← Book details Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 94

Sashe 28

Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Around 10pm Salem ne kwance sai juye2 yake,hannuwanshi biyu dafe da maranshi, da kyar ya mike ya balli magani yasha, Amman har 10:30 bai samu sauki
"Wane irin matsala ne wannan... Why is the medicine not working..." Yana cikin haka wayanshi yafara ringing, da kyar yayi picking kasancewan yasan mai kira
"Guy how far?" Ya fada mashi ahankali, da sauri Khalid yace
"Bestie meke damunka?" Ahankali Salem yace
"Am having abdominal pain"
"Sorry dear.. Kasha drugs dinka mana"
"Nasha..its not working" yafada yana nishi
"Guy in banda abinka ..gaka da mata Amman you are suffering your self.." Ahankali Salem yace.
"Wace mata?"
"Wacce ka kai sambisa forest mana" shuru Salem yayi For a moment
"Wallahi mantawa nake daita...dukkan hankali na yana kan tawa"
"But you don't have tawa now..sai kayi amfani da abinda kake dashi" ahankali Salem yace
"I don't want to use that gal...nasan in Allah yabani tawa ta isheni..kuma tawa is not the kind of gal dazata zauna da kishiya..kawai just pray for me in sameta..don na samu labarin Umma ta sa a dauketa and dazun da safe itama saida maminta ta doketa because of me..am just confused"
"Am sorry you are going through a lot...I wish there is something I can do to help"
"Just help me prayer"
"I will.. About that gal..your wife in sambiza, meye ma sunan ta?"
"Ban saniba..but I think it's sameera"
" to ita sameera tunda ba zama zakayi daita ba.. I suggest you let her go" Salem da sai cije lower lip dinshi yake saboda azaban da cikin shi keyi mashi yace
"I will.. But not yet...she has to learn her lessons"
"But..." Bai karasaba Salem ya katseshi dacewa
"Best..let's talk tomorrow.. Wallahi yanzu kaman zan mutu nakeji"
"OK" Salem katse wayan yayi ya rike yana juye2 , muryan tawa kawai yakeson ji, Amman bayason ya jamata wani fadan.
Har 11 baiyi bacci ba sai nishi yake kaman daga sama yaji ta kirashi, kaman yana jira yayi picking
"Habibty" yafada Amman dakaji kasan bashi da lafiya, cikin rada tace.
"Ifemi meke damunka?" Ahankali Salem yace
"Wayyo cikina" yafada yana kara rike cikin shi da hannu daya
"Habibty cikina zai kashe ni" kaman zatayi kuka tace.
"Sorry.. Sorry ifemi.. Please kasha drugs"
"Love I don't need drug.. I need you..please let's get married before next month.. Please I need you" tawa shuru tayi
"Please am dying"
"Stop calling death for your self.. Allah zai baka lafiya"
"Habibty baki ganeba.. I am 35..I have known no woman.. I need a woman.. That woman is you" yafada yana nishi sosai, still cikin rada tawa tace
"Ife..its not fair...the way you are talking to me is not fair..am just 18 kuma kana gayamin irin wannan maganan.. So kake ka lalatani?.. Do you want to take my pride away?..."
"No..am sorry.. I can't help it..kusan shekara ta takwas ina Neman the right person...now I have found you.. Dukkan feeling din da nake suppressing da drugs is rushing back..and is killing me.. Banason in fada wata hanya.." Tawa dai batasan abinda zatace ba, duk nishin Salem ya shika mata kunne,
"Sorry"
"Thanks.. Just go to Sleep"
"No..zan tsaya kayi bacci tukunna"
"Then let me call you back" yafada batare daya ji opinion dintaba ya ya katse wayan, yakirata, haka suka dinga hira, inbasuba babu maijin abinda sukecewa, sai around 12:30 bacci yayi gaba dashi sannan itama ta kwanta.
💚💜❤💙💛
ZAKISAN KONI WAYE
💜❤💙💛💚

®zuwairat(ummu maryam)

3⃣1⃣

Kowannensu mafarkin junansu yayi, sai yau Salem yaga fuskan yarinyan dayake mafarkin ya dauka a taxi da fararen kaya, kuma tawace, itakuma tawa mafarkin, Cinderella tayi, kuma wai itace Cinderella, and the most handsome guy on earth took her away from all problems.

Wacegari Salem yadawo daga masjid ya koma ya kwanta, har lokacin bai jin dadi sosai, around 9am ya kira tawa ya sanar mata Abdul zaizo daukan abinci
"Har yanzu baka da lafiya ne?" Ta tambayeshi
"Am OK...thanks for yesterday"
"You are welcome.. Ife..bari in kammala shirya kayan kafin ya iso"
"OK" Salem saurare yake ko zata gayamashi Mtn sun turo mata message Amman shuru, kashe wayan yayi ya kara kiran, shugaban Mtn ya tambayeshi ko an tura mata yace eh sun tura har sau biyar. Kashewa yakira shugaban police ya tambayeshi ya tura police location din daya basu, shima cewa yayi sun tura three undercover police, amma har yanzu baa kama yaron dayace akamaba.

