← Book details Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 94

Sashe 55

Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

5⃣5⃣

Tafi kwana uku tana practicing rawa kafin ta iya, acikin kwana ukun kullum Haj kudirat Sai tayi mata spa treatment, Sannan ga special gyaran gashi banda wankan turaren da takeyi mata kuma tana bata abinci mai rai da lafiya tana ci, kullum cikin waya suke da Salem

A week later Salem ya shigo kwara for the pre wedding pics, adakin baki aka saukeshi, abinci mai kyau kala2 aka jera mashi, yaci ya koshi amma kawai idanuwanshi a hanya ko zai ga Tawakaltu, har lokacin zuhr bai ganta ba.
Abangaren tawa kam jet din Salem na landing taso tarenshi amma Haj ta hana ta, wai dole shi zaizo gareta that it is called dignity.
Kwalliya ta sansara mata ta zauna kaman wata sarauniya tana jiran zuwanshi.
Shikuma Salem yana dawowa daga masjid ya rasa sukuni, wayanshi ya dauka yayi dailing number ta, ringing yafara daga chan bangaren tawa ta dauka tare dacewa
"Hello sugar..." Tafada ahankali kaman yanda Haj ta umarceta, Salem daga wayan yayi daga kunnenshi ya kalleta Sannan ya maida wayan kunnenshi
"Habibty.. What did you call me?.." Ya tambayeta, cikin sanyin murya takara cewa
"Sugar.." Dariya Salem yayi yana biting bottom lip dinshi
"Habibty.. You sound naughty..."
"Meye naughy kuma?..." Ta tafada kaman wacce tayi aiki ta gaji, Salem shuru yayi yana lumshe idanuwa don yanda muryanta ke shiga har cikin ranshi.
"Habibty.. Kusan hour uku ina cikin palace amma you don't seem to want to see me..." Dan murmushi tayi
"Am a little bit busy ne...amma kana Iya zuwa ganina yanzu.." Dariya Salem yayi
"Habibty are serious?... I fly all the way to see you... Kuma bazaki Iya zuwa ganina ba?... Its not fair..."
"Sorry sugar...but please come to me..." Salem ji yayi kafafunshi na sayi don yanda take magana
"Habibty.. Who is corrupting you?.. Who ever..thank the person.. Cos am loving it.." Yafada cikin whisper, tawa Dan dariya tayi, Salem yacigaba dacewa
"Now my princess.. Gayamin inda kike cos I can't wait to lay my eyes on you" ahankali tawa ta fada mashi inda take, bai bhata lokaci ba ya katse wayan Sannan ya fito ya nufi discription din data bashi, palace din babu hayaniya haka yabashi daman zuwa bakin kofan data kwatanta mashi yayi knocking, Haj kudirat ta bude, gaisawa sukayi Sannan tace
"Daman inason ganinka.." Salem na dan waige2 yace
"OK...am here.." Nan Haj kudirat ta fada mashi da akwai Dan abubuwan daya kamata yasani game da traditions dinsu Sannan ta fada mashi da akwai training dasuyi da tawa, duk bayanin da takeyi sam baijinta Sai neman ta inda tawa zata bullo yake,
"Kayi shuru.." Ta fada mashi, da sauri yace
"Is OK ma'am..." Dan girgiza kanta tayi sannan ta shiga tayiwa tawa magana, fitowa tayi ta shiga bedroom dinta.
Tawa kama tana jira ta saka Vail din jallabiya dake jikin ta bude kofa tafito, gaban ta Sai faduwa take, Salem na ganin ta ya kwalo idanuwa cos ko kadan bai ganeta, ahankali ta karaso wurin shi tana girgiza ta durkusa ta gaidashi, kasa amsawa yayi Sai kura mata ido kawai yayi, ahankali ta daga kanta ta kalleshi tana yi mashi murmushi, muryan shi na rawa yace
"Habibty kece?... " cikin zolaya tace
"Yes of course..." Tafada tana zama gaban shi anan kasa.
"You are my own rihanna" dariya kawai tayi
"Bari in kawo maka abun sha..." San bata fuska yayi
"Just sit let me watch you" ya umarceta,irin zaman da aka koya mata tayi Salem banda kallon ta babu abinda yake, kallon kafanta yayi yaga sunyi sumul
"Hmmm.." Kawai yace under his breath, kallon shi tayi eye balls to eye balls Sannan tace
"Meye..." Yanda take magana tamkar ba yarinyan daya ganin last few months tana saida abinci gefen hanyaba
"Don't underestimate people.." Ya fada cikin ranshi
"I missed you..." Ya fada cikin whisper kara dacewa
"I can't wait for the next 4 weeks..." Gaban tawa Dan faduwa yayi amma sai ta sakar mashi wani shuumin murmushi, Dan dukar da kanshi yayi kusa daita
"Princess.. Are you flirting with me?..." Dan kallon shi tayi ya kashe mata ido daya, Dan kauda kanta tayi
"Yasu first love da Abba?"
"Suna lafiya.."
"Habibty.. Me kike ci?.. You look ravishing..."
