← Book details Tabarmar Kashi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 88

Sashe 65

Tabarmar Kashi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ai bata ma gama sanin waye toufeeg din a zahirance ba sai bayan haduwarta da hadaddun qawayen data maye gurbin rayuwarta dasu,ta sake sanin waye mahaifin toufeeq, a nan suka hure mata kunne akan ta qara yawan buqatunta tana sake samun abubuwan rayuwa masu tarin yawana jikinsa,su saka sanya ta fara raina hidimar da yake mata,saboda suna gaya mata
"A arzigin ubansa,wannan hidimar da yakeyi miki tayi matuqar yin kadan" yana mata kwarjini sosai,tana kuma kunyar ta tambaya kanta tsaye,sai ta fara shigo da qarairayi tana karbar kudade a hannunsa.

Bai taba hanata ba,duk da sannu a hankali ya fara fahimtar wasu kudaden da take karba setup ne kawai,yana yi matan, saboda kawai a lokacin bugatunta basa hawa kansa,kuma basufi qarfin samunsa ba.

Sanda ya gabatar da zancan aurensa ga Dr jarma hankalin hajiya garama yayi mugun tashi,ko kusa ko alama bata taba tsammanin zaiyi zancan aure a lokacin ba, babban abinda ya Sanya take sake ingiza Dr jarma akan yabar toufeeq ya nema na kansa kada ya sangarce ya shagala da dukiyar sa ba,ba komai bane sai don taja lokaci zuwa sanda HASEENA zata sake tasawa,ta zama mutum, kuma a nata lissafin sanda haseena zata gama nata karatun zuwa lokacin ya zama wani me fada aji,yayi irin kudin da take buqata daga mijin diyarta, tunda toufeeg din yana da wani irin nasibi da albarkar hannu.

Kiransa tayi tayi masa fada sosai bayan ta gama binciken wace ameesha?,diyar wacece?.

Fadan da tayi masa ta bullo masa ta bayan gida ne
"A matsayin da mahaifinka yake dashi, da baiwar da Allah yayi maka,ai abun kunya ne ace kaje ka nemo aure a wannan gidan"
"Arzigin kaykkyawar nasaba shine arziqi bana dukiya ba,so ni banga abun damuwa ba mommy, please cool down" ya fada da I don't care manner dinsa.

Duk hanyar da zatabi don ta ruguza abun bai yiwu ba saboda rabo da Allah ya tsaga a tsakani,tana ji tana gani akayi auren, saidai kuma ta barwa ranta lallai saita ruguza abun ko ba dade ko ba jima, don ba zata bari ma haseena ta zauna da kowacce mace da sunan kishiya ba.

Tun lokacin shagalin bikin ameeshan ta fidda tsarukan biki na kere sa'a da kuma kashe kudade,yayi wasu wasu kuma yace bashi da kudi bazai iya ba.

Maganar data sosa ran ameesha, zugar tawagar qawaye kuma suka sake azata akai suna fadin
"Anya zaki qulla abun arziqi da mutumin nan?, ki dubi dukiya irin ta mahaifinsa amma ya dinga ambatar babu?, ina babu taga gurbin zama a family dinsu ma gaba daya?.

Washegarin ranar da Ameesha ta tare bayan sunyi first night dinsu,tana langabe a jikinsa saboda hannu da tasha a hannunsa tace dashi
"Mota nakeso a matsayin tukuicina na first night" gyara zamansa yayi
"A yanzun bani da kudin siyan wata sabuwar motar, motocina guda biyu,duk sanda kk fara fita kidauki guda daya aro kafin na samu sukunin siya miki".

Tashi tayi ta zauna sosai tana kallonsa
"Nikam mamaki yake kamani idan kana cewa
BABU.kasan me wannan kalmar ke nufi? duk tarin dukiyar da Allah ya mallaka muku kai da mahaifinka?" Murmushi yayi ya girgiza kai, zuciyarsa na girgiza sosai da yadda ta iya buda baki kanta tsaye ta fadi abinda ya fahimci ya jima a zuiciyarta,yau ta amayar dashi da alama ta gaji da boyonsa
"Bana lissafi da abinda ba gumina bane ya tarashi ba,sanann ban isa nayi rabon gadon mutumin dake rayuwa lafiya lau cikin iyalinsa ba,duk abinda naga ya kamaci nayi miki zanyi miki gwargwadon wadatata ba wadatar mahaifina ba,nayi miki alqawarin ko sau daya ba zakiyi kukan rashin ci sha ko suttura ko kuma kudin da zaki biya bugatunki ba tare da almubazzaranci ba".

