← Book details Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 94

Sashe 71

Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Salem na cin abinci amma idanuwanshi kan tawa, har ya gama cin abinci bata ce kala ba,yana gamawa ya goge bakinshi
"Habibty..." Ya kirata ahankali, bata amsa ba amma ta daga eyes dinta ta kalleshi,
"Am sorry...ki yafemin..." Kauda kanta tayi gefe daya tare da dan turo baki, mikewa yayi ya koma kujeran dake kusa daita ya
"Yanzu kin yarda da gaskiya magana ta?,..." Dan kallon shi tayi
"How can you take such an action?..." Bata idaba ya katseta dacewa
"Baby am sorry... Lokacin ina Neman ways of punishing her of her lack of moral training...I wasn't thinking... Kawai revenge was the only thing in my mind...wallahi I regret what I did cos bansan nemesis will caught up to me ba..." Tawa shuru tayi batace komaiba,
"To yanzu kin yafemin for not being truthful?..." Ya tambayeta yana kama hannun ta, Ahankali tace
"Ni yanzu tsoro kake bani...don nima ina Iya yimaka laifi ka hukuntani fiye da haka..." Da sauri ya girgiza mata kai
"No way...you are special... Gashi har hannuna kika kusa karyawa amma ban ce maki komaiba?.. Wallahi no body tries me that way...so kin yafemin?... Let's continue with our life as we planned it..." Yafada cikin sanyin murya, tawa Dan turo baki tayi Sannan tace
"On one condition zan yafe maka.." Da sauri Salem yace
"Anything for my princess..." Shuru tayi ta dora hannun ta kan nashi dake cikin nata
"Ka maidata... Ka auri mu biyu..." Tafada tana kallon shi eyeball to eyeball, ahankali ya zare hannun shi, tana Dan girgiza kanshi ahankali
"No baby...na riga na saketa..besides bani da raayin mata biyu...kawai let's just let her go..." Tawa murtuke fuska tayi
"To shikenan.." Tabfada tana kokarin mikewa, da sauri Salem ya rike ta
"Haba... Wannan abun is a secret...banason su Umma su Sani cos I know they will not take it likely.... Kuma saki uku nayi mata..."
"Ai she's mesturating..kuma baa saki in mutum bashi da tsarki...and am sure Umma will be happy to know tana da Hausa daughter in-law..." Salem Dan murmushi yayi
"Baby ko bata sakuba kara sakinta zanyi...bawai don banason zama daitaba sai don ko na zauna daita ba zanyi adalci tsakanin Ku ba...all my heart belongs to you...kawai.." Kuka tawa tafarayi tana cewa
"Wallahi ka maida matanka...kuma ni bazan zauna ba..." Kallon mamaki yayi mata
"Dama kinason kishiya?..." Ya tambayeta yakara kama hannun ta
"Ni ba kishiya nakeso ba..amma gaskiya banason ka rabu daita..." Salem dariya yayi
"Aa kishiya kikeso..don't worry zan auro wata amma ba ameera ba...she have lost her chance...you can eat your cake and have it back..." Kuka sosai Tawakaltu ta farayi tana cewa
"Sai ka maidata...in ba hakaba nima tafiyata zanyi..." Dariya Salem ya karayi
"Ki bar wahalal da kanki kan wannan maganan... Am not taking her back.. Kuma ke ko duniya zata tashi bani rabuwa dake..." Tawa kara mikewa tayi ya kara riketa
"Baby please daman baki sona...cos duk mace mai son mijinta ba ta rokonshi ya kara mata kishiya..."
"Ba haka bane...kawai I don't want to think cewa mijina ya taba sakin wata...banason nima kayimin haka..." Ta fada tana kuka sosai, shima mikewa yayi hannunshi cikin nata ya fara goge hawaye fuskan ta
"Please stop crying... Enough of your tears..." Yafada while wiping her tears,
"To ka maidata please..." Salem kura mata ido yayi yaji tausayinta inda da akwai aure tsakanin shi da ameera da ya zauna daita amma ya San yanzu ba halal dinshi bace,
"Baby kinason in fada hallaka?.." Ya tambayeta ahankali, kai ta girgiza mashi
"Then forget about it... Saki one two three nayi mata...so bazan Iya zama daitaba har sai tayi wani auren...so please ki bar wannan maganan..." Tawa buge kafafunta tayi kasa kaman yarinya
