← Book details Tabarmar Kashi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 88

Sashe 85

Tabarmar Kashi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana matugar son asad da as'ad,duk sanda yazo Nigeria baya rabo da yaran.

Hannunta ta sanya ta shafi cikin nata tana mamakin ace juna biyu ne da ita, kuma har ana iya gani amma ita bata ankara ba?.

Shuru ta sakeyi tana wani tunani, kwanakin nan tana danjin motsi a mararta,amma saboda ba cikin nutsuwarta take sosai ba bata ma baiwa ranta komai ba.

"Yaaya another half zaiji?" Ta yiwa kanta tambayar,sal kuma wani abu ya ratsa zuciyarta.

Wanne toufeeq din?, toufeeq din da suke tafka rigima yau kusan sati guda kenan?, ko zuwanta bikinma ta taho ne da yawun maii kawai.

Kanta ta kwantar tana dubam fuskar
wayarta,tunda suka taho din ko sau daya bai nemeta ko ya kirata ba,yaransa ma a wayar fadeela suke gaisawa kamar baya qasar, bayan kuma yana nan
"Qila ma yana can suna waya da Hamdiyya" zuciyarta ta raya mata.

Ido ta runtse tana jin zafin iya tuna hakan da tayi,cikin ranta tana kiran sunayen Allah hadi da tuna maganganun da ya furta mata ranar da zata taho
"Kije abinki, ban hanaki ba, kome kikayi dai daine,tunda kin gama da zuciyata,kin kuma san soyayyar da nake miki,amma wallahi na gama yarda mace tayi amfani da soyayyar da nake mata ta wahalar da rayuwata, akwai masu sona dake da yawan gaske, zan qara aure na ne, kema kiyi abinda duk kikeso" hawaye ya sauko mata tasa gefan mayafinta ta daukeshi, ashe duk abinda akewa rigimar ma yana tare da ita su duka basu sani ba.

Sanda suka isa guri ya dauki harama sosai, tace yusuf ya riqe key din motar zata kirashi idan ta tashi tafiya,saita wuce ciki.

Batasan ya akayi ba tana shiga MC ya kama sunanta lokacin da aka kira ango da amarya,kwata kwata batayi niyyar hawa wajen ba,amma saboda ba yadda zatayi ta mige ta bude jakarta ta fidda rafas guda biyu na dubu daddaya sabbi qal a mige suna daukan idanu.

Liqi sosai takewa nadeeya da nadir,me ya cika gurin da kambamata da kiran sunanta saboda ganin yadda take barin kudi,farinciki da qaunar s
ahar ya sake lullube nadiya.

Cikin sabgar bikin tun daga kamawarta har zuwa yau da za'a gargare s
ahar din ita ta zame mata uwa kuma babbar yaaya.

Riqota taji anyi ta baya,ta waiwaya kadan sai taga fadeela
"Abby yana motarki yana kiranki" mamaki yadan kamata ta kauda wannan ta migawa fadeela sauran kudin tace ta liga musu,ta soma sauka daga step din a nutse, idanuwa suka sake yawa a kanta MC ya fara kwarara sagon godiya wanda har ya fita daga hall din bai daina zubata ba.

Dukka hannayensa biyu ya saka yana dafe steering motar yana lumshe idanunsa hadi da furzar da iska me zafi a bakinsa.

Har cikin tsakiyar zuciyarsa yakejin suya da zafin yadda bakin wani qato ke kiran sunan s
ahar din yana maimaitawa kamar shi va rada mata sunan, sosai yakejin zafi a zuciyarsa,yana cewa ya hanata zuwa gurin dinner din?, bama ta nadeeya ba, kowacce dinner idan ba tare suke ba, saboda shi kadai yasan abinda yake gani, Allah ya mata ajiyar wani irin kyau me sanyi da daukan hankali,irin kyan dake iya zamewa fitina ga mazaje idan ba'a hadu da mace mai kamun kai da miji mai kula ba.

Shi kansa kullum ta Allah ya sake ganinta yake kamar wata sabuwa a idanunsa.

Hana jan qofar ta bude, saita sake budeta sosai tana matsawa gaba zata shiga.

