← Book details Tabarmar Kashi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 88

Sashe 2

Tabarmar Kashi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abu mafi razani dake jijiga zuciyarta,kaddarar auren adam me daci ce da hallaka dukkan buri da gusar da fata ko sha'awar ci gaba da rayuwa ta aure dama ta duniya gaba daya..
...ita kuma qaddarar auren mahmud fa? yaya zata zo mata?.

Tambayar kenan dake barazanar fasa mata zuciya a duk sanda tazo kanta.

Ta sani cewa saidai suyi zaman haquri ita da mahmud kawai,amma babu ta yadda za'ayi ya samu yadda yakeso daga gurinta,ta gaya masa wannan ta sake nanata masa,ya shaida masa yes......a shirye yake yayi haquri da ita ya kuna zauna da ita koma a yaya ne.

Wani sashe a zuciyarta kowacce rana nana ya mata cewa JINSIN MAOARYATA
NE,JINSIN MAHA'NTA NE,duk abinda suka gaya maka bashi kake tararwa ba bayan aure,yaudara da cin amana da karya alqawari sun lullube zukata da harsunansu, bata tunanin akwai wata kalma ta soyayya da jan hankali, nuna zallar kulawa da rayuwa yare har bayan mutuwa wadda adam bai furta mata ba,amma yaya sakamakon hakan ya kasance?.

To auren me zatayi?

AUREN BIYAYYA kenan ko me? tunda dai ita din batakai lokacin da za'a ce tayi auren kai buta da ruwan wanka bandaki ba.

Tsakiyar wanann tunanin wayarta tayi burari,ta waiwaya a nutse tana duban me kiran,zuciyarta na gaya mata mahmud ne, wanda zuwa yanzu ta fara tsanarsa tare da tsanar komai daya shafeshi, yana yaiwata kiranta da sunan caring,caring din da ita kuma bata sonshi, don duk abinda yayi sai taga kamar yana bin footprint na adam ne.

Mamaki yadan kamata gain sunan nadeeya.

Bawai bata kiranta ba,a'ah,tun daga randa ta baro gidan,har tayi kwanaki bakwai babu ranar da bzata fito ta fadi bata kirata ba tana roqonta akan ya dawo.

Randa tayi alqawarin ba zata sake kiranta ba tayi fushi ne saboda ta tabbatar mata ba zata dawo ba,suyi haquri ta kula da fadeela,tun daga ranar bata sake kiranta din ba,saidai kullum zata bar mata good morning massage through watsapp dinta.

Wugar hannunta ta ajjiye ta miga hannu ta dauki wayar,ta daga kiran ta karashi a kunnenta.

Gabanta yayi mummunar faduwa jin sautin kukan nadeeya,tayi saurin kama sunan
Allah sannan ta samu qwari gwiwar tambaya
"Sister nadeeya,me ya faru?"
"Fadeela ce.

" Sai kuma maganar tata ta
tsaya,abinda ya haddasawa s
ahar wani irin muguwar faduwar gaba,ta sake kiran sunayen
Allah
"Karki cemin wani mummunan abu ya faru da ita"
*HUGUMA*
* TABARMAR KASHI_*6
Book 02 Page 02
"Ke da mahaifinta dama ba burinku kenan ba? vanzu haka tana asibiti, kuma ko meye ya faru da ita kune ke da alhakin hakan" daga haka ta katse wayar,tabar s
ahar da waya a hannu.

"Gaskiya ta fada,meye laifin yarinya da zaku shiga rayuwarta ku gigita mata ita?,rana daya saboda baki shiri da mahaifinta ya birkitaki ke kuma ki tattaro ki bar yarinya kwatsam?"
"Bai isa ya birkitani ba,baida wannan qarfin ikon,abinda na sani kawai bazan taba iya rayuwa dashi a muhalli daya ba muna shagar iska daya
"'I dan kukayi kisan kai ai ku kuka sani" afifa ta fada cikin jin haushi tana migewa a wajen.

Maganar Allah itama zuwa yanzun haushinsu takeji,kamar masu ganin hanjin juna? babu dama su hadi guri guda sai kowa ya hau tashi kamar kububuwa?.

