← Book details Tabarmar Kashi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 88

Sashe 73

Tabarmar Kashi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maji tana gama shafa addu'o'inta ta miqe,dr
jarma da a yau soyayya tayi aikinta,yayi galaba akan mail tarihi ya kuma maimaita kansa bayan tsahon shakaru kusan talatin,ya daga kansa yana jin zuciyarsa fess ta shayar dashi wani tafki daya manta rabonsa da samun makamancinsa,duk da tanata kumbure kumbure tana kuma basarwa amma sam bai dameshi ba,ya sani magana ta riga ta qare a tsakaninsu,aikin da yayi saura ba me yawa bane yanzun a gabansa
"Ina zaki fita da safe haka?"
"Zan tavar dasu nadeeya kada su kwanta suyita bacci basu tashi sunyi sallah ba" murmushi kawai ya saka ya maida kansa saman pillow yana cewa
"Da kin dawo kawai kinyi kwanciyarki, don nasan toufeeq bai taba makara sallar asuba ba na tabbatar sun tashi sunvi" a mamakance ta juyo tana kallon dr dake kwance
"Toufeeq kuma?, toufeeq din da yake a daya hotel din, me ya kawoshi nan kuma?"
"Matarsa kika dauko masa shi yasa ya biyoku,da da baki dauko masa matarsa ba kin ganshi ne?" Cikin hanzari ta zura slippers dinta tana salati gasa gasa toronta Allah toronta kada ya warware aikin likitan nan azo a zamu sabani.

Caraf Dr jarma ya rigota
"Dawo ki zauna, ba inda zakie kina zaton kin fishi son cikin nan?,na tabbata yasan abinda yakeyi, ba abinda zai sameshi, kwanta ki huta hakanan" ya gwada mata garfi ya maidota kan gadon,tilas ba yadda zatayi haka ta koma ta kwanta tana qwafa amma qasan ranta.

"Qarfin hali" taji Dr ya fada.

Tasan sarai da ita yake amma sai tayi kamar bata jishi ba.

Duk ta rude saboda kunya da tunanin sa wanne ido zata kalli su maji? amma shi sai taga hankalinsa a kwance yake,hasalima ko a jikinsa,yayi zamansa saman stool daure da towel yana waya da jibril ya shiga wani
shago ya siyo masa kaya ya bayar a reception a kawo masa.

Ya gama wayarsa yayi wankansa,ya dawo ya shirya hankali kwance a gabanta,sai nata idanun taja ta kulle har ya gama.

Ji tayi yana bude qofar dakin,sai ta zabura ta zauna tana dubansa a marairaice, shima ita din yake kalla.

Fasa budewa yayi ya dawo da baya a hankali yana
cewa
"Ki daina razana hakanan, ki rufamin asiri gurin maji, kinga dai banyi komai ba,dan kadan ma nace adanji tausayina a sanmin amma ba'a bani ba, kada zaburar nan ta haifar da wani abu kisa maji ta hukuntani".

Narke masa sosai tayi tana sauke masa kukan shagwaba.

Zubewa yayi a gabanta gaba daya ya tsugunna saman gafafunsa ya kamo zara zaran yatsunta yana kallon qwayar idanunta
"This shagwaba.....bani da jarumtar shanyeta fa ba tare da na biya tukuicinta ba, ki taimaka ki sassauta min" sosai ya bata kunya, gashi ya tsareta da ido, ta dan kauda kanta gefe tana fadin
"'Amma....ta yaya zan iya zuwa na gaida maji don Allah"
"Zo na rakaki" ya furta yana game tafukan hannayensu guri guda.

Yadda s
ahar ke sissingewa tana jin kunya da nauyin maji haka suka bar majin itama da kunya da nauyinsu.

Wato namiji dai komai qanqanta ko girmansa duka halinnan dai guda daya ne.

Ta gefan ido take kallon
Dr jarma, ya wani sake yana hira da toufeeq din sosai, farinciki ne zallah saman fuskarsa da zai nunawa mutum me shekaru da zurfin hangen nesa lallai a yau din va cimma burinsa.

Shan tea din kawai take amma kunya ta cikata tsakanin Dr jarma din da toufeeq dan dikinta da sahar surukarta batasan wanda tafi jin kunya ba.

