← Book details Tabarmar Kashi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 88

Sashe 66

Tabarmar Kashi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har zai fita ya dawo ya yanka mata zazzafan warning
"Koda wasa wani abu ya samu cikina,na rantse da ubangijin sammai da qassai sai nayi miki daurin da koda dukka qasarnan gatanki ne basu isa su karbeki ba".

Al'amarin ba qaramin farantawa haiiya garama yayi ba
"Ai duk mutumin daka ganshi a waje nan ne yafi dacewa da shi shi yasa Allah ya barshi a nan, ai duk inda talaka yake matsiyaci ne(ita ta manta tushenta),ni dama tunda naga idonta Muhammad nasan ba son Allah da ma'aiki takeyi maka ba,dukiyarka take so".

Baice mata komai ba,saboda shi kadai yasan yanayin da yake ciki.

Yayi tsammanin so guda daya ne tak!, ya dauka so na gaskiya shine so,wanda babu wani abu da yake iya canzashi, bai taba dauka akwai randa ameesha zata iya neman saki daga hannunsa ba saboda kawai raguwar abun duniya daga hannunsa, bayan bai gaza mata ta fannin ci sha suttura ko lafiyarta ba har a lokacin kuma.

Duniya ta yiwa
/ hajiya garama dadi, dama wani mugun tsana ta yiwa ameeshan,ko kusa ko alama bata gaunarta,don ko sau daya babu jituwa a tsakaninsu.

Sosai hankalin mamarta ya tashi, tayi kuka tayi fadan amma ameesha tayi kunnen uwae shegu,a sannan tayi wani irin kyau ta sake zama mace me aji ta kuma sake sanin cewa ita din matar manya ce duk ta silar auren toufeeq,ta samu sutturu masu aji, ta kuma sake smaun wayewar da take hangen doguwar shimfidaddiyar rayuwa data dara ta gidan toufeeq.yanzu abu daya ne zai zame mata cikas cikin da take dauke dashi,a galla akwai wasu watanni masu yawa a gabanta kafin ta haife ta kuma yaye,ita a yanzun koda haihuwarsa ta samu tayi, komai da zai biyo baya me sauqi ne.

Warning din da toufeeg ya karta mata shine abu guda daya da zai hanata juye cikin.

Ta sani su din ba qananun mutane bane don dai kawai toufeeq din yana daukan kansa ba'a kowa ba, danginta kuma basa da garfin karawa dashi,so haquri ya zame mata dole kenan.

A zahiri tana son toufeeg sosai amma rayuwar data tsarawa kanta ta fuskanci ta sha banban datasa rayuwar da ya tsara,dole to ta ajiye nasa tsarin don cikar nata tsari da burin.

Allah me musanyawa bawan da ya dogara dashi daga mummuna zuwa abu mafi kyau cikin rayuwarsa.

Wata guda kacal da rabuwarsa da ameesha wani Erin
1 gofofin alkhairi suka dinga bude masa ta kowacce fuska.wasu alkhairan shi kansa bai taba tsammanin samunsu ba a irin wannan lokacin.

Lokaci qalilan ya maida ninkin abinda ya rasa harda ma ninkin abinda ya rasa din a baya.

Cikin wata hudu kacal duk wanda ya kalleshi yasan ya samu sauyi na rayuwa fiye da rayuwarsa ta baya,ya warware sosai yaci gaba da harkokinsa,sabbin hanyoyin neman kudi suka bude masa fiye da zato.

Har a lokacin yana lissafe da watannin cikinsa dake jikin ameesha,kowanne wata yana aika mata da komai da yasan zata bugata, dai dai da ruwan sha na roba haka yake ajiye mata, komai na watanni biyu yake ajewa ninkin abinda zata bugata kenan, hakan baya hanashi sake aika mata da wani bayan kowanne wata.

Mamanta naso gwarai ta ganshi amma bata samu wannan damar ba, saboda bata da wayar hannu,sannan kuma shi kansa toufeeq din bai sake taka gidan ba tun daga ranar, amma kuma hakan bai hanashi yiwa mama din aike ba kamar yadda yakeyi mata a baya.

