← Book details Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 94

Sashe 54

Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

💛💚💜💙❤
ZAKISAN KONI WAYE
💙❤💛💚💜

®zuwairat(ummu Maryam)

5⃣4⃣

Tana gama ci Haj ta kwace plate, itakuma ta kuskura bakinta ta tayi sallan ishai kafin ta gama har ta hada mata ruwan wanka, tana mikewa tashiga bathroom tayi wanka ta fito, kayan bacci yagani kan gado ta dauka ta saka ta ta fara irin tafiyan da aka koya mata tanayi tana murmushi don kawai hangen Salem take yana kallon ta tana irin wannan tafiyan

💙❤💛💚💜

Salem na wurin dinner da parents dinshi kasancewan har lokacin bai koma abuja ba, wayanshi ya fara ringing yana dubawa ya saki murmushi, picking yayi yana cewa
"The minister da kanshi..." Yafada yana mikewa daga kan dinning, barin wurin yayi suna gaisawa cikin mutunci, congrats mutumin yayi mashi Sannan ya fara cewa
"Wai yaushe ake fara wedding events..." Mutumin ya tambayi Salem
"In the next four weeks.. Insha Allah.." Dariya sukayi suna Dan hira kafin Salem yace
"Daman inason tambayan ka...waye ya yi maku prewedding pictures?.. Na gansu on social media sunyi min kyau .." Dariya mutumin yayi
"No problem... Daman ina Neman gudumuwar da zan baka..so I will arrange and pay for the pre wedding pics..." Dariya kawai Salem yayi sukayi ban kwana. Bai koma dinning ba ya fadawa guys dinshi su shirya su koma abuja cos gobe Monday, bankwana yayiwa su ummanshi Sannan suka wuce.
Shi kadai Sai murmushi yake, bakomai yake tunawa ba illa tawa da Haj kudirat, daman ya riga ya bada ATM da pins din, kawai jira suke gobe sukai.

Suna isa abuja yayi wanka Sannan yayi sallan ishai ya dawo ya kwanta yana tunanin ko ya kira tawanshi cos ta fada mashi yanzu suna tare da Matan. Kwantawa yayi yana lumshe idanuwa kaman mai jin bacci yana tunanin in the next five weeks yana da aure, nace mantawa kayi cos kana da aure for the past two and halve months.

Har 10pm bacci bai daukeshi ba, wayanshi ya dauka yayi dialing number tawa, ringing ya dingayi amma no response. Ajiye wayan yayi ya kwanta amma bai samu bacci ba Sai bayan 12.

The following day ya tafi office as usual, har lokacin bai kara kiran tawa ba itakuma bata kirashi ba Sai expecting call dinta yake.

Abangaren Umma gari na wayewa ta fadawa sisters dinta biyu Sai sisters Abba biyu suzo zaa kawo kaya don su tayata zaba, harda su shuwa da zasuzo.
Yawancin yanuwan Umma basuso auren amma basu Iya cewa komai, around 10 bus biyu suka shigo gidan har da Haj hannatu don itake dilan kayan. Manyan boxes aka fqra shigowa dasu katon falon Umma. Bayan kaman minti talatin aka bude kayan. Kayane na manya don babu atampa, lace, materials ko shadda da Kudinsu ya yi kasa da 30k, Umma cewa tayi
"Suyi choosing super da aura 24, shadda 24, Vails 24/..atakaice komai 24"
"Yes Umma" su shuwa sukace, Sai wata daga cikin sisters din Umma wacce suke kira ammi tace
"Bayerabiyar zaa yiwa wannan uban siyayyan?.. $" da sauri ilham ta kalleta
"Yo ammi Yoruba ba mutum bane?..." Bata idaba ta buge mata baki
"Dalla rufe min baki..duk Baku ganin kowa da idon arziki..." Ahankali wata kanwar Abba tace
"A ba karya tayiba..Yoruba ba mutum bace..." Na fada ya fara tsakanin su, daman ba jituwa suke ba da kyar aka samu sukayi shuru shima saida Umma ta bude wuta tana cewa
"Salem ni na haifeshi..kuma na amince mashi ya aureta don banason rabo yayi gaba dani..don haka kowa ta maida wukanta..."
"Dama ke ke daure masu gindi.." Inji ammi
"Mi kikeson inyi?...ya nace Sai ita..nidai na hakura don har istahara nayi..." Saki sisters din Umma sukaja Sannan karaman tace
"To gaskiya a gama wannan ya auro bafulata ko bahaushiya.." Karaf shuwa tace
"Kam Allah ya sauwake yaya yayi mata biyu..." Bata idaba ammi ta nufota, da gudu ta bar wajen don tasan ba wuya taci na jakki. Sai wajen 12 suka gama zaban kayan, falon Umma babu wurin saka kafa don yanda kaya ya cika koina.

