Sashe 44
Tabarmar Kashi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Caraf ya kama hannunta ya riqe, sai ya zagaya ta bayanta ya manne jikinsa ta bayanta yana sake riqe daya hannun nata,ya zamana dukka hannuwanta suna rige a hannunsa
"'Na yarda marowaciya ce ke" ya furta cikin hade rai ya miga hannunta dake rige cikin nasa ya dauki plate, ya sarrafa daya hannun nata da nashi hannun ya zuba couse couse din,sannan ya sake mata hannu yana tallafe plate din.
Jikinta na rawa ta rufe tukunyar, tayi taku biyu zata bar kitchen din yasha gabanta yana kai lomar abincin bakinsa.
Da ido ya tsareta yana ci gaba da cin abincin wani irin taste dadi yana ratsashi, duk yadda jacob yakai ga iya abinci,ya kuma sallama masa akan hakan a yau yaji wadda ta dameshi ta shanye.
Yadda baice mata komai ba haka itama bata ce masa ba yadda bata nema ya bata hanya ba shima bai bata din ba,a haka yaci gaba cin abincin yana kallonta,har nadeeya da taji shurun yayi yawa s
ahar din bata fito ba, kuma tanason gaya mata ta fiddo wasu fruit din yaa moha ya shanye wancan,da ta leqo ta gansu a haka,sai tasa sawunta a likkafa cikin sand'a ta koma,kuma har ta koma din ba wanda yaji motsinta a cikinsu.
Lomomi kadan ya rage ya ajjiye plate din saman freezer wadda tafi kusa dasu
"Baiyi dadi ba" ya fada yana yarfar da hannunsa,ya juya ya dauki ruwa ya balle murfin yana sha yana karantar fuskarta.
Tayi algawarin daina biye masa, don haka sai ta rabashi kawai ta fita a kitchen din.
Murmushi ya saki, yadda yaga ta iya jurewa batayi magana ba,duk da ba haka yaso ba, don bakinta yazo ya sake sha, don hakan ba garamin dadi yakeyi masa ba.
Bai ganta a falo ba,cikin dakewarsa wanda ba zakace shine ya gama neman rigima yanzu ba a Kitchen ba yace da nadeeya
"Daga yanzu zuwa ko ysuhe, duk lokacin da hajiya ta fita unguwa ko wani guri ki sanarmin, immediately, but ina bugatar sirri,kin gane?" Kai ta gyada sannan tayi masa a dawo lafiya,cikin ranta tana mamakin dalilinsa na bata wannan aikin.
Kamar zata kifa lokacin da take sauke masa ruwa da drinks sanda yake zaune a gaban Dr jarma.
Tun bayan da yayi aure wanna shine ganinta dashi na biyu,saboda gaba daya ta daina zuwa gidansu.
Ko bayan data fita bayan hannunta ta sanya tana share hawaye, ta gaji da zaman jiran nan, ta qagu alqawarin da mommynta tayi mata na cewa nan da wani dan lokaci zai kawo kansa wannan algawarin ya cika,haqiqa akwai mutane da yawa da sai ta dauki fansa a kansu,hajiya qarama data zama mutum ta farko wadda ta yaudareta game da lamarin toufeeg tana cikinsu,koma tace itace mutum ta farko.
Tun zamansa gaban Dr jarma ya fahimci kamar cikin farinciki Dr jarma din yake, bai taba komai cikin abinda aka kawo masa ba kamar ko yaushe ya gyara zama,kansa a qasa bakinsa cike da addu' ar Allah ya dorashi kan Dr din
"Abba alfarma nazo nema" ya fada yana dan shafa sumarsa dake sheqi.
Zamansa ya gyara yana dubansa
"Wacece alfarma kenan Muhammadu?"
