← Book details Tabarmar Kashi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 88

Sashe 34

Tabarmar Kashi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Faduwa tayi a gurin tana hurwa tana kuka sosai, saboda tasan muddin tabar aiki a gidan asirinta ya tonu,mutane masu yawan gaske ne suke neman damar yin aiki a gidan amma basu samu ba
Tsawa ya buga mata wanda ta sanya ba shiri ta tattara zaninta ta fice tana kuka.

Shuru yayi yana maida jikinsa ga kujerar idanunsa a lumshe
"To maganin meye?" Tambayar da Dr anwar dinma bai bashi amsa ba, yace masa baida alaqa sam da ciwon fadeelan, suna kuma ci gaba da bincike.

"Wanne magani kenan ake bata yanxu?" Tambayar da tazo kansa kenan,ya kuma miqe a nutse ya sanya flip flops slippers dinsa yana baro sashen.

Tuni ta gama cin nata abincin ita da fadeelan, nadeeya ce tayi saura,don haka suka barta a falon suka wuce daki don ta shiryata ta bata maganinta tasha.

Toilet ta kaita, kamar ko yaushe yanzu ta fara canza pattern na wankanta, zata hada mata kayan wankan gaba daya,tayi mata tsarki ta wanke mata bayanta da sauran inda hannunta bazai kai ba,sauran kuma saita tsaya tana kallonta tayi da kanta, tanayi tana gyara mata har su kammala.

Sanda yayi sallama dakin basuji shi ba,suna bandakin tanata tsokanar fadeelan saboda yau ta dage bayan nata ma zata wanke da kanta.

A nutse ya garasa shigowa,ya maida murfin qofar ya rufe, idanunsa suka sauka akan dressing table din fadeelan inda kayan baccinta maganin nata da sauran tarkacen kayan nata suke.

Kai tsaye ya dauki robar maganin yana dubawa,sak irin maganin da yasan yana siyowa da kudinsa va damgashi ga hajiva garama har na tsahon watanni shid,bayan wata shidan kuwa baya taba batan lissafi zai sake kawo wani na wata shidan.

Bude robar yayi ya zazzago maganin.

Shine asin da asin babu banbamci, sai ya maida murfin maganin ya rufe ya maidashi inda vake vana fadin
"Hasbunallahu wani'imal wakil" wane sashe na zuciyarsa kuma na tambayar sa,waye yake bata kudin siyan maganin?.

Lokaci daya komai ya rikice masa,lissafi yaso qwace masa,ga hajiyan da wani magani sabanin wanda ake baiwa fadeelan, ita kuma gata da irin maganin fadeelan ba tare da yasan waye yake siya ba.

Komawa yayi ya zauna saman sofa bed,har ta gama wankan suka fito tana tsane mata gashinta da hoodie towel din data rataya mata saman kanta.

"Abby...." Fadeela ta fadi, abinda ya jawo hankalin s
ahar sal tadan ja da baya tana boye jikinta a qofar.

"Abbyyy..." Maganar yarinyar ta magale mata a maqoshi,a hankali yatsun hannunta dana gafafunta suka fara motsawa suna shacking.

Dukkaninsu suka fahimci abinda ke shirin faruwa da ita,lokaci guda kuma kowanne ya taso da mugun hanzari suka nufo fadeelan,shi ta gaba s
ahar ta baya,suka kuma isa gareta lokaci guda tare da rarumota cikin jikinsu saboda kada tayi mummunar faduwar da zata ji ciwo.

Shi yayi nasarar rungume fadeelan,yayin da s
ahar ta saki wani irin kuka mara sauti cikin narkewar zuciya tana kiran sunan fadeela
"Shshshsh" ya fada yana dora yatsansa saman lips dinsa duk da cewa shima cikin tashin hankalin yake
"Stop crying" ya sake fada da muryarsa da taynkaushi.va mige a nutse ya kaita saman sofa bed ya kwantar da ita sosai yana ambaton sunan Allah a ransa.

Ta dauki tsahon kwanaki masu dama rabon da ta samu wannan attack din,kusan zai iya cewa harma ya manta,ya kuma tsammaci lalurar ta tafi kenan.

