← Book details Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 94

Sashe 35

Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

®zuwairat (ummu maryam)

3⃣8⃣

Kan daya daga cikin kujeran wajen Salem ya zauna, fara maido recording din baya sukayi, Salem kurawa monitor din ido yayi, ana zuwa inda tawa ta fita, da farko ya saidasu, fara playing dinta akayi, har inda gate ya wulla ta saida ya gani, idanuwanshi cikowa yayi da kwalla, kallon su yayi
"Kuna ina wannan lokacin?" Ya tambayesu
"Sir muna masjid cos 5:20am ne" daya ya amsa mashi, cigaba da playing yayi har inda tawa ta fita tana kallon gidan tana goge hawaye, kan Wanda ke waje ya maida kanshi , nan yaga sannan wasu suka saida tawa..da sauri Salem ya mike tsaye, gani yayi suna yi mata magana kuma the next minute suka fara nuna mata bindiga, hannu Salem ya dora bisa kai, yana kallo suka tafi daita.. Komawa yayi kasa ya fashe da kuka kaman Dan yaro, don gani yake tamkar an kashe ta, dayan daga cikin guys din yadan dafa mashi kafada, da karfi Salem ya tureshi sannan ya mike tsaye,
"Kuna ina sanda aka dauketa!" Yafada da karfi, dukkan su shuru sukayi suna kallon juna
"I said kuna ina!?..." Still shuru sukayi.. Ahankali Salem ya fara cewa
"What have I done to deserve this From you guys... Na baku free food.. Free shelter...the best cloth...and you can't do your job...saboda in wani ya gaji ya huta sai wani ya hau aiki, shiyasa na dauki Ku uku aiki..amma hakan bai da amfani... Nasan you guys are incompetent.. All of you are fired!!!" Ya fada sannan ya fice daga dakin yana kuka...yasan in ba Umma ba babu wacce zatasan yana abj balle ayi kidnapping tawa..
"Umma..why..." Kuka ne yaci karfinshi, kasa ya zauna gaban jet yana kuka kaman yaro, pilot ne yazo ya dinga rarrashin shi, saida yayi mai isanshi sannan ya mike ya kalli pilot din
"Call me those fools outside" yafada cikin husky voice, da sauri pilot ya kirawo su Abdul, cikin jet ya shiga da sauri su Abdul suka yi parking motan su suka shiga cikin jet sannan pilot ya kalleshi
"Sir ina zamu?"
"Yola" yafada yana kafa speck a fuskanshi.

Around 3:45pm suka isa yola, personal house dinshi suka sauka sannan suka dau motan sukayi family home, agaban masjid dake gidansu sukayi sallah sannan Salem yayi trekking zuwa gidansu, yana daf da shiga gidan yadan juya aikam sai ya hangi bag din tawa cikin flowers din kofan gidansu, da sauri ya karasa wurin ya dauki bag din ya bude gani yayi har kudinta na cikin bag din...wani sabon kuka yafarayi
"What did Umma do to you...you caused it..why do you have to run from me?.....is it a crime to love you?..." Kan ya dora da bangon gate dinsu yana kuka, yafi minti goma wurin sannan ya shiga ciki. Already guards suna jiranshi, yana zuwa yav kalle su
"Don't let anybody into this falo..except Abba.. Kun gane?" Yafada yana nuna masu side din Umma
"Yes sir" suka amsa mashi sannan yashiga ciki.