Fes ya bude idanunsa da suka canza launi a kanta vana kallonta
"Kata'i" ya samu kansa da furtawa,wani bacin rai yana sake lullubeshi saboda mahaukacin kyan da tayi,abu daya ya hana zuciyarsa gazawa,shigarta ta boye halittun jikinta sosai,saidai yau din tayi masa mahaukacin kyan da sai daya dauki mintuna yana dubanta kafin ya janye idonsa ya maida gaban motar yana jin kamar ya fashe da kukan takaici.

Me yasa ya biye mata sukayi fada har ta samu damar yin tafiye tafiyenta ita kadai?.

Fuskarta ta hade tsam kafin ta shiga motar bakinta dauke da sallama,har yanzu tana jin zafin cewa zai qara auren da yace zaiyi.

Maida murfin tayi ta rufe,bai waiwayo ba vace
"Waye ya baki izinin zuwa nan?"
"Maji ce" ta amsa masa kai tsaye tana jin zuciyarta tana mata zafi itama
"Mugullin motar ma itace tace ki bawa wani gardin ya kawoki?" Waiwayawa tayi da hanzari
"Yusuf dinne gardi?" Ta jefa masa tambayar tana ) dubansa, shima juyowa yayi yana dubanta
"(dan ba gardi bane mene?" Abinda ta gani a idonsa ya sanyata janye dubanta daga kansa ba tare da tace komai ba
"Soyayyarki da nake miki ce ta Sanya kika fara rainani ko?" Yayi mata tambayar da zafi zafinsa yana jiran amsarta.

"Wannan kwallivar da kika fita da ita wani gazami yana kiran sunanki ta mic shima duka maji dince tace kiyi?" Ya sake jefa mata tambayar.

Gaba daya taji ta diririce da tarin tambayoyinsa, ta rasa wacce amsar zata bashi,sai kawai ta fashe masa da kuka
"Ba aurenka zakayi ba?, kaje kayi,nima ka barni nayi rayuwata,dama ai ba sona kakeyi ba"
"Ni dake waye baison wani? 3yrs amma ana zancan haihuwa kina dojewa,kije ki zauna abunki zan dauko wadda zata yita haifamin yara, kuma zakisan da gaske nake" daga haka ya tayar da motar ya fusgeta cikin bacin rai suka haura kwalta.

Sai da yayi dai dai akan titi sannan ya sassauta gudun saboda yadda kukanta vake kassara jiki da zuciyarsa,amma ko akan fuska yaqi ya nuna hakan,bayaso ya bata wata qofa da zata gane lagonsa.

Har taci kukanta ta godewa Allah basu isa gida ba,bata fahimci yawo kadai suka dinga yi saman titi ba sai bayan da taga sun qara goma a hanyar kafin su dauki hanyar gida.

Sanda suka isa gidan ita ta fara fita a motar,sai bayan mintuna kusan goma ya rufe motar ya wuce ciki shima.

Dakinta ta wuce abinta,ta fidda kayan jikinta ta fada wanka tana ajiyar zuciyar kuka.

Karo na farko data fara kuka hankalinsa bai tashi ba bai kuma saurareta ba,abinda yayi matuqar sanyaya mata jiki kenan.

Koda ta gama wankan tsaye tayi gaban madubin bandakin daure da towel tana kallon kanta, idanunta ta sauke akan cikinta,kamar yasan shi take kalla wani motsi mai garfi ya ratsa ta qasan mararta.

Hannu ta saka ta dafe marar tana furta
"'Subhana man khalaqal Janeen fil arham" wani hawaye yana cika mata idanu.

Karkiyi missing last page
Zafafabiyar
"HUGUMA
TABARMAR KASHI_*
Book 02 Page 75
Tasbihi ta dinga yi ga ubangiji cikin ranta,komai na rayuwa yana da iyaka,hakanan duk abinda bawa yaga bai samu ba lokacinsa ne baiyi ba.

Cikin mutuwar iiki ta shirya ta haye gado, idanunta a rufe zuciyarta har yanzu babu dadi.