Tun daga lokacin da nadeeya ta kirata har zuwa wayewar gari ta gaza moruwa gaba daya, lokaci lokaci sai ta samu kanta da duba wayarta,tanason kiran nadeeyan amma kuma batason tayi abinda zai sanya zuciyarta karyewa.

Ko a daren jiya baccinta rabi da rabi ne,iya baccin data samu yi din cike yake da mafarkan fadeela na koke koke,abinda ya hadu kenan yayi mata rubdugu ya kassara duk wani walwala da karsashinta.

Don ko da safe kwance tayi a daki,ta kasa fita ko ina.

Ba abinda takeson gani a wannan lokacin irin fuskar fadeela,ta rungume yarinyar a jikinta kamar yadda suka saba,to amma kuma ta yaya?,batason cin fuska da cin zarafi don haka ya zama dole komai wuya komai daci ta nisanci dukan abinda yake da jibi da MT JARMA.

Zuwa la'asar juriyarta da dukka
haqurinta ya qare,wunin daki tayi ita kadai afifa yau tana asibiti gaba daya,ta kalli agogo,biyar saura,lokaci irin wannan lokaci ne nayin karatunsu ita da fadeela,ko ya halin karatunta ya shiga ciki?,duk yadda taso ta jure sai da qwalla ta cika idanunta,saboda ta tuna algawarin da tayi mata na har ta gama exam tare zasuyi karatun,to saura guda biyu ta kammala ta baro gidan,batasan waye ya tallafeta sukayi karatun biyun da sukayi saura ba.

Batasan ya akayi ba sai kawai ta samu kanta da laluben number nadeeya cikin jerin calls dinta na yau,ta danna number tayi dialing.

Hannunsa zube a aljihun silky trouser dinsa daya dace da short sleeve shirt din dake jikinsa,yana takawa a nutse tamkar saboda shi daya akayi hanyar da zata sadaka da dakunan AMENITY na asibitin.

Manyan dakuna dake dauke da dukkan wasu kayan buqata tamkar kana gidanka.

Ko baka sanshi ba kalli fuskarsa kasan wani kwantaccen fushi ne zalla a samanta,saidai tarin nutsuwar da yake da ita data cakude da miskilancinsa ya sanya ba lallai ka lura da hakan ba kai tsaye.

Babu abinda ke amsa kuwwa a kunnensa sai bayanan Dr anwar,wanda yake jaddada masa dole ya kiyaye yasan meye asalin abinda ya sanya fadeela a wanann mummunar damuwar,dole ne yayi qoqarin sama mata abinda zai sanya hankalinta kwanciya ya dawo da ita walwalarta,ko don lalurar da take da ita, wadda ta ragu sosai fiye da baya.

Shi kansa dr anwar mantawa yakeyi wani lokaci da lalurar tata,saboda komawa baya da takeyi tana raguwa da kadan da kadan a yan watannin da s
ahar din ta kasance da ita.

Idan yayi zuzzurfan tunani hakan yana nufin babu makawa sai ta dawo cikin rayuwarsu?,kenan tayi galaba dukka shirinta yayi tasiri kenan?,sai ya furzar da iska me zafi daga bakinsa,ransa yana gonewa,yana jin wani irin zafin yarinyar a ransa.

Daga ranar da ya shata layi tsakaninsa da kowacce diya mace,babu macen data sake shigowa rayuwarsa tayi masa wannan karan tsayen sai ita.

Dai dai sanda ya isa gofar dakin,ya sanya hannu ya murda handle din ya bude,saidai kafin yakai ga shiga yaji sautin siririyar muryar fadeela da ko yaushe bata rabuwa da kuka tana kiran sunan
"AUNTY N,don Allah ki dawo, Allah bazan zauna ba nima idan baki dawo ba,kinmin alqawari amma shine baki cika ba? kullum kuka nakeyi,amma abby yace bazanzo ba,a nan zan zauna,kema kiyi zamanki".

Dukkansu ita da nadeeya basuga shigowarsa ba,bare baaba ramatu dake sallah saman abun sallah.

Kai tsaye ya sanya hannu ya zare wayar dake magale a kunnen fadeela,ya juya a nutse yana fita a dakin,ransa na zafi.

