← Book details Tabarmar Kashi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 88

Sashe 62

Tabarmar Kashi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Qaramin murmushi ya saki yana karantarta,har yau bata taba tsaida idanunta a jikinsa ta gare masa kallo ba,yana lura da duk wani motsinta tun ba yau ba.

Ya gama fidda kayan daga shi sai pant,ya fara takowa a hankali,bai tsaya ba har ya cimmata, ya tsaya dab da ita yana dan taka yatsunta da nasa yatsar ta vadda zatasan da isowarsa.

Sarai ta jishi, amma bugawar
da zuciyarta keyi ya hanata motsawa
"A bani towel" va furta vana kallonta.

Cikin rawar jiki ta
waiwaya tana duban gefanta ko zataga towel din, suna
ninke a kusa da ita,hannu ta miga ta dauko ta miga masa ta baya ba tare data waiwayo ba.

Hannunsa ya miga ya riqe towel din hadi da jawota gaba daya sai gata a tsaye a gabansa,dukka qugunta ya kama ya rigeta tsam yana matsowa da ita jikinsa ya mannata da qugunsa.

Wani irin shock mai qarfi ya fusgeta ya kuma ratsa kowanne sashe na jikinta ya tayar mata da tsigar jiki, dumin fatarsa yana ratsata qwarai
"'Look into my eyes" yafadi qasa qasa shima yana jin
wani yanayi na sauka a nasa jikin sanadiyyar haduwar
jikkunansu guri guda.

Na second daya tak ta iya daga kai ta kalleshi sai taji ba zata iya jurewa ba.

Ya sani
dama saboda abinda ya sakar mata ta cikin idon zaiyi wahala ta iya jura,sai ya saki qaramin murmushi na gefan baki yana kallon lips dinta.

A duniya labbanta na daya daga cikin abinda ke tafiya da tunaninsa yake kuma jin marmari, iya kallonsu kadai suna haifar masa da tarin bugatuwa zuwa gareta
"You are one person with the power to give me a
thousand feelings...can i order a large tight hug until I
feel okay please?" Ya fadi yanason kallon tsakiyar
qwayar idanunta da har yanxu taqi yarda ta kalleshi dasu, saboda wani irin feeling da yake saukar mata
"Please" ya fada a narke, nan ma bata amsa ba,kasa jurewa tayl a karo na biyu,yanzun kuma taji duk duniya idanun nasa takeson kallo,tanason ta tabbatar da salon muryar da kuma wannan shagwabewar ita MT JARMA yake yiwa.

Sosai vaja numfashi sanda idanunta suka shiga nasa,ya kama kanta da hannunsa dukka biyun ya riqe, numfashinsa na kai kawo da sauri cikin zafin nama ya matso da fuskarta dai dai tasa
"You just stole my words" ya garashe fada yana hade bakinsu guri guda.

Wani irin kiss me zafi yake sauke mata ko ta ina, tuni ya sanya jikinta itama ya dauki rawa, lokaci kadan ya fara juye mata tsantsar kewarta da yayi da kuma yadda zuciyarsa ta azabtu da soyayyarta, tun tana iya dauka har ta fahimci abun nasa nisa yakeyi, kamar yana shirin ficewa daga hayyacinsa.

Kasa tsaiwa sukayi dukkansu suka zube saman lallausan carfet din dake iya area din da suke a tsaye.

Sai tayi qarfin halin tureshi, muryarta na fita da qyar saboda gudun da zuciyarta keyi
Am in...am in.... miscarriage bi.." Bai bari ta garasa ba
ya zame jikinsa va tsani ya tuna wai tayi
miscarriage, shikenan ya rasa babynsa? bai kuma san ranar maida wani ba, sai kawai ya zura jallabiyyar daya fidda ya nufi gofar fita zuwa parlor yana hada hanya.

Ta jima zaune a gurin tana maida numfashi kafin ta iya migewa ta shige toilet don cire pad din jikinta ta sauya wata.