Jefi jefi take jan sahar da hira wadda itama kunyar ta hanata tabuka komai,a haka hajiya qarama ta tura gofar da dama ba rufeta akayi sosai ba ta shigo.

Kamar zuciyarta zatayi tsalle ta fito haka taji,ga maji ga mahmud again ga kuma toufeeg, toufeeq din da sannu sannu take kallo yana komawa qarqashin iko da mulkin maji din ta ruwan sanyi,sai ta girgiza kai,wannan babbar asara ce da tabewa a gareta, ba zata taba yarda wannan abu da ya fara afkuwa yaci gaba da wanzuwa a haka ba.

Tana wani shan qamshi ta shigo dakin, ta samu waje ta zauna Dr mahmud na tambayar ta fito
Eh, ai naga ba kasafai kuka fiyawa tunawa da kun aje mutum a dakin ba" dire cup din hannunta maji tayi ba tare data dubi sashenta.

Ta shirya sauya taku don haka ta hadiye wani abu da ya tsaya mata a wuya tace
"Barka da safiya matar yaaya" wani kallo maji ta ajewa hajiya garama, a hankali ta sakarwa hajiya qarama din murmushi, a kallo daya tak ta fahimci inda maganar ta dosa
"Barkanki fauziyya* ta smisa mata a taqsics taria barys dubanta daga kanta.

Duk yadda toufeed yasi controlling carisa gaidata don ya sake binneta ya pra isovar fariar da /5 gayawa duniya wace ita, da fiddata a rayanarsa fitsrea ta har abada da kuma sarin hukuncin da yay imani sal yali kowanne hukunci yi mata cio a rayura sai ya kasa.

Tsar ya mique abinsa, yanata cocarin had ye bein fan dake taso masa a duk sadda ya kalli fuskar ha, ja garama, baya ga amneesha itace mutum ta biyu a durija da tayi masa abinda zai koma ga manaliccinsa da tabonsa.

"Zuwa nayi na gaya maka inason na koma gida,zan yank. ticket zuw anjima in sha Allah" hajya carama ta fada tana hadiye wani abu me daci da ya tsaya mata a wuya,ciwo kan ciwo,duka kan duka,yadda toufeed yayi watsin ruwan tsarki da ita ta karanci hakan.

Tayi laluben duniya ta gano wanne laifi ta aika masa data cancandl yayi mata wannian rashin arzigin a matsayinta na wra kuma uwar goyo a gareshi?.

Abu daya zuciyarta keta nanata mata,s
ahar ce kawai ta shiga tsakaninsu, ita ta avatar da kornai,shi yasa batajin zata sassauta miata. duk randa ta tashi miga hukuntata,sai ta san ya yarinyar tayi dana sanin saninta a rayuwa,sai ta saryata ta zama izina ga kowacce diya mace dare shirin sake shiga rayuwar toufeeq din,ciki harda uwar data haifesa
_uhmm, kifi na ganinka me jar koma_
"Ki gara haquri duka saura kwanaki biyar mu wuce gaba daya har da ita fadeelan,zan saka a yau din a duba mana ticket da zai maidamu gida lokaci daya" sai data hadiye wani abu a gasan ranta sannan ta dauke dubanta ta mayar ga yayanta
"Yaaya, vanzu lalacewata yakai toufeeq ya wuce ba tare da ya gaidani ba?, hakan ba 'yar manuniya bace ga matarsa tayimin duk wani diban albarka da taga dama?" Dan dubanta kadan maji tayi, sai ta mige a nutse ta fice tabar musu dakin.

Cikin ranta takejin indai toufeeq din bai gaidata ba bai kyauta ba da gaske, koba komai ganwar uba uwa ce komai lalacewarta ita da Dr din duka ba wanda ya lura da hakan.

Reception ta wuce tana fidda wayarta ta kirashi tace ya sameta a can.