"Thank you.."
"Princess..." Ya kirata sounding so lustrous
"Naam.." Ta amsa batare data kalleshi ba
"Me kika kirani dazun?..." Dasauri ta rufe fuskanta kaman wata mai jin kunya
"Am waiting.. Call me that in front of me..." Ya kara fada mata, fuskanta rufe tace
"My...sugar..." Salem Dan dariya yayi
"Habibty.. Wait until you have tasted me..." Tawa Dan turo baki tayi
"Zaka farako?..."
"Kedai kika fara..." Dan hira suka cigaba dayi, kaman an chunkuleta tace
"Baby...da akwai abinda ban Sani game da kaiba?.." Salem tsaya kallon yanda take fidda magana kaman bataso yayi for a moment Sannan yace
"Why are asking love?.." Ahankali tace
"naji ana cewa da kyar mutum yasan 10 to 30% na halin maza..ni kuma am thinking I know you..." Kura mata ido yayi yana tunanin abinda tace, shidai yasan bashi da wani secret saidai case dinshi da Aisha, kuma yana ganin ko ta Sani nan gaba bazai zama case ba
"Honey kayi shuru.. Ko da akwai abinda ya kamata in Sani..." Tafada tana kama mashi hannu, da sauri ya dawo hayyacin shi, rike hannun ta yayi da two hands dinshi, kaman ya fada mata gaskiyan abinda ke faruwa yayi kuma ya fada mata ko yau yana iya sakinta kuma ya tabbatar mata bai taba komai da itaba amma this moment is precious, he don't want to ruin it, kallon eye balls dinta data maida kaman na maijin bacci yayi Sannan ya saki murmushi
"Habibty.. Bani da secret.. You know komai about me...sai dai ina Abu guda daya..." Da sauri ta zaro idanuwa Sannan tace
"Please what?.." Tafada gaban ta na Dan faduwa don, yatsan shi yasa yafara shafa tafin hannun in a circular form Sannan yace
"I think I can last 4 to 5 hours in bed.. " zare hannun ta tayi tadan kauda kanta gefe tana Dan murmushi,
"I don't want you to be surprise.. So prepare well for me..." Tawa shuru tayi don tasan karyake, amma cikin ranta tasan yana hiding wani secret,
"Hmmm...I just want to know everything about you... Banason Sai bayan aure in gane wani Abu Mara kyau game da kai..."
"Haba habibty saikace ina yankan kanu?... To tell me abinda kike gani zai tada maki hankali.."
"Nidai I don't know.. Amma am telling you..it won't be okay..." Sai kuma tayi shuru don tasan irin tempern ta..tasan she's respective amma she don't take bullshit
"Habibty relax.." Yafada in reassuring tune don yasan zai saki ameera batare datasan anyiba.
"Habibty.. Wacce zatayi planning traditional wedding zata zo nan around 5pm yau...zata kawo pictures Sai ki zabi irin kayan da kike bukata" Dan turo baki tayi
"Is it necessary?.. Kawai duk abinda ka zaba is OK by me..." Dan bakinta ya rike
"No...just choose.. Kinsan its your time.. Inason komai yazama yanda kike so..." Dan rike hannun shi tayi daga bakinta
"OK.." Hannun ta ya cigaba da murzawa kaman yana shafa kwai
"An kawo kayan da ladies zasu saka?.." Ya tambayeta
"Eh..naji su dija nata kiran friends dinsu suzo su amshi ashobi..kasan ni bani da friends" Dan dariya yayi
"Daman banason mata mai tarin kawaye..suna leading ko misleading mutum..amma akano baki da friend ko daya..." Shuru tayi kaman tana tunani
"Sai guda daya itama wurin aiki muke haduwa..mami bata yarda inje gidansu..."
"Sai ki bada address dinta a tura mata invitation.."
"OK..." Shuru yadan biyo baya Sannan yace
"Habibty mu shiga cikin gari mana?..." Ido ta kwalo
"Bansan koina ba..besides wannan Matan bata barina fita ko ina.."
"No..problem...da karfe nawa zaayi pics din?" Ya tambayeta har lokacin hannun ta cikin nashi
"Wai dole ne?.."
"Yes love... I want to show you to the world.. I want people to know some delay is a blessings.." Daga kai tayi takara sakar mashi wani lustful smile
"This smile is killing me.." Yafada kasan makoshinshi, wani takara sakar mashi Sannan ta mike
"Where to.." Ya tambayeta yana lumshe idanuwa
"Ruwa zan kawo maka...maganan da mukayi yanzu ya isa ya saka jin dry throat.." Dan Jan hannun ta yayi ta kusa fadawa kanshi, da sauri ta zari hannun ta ta taka cikin kasaita ta duka ta bude fridge, Salem gyara zama yayi yana kallon yanda take tafiya komai nata na shaking, juice ta dauko ta saka kan tray dake kan fridge Sannan ta shiga kitchen ta dauko cup ta kawo mashi, tamkar mirror ya maidata don ko blinking baiyi.

