi batace komai ba yacigaba dacewa
"Kuma zanyi Maganin stubbornness dinki...when the time is right..." Yafada kasan makoshinshi, su biyu shuru sukayi suna sauraron breathing din junan su, ahankali Salem yace
"Habibty kinsan kasan da zanyi honeymoon dina?..." Cikin whisper tace
"No"
"Instabul...INA gida on the mountain view...daga nan zai in wuce Hollywood chan ma ina da gida kuma in kina wurin duk american actors and actress zaki gansu...sai kumaBeverly hills California ..in short zan 12 countries for my honeymoon...." Tawa shuru tayi tana tunanin yanzu inda ummanshi da mami sun amince da daita zaayi wannan yawon ganin duniyan, wasu hawayene ya kara zubo mata, ahankali Salem yace
"Habibty kinyi shuru... Ko jealous din ne...and habibty kinsan in matata ta haihu indai inagida ni zan dinga chanza diapers.. I want to be the perfect hubby..." Ita dai tawa shuru tayi batace kala ba, karaf taji su mami sun dawo sai Neman ta ake a falo, da sauri tace
"Sir I have to go...su mami sun dawo..."
"OK...good night... Love you" bata amsa mashi ba ta katse wayan tana goge hawayenta.

Tana fita falo taga mami na kuka yayanta sai rarrashin ta take, nan take hankali ta ya tashi, da sauri ta karasa inda mami take ta durkusa gabanta
"Mami...menene?.. Why are you crying?" Mami bata amsa ba tacigaba da kuka, mami kallon yayanta tayi tana cewa
"Nasan kilan ya samu labarin ni da yata suna garin nan...yanzu anty in ya koremu ina zani da yarinyan nan... Ban Iya komawa Kano...." Tafada cikin kuka sosai, itadai tawa har lokacin batasan abinda mami ke cewaba,
"Haba.. Kinsan koma meye he's your father... Kawai kiyi hakuri gobe muje muji kiran dayake yi maki...kuma ai ba ke kadai ya kiraba... Dukkan mu ya kira...."
"anty stop saying that.. Kinsan wannan yaron don ni da yata zaayi shi...I think the best option shine in koma garin mijina..."
"No!" Yayanta ta daga mata tsawa, sannan ta sausauta murya tafara cewa
"Ai kina zuwa wajena tun ba yauba...kuma baitaba kirankiba sai ka yanzu...for the past 19 years oba bai nuna yanason ganimki ba sai yanzu..in kika ki zuwa kin kara disrespecting dinshi so kawai gobe muje..." Sai lokacin tawa tagane kakanta ne yakeson ganin mami, ba mamiba har ita gabanta faduwa take, don bata taba ganin shi, hannun ta tasa ta gogewa mami hawayenta tana cewa
"Stop crying"

❤💙💛💜💚

Ameera sabon holewa ake don tun rananda Salem ya bargida tasa guard dinshi yayi mata shopping din kayan dadi take shagalin ta, baa kara hura wuta gidanba don dama tun gida Abinci bai dametaba barta kawai da kayan lashe2, Yanzu kullum tana waya da gida kuma ko kadan batayi gigin fada masu abinda ke faruwa ba, kullum mom na fada mata ta turo mata pictures din gidanta sai tace zata turo, ko yanzu waya suke da mom tana cewa
" mom har yanzu baki turo min number zeenat ba..."
"Oh sorry habibty... Bari in kira Hajiyan ta ta fada mata ta kiraki yanzu nan..."
"Yau wa mom nagode.." Dadi mom taji don halin ameera nada Dana yanzu ba daya bane cos yanzu tana kwantar da hankali suyi hira
"Habibty ki gaida mijinki....kuma insha Allah anty Sadiya tana nan tafe..." Dan baki ameera ta tabe don wani haushin anty takeji
"To mom..." Sallama sukayi sannan ta ajiye wayan ta dauki sauran snickers data ci ta rage ta cigaba daci tana korawa da juice.
Chapter 42 · 0% Book details