← Book details Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 94

Sashe 21

Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka suka sha hiransu har lokacin sallan asar sannan sukaje tare suka dawo, suna dawowa sukaci abinci, side din ummanshi ya wuce cos ba tare sukaci abinci ba, falon ta ya taddata zaune wata yarinya na massaging kafanta, tana Ganin Salem ta sallami yarinyan,
"My handsome son"
"Yes Umma"
"The richest guy in Africa"
"Yes Umma"
"The most eligible bachelor in Africa"
"Yes Umma"
"Umma's only son..."
"Umma kirarin ya isa hakanan" ya fadawa ummanshi don inda sabo yasaba da kirarin Umma. Zama yayi kusa daita suka fara labarin duniya, hira suke Amman yarasa ta inda zai fada mata abinda ke zuciyanshi. Ahankali ya daga kai ya kalleta
"Umma albishirinki?"
"Goro"
"Umma na samu Matan aure" da sauri Umma ta tallabo fuskanshi
"Son are serious.. Ko you are just pulling my legs"
"No Umma.. Am serious"
"Yar gidan wacece?" Ahankali Salem yace
"Yar talakawace.." Shuru Umma tadanyi sannan tace
"No problem.. There is enough money to go round" Salem murmushi yayi sannan yace
"One more thing"
"Meye kuma?" Salem shuru yayi for a moment tare da gyara zamanshi sannan yace
"She's not Fulani or Hausa.." Surprise look Umma ta watsa mashi
"Then wace yarece?"
"Yorubace..."
"What!!!!"

💜💚💙💛❤
Yau Friday akayi yinin biki gidansu ameera, dukda baa gayyaci mutane da yawaba bai hana gidan shika da mutane ba, don inkazo gidan babu masakan tsinke, aranan aka maido ameera gidansu, tasha ado cikin wani tsadadded code lace, fuskanta yasha heavy makeup, ko rashin waya da Wanda zata aura bai dametaba, kawayenta duk suna kusa daita sai iskancin su suke, ameera kam bata ki a dauketa yanzu akaiwa Salem ba, cikin zuciyanta sai Allah yaisa takewa anty Sadiya saboda banda sexual desire babu abinda ke damunta, ganitake gobe in Salem bai nemetaba zata fidda kunya ta nemeshi
💛❤💜💙💚
ZAKISAN KONI WAYE
💜💛💙❤💚

®zuwairat(ummu Maryam)
2⃣4⃣

Tawa sai trying number Salem take, yana ringing Amman baya dauka, duk ta tada hankalin ta, tana wajen aiki Amman hankalinta baya wajen don gani take kaman wani abu ya samu Salem
"Wai wani abu ke damunki naga sai tsoki kike" Zara ta tambayi tawa
"Tunda safe nake trying number sir Salem yana ringing Amman bai dauka,..Allah yasa lafiya" tawa tafada kaman zatayi kuka, daria Zara tayi
"Har kin shirya da wanfa ya taba maki precious boobs dinki?.."
"Ohhh...Zara stop it ina maganan abin sona kina maganan boobs" daria Zara ta karayi wanda yasa tawa kara kuluwa, tsoki taja ta bar wajen, komawa tayi waje ta zauna tare dayin tagumi.