Gari na wayewa, bayan sunci breakfast mai rai da lafiya ameera tabawa diyar hinde dubu 60 tace ta sayo small plasma TV Sai startime.
Ita da ta tafi tun 8am bata dawoba Sai 11:30am. Tana shigowa duka suka dauki tsalle banda ameera dake kallon yanda suke jin dadi, kuma jindadinsu na sata farin ciki ba kadanba.
Da kyar ta roki masu gadi sukayi masu fixging don saida suka amshi 5k hannun ta Sannan.
Suna fara kallon ameera ta saki ajiyan zuciya don yanda hinde da yaranta suke shewa, yanzu ji take tamkar suna na wani alaka. Lokacin zuhr nayi ta kalli babban diyar hinde
"muje muyi alwallah.." Mikewa tayi amma badan ta soba don tashar dadin kowa suke kallo. Suna fita waje ta suna ruwa cikin kettle biyu ta dauki daya ta mikawa ameera daya, Tsugunnawa tayi tafara alwallah, kusa daita ameera ta dawo Sannan ta fara cewa
"Yar uwa har yanzu baki fadamin abinda ya taba auren ki da mijinki ba..." Diyar hinde ta ajiye butanta Sannan ta kalli ameera
"Wallahi ba komai bane illa bai daga kafa..." Sam ameera bata gane inda ta dosaba, dan dariya tayi sannan tace
"Ban ganeba?... Bai daga kafa kiyi me?" Shuru tayi ta sunkuyar da kanta kasa don kunya takeji tayi mata dalla2
"Ki fadamin mana.." Ameera ta tambayeta, shuru tayi kaman bazatace komai ba Sannan tace
"Bai Bari na hutawa...kullum cikin auratayya muke..." Dan kallon tuhuma ameera tayi mata
"Aurat...oho..." Ta fada da Dan karfi don Sai lokacin ta gane inda ta dosa, Dan dariyan rainin hankali tayi tana cewa
"Don wannan Sai ki rabu da mijin ki?.." Ido diyar hinde ta kwalo tana kallon ta
"Haka kikace?..hmmm..kiyi adua Allah ya rabaki Dana mijin da baya daga kafa... Basu da tausayi..." Har lokacin ameera bata bar dariya ba, cewa tayi
"Amma ina ganin wannan bai isa yasaki rabuwa da mijinki ba..saidai in baki sonshi..." Dan baki diyar hinde ta tabe Sannan tace
"Wasa ki ganin abun...misali kina Iya zama da mijin da kullum babu ranar banza?...Sannan ko da rana wani lokacin bukata yake...sau hudu ina bari..har hakuri likita ya bashi yadan dinga ragamin...amma baiyiba..." Shuru ameera tayi tana cewa
"This is serious..."
"Kedai kiyi adua Allah yabaki namijin da bashi da jaraba..." Ameera batace komaiba ta don ita tunani take me zatayi da 1 minute man, she need a hard guy, cikin zolaya tace
"Kilan flowern ki nayi mashi sugar.. Shiyasa yakasa daga maki kafa..."
"Kedai raba kanki da jarababben namiji"

