← Book details Tabarmar Kashi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 88

Sashe 43

Tabarmar Kashi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mamaki ya hanata motsawa, sai kuma yadda kunnuwanta suka jiye mata adadin qarfin bugun zuciyarsa da ya qaru matuqa, ala dole tayi luf tana jin bugun sosai cikin kunnuwanta,abinda zai shaida maka lallai yana cikin fushi
"'Baki yarda da gargadin dana yi miki ba?" Duk da zuciyarta ta qone sosai da kalar rungumar da ya yiwa s
ahar din wanda ita daya tasan gardinta da dadinta, da
kuma sirrin dake tattare da wannan ingarman girjin nasa
data jima tana kewa,ta kuma gaza samun
kwatankwacinsa acan inda take harin
"Babu me rabani da kai sai Allah moha..... you are mine
forever" cikin nutsuwa ya dauke kallonsa daga
kanta,yasa hannu daya ya jawowa s
ahar kujera ya
zaunar da ita a kai
"'Huta a nan" ya fada cikin kulawar da sai da Ameesha
taji kamar numfashinta zaiyi skipping na wasu daqiqu.

Tasan toufeeg ciki da bai fiye da kowa,soyayyarsa
kulawarsa da tsantsar iya ririta mace wani abune da ta
gama lalube daga gurin kaffff mazan data hadu dasu
bata samu wanda yake da koda rabin rabinsa baya
tattara abubuwa masu yawan da sai an tara maza dari
ba'a samu qwaya daya rak irinsa ba.

Wayar da ake kiran security kawai ya danna ya koma
ya tsaya kusa da s
ahar kamar wanda yake bata kariya
"Inason ka bani dama mu fahimei juna, nayi maka kuma
bayani mu yafewa juna na dawo na kula da 'yata" runtse
ido yayi,ju yayi kaman ta soka masa wuqa a qahon
zuciyarsa,har bayason ta furta fadeela diyarta ce.

Bazai iya bata yawun bakinsa ma a kanta ba sai yaja waya yayi kira zuwa wajen saima
"Come in" ya fada a kausashe yana ajjiye wayar saima da security uku suka shigo, mata biyu namiji daya
Migewa yayi sosai iyakar tsahonsa yana dubansu,hatta s
ahar satar kallonsa take ta qasan ido,yadda lokaci daya ya koma Muhammad toufeeq jarma din data sani farkon haduwarta dashi, kaman ba shine yanzun nan ya gama karyar da wuya da murya a gareta ba
"Who allowed that women to enter?" Kallon kallo aka fara a tsakaninsu,kowa yana tsoron magana yana kuma tsoron gaddarar yau ta fada kansa ta kora daga aiki, duk da cewa tunda ya dawo din ko ma'aikaci dava bai kora ba.

"We are sorry sir, don Allah, bamusan bakason ta shigo ba" daya daga cikin matan tayi qarfin halin fada zuciya a karye
"Take her outside, and daga yau,idan na sake ganin gilmawar fuskarta cikin kamfanin nan ku tabbatar kun rasa aikinku" yana kaiwa garshe suka cafketa su biyun,don kuwa ba zata jaza musu asara ba,don kaf fadin kano dama Nigeria basajin akwai company da zasu samu me dadin aiki da kuma albashi me tsoka wanda yayi kamanceceniya da kamfanin MT JARMA.

"Ni ka wulaganta haka?" Abinda ta iya fadi kenan saboda tuni suka garasa yin waje da ita.

Sai a sannan ya waiwayo ga saima ,wadda kallon idanunsa kadai ya sanyata taji kamar zata saki fitsari a wandonta
"You are fired" ya fada kansa tsaye.

Ya jima yanason rabuwa da zaman yarinyar cikin office dinsa,amma ya rasa da wanne irin laifi zai kamata,sai yanzun da wannan dalilin yazo.

"Nan din ba Bar bane ko club da zaki dinga barin mata anyhow suna shigo min,bayan kin sani tare muke aiki da iyalina a ciki" yayi mata bayanin yana juya baya ba tare dava dubeta ba.