💚❤💜💛💙

"What's today's date?" Umma ta tambayi Salem
"18 November" Salem ya amsa mata gabanshi na faduwa,
"Today is not first April.. So what sought of joke is that?" Umma ta tambayeshi muryan ta babu alaman wasa, ahankali Salem yace
"Umma.. Am not joking.. Am in love with a Yoruba..."
"Shut up!!!" Umma ta daka mashi tsawa, mikewa tayi tayi tsaye kanshi
"Daman haka kake ban saniba?..you look matured..but you are stupid.. Ina Fulani ina wata yare waishi Yoruba?.. To tunda bakason samu matan aure zan samo maka..this discussion is over.." Tana kaiwa nan tafara tafiya, tunda tafara magana Salem ya had kanshi da kwaiwa, yanajin Umma tabar wajen ya mike da sauri ya bi bayan ta
"Umma am sorry I disappointed you...but she's the one my heart choose.. I love her..in ban same taba zan rasa raina" afusace Umma tajuyo
"Then get ready to die..don bazan iyazama wata yare ta haifamani jikokiba..ta koyawa jikokina aladan da ba namuba..sam hakan bazai taba yuwaba..if you are dreaming wake up" juyawa tayi ta fara shiga bedroom Salem yakara binta da sauri
"Umma yarinyan bata ma iya yarensuba balle Ashe zata koyawa jikokinki...please Umma support me this once...I love her..please" Umma bata saurareshiba ta shige bedroom dinta, har lokacin Salem bai bar binta ba, abakin gado ta zauna ta dora kafa daya kan daya, gabanta Salem yayi kneeling
"Umma ban taba so ya mace ba sai yarinyan.. Umma in har kina sona ki so Tawakaltu.. Please" har lokacin Umma bata ce komaiba sai karkada kafa take, Amman fuskanta babu alaman amincewa
"Please first love help me..ina bin umarnin ki...ban taba yi maki gardama ba..nima dan Allah kiyi min wannan.."
"Kai kar ka yimin maganan banza!!" Ta daka mashi tsawa
"Yazaayi dana ya auri Yoruba?..me kakeso in gayawa family?...me kakeso mutane suce.. So kake adinga ganin mu kaman bamu isa da yaranmu ba?...to indai nice saidai ka mutu ba mata Amman bazaka kawo min Yoruba amatsayin surukaba...this discussion is over" Salem sunkuyar da kanshi kasa yayi, bai ankaraba yaji hawaye na zubowa daga idanuwanshi, ahankali ya mike sannan yafara cewa
"Umma I thought you love me..but am wrong don nasan inda kinason ko mahaukaciya nace inaso kema zaki sota..." Dan goge hawayen fuskanshi yayi sannan yacigaba dacewa
"Umma ban taba ketara umarnin kiba...banson karanta doctor kika yi forcing dina..I never complaint.. Banson karatu a Europe..har na samu admission a Oxford Amman kika ce dole sai peacock still I don't complain... Umma banason rayuwa a Nigeria Amman kika yi forcing dina na zauna...you choose friends for me...You choose everything for me...but am not going to let you choose my life partner...no problem tunda kinfi son family fiye dani...Amman let me make one thing crystal clear... Nobody will stop me from marrying Tawakaltu.. I love her and she's my choice.." Yana kaiwa nan ya fice daga cikin dakin
"Salem come back here now" Umma ta fada a tsawace , Amman bai juyawa ba yacigaba da tafiya, hannu yasa cikin aljihunshi yafara Neman wayoyinshi Amman bai gansuba, tsakar gidan ya tsaya ya kwallawa pilot dinshi kira sai ga guy din ya fito daga cikin wani party da gudu
"Get your things.. We are leaving.. Kuma check if my phones are in the jet" Da sauri guy din ya koma ciki ya shirya cikin sauri, shima Salem part din abbanshi ya koma ya gayamashi yanda sukayi da Umma sannan ya kara dacewa
"So Abba zan wuce abuja..I will call you"
"Amman I wish you can stay more" Abba ya fada mashi, ban kwana sukayi sannan ya fito, direct cikin jet ya wuce ya zauna sai yaga Ashe nan ya bar wayoyinshi, family phone ya dauka sai yaga 46 miss calls. Budewa yayi yaga duka tawace ta kirashi, lumshe idanuwa yayi wasu sabbin hawaye na taruwa idanuwanshi, pilot din tada jet din yayi.
Umma najin antada jet ta fito da sauri, kafin ta fito waje har sun tashi sama, ranta kara baci yayi
"Wace yarinya CE dana yakeson fifita ta kaina?..Salem always obeys me...dole in san yarinyan" tafada sannan ta koma ciki rai bace, Abba yana kallon ta ta window, Abba irin mutanen nan ne masu sanyi don Umma kadai ke making 80% of the family decisions, don ko kannen Salem biyu ita ta zaba masu miji.