Tafiyar da yayi china wadda dawowarsa yayi dai dai da shigar cikin ameesha watan haihuwa, ya iso da siyayyar kayan baby me azabar yawa, har hajiya garama ta kasa jurewa
"Kai kam kamar wanda za'a haifawa taron arfa?, yariyar da basusan mutunci da darajarka ba toufeeq kae yiwa* wadan nan hidindimun?, kamar wanda ya rasa mafadi?"
Dan qaramin murmushi kawai ya saki,a sannan kome hajiya qaraman ta fadi baya bata ransa ko yaga cewa hakan ba dai dai bane, saidai idan abinda tace din yaji baiyi masa ba ko bai gamsu ba ya canza da abinda zuciyarsa ta kwanta da shi
"Mahaifiyar ta nagartacciyar macace,wadda nake da imanin da halinta tayo tare zamu tsufa ni da ita din, saidai mutuwa ta raba, haihuwa kuma ta fari ce hajiya, ko china din gaba daya ake da bugatar na siya masa indai arzigina ya kai zan siya din"
"To mara kunya,tashi ka bani waje" ta waske da fadin hakan ta bishi da kallo sanda yake barin wajen ranta a mugun quntace.

Lokacin da siyayyar kayan fitar suna nata da kayan baby ta iski ameesha ta gama saddaqarwa toufeeq din ya fara komawa CLASSY TOUFEEQ JARMA din da takeson gani, ta kasa zaune ta kasa tsaye a ranar sai data samu dukkan information da take nema akan TOUFEEQ din
"Turgashi, seema kina gain ban tafka wauta ba muddin na yarda na haihu a gida?bayan har yanzu da sonsa nake kwana da sonshi nake tashi?" Tace da gawarta da sukeJ zaune cikin dakinta dake eikin gidansu,wanda ta qawata fiye da kowanne guri na gidan.

Tayi furucin ne a sanda take tsaye saman kan qawar tata da tirtsetsen cikinta da take lissafe da randa zata saukeshi ta huta
"Ba garamar wauta ba,wannan arzigin dake yafi dacewa,ke yafi cancantar ki cishi"
"Yanzu meye mafita?, ta yaya zan jawo hanakalinsa?"
"Ke kike da hanya kuwa" seema ta fada tana mata nuni da cikinta.

Murmushi ta saki tana shafa cikin nata hadi da gyada kai,sai ta koma ta zauna ta jawo wayarta ta fara kiran number wayar toufeeq din.

Har ta garashi ringing dinta ta katse bai daga ba,a qalla ta kirashi ya kusa sau goma amma abiyi picking ba,wannan ya soma daga mata hankali,seema tace
"Yasan ke kike kiransa karanto min numbers din na kira miki shi a wayata ko za'a dace ya daga"
Harara ta watsawa seemar tana jin kamar ta mareta,ita zata bawa kura ajiyar nama?.

"An gaya miki yana daga baqin numbers ne? ai saidai ki dige kina kiransa amma bazai dauka ba,bari ki gani" ameesha ta fada tana gyara zama tare da tura masa gajeran text.

Ba dadewa saiga kiransa, murmushi ameesha tayi
ta migawa seema wayar
"Ki daga kice masa yazo yanzun kamar labour nakeyi yazo mu wuce asibiti" lokacin yana tare da wasu baqi,jin zancan yasa ya barsu ya tsallako ya taho.

Yayi mamaki da ya ganta tana fitowa lafiya sumul, Ransa kuma va baci da jin abinda vasa ta kirashi da wannan sigar data daga hankalinsa.

Har ta gama bayaninta da koke koke baice mata ta tafas ba,sai data gama sannan ya juya ya bude motarsa zai shige kafin ya waiwayo
"Karki sake maimaita yimin irin wannan shashancin, don ni din ba mara aikin yi bane ba zaman banza nake ba da zaman jiran kiran wayarki" sai ya tashi motarsa yabar gurin.