"Hello..
...hello,nadeee" sautin lallausar
muryarta ya sauka a kunnensa lokacin da yake magala wayar a kunnensa,ya lumshe ido yana jin tsanar
"Nawa kike da bugatar a biyaki ki dawo cikin ravuwar da kika riga kika shigeta cikin shirin faruwar hakan?" Cak komai ya tsaye mata,cikin mamaki ta kalli number,ta sake tabbatarwa number nadeeya ce,don dama ita din bata taba ajiyar number dinsa a wayarta ba,saita sauke wayar daga kunnenta kawai ta katse kiran,saboda bata jin zata iya tsaiwa ta saurareshi.

Komawa tayi ta lafe a gado,zuciyarta na wani bugawa a jejjere,kwata kwata ta manta da sautin murvarsa cikin kwanyarta,don bata sake iinta ba sai a yau din.

Idanunta ta mayar ta kulle,sautika biyu na tsalle tsakanin qirjinta da kunnuwanta,sautin innocent fadeela,da kuma sautin deep and husky voice dinsa.

Labbansa na qasa ya cije lokacin da ya fahimci ta kashe masa waya ne,abinda yafi tsana kenan a rayuwarsa,sai ya sake tunzura ya kuma dannawa number din nata kira.

Karar wayarta a karo na biyu ya
sanyata bude idanunta,ta kalli wayar,kamar ba zata daga ba sai kuma taga nadeeya dince,ta dannan Koren shudi ta sanya kiran a handsfree
"Muddin kika sake kashemin waya sai na baki mamaki,don har cikin gidanku zan iskeki,nace nawa kikeso a biyaki ki dawo bakin aikinki?"
Yayi maganar cike da wata izza da gasaita.

Tunawa tayi da matsayinta a rayuwa,da kima da kuma darajarta ta diya mace,wannan ya bata qwarin gwiwa,ta mige ta zauna sosai saman gadonta
"Bazan dawo ba!" Ta gaya masa kanta tsaye,ta kuma dakata tana jiran abinda zaya fadi.

Har tsakiyar kansa yaji saukar muryar tata da kalaman da suke nuna rashin toro ko daga gafa
"Dole ki dawo,ki qarasa abinda kika fara shiryawa,dole ki dawo inason naga iya gudun ruwanki na kuma qurewa wasanki gudu donki tabbatar da banbamcin dake tsakaninmu" ya fadu a zafafe.

Katse wayar kawai tayi saboda yadda deep voice dinsa ke shiga kanta sosai,tana ratsa jijiyoyin jikinta tana jin kamar yana a cikin dakinne.

Ba iya katse kiran ta tsaya ba,gaba daya wayarma ta kashe,ta koma ta kwanta rub da ciki idanunta a lumshe,muryarsa naci gaba da yawo a kanta.

Abu guda daya data sake amincewa dashi,yana da izza izgili da girman kai,ta fahimci akwai damuwa sosai cikin muryarsa, damuwar kuma bata rasa nasaba da ciwon fadeela daya sanyasu dukka a damuwaryanaso ne ta dawo taci gaba da kula da fadeelan duk da ransa baiso hakan ba.amma shi baisan hanyar da zai lallaba mutumin da yake neman abu a gurinsa ba,a haka zata koma? kai koda da sigar lallashi yazo mata bata jin zata koma,bare a yadda yazo mata cikin izza da gadara,sai ta gyara kwanciyarta ranta na turereniyar abubuwa guda biyu,tausayin fadeela da kuma takaicin kalamansa.

Hannayensa ya yarfar,nadamar karbar kiran dayi mata tayin dawowa na lullubeshi,tunda yake babu wani mahaluki daya taba masa abinda tayi masan, ji yayi kamar yayi jifa da wayar,ya juya wayar a hankali yana qare mata kallo
"Ta yimin dai dai, kuma haka shike nuna baka shirya samarwa 'yarka lafiya ba" sautin murvar Dr jarma ya ratsa kunnuwansa.

Da sauri ya waiwaya bayansa yana duban mahaifin nasa,sam baiyi zato ko tsammanin ganinsa a gurin ba,tunda ma tun wancan satin sukayi sallama dashi ya tafi china,kuma a galla zai kwashe wata guda bai dawo ba.

Rusunawa yayi ya rage tsahonsa
"Barka da warhaka"
"Aikai za'a yiwa barka muhammadu" daga furta hakan da yayi sai ya juya kawai ba tare da yace dashi komai ba.
Chapter 2 · 0% Book details