Hakan da ya fadi baiyi mata sam,tun a satin ta fara fushi dashi akan ya gaza siya mata mota,bata kuma sake bari ya tabata ba,har sai bayan wata guda da ya kawo mata motar har farfajiyar gidan.

Ba kunya ba tsoron Allah ta ware,ta dinga murna tana waya da qawayenta tana labarta musu zuwan motar,ranar kyautatawa sabuwa tare da wani sakin jiki na musamman, tun a sannan jikinsa ya fara sanyi, tunani kala daban daban ya shiga kai kawo a ransa.

Watansu uku kacal ta soma ciwo wanda aka tabbatar musu da shigar ciki na watanni biyu, abinda bai taba kawowa ba,don kuka ameesha ta dinga yi,da yabi ba'asi babu kunya tace dashi
"Nifa ban shirya haihuwa yanzu ba,haba.....kamar wata akuya,aure wata uku kawai? ,bana tunani cikin friends dina da akayi aurenmu tare akwai wadda ke da ciki, sai kuma ni?duka duka ma sau nawa mukayi tarayya?, uku ne fa kawai" Kansa kawai ya kawar ransa yana baci zuciyarsa na masa suya Sosai,dazun kafin su fito ya raba rigima tsakaninta da hajiya qarama,ci mata mutunci tayi sosai abinda ya hanashi daukan mataki rashin lafiyarta,gashi yanzun ta sake dasa masa wani bacin ran
"Me kikeso yanzu kice?" Ita kanta kafin ta furta sai dataji shakka,saboda tasan halinsa sarai,idan ransa ya baci ko va baude bashi da dadin sha' ani,ciki ciki tace
"Kawai, kawai aje a zubar dashi,
a sakamin implants,kamar nan da next two years sai a cire kafin na samu ciki na haihu aqalla munyi 4 to 3yrs" wani wawan birki yaja tsakiyar titi,saura kadan ya daki motar dake gabansu
"Ni inaso, kuma ina gaunarsa ko da dan qadangare zaki haifa,sannan ina miki rantsuwa da ubangijin da ya busamin numfashi, duk ranar da kika sake yimin magana makamanciyar wannan sai kin gane ni toufeeq asalin tataccen mara mutunci ne" daga haka bai qara ba ya tashi motar ya figeta da mugun gudu,har tana yin gaba kamar zata daki gaban motar.

Har suka isa gida bai sake kallon koda koda gefen da take ba,duk da kikan da taketa yi har da sheshsheqa.

Suna isa gidan ya fita a motar abinsa ya barta.

Cikin watanni uku kacal tayi masa abubuwa masu tarin yawa,abu daya zuwa biyu yasa yake shanye komai,darajar so da zuciyarsa ke mata zalla mara algus kuma fisabilillahi, sai kuma mahaifiyarta da a kullum yaje gaidata ko yayi mata aike take bashi tausayi,bakinta baya gajiya da gode masa da sanya masa albarka tare da bashi amanar ameesha,don a koda yaushe takance bata dauke tsammani da mutuwar ta ba.

Yadda ya watsar da ita itama data gama kukan baqinciki kan yadda cikin zai kawo mata cikas akan sabuwar rayuwar morewa da more arziqin mazajen da suka aura da cikin zai kawo mata, taga baibi ta kanta ba kwana daya biyu har zata nema sulhu sai ta fasa,zugar qawaye da tarin shawarwari batakai marasa kan gado sukayi mata caaa a saman kai,sai itama ta watsar dashi taci gaba da rayuwarta.

Shawara daya ce tasu da bata zauna mata a kai ba,na tayi amfani da qwayar zubda ciki ta cire cikin kawai.

