Sashe 50
Tabarmar Kashi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ranar data isa gidan Mahmud da takardar shaidar saki a ranar baiwar Allah shifa na cikin farinciki,karon farko tun bayan karayar arziqinsa ya sake siyan mota,a lokacin yace ta dinga hawa tana hidimar gida,kai yara makaranta da daukosu,da sauran abinda ba'a rasa ba,idan ta kama kuma shima zai karba ya hau ya fita sabgoginsa,kafin ya samu damar siya mata tata.
Sallamar fauziyya kadai a gidan janye da meenal da faggon kaya ya sanya maji cikin matsanancin faduwar gaba,tana fadin cewa sakinta yayi maji ta samu ta daddafa kuiera ta zauna a kai cikin zucivarta tana ian
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" yadda takeji cikin ranta da jikinta a sannan tamkar ita aka saka ba fauziyya ba.
Zaman dai bai sauya zani ba,saima canza salo da fauziyyan tayi, cikin salon wata hikima da iya taku take tatsar kudi daga hannun Mahmud, adadin kudin da ko ita maji wadda ita tasha wahalar kusan komai kawo yanzu bata samesu ba daga jikinsa.
Tunda majin ta qyalla idanu ta fuskanci mugun shiru fauziyya ta yi, wanda ya ninka na baya,saboda ayanzun ta samu makiran qawaye gwanaye iya bin malaman tsubbu, sai ta hana kanta sakat da addu'a ba dare ba rana,wanann ya sakawa majin qarfin zuciya da ruhi,duk wani kalar iskanci da fauziyya tayi mata awancan zaman wanna karon ko daya bata dauka ba,wanann ya kawo gagarumin sabani tsakaninta da mahmud, saboda muddin kanason kaga tashin hankalinsa ka taba fauziyya da 'yar lelenta meenal.
Yarinyar Allah ya zuba mata rashin ji na tsiya,zuwansu ba dadewa amma ta fashe duk wani kayan ado da alatu na falon gidan.
Lokaci galilan kuma ta fiddo dabi' ar tara mata qawaye a gidan,sabbin qawaye irinta,wadanda suka bawa duniya amana da dukkan qauna,suka kuma riqeta da kyau,wasu 'yammata ne wasu kuma zawarawa ne kamarta,cikinsu kuma akwai MANSURA wadda tafi kowa zagewa tare da rawar kai.
Da farko falonta ake zuwa a baje,fauziyya ta shiga kitchen cikin taqamarta da jin izza harda yin gayyata ta bare duk abinda takeso tayi musu abincin wadata da alfarma,su bata ko ina a kuma fice abata guri a barta da aiki.
Idanunta maji ta rufe, cikin tsayayyar nan tata da dakewa randa suka cika sati guda suna mata tayi musu tasss daga fauziyyan har qawayen,kai fauziyya ta jinjina
"Zakiyi nadama" kamar yadda ta furta kuwa daren ranar majin bata samu cikakken bacci ba,saboda mugun tashin hankalin data haddasa tsakaninta da mahmud,ya gaggaya mata maganganu masu zafi da gori wanda tunda sukayi aure bai taba gaya mata irinsu ba.
Ta kwana tana kuka tana kuma gayawa Allah,da safe kuma tayi qoqarin ta tashi kamar komai bai faru ba, abu daya ta sani, ko zasu dawwama suna rikici da Mahmud, ba zata. dauki wasu bagin halayen cin fuska na fauziyya ba,ba ita kadai bama,ace har gawayenta suna da power din shiga mata kitchen suyi yadda sukeso?, bazai yiwu ba, inda ita daya ce zata iya kau da kai, saboda kau da kai da haquri ta sani su kadai ne suka kawota warhaka gidan.
Ba'a jima da gama wannan ba tana zaune da wani yammaci tana gyarawa su toufeeq farce fauziyya ta shigo,tanata baza qamshi hade da taunar chewing gum, tunda taji hayaniyar tarkacen qawayenta na banza marasa da'a ta hada kan yaranta cikin falonta suka zauna a nan
"Key zaki bani" a nutse ta daga kai ta kalleta
"Key na me fa?"
