← Book details Tabarmar Kashi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 88

Sashe 51

Tabarmar Kashi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana kammala abincin ta fita a kitchen din tana fatan samun wata iskar da babu qamshin abincin a ciki kota samu ta dawo dai dai,ta kama hannun nadeeya ta saka toufeeq a gaba suka wuce, zuciyarta na tuna mata da kalaman da fauziyya ta gaya mata kwanaki uku da suka wuce,wadanda suka sanya maji din dauketa da mari, abinda bata taba yi mata ba kenan.

"Badai yara ba? sai na rabaki dasu rabuwa ta har abada,saina tabbatar miki da cewa ni fauziyya ni kika haifawa su".

Ta jira abinda zai biyo baya akan marin da tayi mata amma har yanzu bataga alaman Mahmud ma yasan da abun ba,hakan bawai ya bata kwanciyar hankali bane, a'ah, ta sani tabbas akwai abinda zai biyo baya.

"Abba ya dawo maji,muna masa sannu da zuwa bai amsa ba" toufeeq ya fadi mata,saita kalleshi da mamaki,don bataji shigowarta ba bai kuma nemeta ba,qilan yau an birkitashi ne kamar yadda ake masa duk sanda akaga dama.

Batabi takan zancan toufeeq ba,sai ta zauna tana jira ta koma dai dai sannan ta iskeshi.

Motsin da ta danji a kitchen ya sanyata yunqurawa babu shiri saboda tunawa da tayi ta baro abincinsu ta cewa da toufeeq "Ina zuwa ku zauna".

Tun kafin ta garasa ta hangi fauziyya a ciki gabanta ya fadi ta kirayi sunan Allah tana qarasawa da gaggawa.

Shigarta yayi dai dai da ware wani abu baqi cikin kwalba da fauziyya tayi tana shirin antayawa a cooler din abincin Mahmud.

Caraf tayi da hannun fauziyya tana kallonta
"Me kike shirin aikatawa maqiyar Allah da manzansa" maimakon ta amsa mata yadda suka saba sai kawai taga ta saki kwalbar,maji tadan ja baya tana duban kwalbar data fadi qasa ta fashe,wani irin wari wari yana fita daga ciki, shi ba warin fiya fiya ba shi ba na maganin bera ba, kafin ta gama wannan nazarin fauziyyan ta zame hannunta ta kama hannun majin ta rige tsam kamar me shirin hanata tabawa,sai kuma taji ta kwazara ihu tana kiran sunansa
"Yaaya!, innalillahi wa inna ilaihi raji'un yaaya kazo ka gani* tunanin maji ne ya juye, ta kasa fahimtar abinda fauziyyan ke shirin alkatawa.

Cikin qasa da second talatin ya iso qofar kitchen din, hannunsa riqe da wasu takardu,wani irin lafiyayyen fushi na kwance kan fuskarsa
"Yaaya,kaga abinda na kamata tana shirin zuba maka,yaaya dama kasheka takeson yi,bata qaunarka" fauziyya dake wani irin rawar jiki ta fada hawaye na wanke mata fuska.

Wani tashin hankali ne va bayvana baro baro saman fuskarsa ya zubawa maji ido, majin da lokaci guda tunaninta ya juye, tsananin kidima da rudewa da jin yadda fauziyya ta juyar da abin kanta lokaci guda ya gigitata
"Shifa?,kece shifa da kanki?, bazan musa zancan fauziyya ba,saboda gashi na gani da idanuna" sai ya watsa mata takardun hannunsa saman fuskarta
"Sati uku cur na fuskanci ana dauke takardun kadarorina,sama da qasa na dinga nemansu daya bayan daya ina rasawa,sai gasu guda shidan cif a dakinki, ashe kin shirya kasheni ne ki mallaki abinda na tara ko?" Wani irin kukan baginciki ne ya balle mata
"Wallahi wallahi bani na daukar maka ba bansan dasu ba" ta fada tana jin ranta yana daci,sharrin kisa da sata duka lokaci guda?.

