← Book details Tabarmar Kashi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 88

Sashe 33

Tabarmar Kashi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gown din me siririn hannu ce, kuma bata gama saukowa ba sai ta dora hijab da ya sauka har gasan gafafunta,ta zura wasu takalma masu laushi ta fito a sashen nata.

Dab da zata isa ga sassansu fadeela hajia garama ta fito.

Kamar ko yaushe cikin shigar fariya da alfarma, mayafinta a kafada don ita din ba ma'abociyar yafa mayafi bace.

Wani kallo tabi sahar din dashi sannan ta saki murmushi tayi gaba
"A'uzu bi khalimatillahit taammati minsharri ma khalaqa,Allahummakhfinihim bima shi'ita" ta samu kanta da furtawa saboda wani faduwar gaba da saukar mata sanadin murmushin murmushin da ta gani akan fuskarta.

Baaba ramatu ta samu da zuwaira suna hira a falon,ko ina a tsaftace kamar ko yaushe,suka gaisa cikin girmamawa sannan ta wuce kitchen bayan tace da zuwaira da ta mige zata bita suyi zamansu,abu me sauqi zata hada.

Veggies couscous ta shirya tare da egg
souce, tasan fadeela da son kayan zaqi,ba kuma kasafai take barinta vanzu tayi ciye ciyen kayan kwalin nan na banza da wofi ba,sai ta bude freezer ta fidda kankana ayaba yoghurt ta hado da madara ta zuba sugar tayi mata blending water melon smoothie data cikawa madara sosai.

Tana juyeshi a wasu madaidaitan drinking glasses masu bamboo lids bayan ta zare glass straw din da suke dashi nadeeya ta shigo.

"Aunty N,yauma akwai special abu da alama, qamshi tun daga compound" tayi maganar tana legen smoothie din da take juyewa
"Abincin faddee ne" dan fuska nadeeya ta bata
"Amma ana wasa tare ci banban, nidai wannan smoothie din za'a tallafeni dashi,yau nasha rana, inajin ajiye aikin nan zanyi" ta fada tana narke fuska.

Murmushi s
ahar ta saki ta maida murfin ta rufe ta zura mata straw din ta miga mata.

Zuqa daya tayi ta lumshe ido
"Anty N,bazan iya shan wannan abun a tsaye ba bari na garasa daki"
"A fito lafiya " ta fada tana murmushin santin da taga
nadeeya din tanayi.

Cikin fridge ta maidashi inda sanyi bazaiyi masa
yawa sosai ba,saboda ta saka ice cube qurin blending din so da sanyinsa.

Muryarta taji tana qwala mata kira
"Tom an dawo kenan" ta fadi a ranta tana murmushi, a hankali taii sautin nata yana matsowa kitchen din,sanda ta lita dab da gofa saita waiwayo tana murmushi hadi da dan harara a idanunta na yadda ta tafi school bata nemeta ba yau din.

Maimakon fadeela sai idanunta suka hadu da nashi,gabanta ya fadi,ta dauki hannunta tana nadeshi a girjinta saboda yanayin rigar da take sanye dashi, already ta cire hijabinta tun shigowarta kitchen din, saboda tasan babu wanda yake shigowa, daga ita sai baaba ramatu sai zuwaira.

Sam bata kawo zai shigo ba,saboda bata taba ganinsa cikin kitchen din ba sam.

Duk yadda yaso yiwa idonsa shamaki a kanta amma hakan ya faskara,sambala sambalan singalalin hannunta dake da lallausar fata me santsi yabi da kallo, a hankali ya zarce da kallon qirjinta data lullube da kyau da singalalin hannun nata,saidai duk da hakan hannun nata bai wadatar ba,saboda cikarsu da tsaiwarsu ya sanya suka fito ta saman rigar fam dasu.

Kadan kadan zuciyarta ke bugawa tana duban fuskar fadeela tare da qoqarin waskewa da nuna bata damu da shigowar tasa ba.

A kasalance ya dauke idanunsa yana cewa da fadeela
"Sauka angel ki qarasa" saboda dama ha daukota ne a bayansa da kansa yau din.