Idanunsa suna kan agogo yana yana lissafa adadin mintunan kamar yadda ya saba,yayin da sautin kukan s
ahar ke shiga masa kunnuwa,sai ya dinga jin kamar ana soka masa allura cikin qwaqwalwarsa,wani irin ciwon kai ya fara saukar masa kadan kadan har cikin idanunsa.

Wannan karon bata gara ba akan mintunan data saba yi, ta bude idanunta a hankali tana kallonsu.

"Aunty N,faduwa nayi ko?
na dauka na warke na daina faduwa" furucin da ya sanya s
ahar tsananta kukanta,hawaye masu yawa suka jige mata fuska ta kasa controlling dinsu, gaba daya hannuwanta suna cikin na fadeela ta rigeta tsam
"Zaki daina daughter, zaki daina in sha Allah very soon, in sha Allah,in sha Allah, i promise" duk da yadda kansa yake sarawa hakan bai hanashi dubanta ba,bai taba ganin hawayenta da kukanta ba kamar yau, kamar ma ta fishi shiga tashin hankali.

A nutse ta mige ta dauko tissue ta dawo ta zauna a gefanta tana share mata majinar data zuba daga bakinta hade da yawu.

Hannu fadeelan ta miga tana share mata fuska
"Ki daina kuka anty N,na dauka na warke ne, amma ai na saba" migewa tsaye yayi yana saka hannunsa a aljihun wandonsa kansa yana sake sarawa,yanajin kalaman fadeela har cikin zuciyarsa,yana jin kamar ya gaza.
_WASHEGARL
Cikin jikinta fadeelan ta kwana a daren jiya,da safe ma tace yau ba school, tunda juma'a ce ta zauna a gida ta haqura.

Da safer tayi mata duk abinda ya kamata, duk da cewa Zuciyarta babu dadi,haka gangar jikinta babu kuzari, amma haka ta daure ta koma sashensu.

Me share share ta samu yana aikinsa,kamar yadda toufeeq din ya maidashi akin sassafe, shida zuwa bakwai ya gama komai,idan kuma ya makara saidai ya bari kuma sai bayan sun fita office.

Gefe yaja yana sadda kansa gasa sanda yaji sallamarta
"Good morning maa" ya fada ba tare daya kalleta ba
"Morning"' ta amsa masa tana wucewa.

Samun kanta tayi da kallon gofar dakin nasa, ba alamun da mutum a ciki,duk da cewa daman kusan kullum kamar haka qofar yake, amma yau sai taji abun yadan ja hankalinta, duk da haka ta watsar ta isa nata dakin tana shiryawa a hanzarce don kada tayi late.

Ta zarta lokacin shirin nata, amma ga mamakinta har ta kammala shiryawa ta fito bataji wanann sassanyan qamshin nasa da duk safiya yake gaya mata kammala shirin boss din ba.

Ta iso parlor babu kowa, dama jacob ne zaka samu ya raya falon da qamshin abincinsa, shima tunda yaje gida wanna yayi qaura.

Yankewa tayi ta fita farfajiyar gidan saidai kafin ma ta qarasa duka taga babu motocin da suke fita din ko guda daya
"Good morning madam,ya jikin oga din?" Muryar jibril dake magana cikin girmamawa ya furta.

Da dan sauri ta waiwayo
"Jikin oga kuma?" Ta tambayi kanta da kanta,ta tambayi jibril din kamar zubewar kimarta ne, saita amshe kawai
"Jiki da sauqi alhmdlh"
"Allah ya qara afuwa"
"Ameen" ta amsashi.

Qafafunta babu qarfi sam ta koma ciki, taja burki a falon ta tsaya tana tunanin meye abunyi?, at last taga babu wani abu da ya rage illa ta shiga dakin da kanta.

"HUGUMA*
"_TABARMAR KASHI_'
Book 02 Page 30
Sau biyu tana dora hannunta akan handle din tana janyewa.

Tana tunanin yadda zata shiga dakinsa yau a karon farko, tana kuma tunani da tsoron kada ya fasarata.

To amma kuma zuwan ya zame mata tamkar wajibi,don kowa a gidan da zai buqaci jin yanayin lafiyarsa ita zai fara tuntunba daga bakinta kuma za'a so aji komai.