Cikin mamaki take sake kallon pad din, tayi tsammanin zata sameta da jini a jiki, tun ranar da akace tayi miscarriage din bata sake ganin jini ba,sai dan sports data gani zuwa jiya,yau kam babu komai ma a jiki, yau kwanaki hudun yadda ta saka pad din haka take cireta,sai ta jefata dustbin tayi tsarki ta kuma daura alwala tana yankema ranta zuwa asubahin yau idan bataga komai ba zatayi wanka taci gaba da ibadarta.

Saman sofa din dake dakin ta koma ta cure guri daya, tana jin mararta na daurewa sosai, idanunta a lumshe har zuwa sanda ya sake turo gofar ya shigo.

Ta lumsassun idanunta take satar kallonsa har ya wuce bandakin, sai daya rufe qofar sannan ta sake maida idanun nata.

Zurfi qwarai zuciyarta tayi akan nazarinsa da nazarin halaye da dabi'unsa, bata tana tsammanin samunsa da wannan fuskar ba, MT JARMA, mutum mara uzuri mara dagin gafa, mutum me tsananin zafi,wanda bai maida korar ma'aikata a bakin komai ba, bata taba zaton samun wanna side din daga gareshi ba.

Duk wasu qarin dabi' u da take tsammanin samu daga gareshi sai taga akasin hakan.

Zafin kai izza tagama da kuma tarin qasaitarsa takan rasa ina sukayi a duk sanda suke kebe,wani mutum daban take gani a mafi yawancin lokuta,bawai MUHAMMAD TAUFEEQ JARMA ba.

Zafafabiyar
"HUGUMA*
_TABARMAR KASHI-
Book 02 Page 53
Mintuna kusan talatin ya sake fitowa,saita sake bude idonta kadan tana ci gaba da satar kallonsa.

Daure yake da towel yanzun a qugunsa, duk wata siffa da gira da Allah yayi masa ta bayyana,idan tace tsahon rayuwarta bata taba ganin namiji me qira koda kusan tasa ba batayi garya ba,inda za'a dauko adam a tsayar dashi a gabansa,tabbas zai tashi kamar siffar jikin mace ne da kuma wani ingarman namijin.

Zame towel din da yayi ya sanyata maida idanunta ta kulle da garfi harda juya kanta wani sashen.

Murmushi me sauti ya saki yana sane yayi hakan, tun daga shigowarsa har yanzun da ya fito daga wankan ya fahimci tana satar kallonsa
"Idan kin gama qaremin kallon ki tashi kiyi wanka,ki fidda wadan nan kayan ko zakiji dadin bacci" ya fadi yana sanya short necker sannan ya fara feshe jikinsa da tattausan turarensa mai kwantar da zuciya.

Har ya gama bata motsa ba.

Bai sake ce mata komai ba,sai ya taka cikin kamewarsa ya isa gareta sai kawai ji tayi an dagata cak
"Na daina magana biyu daga yau, komai zan vishi ne a aikace".

Bai saurari magiyarta kan ya sauketa ba
"It's too late" yace da ita yana isa toilet din, sai kawai ya tsumbulata gaba daya cikin bathtub.

Qanqame jikinta tayi guri daya
"Pleaaaaaaaassssseee" ta fada murvarta na rawa.

Murmushi ya saka yana fasa shiga cikin kwamin kwankan da yayi niyya,yaja da baya yana nufar qofa sai-kuma ya tsaya cak yana kallon dustbin din data jefa pad, har zaice wani abu sai kuma ya fasa ya sanya kai ya fita.

A reception na hotel din sajjad ya karba musu keys na dakunan sannan suka haura zuwa floor na biyu.

Migawa Dr jarma key din nasa dakin yayi cikin girmamawa sannan yayi gaba yana cewa nadeeya
"'Muje ga naki key din" afifa da nadeeya suka bi bayansa.

"Shifa" Dr jarma ya kira maji wadda sai yanzu ta iskesu ganin tana marawa su sajjad baya.

Tsaiwa tayi cak sannan ta waiwayo tana duban idanunsa.

Nauyinta kadan ya kama Dr jarma
"Ga namu dakin, naga kina shirin bin yara"
"Eh tare dasu zan kwana" ta amsa masa kai tsaye.