Kwantawa yayi yana jira Abdul ya dawo daga gidansu tawa da abinci don wayam ya kwanta jiya.

💜💙💚💛❤

Abdul na zuwa daukan abinci, tawa tayi serving mami sannan ta shiga wanka, shiryawa tayi cikin material mai saukin kudi ta zuba sauran abinci ta fara ci tana duba messages din da akayita tura mata tundare Amman bacci ya hanata dubawa, tana buda na farko taga an rubuta
_"Dear costumer you have win the the sum of 25m and a house in maitama abuja, kindly goto the following address to redeem your price before Thursday"_address da date tagani, daria tayi tacigaba da cin abincinta, sauran ta duba ta ga dukkan su iri dayane,ajiye wayan tayi gefe tana cewa
"419..kawai"

💜💙💛❤💚

Yauma saida aka kira sallan asuba sannan ameera ta koma daki, jikin ta sai zafi yake saboda cizon zauro, kasan leda ta kwanta, bayan kaman hour daya da kwanciyanta hinde ta shigo da sallama, ameera na jinta tayi banza daita, tafi minti talatin sannan ta mike ta fito tana tsaki
"Waike wace irin mutum ce da baki bari gari ya waye kafin kizo gidan mutane?" Hinde tana scratching kanta tace
"Kiyi hakuri.."
"Dalla rufemin baki!" Ta daka mata tsawa kaman mate dinta, hinde shuru tayi bata kara cewa komaiba, ameera kura mata ido tayi for a moment sannan tace
"Wai kin taba ganin sabulu kuwa?" Da sauri hinde tace
"eh..sosaima"
"To me akeyi dashi?" Ta kara tambayan ta, still hinde tana scratching jikin ta ta bude baki zatayi magana ameera ta katseta dacewa
"Dalla ki bar soche sochen nan is disgusting" da sauri ta bar scratching Amman da gani tanaso yinshi
"Nace me akeyi da sabulu?"
"Wanka da wanki "
"Amman babu alaman kina wanka da wankin..don you look irritating" ahankali hinde tafara
"Yar nan..wahalan duniyace ta maidani haka..mijina yarasu ya barni da yara shida, bani da wani aikinyi..ga tsadan rayuwa...kai da yara bakuciba kunyi ta sabulun wankin?.." Ameera kura mata ido tayi na dan lokaci, saita tsinci kanta da tausayawa hinde, kuma itace mutum ta farko dataji ta tausayawa, barin bakin kofan tayi tanufi kitchen, cikin kayan da aka saya mata tabude ta dauki sabulun wankin daya ta wulla mata tana cewa
"Gashi ki koma gida, kiyi wanka akalla sau goma..don banason inga datti ko daya jikin ki...sai ki dawo muyi girkin" da sauri hinde ta dauki sabulun tana cewa
"Nagode.. Allah yasaka da alkhairi" wannan shine karo da farko da ameera taji wata ta cimata albarka kuma taji dadin hakan.
Hinde fita tayi itakuma ameera ta koma ta kwanta, tana tunanin gida.

Bayan minti talatin hinde ta dawo kal kaman baitaba, ameera kallon ta tayi from head to toe yaga jikin ta tas saidai kayan jikinta dukunkun suke, komawa cikin tayi ta dauki Riga da zani cikin kayan da aka ajiye mata ta mikawa hinde
"Gashi shiga chan ki sakasu" tafada tana nuna mata toilet
"Nagode" kawai hinde take ta maimaitawa ta shiga toilet ta chanza kayan tafito kaman ba itaba, sai kallon ta ameera take tana murmushi
"Kin ganki kuwa? Wallahi kaman amarya" dan dariya hinde tayi
"Kai yarnan kece mai kama da amarya.." Ameera hada giran sama Dana kasa tayi data tuna da gaske ne ita amarya ce Amman gaya cikin wannan irritating place.
"Ki shaga kitchen ki debo abinci yanda zai ishemu da yaranki ki dafa....Amman please karki bude kank...cos I know your hair is still disgusting" tana kaiwa nan ta koma cikin wannan karan cikin kurya ta shiga ta kwanta kan foam tana kuka

💜💙💛❤💚

Salem har 1pm tawa bata CE mashi komaiba, kiran shugaban Mtn yayi ya tambayesu meye labari, mutumin cewa yayi sun tura, tsaki Salem yayi sannan yayi masu umarnin su kirata.
Chapter 28 · 0% Book details