Afalo ya tardata tana zaune ita kadai tayi tagumi, ko tunanin me take? Oho. Takalmin kafanshi ya cire, ya karasa inda take, kwantawa yayi kasa flat tare da rike kafan Umma, sai lokacin Umma tasan da mutum cikin falon, kuka sosai Salem ya farayi
"Umma na rokeki da sunan Allah.. Ki bani yar mutane in maida masu..." Umma kallon mamaki tafara yi mashi
"Kai ..kana haukane?.." Kai ya fara daga mata
"Umma am mad in love with tawa..kin dauketa..please tell me where she is..." Umma kokarin kwace kafanta tayi amma Salem yakara rike ankle dinta kaman his life depends on it..
"Umma please tell me inda kika kai tawa...nasan baki sonta amma bansan you can go this length ba..." Kuka ya dingayi har da shessheka.. Umma tsaya kallon ikon rabbi tayi..
"Son..please free my leg.." Girgiza kai yayi
"No Umma.. Na rokeki..kifadamim inda kika kai Tawakaltu.. Menayi?..meye laifina?..is it my fault that I feel in love with the wrong person?... Ba laifi na bane...bani na sa zuciya ta ta kamu da son wacce baki soba... Umma please tell me inda kika sa aka kai taw..." Kuka yaci karfinshi , yana kuka yana tari.. Gashi tun safe ko ruwa baishaba, tari yacigaba dayi sosai kaman ranshi zai fita, shafa mashi kai Umma tafarayi, da sauri ya kauda kanshi yacigaba da tare, saida ya gama yacigaba dacewa
"Ki fadamin..please..." Wani tarin yafarayi, nan fa hankalin Umma yafara tashi, kokarin cire kafanta tayi amma Salem bai saki kafanba
"Son please sit up...you are hurting yourself.."
"Umma you don't care if I die...inda kinasona zakiso abinda nake so..." Tari yacigaba dayi kaman ranshi zaifita,,
"Son please ka tashi..." $ kara girgiza mata kai yayi, yacigaba da tari, saida tarin ya lafa yacigaba da kuka tare dacewa
"Wallahi Umma.. Bantaba tunanin zan kamu da son yarinya hakaba...but I can't help it...nidai ..." Coughing yacigaba dayi ahankali Umma tace
"Ita ta fada maka nayi mata wani abu?..."
"Ai hired guys dinki yarda mata waya sukayi...Umma why...tunda bakin son tawa na hakura daita..amma please tell me where she is.." Yafada cikin kuka, kokarin mikewa tayi amma yanda Salem ya rike mata kafa ya hanata tashi
"Ka sakarmin kafa kafin in bata maka rai..."
"Wallahi ki kashe ni...hakan zai fimin sauki..." Umma kwalawa guards dinta kira tayi suzo su dauke Salem daga dakin amma suna zuwa bakin kofan guards din Salem suka hanasu shiga,..duk yanda sukaso wucewa basu samu hanya ba, sunfi minti ashirin ahaka, Umma gani tayi da gaske Salem yake, gashi sai tari yake babu sassautawa, duk yanda Umma taso lallashin sa abun yaci tura, datace ya sakar mata kafa sai yace
"Please tell me where you took tawa.." Magiya Umma tafarayi sosai amma yaki sakinta, Sam bata son Abba yasan abinda ke faruwa don dukda yana da saukin kai baya tolerating nonsense, Salem kuka yake sosai Umma tarasa yanda zatayi dashi, abu kaman wasa har hour daya tayi Salem yaki sakar mata kafa wai dole saita fada mashi inda ta kai tawa. Ana cikin haka Abba ya dawo, tundaga nesa taga guards din Salem dana Umma tsaye suna kallon juna, kallon Mara dadi, ana parking mota Abba ya fito ya nufo wurin,
"Meke faruwa nan?" Ya tambaya yana kallon each and everyone, daya daga cikin guard din Umma yace
"Sir..Hajiya keta kiran mu amma sun hanamu shiga" Abba kallo guards din Salem yayi
"Meye haka?"
"Sir we are following orders" inji majed, Abba bai kara cewa komai ba ya shiga ciki, nan fa gaban Haj yafara disco ,Abba kallon Salem dake kwance kasa yana kuka,
"Me ke faruwa nan?" Ya tambaya yana kallon su, Salem baice komaiba yacigaba da kuka shi ita kuma Hajiya shuru tayi
"Baku jina ne?"
"Abba ka fadawa Umma tabani tawa..."
"What are you talking about?" Abba ya tambayeshi, cikin kuka ya fada mashi abinda ya faru
"Subhanallahi.. Hajiya is he saying the truth?" Umma shuru tayi, alaman bata da gaskiya, Abba dukawa yayi
"Son stand up..." Da sauri ya girgiza mashi kai
Abba ka fada mata ta gayamin inda ta kai Tawakaltu.. " Abba kallon Umma yayi
"Wai ina kika kai yarinyan mutane?" Ahankali Umma tafara cewa
"Son kayi hakuri... Babu abinda nayi mata...I just beg her to stay away from you.. And she promised..." Kuka sosai Salem yafarayi
"Umma why..." Tari yafarayi sosai yana nishi sama2, da sauri Abba ya dagashi, aikam sai jini hancinshi..kuka Umma tafara
"Wallahi nayi nadama...tun yarinyan na nan nafara nadaman abinda nayi.." Abba dirty look yayi mata sannan ya rike Salem
"Muje part dina in baka first aid kafin in kira doctor.." Ahankali Salem ya girgiza mashi kai
"No Abba.. Allah yasa wannan yazama ajalina..." Tafiya yafarayi, ko tsakiyan dakin bai kaiba ya fadi kasa, da gudu Abba da Umma suka karasa wajenshi, acikin tension Abba ya kira doctor, Umma kwalawa guards kira tayi tana kuka, gabaki dayan su suka shigo dakin, duk ahankali su tashi yayi especially personal guards dinshi. Daukan shi su Abdul sukayi,
"Follow me!" Dad ya umarcesu, da sauri Abba ya fita suka bi bayan shi.

Wani part my dauke da hospital equipment aka kaishe, Salem bude ido yayi yaga mutane triple, maidasu yayi rufe tare da dafa kanshi.

Bayan minti ashirin doc yazo, bai bata lokaci ba ya sa mashi drip.

💚❤💙💜❤

Yau ya komawa ameera sabo cos yau ita kadai ta wuni, gashi da musassara ta wuni ga ciwon kai dana Mara, duk abin duniya ya isheta, bakin gate taje tayi knocking,
" meye?" Suka tambayeta, cikin kuka tace
"Dan Allah Ku kiramin hinde.." Banza sukayi daita,
"Kunji Dan Allah.. Bani da lafiya ne..."
"Kar ki kara aikanmu...darajanki daya da baki da lafiya.. Bari musa akira maki ita" daya daga cikin su ya fada sannan ya kira wani ya aikeshi ya kira hinde.

Bayan kaman minti ashirin sai ga hinde ta shigo gidan , gani tayi ameera durkushe kasa tana kuka hannunta kan maranta
"Lafiya?" Ta tambayeta tana karasowa wajen ta, cikin kuka tace
"Cikina...wayyo..menses zanyi..."
"Meye messes" tafada tana dagata tsaye
"Alada zanyi..." Tafada tana kuka tana yarfa hannuwa,
"Daman haka yake yi maki?" Kai kawai ameera ta daga mata,
"Sannu" hinde ta dinga yimata, ta maidata daki sannan ta dora mata ruwan , bayan yayi dumi ta saka daya daga cikin dankwali ameera ta dinga danne mata cikin ta da bayan ta,, aranan hinde nan gidan ta kwana, banda kuka babu abinda ameera takeyi don a gida in ta fara har Karin ruwa akeyi mata.

💚💙💜💛❤
Chapter 35 · 0% Book details