← Book details Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 94

Sashe 47

Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Dukkan mutane wurin mamaki ne kwance kan fuskansu, banda oba donshi yasan hakan zai faru, Salem kura mata ido yayi da idanuwanshi da suka chanza kala, kaman ya hadiye rai ya mutu kawai yake, kallon tawa data sunkuyar da kai hawaye juna zuba yayi, duk Ilahirin jikin shi shaking yake, amma kam rasa yawu yayi cikin bakinshi, oba baki ya bude yayi niyyan sallaman tawa OBJ yayi saurin cewa
"Daughter.. Ki daga kanki ki kalleshi da kyau...baki sanshi ba?.." Tawa bata samu courage din kara kallon Salem ba, kawai hawaye ne ke zuba fuskanta kaman tap,
"You can go...$" oba ya fada mata, ahankali ta mike kanta kasa ta fita daga wurin, tana fita ta fashe da kuka sosai tana gudu ta nufi part dinsu.

Salem ji yayi iska na Neman yi mashi kadan
"She deny me..." Ya fada ahankali, kaman an tureshi ya fita daga wurin ko takalmi babu kafanshi ya fita da sauri, yana fita ya hangi bayanta ta shiga part dinsu, mami tana ragube upstairs dake opposite inda part dinsu yake, tana kallon abinda ke faruwa, da gudu Salem ya bi bayanta, tana shiga ta zube kasa tana kuka, Salem shiga yayi har falonsu, wani fixga yayi mata ya daga ta tsaye ya wanka mata wani mahaukacin mari
"Ni ke baki saniba!?" Yafada kaman numfashin shi zai dauke, tawa rike hannun wanshi tayi tana kuka, fixge hannun shi yayi ya kara zuba mata wani mari, cikin ihu yace
"What have I done to you?...why me..." Rike mashi hannu ta karayi ya kara fixgewa,
"I said uban me nayi maki?...why are you killing me slowly..." Yafada hawaye na zuba daga idanuwanshi, tawa kara kokarin rike mashi hannu tayi ya fixge ya rike shoulders dinta da hannuwanshi biyu ya fara girgiza ta sosai yana cewa
"Tell me what I have done to you to deserve this humiliation...Tell me abinda nayi maki kika yi insulting dina kikayi insulting parents dina...tell me why you want me dead..." Duk furucin dayayi sai ya girgiza ta kaman zai karyata, yana kuka tana kuka, da karfi ya kara rike shoulders dinta, tawa ta rike mashi hannuwa,
"Tell me...ki fadamin or zan kashe ki in kashe kaina...then we can continue in hell..." Da karfi ya kara girgiza ta
"I said tell me why you deny me..in front of my parents..." Yafada cikin murya kaman na mayunwancin zaki, tawa data fara fita hayyacinta saboda irin girgiza da yakeyi mata ta fara cewa
"Umma.. I promise... Umma.. To..leave you... Alone..." Tafada kaman numfashin ta zai dauke
"Fuck you..fuck your promise.... Umma has given her...blessings..." Yafada cikin kuka kuma he don't care if the whole world is watching, a hankali tawa ta girgiza mashi kai
"She...made...it..clear.. She..don't want...you...to marry...another... Language..." Da karfi ya kara girgiza ta
"I said Umma have given her blessings!" Ya fada cikin tsawa, turata yayi gefe ta fadi kan kujera, shima ji yayi kafanshi bata daukan shi, ahankali ya zame ya zauna kasan carpet yana kuka, tawa mikewa zaune tayi, ta dawo kasa kusa dashi, kafa yasa ya tureta daga wurin shi ya cigaba da kuka kaman anyi mashi albishir da jahannama.

Acikin palace kam dukkan su cikin tension suke, kanin Abba yaso ya bi bayan Salem amma OBJ ya dakatar dashi, Abba kam tunani yake kilan wannan yana Iya zama sanadiyan mutuwan Salem don yasan irin son da Salem ke yiwa Tawakaltu. Dukkan su babu mai bakin magana, Obj ne yayi gyaran murya sannan ya fara cewa
"Nasan there is something behind what happened... Naga sonshi a idanuwanta..." Shuru yayi ya juya wajen da oba ke zaune
"Your royal highness.. Ko kana da masaniya kan abinda ke faruwa?.." Oba gyara zama yayi sannan yace
"Gaskiya nafiku bacin rai kan abinda ya faru cos babu abinda Salem zai nema wurina in hanashi saidai nasamu labarin ummanshi batason ya auri wata yaren..." Abba shuru yayi yana sunkuyar da kanshi kasa don Sam baida kwarin jiki, oba yacigaba dacewa
"Kuma uwar dabance..in har batason Abu..to wannan abun baya albarka..." Da sauri Abba yace
"Your royal highness maganaka gaskiya ce, amma wallahi umman Salem tayi realising mistakes dinta...she has given her blessings,..." Yafada cikin sanyin murya, OBJ mamaki yayi sosai
"Gaskiya in hakane...auren ba mai yuwa bane..amma tunda kace ta bada blessings dinta..maybe if possible kuzo tare daita..don gaskiya bamu yarda a hada auren da uwanda bata so..." Ahankali Abba ya gyada kai alaman understanding, sai tunani yake daman haka mutanen nan suke? ...don yasan da kyar a hana aure a arewa don uwa bataso. Abba sai tunanin inda Salem yake yake.

Salem kam hada kai yayi da gwaiwa yana kuka sosai, da kyar tawa ta Iya kara mikewa ta rarrafa inda yake, cikin kuka tace
"Please... Ife..." Afusace Salem ya daga kanshi
"If you ever call me that again.. I will strangle you to... Death...baki sona...baki taba sona ba..." Kurawa juna ido sukayi hawaye na zubowa daga idon kowanne su, cikin shessheka ta kara cewa
"Please... Tell.. Me...have Umma given... Blessings..." Salem murtuke fuska yayi ya mike ahankali ya goge hawayen fuskanshi, sannan ya juya gareta ya nuna ta da dan yatsa
"Ko kece autan mata..na hakura dake....ko sonki zai kasheni...na hakura dake....amma Allah yaisa tsakanina dake...I will not forgive..." Da sauri tawa ta rike mashi kafa sannan ta mike ahankali, wani irin kallon juna suke, Salem yana tunanin yasan bazai iya rayuwa bada itaba, itama tana tunanin no body is taking away this man from her, she has the right to love and she loves him
"Am not letting you go..." Ta fada mashi, tana kaiwa nan tayi hanyan waje.

Mami na gani Salem ya Dade part dinta bai fito ba ta sauko, adaidai bakin palace ta cikaro da tawa data koma kaman baitaba, duk idanuwanta sun chanza color, fuskanta ya kumbura, rike mata hannu tayi, Salem ma fitowa yayi ya nufosu.
"Habibty were are you going?... What happened to your face..." Ta jerawa tawa tambaya, amma tawa bata saurareta ba ta fixge hannun ta daga hannun mami ta shiga cikin palace da gudu, da gudu Salem ma ya taho, mami tsaya kallon ikon Allah tayi, yanmatan gidan har dasu tima da deeja suna tsaye tsakar gidan suna kallon su, don dazu da suka wuce sun gansu, kuma yanzu sun san sir Salem ne, tima so tayi tashiga part din mami amma sauran yan Matan Suka hanata.
Chapter 47 · 0% Book details