"Abba,don Allah inaso SAHR tayi zamanta a gida,duk aikin da kake tunanin zata tayani, i can do it gaba daya ni kadai,idanma akwai buqatarta, zan ajjiye mata komai a study room dina ta ding aikin daga gida" dan shuru Dr jarma yayi na wasu sakanni, daga yanayin maganar toufeeq kadai ya shanshano wani abu, can gasan ransa dariya tana son kamashi amma ya danneta,sai yadan bata rai kadan
"Yanzunma kanason ka koreta ne da baqin halinka yadda
ka saba ko kuwa?" Da sauri ya girgiza kai
"No, Allah abba ba haka bane"
"To yaya ne?" Yayi masa tambayar yana tsirashi da ido
tare da son qureshi,don yanason samun tabbacin abinda yake zargi.
Sumar sa kawai yayita shafawa,ya kasa cewa Dr jarma komai, baisan ya zai furta masa ba,ta yaya zaiyi masa bayani? abban baisan akwai kunya tsakaninsu ba?
"Muhammadu, ka gayan gaskiya
"Abba....
I don't know how to explain, kawai dai.....
Banason yadda maza suke kallonta,nayi duk iya bakin
gogarina akan hakan ta daina faruwa, har hijabai na dinka mata, amma wallahi abba a banza,abun is annoying me"
Dariyar da Dr jarma yaketa boyewa ta kufce masa, yayi qas da kansa yana kallon yadda toufeeq din da magana doguwa ke masa wahala amma yadda ya karkace yanata rattabo masa bayani wanda simple question ne da a amsa daya ya gama da ita.
Ta wani gefen sai zuciyarsa ta karye yana tuna shekarun baya rayuwa tsakaninsa da SHIFA MAJI,yayi gogarin dai daita fuskarsa ya daga kal yana kallon toufeeq sanda yake fadin
"Don Allah abba a barta, kada kace a'ah" kafadarsa ya dafa yana murmushi
"Daina rogona muhammadu,mutum da matarsa?, ko a
baya ma ai ni bance dole ba, ta fuskar alfarma nazo, kuma naga kayi accepting, ko a lokacin inda kace ba zatayi yi ba ba komai, matarka ce qarqashin dukkan mulkinka da ikonka take,sai abinda kace zatayi,tunda bakaso na janye ta zauna ta kulamin da muhammaduna" sai a lokacin kuma kunya ta saukar masa,yayi qasa da kansa yana qoqarin tuna da meye da meye ne ya gayawa dr jarma din.
"Na gaya maka zanyi tafiya ko? gobe zan wuce Algeria"
ya fadi yana duban toufeeq
"Algeria abba?"
"Eh, zanje na gyaro wata barna, fatana Allah yasa kada gyaran ya daukeni lokaci mai tsaho, don banajin ko da zanyi shekara zan iya dawowa ba tare da na samu yadda nakeso ba" maganar ta dan Sanya toufeeg a duhu,amma duk da haka yayi masa addu'a da fatan alkhairi sosai, suka fada hirarsu irin ta d'a da uba.
"HUGUMA*
_TABARMAR KASHI_*
Book 02 Page 38
Tunda ya shaida mata ta daina fita company ya
zamana kamar gaba ita ta kaita.
Gaba daya tayi qaura
daga sashensa ta koma dakin fadeela ta tattara
hankalinta akan yarinyar, gefe guda kuma tana soma
musu shirin fita asibiti ita da fadeelan ba tare da kowa ya sani ba.
Cikin ilkinsa ya fara jin rashin dadin sassan gaba
daya,a hankali ya fara taba ruhi da zuciyarsa,tun yana
tunanin ba komai bane, sabo ne kawai da hausawa ke
fadin turken wawa ne, har ya karanci lamarin ya fara zarta haka.
A hankali ya fara rasa baccinsa saidai ya yita juyi saman gadon yana tuna sweet moment din nan,wanda yabar masa wani irin tunani me yawan gaske da kuma dadi da sanyaya zukata.
*******Shi daya ne zaune a falonsu, sai tarin ayyukan da suka sanyashi a gaba,wanda gaba daya sam sam baya jin dadinsu,yana yinsu ne bisa tilas.