Kafada ta maqale
"Abby ki qarasa ladanka please,ka shigar dani ka kaini
gurin anty N" ta fada tana maqale kafada
"Ya salam" ya furta a ransa,wannan rigimammiyar ruwa takeson ballo masa.

Magiya ta dage da yi, hakan ya sanya ya fara takowa da ita cikin kitchen din yana gogarin hana idanunsa kawai wanann gurin da ya zame masa kamar wata jarrabawa akan yarinyar.

"'Matso abby ka gani" fadeela ta fada tana miqewa daga bayan nasa,nufinta ta taka bayansa sannan ta maqalewuyan s
ahar
"What?, sauko angel" ya fada yana dan daga kansa yana dubanta.

Sake marairaice fuska tayi
"Please mana abby, munyi algawari fa kace yau bazan taka qafafuna a qasa ba" kai ya girgiza yana tuna sunyi hakan, amma shi bedroom dinta yace zai sauketa.

Idanunsa ya lumshe ya gara taku biyu gaba yadda yarinyar keso,saahar na tsaye tana murmushi idanunta akan fadeela, saidai can qasan zuciyarta wani mugun gudu takeyi kamar wadda tayi gasar tsere, taku biyunsa su suka hade dukka wani tazara dake tsakaninsu,wadan nan abubuwan da suke tone masa idanu,suka zame masa idanunsa barazana suka samu kyakkyawan masauki saman girjinsa.

Yadda yaji saukarsu saman likinsa haka tail vadda girinsa ya tokare nata.

Dukkansu jikkunansu suka karbi wani sago me nauyi da bala'in ratsa zukata,yayin da s
ahar jikinta ya dauki rawar da saura kadan fadeela tasha gasa, banda toufeeq yayi zafin namar taro yarinyar,ya saka dukka hannuwansa ya sauketa a gasa yana duban fuskarta
"She's not brave enough,ba zata iya daukanki ba" ya fada muryarsa tana dan sargewa wanda shi kansa baisan da hakan ba.

Itakam fadeela da batasan dawar garin ba dariya takeyi tana sake magale s
ahar
"Anty N,abby na ya fiki qarfi, amma zamu hada qarfinmu waje daya muma ko?" Kai ta gyada mata a sanyaye tana jin qafafunta babu qwari sam.

Tsaiwa yayi kawai a wajen yana duban fuskarta,yadda lokaci daya hankalinta ya tashi fuskarta kuma cakude da bacin rai kadan.

Kasa motsawa yayi shima yana qoqarin controlling kansa kafin yakai ga takawa yabar wajen,jikinsa a sanyaye ya ja da baya ya jingina da kitchen cabinet din yana sake binta da kallo sanda take rige da hannun fadeela bayan ta maida hijabinta jikinta.

"Ungo wannan ki fara sha kafin kiyi wanka,kizo kici abinci na gama" s
ahar tace da fadeela tana bata drinking glass din.

Harda tsallenta, ta dawo gurin toufeeq bayan zuga
"Yummy abby sha kail" ta furta tana miga masa.

Hannunta ya dafe yana girgiza kai,ta fahimci me yakeson cewa saita maqale wuya
"Please mana abby" a nutse ya durqusa ya sanya straw din a bakinsa ya zuqa.

Har cikin kwanyarsa dadi da gardin fruit dana madarar ya ratsa masa,ya lumshe idonsa yana jin smoothie din yayi masa matuqa,saidai kafin ya sake sha fadeela ta janye abinta ta kafa a baki.

Su suka fara fita a kitchen din yabi warmers din da kallo daya tabbatar abinci ne a ciki,ya shafi cikinsa yana jin yunwa tana taso masa, tunda jacob yaje gida yake wahalar abinci,tun asali mutum ne shi da bakowanne abinci yake iya ci daga hannun kowa ba, gidan cike yake da masu girki da kuma nau'in abinci kala kala amma bai iya ci ba, da abincin jacob kadai ya aminta.

Ba mai yawan ciye ciye bane, amma kuma baya wasa da cikinsa ta fannin abinci, idan ya tashi zaiyi masa ci me kyau,daga nan kuma sai lokaci na gaba.

