← Book details Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 94

Sashe 80

Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan sallan ishai ameera ce kwance tana tunanin Khalid, tana mamakin yanda ya shiga cikin ranta farat daya, amma har yanzu bata bar tunanin meye hadinshi da bodyguard din Salem ba
"Allah yasa is not what am thinking..." Ta fadawa kanta, wayanta ne ya fara ringing taga shine picking tayi suka fara hiran love yanda yake bata labarin gidansu kaman sun shekara tare, bayan kaman minti 20 da fara hiran su affan ya shigo, ameera kallon shi tayi
"Anty ana sallama dake..." Yafada ya fice abinshi, Khalid na jin abinda affan yace yafara jealous
"Baby yanzu zancekikeyi da wani?..."
"No...ina dakina..."
"Ainaji ance ana sallama dake....please don't let any body take you away from me..." Yafada Ahankali, lumshe idanuwa tayi
"Ban sanmai kiranaba..." Ta fada tana mikewa daga kan gado, bakin window taje ta hangi sultan tsaye cikin wasu hadaddun wears, dukda yana dare bai hanata ganin yanda wristwatch dinshi ke kyalliba.
"Baby I loved you even before I meet you in person... Dan Allah kar wani ya rabani dake..." Ameera dai shuru tayi batace komai ba don tana tunanin abinda ya maido sultan gidansu, Khalid najin bata amsa ba yace
"Zan kiraki later.."
"Ok..." Tafada ahankali
"I love you.." Ya fada mata
"Me too..." Ta amsa mashi. Ajiye wayan tayi ta cire kayan bacci dake jikinta ta saka wata doguwar rikan shadda, bata tsaya kwalliya ba ta yafa Vail ta sauko Sai sauri take, Babu kowa falo Sai affan dake game da iPad dinshi, fita tayi tana sauri don anata tunanin mantuwa yayi dazun da sukazo. Sallama tayi masa ya amsa yana kallon glowing face dinta, gaidashi tayi ya amsa mata still bai bar kallon ta ba.
"Yaya ka shigo ciki mana..." Tafada kanta kasa cos sam bata Iya handling yanda yake kallon ta,
"No...wajen ki nazo... I have something I would like to tell you..." Yafada cikin sanyin murya, murmushi karfin hali tayi
"To...ko mu zauna?.." Tafada muryan ta na dan rawa
"Ok..". Wurin wasu kujeru dake compound din ta nufa ya bi bayanta yana kallon yanda take tafiya cikin yanga kuma ba donshi takeyiba, kawai she is use to it, zama tayi shima ya zauna yana kallon ta
" bari in kawo maka ruwa..."
"Am OK...thanks.." Ya amsa mata yana mamakin irin kyawunta, she's beyond beautiful
"I want to ask you a question... Do you believe in love at first site?.." Gaban ameera ne yayi mugun faduwa, ahankali ta girgiza mashi kai alaman Aa
"Me too...I don't believe that...I believe yakamata mace Dana miji su san junansu for a very long time before they will be able to fall in love..."ameera dai kanta kasa don batasan inda ya dosaba Yadanyi shuru Sannan yacigaba dacewa
"Amma I was wrong... Do you know why?..." Ahankali ta girgiza mashi kai
"Because since last week I set my eyes on you.. I haven't slept... Aisha tunanin ki ya hanani sukuni...Aisha am in love with you... Ba San real love ba sai yanzu cos I see you in everything I touch" ameera Sai ta tsinci komai ya tsaya mata, yacigaba dacewa
"Kece mace ta farko da I fall totally for...You are the first lady da nake ganin in ban samuba rayuwa ta zai shiga matsala... Pls I want you to give me a chance..." Yafada cikin murya mai kwantar da zuciyan mai sauraro. Ameera is speechless don inzaa kasheta she don't know what to say
"Kinyi shuru.. In kuma wani ya rigani no problem.. Zan dauki kaddara..." Ya fada ahankali, Dan girgiza mashi kai
"Yaya ba haka bane...amma...." Sai tayi shuru,
"Amma baki sona?..." Da sauri ta girgiza kai
"Not like that...kasan you are like an elder brother to me...kuma ai is not love at first sights tunda tun ina yarinya ka sanni.." Dariya ya danyi
"I have never taken a very good look at you... Nidai Sai last week na ganki clear... I just wish I was the first man to tell you you are the most beautiful lady that in Africa..." Ameera murmushi tayi amma har lokacin kanta kasa, tasan no woman will resist sultan don bata mantawa sanda suke zuwa secondary school dukkan su tsaya kallon shi suke duk ranar dayazo dropping zeenat har fada suke a kanshi don mostly yan mata saboda shi suke kawance da zeenat, she can say he's the first man da so amma he never noticed her, amma yanzu Khalid is in the picture she loves him and she can't reject sultan,
"Kinyi shuru.. Please say something..."
💙💛💜❤💚
ZAKISAN KONI WAYE
❤💜💛💚💙

®zuwairat( ummu Maryam)