"Wai bakajin nace maka bata da tsarki sanda kayi sakin... Please mu zauna tare..."
"Ok sit..." Ya fada yana maidata kan seat, zama tayi shima ya zauna gefen ta, baice komai ba ta juyo ta kalleshi
"Yanzu ka amince?..." Ta tambayeshi
"Please princess can we forget about all this and be happy for a moment?..." Shuru tayi bata ce komaiba, hannun ta ya kama suka mike, wajen gidan sukaje suka zauna nan kasa, matsawa kusa daita yayi ya kai bakinshi kan nata, Dan kauda kanta tayi
"Please.." Ya fada mata ahankali cikin whisper,
"Yanzu two wives gareka..so its your first wife's turn..." Salem bata rai yayi
"Tawakaltu kina wasa daniko?..." Yafada afusace,
"What?.. Nayi karya ne?..AI kwana bakwai akeyi dakin daya sai akoma dayan dakin..." Yanda take maganan yasa shi dariya, kuma cikin few seconds ya kara daure fuska
"Kinsan wallahi ki kiyayi bacin raina cos wallahi ranki sai ya fi nawa baci..." Yana kaiwa nan ya mike ya koma cikin gidan, tawa tabe baki tayi ta kwanta kan grass carpet yana shiga ciki ya hau upstairs, direct bedroom yashiga yaga ameera kwance idanuwanta lumshe kaman mai bacci bakin gadon ya zauna yadan taba kafanta tayi sauri bude idanuwanta tare da komawa zaune, murmushi ya sakar mata itama ta maida mashi martani,
"Babe in tambayeki?.." Yafada yana kallon lulu eyes dinta,
"Yes" ta fada tana gyara zamanta
"Kina sona?.." Ya tambayeta sounding very serious, ameera Dan kura mashi ido tayi tana tunanin ba ajinta bane tace tana sonshi, kuma sanda ya nuna yana sonta bata amince dashi ba
"Please talk to me..." Ya fada mata cikin sanyin murya, murmushi tayi Sannan ta girgiza mashi kai
"No..." Salem kura mata ido yayi for a moment Sannan yace
"To yanzu Tawakaltu ta zake wai saina maidaki...yanzu babu aure tsakanina dake kuma she don't want to understand." Dariya ameera tayi
" don't worry... She will come around.... "
"No..bakisan ta da kafiyaba....very stubborn wallahi..." Still dariya tayi shima yayi dariya,
"Nidai I want to go home...." Ta fada ahankali,
"Yes I know..." Ya amsa mata Sannan ya kara cewa
"Please ki taimaka min ki shawomin kan Tawakaltu.. In kika tafi muna cikin wannan yanayin abun bazaiyi dadiba...."
"To nime zanyi mata.." Ameera ta tambayeshi, shuru yayi for a while Sannan yace
"I want you to make her jealous..." Ya fada mata yana kama hannun ta, kallonshi tayi tasaki murmushi,
"No..please just let me go home..." Bata idaba yayi kneeling gabanta da sauri ta fara kokarin mikar dashi
"Please ka tashi..." Kin tashi yayi
"Sai kin yarda..." Ameera tsaya kallon ikon Allah tayi,bata San haka halin Salem yakeba sai yanzu, awaje da ka ganshi you will think he's somebody with pride and ego amma da ka zauna dashi you will find out he's very simple and fun to be with, hannuwanshi biyu ta kama tanason ta mikar dashi amma ta kasa, sai kara marairacewa yake kaman zaiyi kuka
"Please... Please... Please..." Yafada yana rike da two hands dinta, murmushi tayi
" zanyi amma on one condition.. " dariya Salem yayi
"Wai meyasa in na nemi Abu daga wajanku sai kunbani conditions... Say it.." Ya fada mata har lokacin he's holding her hands
"Inason ka barwa su hinde gidan da suke su cigaba da zama.." Kallon mamaki Salem yayi mata donshi baisan inda ta dosaba
"Wane gida kenan?..."
"Inda ka ajiye ni...."
"Ohh..." Ya fada yana kallon ta ya mamakin yanda akayi selfish ameera ta chanza haka don sai yanzu ya fara amince wa data chanza.
"Na bar masu for good..."
"Yauwa thanks... Nima na amince..." Bata idaba Salem ya mike ya rungume ta, da sauri ya saketa saboda electric bolt dayaji, murmushin karfin hali yayi yabar dakin yana tunanin Allah yasa baiyi mistake ba.
❤💚💙💛💜
ZAKISAN KONI WAYE.
💙💚💜💛❤