"Idan bake bace nine kenan nakaisu dakin
naki?,bayanke ki gayamin wanda yake shiga dakina"
"Babu" ta amsa masa kai tsaye,saboda tasan babu din shine amsar
"Gwara da baki wahalar da shari'a ba,kije na sawwaqe miki na gaji da yadda gidana yaqi zama lafiya sanadiyyarki,na sakeki saki daya"
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, allahumma aiirni fi musibati, wa'akhlifni khairan minha" ta furta da madaukakin sauti dake gauraye da sautin kuka, idanunta suna sauka akan fuskokin nadeeya da toufeeq wadanda suke tsaye daga bakin qofa suna kallonta, daga shi har nadeeya din idanunsu cike yake da hawaye,sai taga uban yaja hannuwansu ya fice dasu ya barsu daga ita sai fauziyya.

Dariya sosai ta fara qyaqyatawa wanda hakan ya tabbatar mata itace ta sauyawa takardun guri daga dakin Mahmud din zuwa nata dakin
"Idan asiri baici ba,ai ita kissa bata da magani" ta furta kai tsaye
"Fauziyya" maji dake hawaye ta kirayi sunanta
"Alfarmar sayyadina rasulillahi S A W,yadda kika birkitamin rayuwar aure na,kika hanamin jin dadin gidan mijina,ina rogar ubangijin sammai da gassai ya hana miki jin dadin aure har gaban abada" daga haka bat
qara ba ta wuce dakinta.

A daren taso tabar gidan,saidai kuma abubuwa biyu suka hanata,na farko tunanin yadda zata hada kudin ticket din da zai maidata Algeria,sauqinta daya babban yayanta yayi mata visa ba dadewa ta shekara biyar, kuma shekara biyu kacal taci a ciki,abu na biyu kuma tana tsaka da hada kayanta jini ya balle mata, koda ta isa bandaki sai ta iske bari ne tayi,barin dan tayin cikin da jini ne zalla,ko ubansa baisan dashi ba, dole ta haqura ta kwana tana bigin kanta da jinin barin da take zubarwa,cikin taimako da dafawar Allah zuwa asubah ya tsagaita.

Kafin gari ya waye ta gama shirya komai nata dana yaran,a daki suka iskota ta kamasu ta shiryasu tsaf tana shirvasun toufeeg yace
"Jiya abba baiyi bacci ba maji,kije ki bashi magani"
"Zaiyi toufeeq" abinda ta iya ce masa kenan.

Ga kaya ga murdawar mara ga yara haka ta ratso
falon gidan zata fice a gidan
"Ina zakijemin da yara?" Ta tsinci muryar mahmud
JARMA yana fadi.

Kafin ta waiwayo ya iso gabanta,yasa hannu ya zame hannun toufeeq da nadeeya
"Ba dasu kika zo ba ina ke ina tafiyar mana da zuri'a?"
Fauziyya dake tsaye a gefe ta fada, ranta fes duniya yau sabuwa a gareta.

Gaban fauziyya ya isa da yaran
"Na mallaka miki su halak malak"
"Na gode yaaya,na tabbatar ko ranar qiyama ummee zatayi alfahari da kulawar da ka bani" tayi maganar tana goge hawayen munafurci.

Cikin dakiya da zallar jarumta maji ta tako gaban yaran, ta dora hannuwanta duka biyun saman kawunansu ta furta
"U'izukuma bi kalimatillahit tammat min kulli shaidanin hammah wamin kulli ainin lammah" ta maimaita sau uku sannan tace
"Ya ubangijin sama da gasa,ina neman alfarma daga gareka cikin karamci da adalcinka tare da isar ga bugatar wanda aka zalunta,wannan addu'ar da nayi musu koda ta zama ta qarshe, koda nisan dake tsakanin uwa da
ya'vanta ya wanzu a tsakaninmu kasa addu'ar tayita bibivarsu har garshen rayuwarsu,na damqa amanarsu a hannunka ya mijibancin al'amarin bayinsa" daga haka ta miqe,ta kuma kalli idanun fauziyya
"Zan sake miki addu'a a Karo na biyu kafin na wuce, yadda kika shiga tsakanina da farincikina,ina roqon
Allah ya gimtse naki farincikin a sanda baki taba zata ko kawowa ba, addu'ar da nayi miki rannan,da wadda nayi miki yanzu kadai sun wadatar, ba zan sake kai qararki gaban Allah ba,sai kuma jiran sakamako".