Kuka ne ya hanata cewa komai, kawai saita juva da gudu gudu ta fice saboda ta gama tozarta tako ina a gaban idanun matar da take bala'in jin zafinta da tsananin kishinta,wanda ita sam saiman bata cikin damuwarta a rayuwa.

"HUGUMA*
"_TABARMAR KASHI_*
Book 02 Page 37
Yana jin qarar rufe gofar saima ya tako zuwa gaban saahar din, saman qafafunsa ya tsugunna vana dubanta da wannan zafin da har yanzu baibar saman fuskarsa da kuma zuciyarsa ba.

Kauda idanunta tayi daga kansa tana jin wata shakkarsa tana shigarta,scene din da ya gabatar yanzu a nan ya sake tabbatar mata har yanzu TOUFEEQ JARMA shine dai,a gareta ne kawai ya sauya.

Yatsunsa ya sanya ya dawo da fuskarta saitin tata fuskar, sai ta sake kau da kai,ya sake maido fuskar tata ta sake kawarwa,a karo na uku ya sake juyo da ita a zafafe sannan yace
"Idan kika sake juyamin qeya sai na miki hukuncin da na fahimci shi kikafi jin toro,idan baki wasa ba saidai a kawo wheel chair a daukeki, kada ki manta ina da sofas masu taushi a resting room" izzarta ce ta motsa,ya akayi ta bari ya karanci ta tsorata da abinda yayi mata?.

So take ta gaggaya masa magana, amma ta sani daga qarshe yamutsatan da batason yayi shi zai aikata mata
"Na kusa kawo qarshen komai" ta fada qasan ranta a fili kuma tana hade rai
"Wayonki da tsiwarki dukka yau na rainasu, saboda baki kishina saiki bar duk wata karya da godiya su dinga tunkarar mijinki gaba gadi ko 'yar shakkarki basa ji saboda sunsan lusara ce MATAR TOUFEEQ?" Da gayya ya kira mata lusarar saboda ta motsa wani abu dake danqare a zuciyarta,yaci nasara kuwa,don take bacin rai ya bayyana
"Ko ba komai ya kamata su dinga jin shakkar tunkarata
haka kai tsaye saboda KE"
"'Ina ruwana da abinda ya shafi rayuwarka?,rayuwarka
daban tawa daban,ka taba ganin anyi kishin abinda ba'a so?, ba'a kuma damu da shi ba?" Ta fada itama gaba gadi.

Murmushi ya saki karon farko shima zuciyarsa a yau ta dandana dacin kalmar RASHIN SO da kuma QIYAYYA.

Kai ya girgiza
"Tashi mu tafi gida" ya furta yans miqewa tare da ja baya ba tare saya sake bi ta kanta ba.

Ranta a quntace itama ta tashi tana jin haushin maganar da ya gaya mata, bataso yabar zancan iya haka ba,sai gashi yayi kamar komai bai faru ba.

Baice mata ci kanki ba a mota har suka dauko fadeela suka wuce gida yana jinsu sunata sabgarsu,bai ce musu komai ba kuma bai hanasu ba.

Yau din sun koma da wuri, yana zaune a motar yana kallonsu har suka qule a sassansu fadeelan, kai ya jinjina
"Zanyi maganinki" ya fadi qasa qasa, kafin ya kashe motar,ya barwa jibril key din a jiki ya fito yana cewa
"Kada kayi nisa,zamu sake fita kaman nan da one hour"
"Okay sir" ya fada cikin girmamawa.

Falon wayam,har yanzu Jacob bai dawo ba, hakanan har yanzu bashi da tsayayyen gurin cin abinci.

Bai tsaya dogon nazari ba ya wuce bedroom dinsa,don yana matuqar bugatar ganin Dr jarma a yau din,don a gobe yace masa zaiyi tafiya,morning flight zaibi, dukbda dai har yanzu bai gaya masa inda zashi ba, kusan kuma basu saba hakan dashi ba, shima bai matsa da tambaya ba, kasancewarsa mutum ba me bun qwaqwafi ba yasan idan ya dace yaji tabbas zai gaya masa.