Around six sukaje Emirates garden sukayi pics, na farko suka English waer jean da t shirt agaban na Salem an rubuta her prince, agaban nata an rubuta his princess, ta tsaya gabanshi ya saka hannun shi cikin aljihun wandonta suna kallon juna,ba karamin kyau sukayi ba.
Nabiyu sun saka kayan Fulani Salem ya rike sanda itakuma rike da kwarya nan ma ba karamin kyau sukayi ba, na uku ya saka shadda fari kal dinkin babban riga amma ba mai zurfi ba, na hudu ta saka gown blue Sai shi yasha blue suit Sai na karshe sun saka kayan Yoruba, Sai around 8 aka gama pics don duk chanzawa da zasuyi Sai an gyara mata fuska suna kan hanyan dawowa ta kalleshi
"Wai kai kayi hiring wayan nan mutanen dasuka dauke mu photo?" Dan girgiza mata kai yayi
"No.. Wani abokina ne...har kayan da muka saka da directors dinshi shi ya dau nauyi.."
"He's nice.." Murmushi kawai yayi Sannan ya kalli drive dake driving dinsu yace
"Take us to the best restaurant in town.."

Atakaice basu dawo gidaba Sai around 10pm har bakin kofan part da take ya rakata saida ya juya yaga babu kowa Sannan yayi saurin hugging dinta , kafin tayi wani Abu har ya hada bakinshi da naya, passionate kiss yayi mata sannan yace
"Good night...make sure you dream of me.."

❤💛💙💚💜
Chapter 55 · 0% Book details