"Sir where are we going?" Pilot ya tambayeshi
"Abuja" ya amsa mashi har lokacin muryan shi bai dawo daidai, waya ya daga zai kira tawa Amman yasan daya kirata zatasan da abinda ke damunshi, dole ya ajiye wayan, baiyi 15 second da ajiyewa ba tafara ringing, dubawa yayi yaga itace, dan murmushi yayi sannan yayi gyaran murya yayi picking
" my choice how far?", wani irin ajiyan zuciya yaji tayi
"Ya akayine?" Ya sake tambayan ta, ahankali tace
"Wallahi oremi hankalina ya tashi, tundazu inata kiranka ba amsa..so..."
"Sai kikayi tunanin na mutu..? Dariya tayi, yacigaba dacewa
" in wani abu ya sameni ya kenan" ahankali tace
"Sai in kashe kaina...I can imagine life with you.." Salem lumshe idanuwa yayi
"I love you.. And no obstacles will stand in the way of our love.." Yafada muryan shi na rawa
"Oremi what's the problem?" Dan daria karfi hali yayi
"Haba habibty ban fi karfin oremi wajen kiba?...Gaskiya ki chanzamin suna" yafada don ta bar maganan
"Ifemi...what's the problem..your voice is down" darian karfi hali ya karayi
"What's the meaning of ifemi" shuru tayi for a moment sannan tace
"Abin sirrine"
"Please tell me"
"I said sirri ne..har yanzu baka fada min abinda ke damunka ba" ahankali yace
"Missing dinki nake..my choice in har ban samekiba. Zan hadiye zuciya in mutu.."
"Hmmm"
"Is that all you could say...hmmm?" Daria tayi
"To me kakeso ince...anyway yasu first love da sauran yan gidan?"
"Suna lafiya..habibty anya zan Iya kaiwa Monday ban ganiba..yau Friday and am missing you die.."
"Nima jinake kaman nayi wata ban gankaba"
"Zan dawo gobe..."
"Aa...kar ka dawo..wahalan zama mota zaiyi maka yawa..sannan su first love zasu iya fushi da kai..."
"Alright.. Zan kiraki later"
"OK...bye" kiss yayi blowing cikin wayan sannan ya katse wayan.
Relaxing yayi yana tunanin abin duniya.

Suna zuwa abuja yayi sallan magrub, sannan ya koma gida, sai yaga Sam gidan baya yi mashi dadi,gidan sai yayi mashi mugun girma,
"Allah kabani tawa ta shikamin gidan nan da joy and happiness.."
Guys dinshi murna wurin su baa magana. Amman Salem baibi ta Kansu ba. Direct bedroom dinshi yawuce ya kwanta yana tunanin maganan Umma.

Yauma kusan kwana sukayi suna waya da tawa, duk yanda yaso tawa ta fada mashi maanan ifemi ki tayi, wani manager dinshi ya kira ya tambayeshi meye ifemi sai mutumin ya gayamashi my love kasancewan mitumin Yoruba ne.

Wacegari Saturday yaso yayi surprising tawa ya koma Kano don kwata2 abuja batayi mashi dadi Amman sai ya tunani yau zaa kawo ameera, tunda wuri agent dinshi ya rakashi ya gano gidan, yafi minti 30 yana daria don exactly yanda yakeson gidan haka yake, don ko cement baa shafa cikin gidan ba, kuma dubawa yayi yaga anzuba dukan abubuwan daya ce azuba, wani gefen gidan ya kalla yaga itace lode da murhu, wani sabon daria ya karayi, kallon agent din yayi
"Kasamo min guys guda biyu suyi guarding gate din nan.. And make sure you get them before 4pm"
"Yes sir"

💙💛❤💜💚
💜💚💙💛❤
ZAKISAN KONI WAYE
💜💙💚💛❤
®zuwairat(ummu maryam )

2⃣5⃣

Yau Friday da misalin karfe biyu aka daura auren ameera da Salem kan sadakin 100k Wanda dad dinta ne ya bada, duk wurin babu wani dangin ango ko daya amma still wurin ya shika sosai, Amman yan gulma sai magana suke wai aure ba dangin ango ko daya acikinsu har yanuwan dad wanda basu shiri, shikam dad cewa yake
"Yan bakin ciki saidai Ku mutu"
Chapter 21 · 0% Book details