Kai ya girgiza
"Kada kiyi haka don Allah shifa,tsahon shekaru talatin ba wani abu,yau dai ki yarda mu hada makwanci, koda kwanan zaune zamuyi ni dake,aqalla ko hira mayi,ko bitar bayan rabuwa mayi"
"Dakai da wa?"
"Da shifa dina" ya amsa mata kai tsaye yana kallonta.

Ta fuskanci lagonta yakeson karyawa,sai kawai ta dauke kai tayi gaba ba tare da tace masa komai ba.

Caraf ya kama luggage dinta ya riqe,nan ma bata ce mas komai ba ta sakar masa tayi gaba abinta
Zare ido nadeeya ta hauyi da gain maji ta shigo dakinta,daga ita sai afifa ne kadai sukasan yanzun maji tana amsa sunan matar Dr mahmud jarma a karo na biyu
"Maji ai munyi sallama ko?" Harara ta watsa mata, dole ta tsuke bakinta ta bata qofa ta shigo.

Tana kintsa dakin tana satar kallon majin, amma bata da bakin magana dole ta qunshe abinta a ciki, saidai gasan ranta tausavin abban nata sai ya kamata.

Kusan minti biyar yayi a tsaye a gurin rige da luggage din shifa data bar masa,jiki a matuqar sanyaye yaja luggage din ya bude dakinsa ya shige da ita.

Yana shirin zama kira ya shigo wayarsa,koda ya duba sai yaga fauziyya ce,ya daga kiran yana zama saman stool
"Fauziyya ya akayi?"
"Wai yaaya ina kuka shiga?"
"'Meye ya faru?" Wani abu me daci ta hadiye
"Yaaya,wanne irin mutane ne marasa mutunci cikin asibitin da fadeela ke jinya? kodai yarinyar ta shirya wulagantani ne kawai?"
"Wai meye fauziyya ya faru?" Ya fada cikin qagauta da jin gorafinta.

"Yanzu yaaya kamar ni?..
... ni fauziyya za'a hana shiga ganin fadeela? bayan na gaya musu matsayina a gurinsu? wai ba'a basu izini ba? wallahi yaya muddin kana sona kana kuma gaunata saika binciko wanda yasa a hanani shiga ganin jikata" ta fada da murya mai rawa dake nuna hawaye takeyi
"Yanzu kina ina?"
"(na Mercure hotel"
"Ki saki wannan dakin ki samu taxi,zan turo miki address din hotel din da muke"
"Tom" ta fada cikin zafin da ita kadai tasan yadda takeji a zuciyarta.

Wayar ta ajiye tana furzar da iska,ta fara fahimtar fissafinta na neman wagajewa ne,a yanzun kuma tana buqatar nutsuwa qwarai tare da takatsantsan wajen fidda sabon takunta
"Bansan wanne kaidi ne zaiyi dai dai da abinda kika
aikatamin ba s
ahar, maji
...maji....bazan taba bari kici gaba da rayuwa kusa da yayana ba bare gaddarar sake zamowa matarsa a karo na biyu ya afka min ba".

Abindata furta kenan tana kallon fuskarta ta cikin
madubi, zuciyarta kamar zata fito ta bakinta saboda
zallar bacin rai.

Da kansa ya fito bayan isowarta hotel din,ya sauka qasa ya shigo da ita.

Suna shigowa veranda din nadeeya na fitowa a dakinsu
"'Mommy ina kika shiga ne tun dazun?" Harara ta ballawa nadeeya din,saboda a yanzun dan sauran tausayin nadeeyan da takeji wanda shine silar da yasa take daga mata qafa bata sakata cikin budget yanzun ya fara ja baya
"Sai yanzu kikasan da ni,saboda kinga uwarki ko?" Yar
Daria kawai ta saki,dr jarma da yanzu bayason jin zancan maji daga bakin fauziyya yace
"Nadeeya,maza ki cewa ummanki ta fito muyi sharing dakina,ke sai ku kwana da mummynku"
"Toh abba" Nadeeya da hakan ya yiwa dadi ta juya zuwa dakin nasu.
Chapter 62 · 0% Book details