Gefe daga kuma abinda ya faru dazun tsakaninsa da meenal ke dawo masa,yarinyar ta koma masa tamkar wata zautacciya,tun tana bashi dariya da mamaki abun har ya fara qureshi, bata kunyar fadi masa komai a gaban kowa, ko a dazu sai da yayi kamar zai mammareta ya samu ta fita a sashen.
Ajiyar zuciya ya sauke yana ajjiye aikin da yakeyi din,jikin kujerar ya koma ya jingina yana dan lumshe idanunsa, babu laifin wadda yake gani sai nata, itakam wai kamar babu zuciya a qirjinta?, da gaske bata damu da al'amuransa ba,bata kishinsa haka yana nufin bata sonshi fa kenan.
Ya baiwa kansa da kansa wannan amsar, abinda ya sanyashi sakin ajiyar zuciya me nauyin.
Fadeela ce tayi sallama ta shigo,ya daga kai yana duban yarinyar sai ya saki murmushi.
Da gaske qiba takeyi abinta,abinda suka debe tsammani kwata kwata daga shi,sun dauka jikinta ne a haka.
Da sassarfa ta iso gareshi, ta fada saman cinyarsa tana kiran sunansa, hancinsa ya shaqi wani daddadan qamshi daga jikin yarinyar
"Ya akayi kika fito at this time haka? bakiga dare ya fara ba?" Juyi tayi a jikinsa
"Ko aunty N batasan na fito bafa?, hmmm cewa tayi itama dare yayi tunda munyi shirin zamu kwanta, kaj ma har turarenta ta shafa min" ido ya lumshe ya bude,yana jin dadin qamshin qwarai, zuciyarsa ta motsa shi qwarai,sai yaji bazai iya jurewa ba,don haka ya miqe yana cewa ina zuwa
Dakinsa ya shiga ya dauki wayarsa ya saka slippers sannan ya kama hannun fadeela suka fito Sassansu suka nufa kai tsaye idanunsa suka sauka a sashen hajilya qarama,yau kwana biyu kenan baiji motsinta ba duka kwanakin ya gaza takawa sassanta ya gaidata kamar yadda ya saba, haka kawai yakejin kamar an cire hakan fit daga zuciyarsa, sake tunawa yayi da kiran da nadeeya tayi masa dazu tana shaida masa,taji hajiyan na magana cikin waya,gobe yinin bikin qawarta, kuma kamar a can zasu wuni.
Kansa ya dauke daga gurin,cikin kamewar nan tasa yayi sallama cikin falonsu nadeeya
Tun bai gama yin sallamar ba ba kuma tare data daga kai ta dubeshi ba gabanta yayi wani irin faduwa, kafiya da taurin kanta ya sanya taqi daga kai ta Kalleshi,sai taci gaba da sabgarta.
Idanunsa a kanta har ya qaraso falon.
Nadeeya ce ta fara gaidashi, ya amsa yans miqa mata hannun fadeela tare da yi mata alamar su tashi a gun lokacin yana gaisawa da baba ramatu.
Sai a sanann ta dan daga kai ba tare data kalli sashen da yake ba tace
"'Barka da dare, ina yini?" Sai ta mige da nufin barin gurin
"Inda ban wuni ba zaki ganni?, dawo ki zauna" ya fada da husky voice dinsa.
Haka kawai jikinta taji ya mace mata,sautin muryarsa ya nuna a dakensa yake, kamar sautin da ta sani lokacin yana MT JARMA dinsa na asali.
"Zaman me kikeyi a nan?" Ya jefa mata tambayar kai tsaye yana soke hannuwansa cikin aljihun wandonsa, tambayar ta sanyata daga kai abisa dole ta dubeshi, sai taji bata da zarrar ci gaba da kallon nasa
"Kula da fadeela" ta bashi amsa tana kau da kai,don ta fuskanci izza ce sosai yau din akan fuskarsa.
Kai ya girgiza, bayason yayi fushi wani me yawa yayi gogarin dai daita muryarsa
"Ki fidda komai naki kizo ki wuce part dinki,can din shine gidanki ba nan ba,karki bari na maimaita miki hakan,just five minutes na baki" daga haka ya wuce ciki.
A daki ya samesu ita da nadeeya.