Ita kanta tasan aikata hakan babban ganganci ne da kuma kuskure me tarin yawa a gareta,tunda tafi kowa sanin waye toufeeg din.

Zafafabiyar
"HUGUMA*
_TABARMAR KASHI_*
Book 02Page 56
Koda suka iso gidanma cikin motar yayi tafiyarsa ya barta bai kuma sake bi takan al 'amuranta ba,ya ajiyeta gefe saboda yadda tayi mugun bata masa rai saidai bai fasa sauke duk wani nauyi da haqgin ta ba, da kuma sauran bugatu da yasan mace me juna biyu zata iya buqata.

Fushi itama ta dauka sosai dashi, hukuncin data yanke na farko na qaurace masa a shimfida, abinda ta manta dama duka duka ina abun yake? sau nawa ta bayar da kai?.

Randa hakan ta fara faruwa migewa yayi ya zauna sosai ya kuma kunna fitilar dakin, idanunsa a kanta sanda take tattare kanta gefe guda cikin fushi
"Me kike nufi?"
"Kai tsaye bazan iya bane, tunda nima ba wai ina samun abinda duk zuciya takeso daga gareka bane"
"Okay" kawai vace da ita.

Tun daga ranar shima ya ajiyeta a side ya shiga sabgar gabansa.

Tun tana daukar abun da saugi tana kumbure kumburenta har ta fahimci duk inda ta dosa shi ya wuce nan, tilas ta fara neman hanyoyin shiri.

Shirin nasu babu jimawa sai kuma Allah ya saukar masa da wani ibtila'i a cikin kasuwancinsa.

Asara ya dinga samu daya bayan daya,kafin kace meye wannan?, komai nasa ya tafi sai abinda ba'a rasa ba.

To duk sanda vanayi irin wannan ya faru dole a samu sauyin rayuwa abubuwan da aka saba yi a baya dole a sassauta wasu ma sugi samuwa don dai a samu a tsira da abinda yayi saura,a kumayi qogari da tanadin mai da rayuwa kan bigirenta na asali.

Sam ameesha tace batasan zancan ba, kawai dai yayi niyyar wulaganta ta ne da tozartata, kamar yadda mata da yawa ba kasafai suke iya fuskantar irin wannan yanayi ba idan ubangiji ya jarabci mazaje da shigarsa ba (akwai mugayen mazaje asalan,wadanda ba'a san samunsu ba saidai rashinsu, mazajen da basusan su yalwatawa iyali ba,suna da arziqi amma matansu saidai suji labari ko su gani a iya jikinsu su kadai, irin wadan nan koda ibtila'i irin wannan ya fada musu,ba kasafai ake zargin mace da kau da kai da rashin nuna tausayi a kansu ba,muddin namiji tsayayye ne wanda yake hidimtawa iyali da wahalta musu kaman toufeeq a labarin nan, to butulci na garshe da zaki masa shine ki nuna baki damu da shigarsa matsala ba,sanann baki zama matar rufin asiri ba, Allah yasa mu dace)..

A wanann lokacin da yake fafutukar gain yayi maintaining rayuwarsa tare da goqarin cike gibi da guraben da da wanann babbar gaddarar ta fada masa,daga gefe kuma ameesha na zuba nata lalatar kala kala.

Ko sau daya bai taba yunqurin kaita qara ba,saboda tausayin mahaifiyarta da ko yaushe adduarta Allah ya qaddara dogon zama a tsakaninsu, mutu ka raba.

Cikinta yana da wata hudu kacal ta matsanta masa sai ya saketa, tace sam ba zata iya zama dashi ba,ta gaji da zama cikin talauci bayan mahaifinsa shahararren mai kudi ne, muguntar kai ko kuma girman kaine yake damunsa?, Da bazai shiga dukiyar mahaifinsa ya amfana da ita ba?,itama ta samu damar cika duka burikanta da muradan rayuwarta?.

Maganganun data fada a lokacin masu tsauri ne sosai da suka sosa masa zuciya.

Daga daren har wayewar garin bata barshi ya runtsa ba, haka ya dauki takarda ya rubuta mata saki guda daya.
Chapter 65 · 0% Book details