Uwa uba fadeela, data tashi ta tabbata abby din zata nema.

Kuma ko babu komai rama alkhairi sai dan halak, shine mutum na farko daya fara kulawa da kuma lura da sauyawarta lokacin da ciwon kanta ya motsa.

Sama sama ta soma jin kamar muryar meenal daga falonsu,wanda daga shi sai hallway din da kuma bedrooms dinsu.

Bata sake tunani na biyu ba ta murda gofar kawai ta shige.

Dai dai lokacin da yake kwance cikin duvet, bai jima da komawa ya kwanta ba,saboda a jiyan bai samu wani cikakken bacci ba,gaba d
aya idanunsa ne suka soye yanata hada lissafin da bai samu nutsuwa a kansa ba sai da zuciyarsa ga bashi gamsuwa da rinjaye akan bangare guda.

Koda ya samu baccin sai tashi farkawa ba sai qarfe shida na safe, alfijir ya fara ketowa sosai.

A razane ya sauko, hanzarin da ya sanya kanshi sarawa ya rige kan yana takawa a hankali ya wuce toilet.

Alwala ya daura ya zauna yayi sallarsa,ya duba first aid kit ya balli maganin ciwon kai yasha.

Yana gama lazumin ya lallaba ya koma gadon yana sake qudunduna a duvet din.

Idanunsa ya lumshe a hankali,yanayin da vake tsintar kansa kowacce asuba ya fara sauka ga jikinsa, abinda bai taba tunani ba saboda ganin yadda ya kwana yana fama da tunani bacin rai da kuma ciwon kai.

Matse jikinsa yayi guri daya vana lumshe idanunsa,abun mamaki sai ga hotonta kar cikin duhun idanunsa sanye da farar gown dinta me qaramin hannutsigar jikinsa ta zuba lokacin da ya tuna yadda jikinta ya gogi nasa,sai ya runtse idonsa da kyau ya juya yayi rub da ciki yana gangame pillow da hannunsa tare da ambatar sunan Allah a sarari.

Duk yadda yayi zaton na wasu mintuna ne zuwa awa komai zaiyi narke masa amma abun ya wuce tunaninsa,maganin ciwon kan da yasha sai yakeiin kamar maganin wani garin garfi ya sha bana ciwon kai.

Sake tura kansa yayi cikin duvet din yana kiran sunan Allah gasa qasa,jikinsa yayi dumi sosai ,sai hucin numfashinsa da ya cika duvet din wanda ke gauraye da sassanyan night scent dinsa,da ya rufe idanunsa ita yake gani cikin mabanbantan yanayin da yake ganinta, idan kuma ya bude idon nanma ba sauqi, abun kamar wani tsafi ko sihiri.

Kamar cikin mafarki yaji tattausar muryarta tana yin sallama cikin dakin.

Tsai da numfashinsa yayi na wucin gadi yana cike da mamaki da kuma tantama, idanunsa a rufe ruf ba tare daya motsa ba, kunnuwansa suna jiyo takunta cikin lallausan carfet din dake dakin duk da takun nata baya bada sauti.

Koda bata zurafafa kalle kalle a bedroom din baiya iska da gamshin da yake fiddawa kadai ya isa gaya mata na musamamn ne fiye da kowanne daki dake gidan.

Wasu irin furniture na alfarma masu tafiya da hankali, luxury curtains da suka mamave dakin suka sanvashi ya sake zama wani luf luf da babu lallai ka iva tantance dare ne ko kuwa rana?.

Akwai wadatar hasken fitilu a dakin har kusan color biyu,farin qwai da kuma light blue sai suka hadu suka bada wata kwantacciyar kala me kvau a kowanne sashe na dakin,frames manya manya dake dauke da ayoyin tsari ne a kowacce kusurwa ta dakin.

A kallon da tayi masa sai jikinta ya bata bacci vakeyi,abinda zataso tayi shine komawa,to amma zuwa lokacin ta jiyo muryar haseena daga bakin gofar dakin, zuwa lokacin ma har ta fara knocking.
Chapter 34 · 0% Book details