Ba jimawa ya taddata, ta nuna masa guri ya zauna
"Moha ban zaci samun dabi'ar raina na gaba daga gareka ba,ko meye a tsakanina da fauziyya ba huruminku bane wannan wani abu ne dava shafemu,me yasa baka gaida fauziyya ba?" Qas yayi da kansa, ya rasa wacce amsa zaya bata, ya sani ba Dr ba,ko ita da yayi imanin tasan halinta ciki da waje sai ta girgiza idan taji abinda hajiya qaraman ta aikatawa jininta gudar jikarta, yanzun kuma bayason yacewa kowa komai,so yake su isa gida ya gabatar da komai da hujja
"Bazan iya gaidata bane maji, kiyimin afuwa" ya furta a hankali vana daga idanunsa zuwa kan majin.

Kafeshi tayi da kallo tana mamakin yadda tashi guda kamanninsa da launin idanunsa suka sauya, idan ma idanunta sun gane mata dai dai harda kwanciyar hawaye a qasansu.

Zafafabiyar
"HUGUMA*
_TABARMAR KASHI*
Book 02 Page 63
"Me yasa Mohammed?" Ta jefa masa tambayar a mamakance tana karanto tsantsar duhun bacin ran dake qasan zuciyarsa, tana son karanto zuciyarsa kai tsaye, inn karatun da cikakkiyar uwar da tasan abinda takey, takewa yaron cikinta komai girmansa.

Dauke dubansa yay ya maida gete ransa yana soyewa
"Zakiji maji a gaba, kiyimin afwa" shuru dukkansu sukayi shi da ita,jilkinta ya bata tabbas akwar wani gagarumin abu da ya faru,duk da ba'a shaidar dan yau amma ita din tayi amanna da Muhammad din d'ari bisa d'ari
"Shikenan,Allah ya rufa asiri" ta fada a sanyaye
"Ameen" ya amsa.

Har ya miqe tace
"Ka dauki matarka ku wuce zan saki dakin dana Kama din tunda babu amfani, ruwanka ka taimaki likitocin Kan taimakon da sukayi muku don ku samu ganin diyoyinku, ruwanka kuma ka wargaza aikinsu" sai a sannan yaji kunya ta kamashi,yasa hannu ya shafi lallausar sumar kansa yana murmushi cike da jin kunya
"Allah ya saka da alkhairi ya qara girma".

Kai kawai ta girgiza bayan wucewarsa, har ranta tana jin wani farinciki yana saukar mata,nutsuwa tana gauraye rayuwarta,ta tuna da darensu na jiya ita da Dr jarma din, komai nashi dare zuciyarta ya koma sabo.

Yadda a ajiyan ya dinga bayyana mata bazai taba samun wata mace da zata maye masa gurbinta ba Itama tayr imanin hakanne a tata zuciyar, kawai tana ja masa aji ne saboda ya sake sanin muhimmancinta, tabbas, dan adam abun toro ne, kuma sharrinsa abun neman tsar ne.
_ya ubangiji dukkan wanda zai nufemu da sharri cutatarwa ko quntatawa ga rayuwa da farincikinmu,ya rabbus samawati ka shagaltar dashi da damuwoyinsa,kayi mana tsakani da shi tsayin nisan tazarar da bata da yaka don hasken fuskar annabi muhammad S A W.
*******
Qwarya qwaryar honeymoon suka gudanar a
Germany din tsakanin toufeeq da saahar.

Wata irin narkakkiyar soyayya ce me matugar tsayawa a ral ke huda zuciyar kowannensu.

Wani irin so me matuqar qarfi da tasirin karya kowanne qarfi kafiya zati da turjiya na zuciya.

Karon farko saahar din ta koma masa tamkar wata raqumi da akala,gaba daya ya sauke mata tunaninta,ya goge haddar kanta tasss!!' ,ya tsiyayar mata da man kai babu wani abu da yayi saura cikin zuciya ruhi da gangar jilkinta sai MUHAMMAD TAUFEEQ din.

Gwarzon namijin da cikin lokaci qalilan ya tabbatar mata da karin maganar nan ta hausawa da suke cewa MAZA SUNA SUKA TARA Kuma KOMAI LALACEWAR AL' UMMA AKWAI NA GARI.

Yayi nasarar cisge kowanne mummunan tunani a ranta damuwa da bad memories dake damunta,ya maye gurbinsu da wata zazzatar qauna soyayya da zallar kulawa.
Chapter 73 · 0% Book details