®zuwairat(ummu Maryam)

6⃣8⃣

Falon upstairs ya koma yayi kwanciya shi yana tunanin halin tawa, duk ta dagula mashi lissafi, ameera kam komawa tayi tayi kwanciyan ta, har lokacin bata bar tunanin halin Salem ba, wai Salem ne yayi mata kneeling,
"Hmm wonder shall never end.." Ta fadawa kanta, kara mikewa tayi ta fito falo ta ganshi kwance kan doguwar kujera sai tausayinshi ya kamata, Dan matsawa kusa dashi tayi
"Sir kaje ka kwanta kan gado mana..." Ta fada mashi cikin sanyin murya, daga manyan idanuwanshi yayi ya kalleta,
"Am OK here.." Ya amsa mata har lokacin bai bar kallon taba, da sauri ta dauke kanta, don ba karamin kwarjini yayi mata ba, sauka downstairs tayi yabi bayanta da kallon "wannan yarinyan badai iya steps ba" ya fada yana murmushi.
Tana sauka taga babu tawa falo Sannan babu ita a bedroom kofan waje ta bude ta hangeta kasa kan grass carpet, wurin ta ta nufa, tawa na ganin ta taho ta mike zaune, karasawa tayi wurin ta ta zauna gefen ta suka fara hiransu abun gwanin ban shaawa.
Suna nan har lokacin sallan asar tayi tawa taje tayi ta dawo suka cigaba da hiransu, Salem jin shuru yayi yawa yasa ya leka ta window upstairs ya hangesu zaune suna, tsaya kallon su yayi for a moment Sannan ya sauko ya kasa, waje ya fito ya nufi inda suke, tawata fara daga kai ta kalleshi harara ya watsa mata ya dauke kanshi Sannan ya isa gefen da ameera ke zaune ya zauna gefen ta,
"Habibty how far?.." Ya tambayi ameera
"Fine..." Ta amsa mashi, tun nan wurin cikin tawa ya duri ruwa don sai ta tsinci zafi cikin ranta,
"Daman maza munafukai ne..." Ta fada cikin ranta, hira suka cigaba yi, amma Salem baiyiwa tawa magana saidai ameera, karfin hali tayi don ji take kaman tayi tsuntsu tabar wurin, daga karshe Salem kwantawa yayi nan kasa ya dauki hannun ameera ya Dora kan kirjinshi, amma duk abinda yakeyi idanuwanshi kan tawa don yaga yanda zatayi reacting.
Around 5:30 Mrs Samuel tazo don hada dinner, da sauri tawa ta mike
"Ina zuwa?.." Ya tambayeta sounding very formal, bata amsa mashi ba ta kalli ameera
"Sis bari inje in koyi sabon Abu..." Tafada tana murmushi,
"To let's go together..." Ameera ta fada tana kokarin mikewa,
"Stay with me please..." Salem ya fada mata idanuwanshi lumshe, ameera zama tayi tawa ta shiga ciki, ta barin wurin Salem ya saki hannun ta yana dariya, itama ameera dariya tayi
"Sir your wife is jealous.." Ta fada mashi
"Rabu daita...a hakan takeson kishiya..." Ya fada yana dariya sosai.
"You can go " ya fada mata Sannan itama ta mike ta shiga ciki.
Chapter 71 · 0% Book details