Bata tabajin furucin da ya shiga jikinta yayi mugun kassarata ba irin wannan,amma sam batason majin taga kamar ta karaya,wadan nan addu'o'i biyu suka kasa barin ranta,suka kuma sanyata qudurar anivar kassara duk wani abun da zai zamewa maji farinciki a rayuwarta daga nan har zuwa garshen numfashi,wannan ne kuma ya sanya FADEELA a target na hajiya garama tun ba'a san da wanzuwar mahaifiyarta a duniya ba bare ita kanta.
*HUGUMA*
*_TABARMAR KASHI_*
Book 02 Page 44
Karon farko ta isa gidan aminiyar dake gaunarta dason qawancensu,ta shiga baqinciki da tashin hankali itama tayita roqon maji ta zauna dasu tace a'ah, tabar nigeria kenan har abada daga lokaci irin wannan, alfarma daya take nema tayi mata magana a landline phone dinsu da yayanta ya siya mata ticket na komawa
"Allah ya sawwage ace har saikin nemi yanuwanki" a aljihunta ta siya mata ticket din, kwana biyu kacal maji ta qara ta koma Algeria,wanda tunda tabar nigeria bata gara waiwayarta ba sai a wannan lokacin.

Kawa ga maji ita taci gaba da bibiyar al 'amarin su toufeeq kafin fauziyya ta ganota ta hanata shigowa gidan da ganinsu gaba daya.

Cikin ikon Allah ta shiga neman mai aiki saboda a lokacin ta soma bungasa kasuwancinta da tafiye tafiye,ta kuma qulla aure tsakanin yayanta da daya daga cikin qawayenta,auren da sukayi yarjejeniya tsakaninta da qawarta ta.
tata.

Ruqayya qawar maji ita tayi wuf ta aika da baaba ramatu,saboda yadda da amintar da tayi da ita,ta kuma tabbatar zata bawa yaran dukkan wata kulawa tare da kula da lamarinsu.

A hankali baaba ramatu ta fuskanci yadda fauziyya ta kawar da hankalin yaran gaba daya daga ganin kima da jin maganar kowa,duk abinda ta shimfida ya zauna daram.

Da farko maji na kiransu,idan aka kwana bivu bata kira ba zasu nemi babansu ya kira musu ita suyi magana sannu sannu sai gashi gaba daya daga yaran har babansun sun soma mantawa da wata mai suna MAJI sam cikin gidan,duk wata kewa da qulafucinta da sukeyi ta sanya anzareshi tsaf daga ransu,sai abinda tace sai abinda takeso.

Tun ba'a ie ko ina ba ta raba auren maryam qawarta da dr jarma,ta sake kutun kutun ta aura masa murja itama bayan wasu shekaru ta raba auren da salon kissa da kuma asiri.

Cikin shakarun sai data aura masa mata hudu tana sanyawa yana sakinsu, mace ta garshe da ta aura masa mansura.

Mansura itace babbar aminiya cikin gawaventa, kuma ta kashe aurenta ne don kawai tazo fauziyya ta aura mata Dr jarma,ta fito daga gidan baban labiba ta baro yara hudu labiba auta ta biyar,can qasan zuciyar mansura itama danqare fal da buri da nata qudurin na mallakar Dr jarma da uban dukiyar da ya fara tarawa a dare daya.

Mafarin rashin gaunar da toufeeq yake yiwa mansura din y
a samo asali ne da zuwansa gidan wata rana,a lokacin duka duka shekararsa sha biyar ya samu tana yiwa Dr jarma barbaden magani, wanda kusan maganin nata ne data fauziyya,yawanci mansura ita ke sabuntawa fauziyya aikinta,saboda komai yana tafiya mata dai dai,rayuwa tana mata yadda takeso,bata bugatar Dr jarma ya koma Mahmud dinsa, ta tabbatar inda har yanzu maji na cikin rayuwarsa babu lallai takai matsayin da take kai yanzu a rayuwarta.
Chapter 51 · 0% Book details