Hankalinta yayi gololuwar tashi qwarai, saboda yadda take ganin so kulawa da qauna daga idanun
TOUFEEO din bata taba tsammanin zai juyawa buqatarta baya ba,musamman da ya zamanto a yanzun tana dauke da abu mafi soyuwa a wajensa a jikinta ba.

A ranar da gyar ta iya bacci.

Kwana biyu kacal da faruwar hakan Allah ya yiwa mahaifiyarta rasuwa,wanda shine ya zama silar sassautowar zuciyarsa,ya kuma sauka daga dokin nagin da ya hau,ranar sadakar bakwai ya dauketa ya maidata gidansa da kansa.

Ashe wasa farin girki!!

Zafafabiyar
"HUGUMA*
_TABARMAR KASHI_*
Book 02 Page 57
Zuciyarsa ta sake jin amanna data koma
din, saboda gananun maganganu da yaji sun fara yawo akan shi dinma kada Allah yasa ba irin halin mahaifinsa na auri saki yake dashi ba.

Sanda ta koma din duniya ta samu,don haka ta kwantar da kai sosai, duk wani biyayya kulawa da tattali tana bakin qoqarinta, duk da cikinta yayi nauyi amma bata fasa duk wani abu da tasan yana so din ba.

Wani lokaci tausayinta kan lullubeshi qwarai,ya sanya hannu suyi duk wasu ayyuka tare, tayi wani mugun laushi, ta sauya kwata kwata daga ameesha din da ya sani.

Tun yana mamaki yana d'ari d'ari har ya saki jikinsa, ya kuma barwa ransa rasuwar mahaifiyarta ne ya kawo hakan, tunda ya san ciwon mahaifiya,shi da ba rasuwa ma tayi ba.

Biyayyarta da canzawarta ya sanya shima yake tuquru wajen kyautata mata, ya sakar mata komai da take da bugata.

Wannan ya sanya ta sake ninka biyayyarta,kyautatawa da kulawa da nuna zallar soyayya me zurfi data sake sanyashi sakankacewa da ita,ya kuma sakar mata zuciyarsa,ita kuma hakan ya bude mata gofofi da dama na abubuwa masu yawa.

Cikin wata na goma ta sauka ta haifi fadeela, yarinyar da tazo da wani irin farinjini da tarin alkhairai masu yawa ga mahaifinta harma da mahaifiyar tata.

Suna na kece raini ameesha tayi kanta ya fashe sosai, toufeea ya fasa mata kai ya sanya taji ta kere sa'a cikin mata.

Hankali kwance ta fara rainon fadeela saboda masu aiki biyu da toufeeq ya dauko mata saboda yarinyar.

Wani irin raino takeyi mata kamar ba diyarta ba,a lokacin ya siya mata mota irin wadda takeso saboda dadin zama,a sannan ko watanni biyu fadeela batayi ba ameesha tana iya fita ta barta hannun masu aiki ba zata dawo ba sai yamma awa daya ko biyu kafin toufeeq ya dawo,zata shirya ta shiga sabgoginta cikin gidan sannan ta dauki yarinyar, tun bata gama mallakar hankalin kanta ba ta saba da rashin uwa a kusa.

Kusan baba ramatu ce ta zame mata kamar kaka kuma uwa,ta jima tana wanann dabi'ar kafin toufeeq ya ankara.

Ya nuna mata bacin ransa qwarai, amma saita kwantar da kai ta bashi haguri tare d algawari ba zata sake ba,don a sanann ko zaginta zaiyi bata tada kai bare ta nuna masa ta damu, bata gaunar duk wani abu da zai hadasu, saboda kudade
sosai take karba daga hannunsa, bai kuma taba cewa
a'ah ko don me ba?,shi a ganinsa muddin zaka samu
kulawa daga wajen mace da biyayya meye ba zaka iya
kashe mata ba?,meye ba zaka iyayi mata ba?.

Abu daya ne har a sannan ya gaza canzata akai shine bugatar aure, baisan abinda ke faruwa ba da ita sam,amma ya aza hakan akan yanayin halittar ne wanda yasha banban da rasa neeesa ba kusa ba.
Chapter 66 · 0% Book details