Da qyar ya shawo kansa sannan ya fita a kitchen din shima.

Sassan nasa babu kowa kamar ko yaushe,bedroom dinsa ya wuce,ya soma zare kayan jikinsa cikin wata muguwar kasala,ya zauna yana zare takalmansa idanunsa suka sauka aka robar maganin.

Hannu yasa ya sake daukota yana juyawa,sai ya maida ya miqe yana dauko system dinsa daga inda ya ajiye ya kunnata,akwai result da zai karba yau game da maganin daga gurin Dr anwar,don haka yabar system din tana daidaita ya wuce toilet don yayi wanka kafin ya fito.

"HUGUMA*
'_TABARMAR KASHI*
Book 02Page 29
Sai da ya gama shiryawa tsaf cikin wasu lausasan pyjamas bagaqe a yau amadadin farare da yafi amfani dasu komai ya zauna luf a jikinsa,yaja stool ya zauna vana duba system dinsa.

Dukka hankalinsa va bayar akan bayanan da Dr anwar ya turo masa.

Lokaci daya yaji wani gumi yana tsatstsafo masa,yasa hannunsa a tausashe ya share yana dungule hannunsa ya rufe bakinsa yana tsurawa system din ido
"'Yaya akayi maganin ya kasance daga hannun haliva qarama? me yasa maganin da bai kasance na lalurar fadeelan ba amma take shansa? me hakan ke nufi?" Ya viwa kansa tambayar yana jin hankalinsa yana tashi
"Take it easy" wata zuciyar ta gaya masa
"'Kayi bincike wisely" aka sake nanata masa.

Miqewa yayi yana fita a bedroom din nasa a hankali, ya ciro wayarsa da ya bari a parlor ya fara kiran layin nadeeya.

Bugu daya ta daga
"Yaa moha"
"Me sunan matar nan baga wata gajeriya me jiki dake aiki a sassan momy?" Dan shuru kadan nadeeya tayi sannan tace
"Ko adama?" Kai ya gyada
"Yes, kiyimin kiranta, amma banason kowa yasan na nemeta"
"To yaaya" ta fadi tana ajiye wayar, saita dubi su s
ahar wanda suke zaune zasu fara cin abinci
"Ina zuwa AUNTY N" kai ta gyada mata,saita koma daki ta dauki mayafinta ta fice.

Tun daga yadda ta shiga parlor din zakasan a mugun razane take,ko ina na jikinta rawa yakeyi,gumi kuwa ya gama jiga mata jiki sharkaf.

Yau ta shiga masifar da me fiddata sai Allah, dazun nan hajiyan ta gama yi mata kakkausar jan kunne kamar yadda ta saba a duk lokacin da aka karbo maganin, saidai kuma jan kunnen yau din yafi na kullum, kamar tasan abinda ya faru a hanyarta na kawo mata maganin.

Da hannu ya yiwa nadeeya nuni akan ta tafi,ba musu ta juya,cikin zuciyarta tana taya adama alhini,ko wanne tsautsayi ne yasa ta shiga gonar toufeeq din? wanne irin laifi tayi masa haka?.

Tun kafin yace ta zauna gafafunta suka kasa daukarta, saita sulale tayi zaman dirshan a gurin.

Kallo daya yayi mata ta fashe da kuka, tama mance da wani jan kunne na hajiya qaraman
"Wallahi bansan komai a kai ba indai batun magungunan ne" idanunsa kawai ya zuba mata yana mamakin rudewar da tayi.

Sake debo rantsuwa tayi
"Na rantse da ikon Allah bansan komai ba"
Tun yaushe ake kawo maganin?" Ya jefa mata tambayar
Shekara biyu
shekara biyu a cikin ta uku* ta bashi
amse kowanne sashe na jinta yana kakkarwa.

Wani irin zafi idanunsa yaji sun fara yi masa, abinda zuciyarsa ke hasaso masa har bayaso sukai ga kwanyarsa bare ta sauya masa su ga dayan sashen na zuciyar tasa
*ki hada kayanki gaba daya,na sallameki daga aiki a gidan nan" abindia ya fada kenan.
Chapter 33 · 0% Book details