"Na motar yaya na,zan fita unguwa,wani ma yayi rawa bare dan makadi, a bani na mori arziqin dan uwana ko kuma rai ya baci" bacin rai ne ya tasowa maji,yadda take mata magana a tsaitsaye saman kanta,sai ya maida dubanta ga aikin da takeyi
"Bazan bayar ba,rai kuma ya dade bai baci ba,idan kuma kina da qarfin qwata saiki danne ni ki karba"
"Abu me sauqi, kamar qofar dakin naki baqona ne" ta furta tana takawa zuwa hanyar bedroom dinta.
Tsam maji ta mige ta kuma daka mata tsawa
"Ke fauziyya!, dakata,kikayi kuskuren shigamin daki wallahi saikin gane sakarya ce ke,ina da kaidi da kuma tuggun da yafi naki ninkin baninkin,saidai kawai banbanci na dake ni din ba jahila bace,nasan sakamakon dake iya biyo bayan aiwatar da sharri tuggu da kuma makirci" tsaiwa tai tana duban idanun maji,ta rasa meye a tattare da matar da har yanzu ta kasa juyuwa a gareta kamar yadda take juya yayanta? ita kadai ce yanzu matsalarta
*HUGUMA*
*_TABARMAR KASHI *
Book 02 Page 43
"Zaki bayar ko sai nasa an karbarmin?" Murmushin takaici maii ta sauke
"Har abada ba zaki taba cin galaba a kaina ba fauziyya,yadda baki taba karbar abu a hannuna gaba gadi ba saidai kisa a karbarmiki, har abada a haka zaki qare, ni maji bazan taba sallamamiki komai nawa hannu da hannu ba,saidai kisa na gaba dake din ya karbar miki,zoki wuce ki fitamin a daki" maji ta fada cikin zafinta,abubuwan da fauziyya ke mata tana kau da kai tana tarasu cikin haquri irin nata yau suna taso mata.
Ganin ta tsaya zata bata mata lokaci sai kawai tasa hannu ta fincikota baya ta watsata waje ta maida gofar falonta ta rufe.
A sanyaye ta koma gasan carfet ta
zauna,gabanta na tsananta faduwa,batayi dana sanin abinda ta yiwa fauziyya ba,amma yau tabbas ba shakka tasan abinda zai biyo baya a gidan bame dadi bane, wannan ya sanya ta tattara ta gama yanke musu farcen da wuri,ta hadasu sukayi sallar magariba duk da nadeeya dama shi kansa toufeeq din basukai wannan munzalin ba amma ta soma horas da su,saboda haka kawai cikin jikinta takejin ba zatayi dogon zama dasu ba,ta basu abincin dare sukaci ta kaisu dakinsu ta kunna musu cartoon a tv din dake dakinsu tace idan sun gama kalla suyi bacci,sannan ta dawo ta zauna a falo.
Ko minti talatin ba'a cika ba taji shigowarsa gidan,ta runtse idanunta saboda yadda gabanta ke duka tana kiran sunayen Allah tare da jan addu'o'in
"Allahummakhfinihim bima shi' ita,inna kafainakal mustahzi'een,ya rabbi innalqaumas tad'afuni, wa khadu yaqtulunany fala tushmit biyal'a'ada'a wala taj'alni ma'al gaumizzalimin" a hankali ta dinga maimaitasu qasan ranta idanunta a runtse har zuwa sanda taji ya bankado gofar.
Tana bude idanunta ya fada cikin nasa,a hankali yaji wani abu ya dakeshi, kaifin bala'i da masifar da yakeji suna tafasa cikin ransa sai yaji suna raguwa.
Ci gaba tayi da kafeshi da idanu,yayin da fauziyya da idanunta sukayi luhu luhu na kuka wadda ke tsaye a bayansa tace
"Muje yaya" ganin ya tsaya bai shiga ba bai fita ba.
"Sannu da zuwa" maji ta furta a sanyaye, baice mata komai ba sai hannu da ya miqa mata
"Bani key din motata" idanu suka hada da fauziyya,saita saki murmushi,batace komai ba ta miqe tsam,ta shiga dakinta ta fito dashi ta miqa masa.