7⃣5⃣

*Masoyan ina godiya, duk ina ganin messages dinku, Allah ya bar kauna* 💋💋💋💃

Still shuru tayi batasan abinda zata ce ba, sultan kam banda kallon ta babu abinda yake, yasan in bai samu ameera ba da akwai problem, itama ameera tana tunanin just few weeks back tana ganin her life is coming to an end for loosing Salem amma ance when one door closes another door is definitely opening, da sauri ta firgita saboda hannun sultan dataji cikin nata, wani irin shocking taji, da sauri ta daga kai ta kalleshi
"Please.. Give me a chance..." Ya fada in a whisper, Ahankali ta gyada mashi kai, manyan idanuwanshi ya kwalo
"You mean you have given me a chance?..." Ya tambayeta har lokacin yana rike da hannun ta
"Yes.." Tafada cikin sanyin murya
"Thank you... Thank you so much..." Yafada yana murza hannun ta ahankali, da sauri ya fiddo wayanshi, ya amshi number ta Sannan yace
" go and have your beauty sleep... I will come back tomorrow.. " yafada yana mikewa, ahankali itama a mike
"Allah ya kaimu..." Ta amsa mashi.
Yana tafiya ta shiga ciki jikinta babu kwari,
"Yanzu meye abunyi,?...I can't dump Khalid.. And I can't reject sultan... What have I put myself into?...." Ta tambayi kanta, dakin mom ta je ta tardata zaune tana shafa mai dagani wanka ta fito, ahankali ta sulale ta zauna kasa,
"Habibty what's wrong?.." Mom ta tambayeta, nan ta fadawa mom komai,
"Ikon Allah...hmmm amma dole ki zabi daya daga cikin su..."
"Nidai nafison Khalid..." Tafada kaman an fixgi maganan daga bakinta,
"You are not serious... Ga dan gida Wanda muka San kowa nashi Sai ki tafi ga Wanda bamu San ko shi wayeba?..." Tafada da dan nagging,
"Amma mom zaayi bincike kanshi ko?..."
"Keep quite...bincike bazai taba saki sanin dukkan boyeyyen halayen mutum ba..." Ameera shuru tayi don already ta riga tayi plan din yanda rayuwan su zai kasance insuyi aure.
"Allah na gani bazan raba abinda Allah ya hadaba...in Khalid ne alkhairi Allah ya zaba maki shi...in kuma sultan ne to shikenan.....kuma ki Sani ko wane shawara zaki yanke ki hada da praying...ni kuma zan tayaki daman cikinta nake.. " tafada cikin kwanciya hankali
"Yes mommy..."
"And remember to make your decision very fast don Allah na ganin banason ki kara full five months gidan..."
"Haba mommy... Five months kaman bakusona???...ina laifina in ida kammala studies dina?..." Murmushin takaici mom tayi
"You don't have common sense... Yanzu kina gurin zama gidan nan for the next two years?... Baki jin abinda yan bakin ciki da yan hassada marasa ilimin addini dana boko suke cewa?...AI yanzu kawai Allah ya zaba maki mafi alkhairi acikin su..." Ameera shuru tayi tana tunanin small and petty talks da mutane keyi Kansu alhamdulillah suna da iliminsu kuma suna amfani dashi, so dukkan su a under slippers dinsu suke, sam maganan mutane baya damunsu, cos as you know silent is always the best answer to fools and those that lack moral and home training.
"To mommy... Amma nidai nafison Khalid..."
"Just do istahara...kuma nasan Allah zai zaba maki Wanda yafi alkhairi acikin su..."
"Allah yasa mommy.. Amma mommy sir sa..." Bata idaba mom tayi mata dakuwa
"Kinci ubanki...tashi ki bani wuri... Yanzu ko ance ki bi bayan mowa Sai ki yarda?..." Ameera bata kara cewa komai ba ta tashi, tasan har yanzu tana son Salem amma in ta tuna abinda yayiwa Tawakaltu Sai ta tsaneshi. Bedroom dinta ta koma ta tarda miss call din Khalid birjit,tana daukan wayan ya fara ringing picking tayi ya fara yimata magana dajin yanda yake magana kasan kishine kawai,shima sultan yana komawa gida yayi kokarin kiran wayanta yaji user busy shima kishi don yasan da wani take waya.

Bayan ya dawo daga office din doc da minti biyu doc ya shigo, kara duba Tawakaltu yayi tare dayi mata tambayoyi Sannan ya sallameta tare da rubuta mata prescription na vitamins da zata dinga sha, har doc zai fita Salem ya kalleshi
"What about mined...about what I told you earlier...." Ya fada mashi don yasan kasan turawa baka iya zuwa pharmacy sayan magani ba tare da prescription daga qualified and professional doc ba.
Doc bai bata lokaciba ya ya rubuta mashi Sannan suka tafi, taxi suka hau ya kaisu resort dinsu.
Order abinci yayi placing Sannan sukayi, suna fitowa aka kawo abinci.
Bayan kaman minti 40 suka gama ya balla mata Maganin ta ta sha Sannan ya dauko nashi zaisha, rike mashi hannu tayi, tare da girgiza mashi kai
"Pls don't drink it..." Shima rike hannun ta yayi
"I have to....I don't want to dismounting my first child..." Yafada in a funny way
"Nidai kar kasha...we will look for another way...."
"Princess babu other way..."
"Da akwai mana..." Tafada tana daga mashi gira... " murmushi yayi,
"Tell me.." Ya fada mata, kiranshi tayi da dan yatsa daya, lumshe idanuwa yayi ya matsa daf daita,
"Bring your ear..." Ta fada mashi, ba gardama ya kai kunnenshi saitin bakinta, magana ta fara gaya mashi ahankali, gani nayi Salem na murmushi , daga kanshi yayi ya kalleta taka daga mashi gira
"Are sure you will be doing that?..." Murmushi itama tayi
"Yes...I have done it before.. Haven't I?..."
"Yes you have..." Yafada yana shawota jikinshi,
"And I will buy you a house in lekki and Dubai..." Dariya tayi
"There is no need for that..."
"Nidai Sai na saya maki...." Yafada yana kissing dinta.
Chapter 80 · 0% Book details