Ya fara zare kayansa, idanunsa suna bisa gadon Duk lokacin da ya kalli gadon babu abinda yake tuna masa sai wancan moment din, wani abu guda daya da ya tsaye masa a rai, ya kuma kasa mantawa, abinda duk sanda ya tuna sai yaji ilahirin tsigar jikinsa ta tashi, ko me vakevi kuwa.

Wani qaramin murmushi ya subuce masa lokacin da ya tuna da sauran abubuwan da suka faru,gaba daya bata da wayo sam ta irin wannan bangarorin, autar ce da gaske
"Akwai tsiwa,sai tsoro" ya furta gasa gasa, ya dan kada kai yana jin buqatuwar kasancewa da ita na mamayarsa.

Abinda ya farun ya zama kamar ta lasa masa zuma me azabar zaqi ne a bakinsa, kwana biyu rak amma ji yake kamar ya shekara rabonsa da ita, laluben rigimar da zai jawo kawai yakeyi wadda zata bashi dama ya sake kutsawa zuwa wannan alfarmar tata da yake fatan ya dawwama har abada a cikinta.

A gurguje ya shirya bayan ya fito, cikin wani yadi me azabar kyau da daukar idanu sky blue,yana da taushi da kuma qarancin kauri, jikinsa sai fitar da qamshi yakeyi me dadi, saidai kuma cikinsa wayam yake yunwa yakeji amma ya bari idan sun fita ya laluba gidan abingi me kyau yayi takeaway.

Half cover me kyau ya zubawa gafansa ya dauki wayarsa dake tsuwwa yana duba me kiran.

Sajjad ne,ya kara wayar a kunnensa yana ficewa.

Har yayi gaba ya tuna yanason magana da nadeeya, don haka ya koma da baya ya shigal sashen.

A parlor ya samu nadeeyan tana kallo,gefenta bowl ne da aka yayyanka kankana ayaba da madara,sai abun sugar dake ajjiye ba'a kai ga zubawa ba.

"Ina zuwa" yace da sajjad yana sauke wavar idanunsa akan bowl din sanda take gaidashi
"Wannan fa?"
"Aunty N ce ta hada zata sha, fadeela ta tasheta kitchen wai tayi mata veggies couscous" a nutse ya koma ya zauna,ya dauki bowl din ya fara juyawa
"Kun zuba sugar ne?" Kai ta girgiza
"Bata saka ba" bismillah yayi ya fara sha, gardin madara dana fruit din dake ciki suka gauraye harshensa,sannu sannu sai gashi ya gama da shi gaba daya ya ajjiye bowl din tare da nufar kitchen din, gamshin da yajeji a ciki yana jan hankalinsa.

Tsaye take gaban gas ta bawa gofa baya,sanye take da wata farar gown cotton me hannun vest, iyakar gown din qaurinta,saidai ta fidda shape dinta qwarai,ko a inda yake tsaye yana hangenta,yana iya gain faffadan qugunta da ya zamu ado da tsayayyun mazaunai.

Ido ya lumshe vanayin jikinsa ya fara canzawa, qwaqwalwarsa na tuna masa maganar was abokan sajjad
"Mace me qugu da hips duniya ce, ai tayi alaji" ya yarda da hakan dari bisa dari, a yanzun ya zama shaida akan hakan.

Amma muddin maza suna iya banbance irin wadan nan halittun daga wajen mata bayan ba matansu bane na aure, to ya zame masa dole yayi dukkan me yiwuwa ya bata dukkan tsaro da kariya fiye da yada zai bawa duk wani abu nasa kariya, domin shi yasan me yaji a jikinsa,me kuma ya gani yake kan ganin.

Qamshinsa kawai ta shaqa ta tabbatar yana gurin, amma saboda tana kokwanto sai tayi kaman tana gyara jelar gashinta dake fake tsakiyar kanta ta kalli gefanta.

Yana tsaye yana kallonsu, fadeela take zubawa abinci,sai ta maze kamar bata ganshi ba,ta kammala zubawa fadeelan ta miga mata,sai ta kwasa da gudu tana ficewa.

Maida spoon din tayi cikin tukunyar tana niyyar rufewa.
Chapter 43 · 0% Book details