Tawa na tashi Matan ta maidata bayan tayi sallan subhi, for the first time ta kara bacci cos ta saba da aiki bayan sallah asuba. Haj kitchen ta shiga ta hada mata nice ugwu soup Sai Sai hot tea. Tana farkawa ta shiga wanka cos already ta hada mata ruwan wanka. Kan gado ta tadda wani mini skirt da shimi, daga skirt din tayi taga in ta saka bata Iya bending cos pant dinta zai bayyana. Badan ta so ba ta dauka ta saka ta fito tana tafiya tana rangwada kaman Salem din na zaune. Kan dinning ta zauna tayi breakfast da miyan ugwu da tea. Saida ta gama Haj kudirat ta kalleta
"Now give me that sexy look and smile.." Tawa mikewa tayi ta fara tafiya kaman wata model Sannan ta zauna tana yiwa kudirat wani irin shuumin murmushi kaman yanda ta koya mata,
"Excellent..now yau zamuyi rawa" tawa kallon ta tayi tana tunanin
"Here comes the problem.." Tafada cikin ranta
"As a woman.. Ba Sai lokaci wedding ko wani shagali zakiyi rawa ba, turawa sunawa hubby dinsu pole dancing amma tunda mu bamu da pole Sai muyi lap dance...Yakama a matsiyin ki na yarinyan dazatayi aure ta koyi sexy dance steps da zakayiwa hubby.. Lap dance shine kiyi rawa kina Dan shaking jikin ki Sannan ki zauna kan laps din hubby ki..make sure kinyi sexy dress kaman yanda kikayi yanzu Sannan make sure you don't break eye contact with him..." Tawa dai jinta kawai take don tasan da akwai matsala.
"The most shameful thing shine na miji yaga nakedness dinki..so the moment haka ya faru tsakanin ki da mijinki then babu sauran kunya..so zaki fidda kunya..." Ta fada tana kunna wakan Beyonce cikin MP3 dake kan dinning. Wakan am a diva ya fara tashi, mikewa Haj tayi ta umarce tawa da ta juyo da kujeran dinning ta kalleta, ahankali ta fara rawa tana Dan juya jikin ta ahankali tana shafa jikin ta da kaman tana shafa kwai, Sai girgiza jikinta take tana Dan bin wakan Ahankali, duk abinda take eye balls dinta cikin na tawa, itakam tawa baki ta bude tana kallon ikon Allah
"Close your mouth.. I know am incredible.." Tafada tana karasowa wajen tawa, Sai lokacin tawa tasan bakinta bude take . tana zuwa wurin tawa ta bude kafanta ta Dan zauna kan cinyan ta tana kada hips dinta, Dan dukawa tayi boobs dinta na shafa fuskan tawa. Duk abubuwa da take idanuwanta cikin na tawa. Mikewa tayi sannan tace
"Your turn.." Tafada tana zama. Ahankali tawa ta girgiza kanta
"Ma'am.. I can't.."
"No...babu word impossible.. Saidai I'm possible.. So stand up and give it a try.. Banason gardama.." Tafada tana maida wakan farko. Jiki ba kwari ta mike tafara takawa amma duk step din da zatayi Sai ta kushe ta, sunfi hour biyu suna Abu daya amma still she's not getting it right, Idayat ta shigo da ATM da Salem ya aiko dashi, dariya tayi dataga yanda tawa ke rawa.
"Kina da aiki.." Ta fada tana mikawa Haj ATM din ta fita.
"Yanzu zanshiga Dubai market in sayo maki abubuwan da zaki bukata.. Kiyi ta practicing kafin in dawo.." Ta fada mata sannan ta fita, tawa zama tayi ta rafka uban tagumi.
Sai lokacin tawa ta tuna da wayanta, da sauri ta dauko nan ta cikaro da miss calls din Salem har dana Daren jiya, nan take tayi calling dinshi.

Sai bayan zuhr Haj tadawo da uban kaya kala2, perfumes kaman a shop ga Arabian Sannan American, ga expensive cosmetic Sai mayukan shafa complete set daga company dass.

❤💛💚💜
Pls kuyi hakuri, commitment ne sukayi min yawa, so har yanzu zaku dinga kina shuru so zaku Dan ji ni quite for a while, hope you will bear with me...thanks💋💋

❤💛💙💚💜
ZAKISAN KONI WAYE
💛❤💙💚💜

®zuwairat(ummu Maryam)
Chapter 54 · 0% Book details