Juyawa yayi ya miqawa fauziyya
"Ki riqe a hannunki ki dinga hawa,duk lokacin da ni nake da buqata na dinga amsa daga hannun naki,jeki" sanyaya gwiwar fauziyya din tayi, ba haka taso ba,so tayi yayi mata irin cin mutuncin da ya saba yi mata a gabanta,ya wulaqantata ya fifita darajarta akan tata.
Juya key din tayi a hannunta sannan ta juya ta fice shi kuma yazo zai wuce cikin dakin nasa ba tare da ya sake bi takan maji ba.
Kasa motsawa tayi tana zaune a gurin har ya gama abinda zaiyi ya fito,ya buqaci abinci ta zuba masa,yayi kiran shalelen tasa tazo suci abinci yadda suka saba tace ai ta fita dana mota.
Maji na zaune tana nazarin rayuwa,me gobensu zata haifar ita da mahmud da irin wannan makauniyar rayuwar dake wakana a tsakaninsu.
A daren bayan sun gama shirin kwanciya ta sameshi cikin kwantar da kai take tambayarsa abinda vake damunsa tare da shawarar yayi gogari ya daidata gidansa
"'Ni ba abinda yake damuna, hankalina yana tashi idan fauziyya bata cikin walwala, raina yan baci idan nata ran ya baci saboda ba abinda nake tunawa sai amanarta da mahaifiyata ta barmin" yadda yake maganar kadai ya sake tabbatarwa da maji lallai abub yayi girma ya wuce duk inda ake zato,daga wannan lokacin ta sanya idanu kan fauziyya fiye da baya,babu jimawa kuma ta fahimci irin aikin asirin da takeyi akan yayan nata kuma miji ga maji din.
Randa ta karanci hakan ta samu fauziyyan na zuba wasu abubuwa cikin abincin Mahmud din maji tayi ram da hannunta tana kallonta
"Kin ganowa kanki ranar barinki gidan nan sakarmin hannuna" ta fada kanta tsaye bacin rai ya hana maji magana, wacce iriyar baqar masifa ce haka?,duka duka shekarunsu dava da fauziyya har yanzu babu wanda ya rufa shekara arba'in, gaba daya ba zasu wuce talatin da bivar ba amma ta zama wata bagar masifa?.
"Kinyi asara wallahi,sannan bana danasanin barina gidan nan saboda nayi imani duk sanda hakan ta faru cikin qaddarata yake,ke baki isa ki zanamin gaddarata ba".
Tun daga wannan ranar fauziyyan ta dauki damara,saboda ta sani maji din nada wani irin kariva da take hana asiri cimmata nan da nan, kuma tasan hakan baya rasa nasaba da yawan addu'a da azumin nafila da bata rabo dashi.
* MAMAYA *
Tun daga wancan lokacin da ta kama fauziyyan take kaf kaf da abincinsu su duka cikin gidan, don tayi imani ba abinda fauziyyan ba zata iya aikatawa ba.
Ranar da ta zama baqar rana a gareta, ranar data shiga tarihin rayuwarta,ranar da ba zata taba mancewa da ita ba,ranar kuma data zama mafarin zanen dukkan qaddarorin da suka wanzu a rayuwarta dana iyalinta.
A wani yammaci liqis wanda kadan ya rage magariba ta kunno kai,ta gama abincin dare cikin galabaita saboda yadda qamshin girkin yake damunta yana hautsina mata kayan ciki, yanayi ne dakan faru da ita a duk lokacin da take da qaramin ciki,ko a yanxun tana tsammanin cikinne saidai haka kawai ta kasa gwadawa bare ta tabbatar, saboda yanayin da take ciki wanda zaiyi wuya ta samu nutsuwa ta kwana uku cikin gidan fauziyya bata sakata a masifa ba,abinda yake dakushe kaifin abun wanda a yanzu sukanyi sati daya har zuwa biyu lafiya lafiya shine addu'ar data tashi tsaye tana yi, ba dare ba rana.