Sunayen Allah ta dinga ambata a hankali, har wani bacci me nauyi yayi awon gaba da ita:
Tunda suka shiga gidan ya wuce sassansa ya kasa nutsuwa cikin ransa,duk shirinsa zuwa kwanciyarsa kukanta ke masa amsa kuwwa a kunnensa, saidai duk da haka baiso ta gane lagonsa, da haka ya dake ya gama shirinsa.

Har va kwanta ya dinga juyi,sam bacci ya gauracewa idanunsa, kusan minti arba'in yana a haka.

Migewa yayi ya kunna wutar dakin ya sanya slippers dinsa ya dauki wayarsa ya fito.

A nutse ya isa sassanta hancinsa na shagar wannan daddadan gamshin da yake mugun tasiri, qamshin da bai taba jin makamancin sa a wani waje ba sai a sassanta sai kuma jikinta,qamshi ne na musamman da gurinta kawai yakejin irinsa
Shuru har ya isa gofar bedroom dinta, cikin jikinsa ya dinga jin kewar yaransa, da yanzun suna zaune a nan yana fama da rigimaru da fadace fadacensu.

Dim light ne kawai a dakin, ya saki gofar ya taka
zuwa ciki.

Daga gaban gadon ya tsaya,ya sanya hannu ya kunna side drawer lamp sai ya rage haskenta kadan ya jawo stool ya zauna gaban gadon.

Fes fuskarta ta bayyana cikin dan garamin hasken fitilar, innocent face din nan da yaga zallar kishinsa muraran a kwance a samanta, tuna hakan kadai ya sanya murmushi ya subuce masa,sai ya miga hannu ya shafi gefan fuskarta yana jin tausayinta kadan kadan yana ratsashi, ko yaushe qara kyau takeyi,sam shekarunta basa wani nunawa, idan kaga sa'ad da as'ad ba zaka ce itace ta haifesu ba sam.

Ya kusa awa guda zaune a wajen kafin ya miqe, a nutse ya gyara mata duvet dinta ya mayar mata da lallausan gashin ta baya ya kashe fitilar bayan yayi kissing dinta ya fito.

Yana matuqar son kasancewa cikin ilkinta a daren da ya fara busa wani yanayi na sanyi sanyi,amma kuma yana son ya zama taayayyen namiji,wanda so baya rufe masa idanu ya hanashi aiwatar da abinda ya dace.

Yana shirin komawa ya kwanta kiran maji ya shigo masa waya,ya zauna sosai sannan ya daga wayar
"Tare kuka fita da maami?" Kansa yadan shafa, s
ahar na vawan sakashi sauka a layi a cikin idanun maji
"Eh muna gida"
"Allah ya tashemu lafiya" ta fada a taqaice, don idan da sabo ta riga ta saba,musamman da ya zamana wannan zuwan da tayi din shi ba haka yaso ba,yafiso kullum tazo ne ta koma.

"Zakuci ganiyarku tunda kuka bar yaran nan sun dawo din kenan" ta fadi a hankali.

Hilma (wata cousin dinta)ta tabe baki
"Wai nikam maji ko kishi yaronki bakyayi?, duka yarinyar nan ta gama juya masa tunani? ba zuwa ne na farko ba,duk zuwan da nakeyi abinda na karanta kamar yarinyar nan ta gama dashi, ya zama kamar wani bita zai zai, ya sanya ayiya ajiye miki yara suna yawo, ya maidata kamar alihunsa ke kina zaune?" Wayar ta saka tana duban hilma baki bude
"Kinsan akan waye kike magana? to s
ahar ko kamata nayi tana zubawa moha maganin mallaka a abinci saidai na tayata juyawa,saboda nayi imanin ba mallakar da zata cutar da shi zatayi masa ba,babu suruka irin tawa kaf zamanin nan saidai tsakanin rabo don Allah karki sake magana makamancin haka akanta, inda kinsan me ta yiwa rayuwarmu mu duka da baki fadi haka ba" sanyi jikin hilma yayi, bata kuma sake cewa komai ba taja bakinta tayi shuru.

Washegari jikinta babu qwari ta tashi, amma a
daddafe ta shirya masa sassaugan breakfast ta koma daki ta kwanta.
Chapter 85 · 0% Book details