← Book details Tabarmar Kashi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 88

Sashe 58

Tabarmar Kashi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A rude ta dagota tana tambayarta
"Ke lafiya? me ya sameki haka?" Cikin sheshsheqar kuka ta gaya mata
"Banason qarya da sakarci, yanzun nan na shiga dubashi na sameshi yana bacci,sannan bugu da gari ma babu ta yadda za'a yi toufeeq ya gaya miki haka" masifa da fada sosai ta rufe hajiya garama dashi
"Haka kike gani ko? zan miki qarya ne?, komai nace yayi sai kinyi shakka, bayan a gaban idanunki yakeyin wasu abubuwan?, ina dukka tutiyarki da alfaharinki? ina abubuwan da kike alfahari da su? duk ni a wajena a banza suke tunda toufeeq kawai kin kasa mallakamin shi to wallahi wallahi nan da watanni biyu masu zuwa indai baki mallakamin muradin zuciya ta, kema ba zakiga abinda ranki yakeso ba" tsananin bacin rai ya sanya hajiya garama ware hannunta ta mari haseena, karo na farko da hakan ta faru tsayin rayuwarta
"Baki da hankali ni kike gayawa haka?" Dafe da kuncinta take duban hajiyan
"Ni kika mara momy?" Yadda tayi tambayar a tsaye tamkar hajiyarce diya ta mari mahaifiyarta haseena. kallon da take binta da shi ya sanyaya jikinta,sai a sannan ta tuna, mahaifinta sai da yayi mata bayani kafin va barta ta taho
"Ba'a bata mata rai,saboda tana da wani hali me kama da cutar tsananin fushi" da sauri ta kamo hannunta ta rige tana fadin
"Kiyi haquri, nayi miki alqawarin mallakar toufeeq a wata guda kacal, qasa da abinda kika buqata"
"Ashe zan take faranti kenan kowa ya rasa" muryar hajiya Muneera ta baqunci kunnensu, abinda ya sanya suka maida hankalinsu bakin qofa.

Kaifin idanunsu bai hanata ci gaba da qarasowa falon ba, itama su take kalla
"Ashe da gaske ke din 'yar kunama ce fauziyya?,ni zaki yaudara kiyi wasa da tunani na? ki lasawa diyata zuma a baki yanzun kuma ki maye mata gurbinta da madaci?, tunda haka abun ya zama nafsi nafsi, kowa divan cikinsa ya sani to ki kwana da sanin muddin labiba bata samu toufeea ba haseena ma ta rasashi har abada" tana sauke furucin haseena na sauke mata lafiyayyen mari a fuska.

Tsananin mamakin dava zarta zafin marin da shi hajiya Muneera ke kallon haseena baki bude
"Shashasha. ke har kin isa ki hanani samun muradin raina? ba mutum ba, ko mutuwa banajin tayi wannan isar"
"Kinyimin dai dai,ai da kin barta ma baki maretan ba" sai hajiya qarama ta matso gaban hajiya Muneera din tana mata wani kallo
"Bazance karki taka faranti ba,ki taka,amma ki takashi kina da sanin cewa idan zai bare zai bare ne harda aurenki da YAYA NA, zakiga mummunan sakamakon da baki taba tunanin aukuwarsa ba,karki manta inada qarfin sawa a auro a kuma saki a duk sanda naso hakan" Sai a sannan ta sauke hannuwanta daga kuncinta inda haseena ta mareta
"Bavan kuma va bare da aure na alagarki da yayanki shine abu na garshe da zai garasa zirarewa daga farantin,wannan marin da 'yarki tayimin ki rubuta ki ajiye,sai ya zame muku nadama da ba zaku iya kauce mata ba, fauziyya kada ki manta,ni dake kar tasan kar ne
wanda ya fasa a tsakanina dake baya ya raina Allah"
"Da kyau!" Hajiya garama ta fada sai haiiya mansuran ta tsugunna ta dauki jakarta data fadi a gurin,ta kuma juya tana fita daga sashen cikin matsanancin baqinciki vau ace yarinya kamar haseena da aka haifa a gabanta?,yarinyar da ko autarta ya girmeta ita zata daga hannu ta sauke a fuskarta?.

Gaba daya hankalinsa bai kwanta ba har sai daya tabbatar ya sanya a nema masa visan Germany.

Duka duka so yayi ace ya samu cikin sati guda kacal,amma aka shaida masa bazaiyiwu ba,short stay ma zata iya daukan sati biyu kafin ta samu
"It's too long ya rabbi* ya furta qasa qasa yana karanta bayaman da aka turo masan.

Hakanan don babu yadda zaiyi yayi accepting a hakan ya sanyama ranshi salama da dangana, amma ji yakeyi ranar kamar ba zata zo ba, kamar ba zasu hadu ba.

A ranar bayan Dr anwar ya cire masa garin ruwan yayi booking na daki a bristol palace, suit din da ya saba kamawa ya kama na tsahon sati biyun, sabodia baya jin zai iya ci gaba da zama gida daya tare da hajiya garaman.

Ya riga ya saita camera din da wayarsa, koda yana can zai iya ganin dukkan abinda yaso.

Nadeeya batasan abinda yake faruwa ba kawai taji toufeeg din yace ta shirya kayanta kaman na 2weeks zasu bar gidan su sha iska, hakanan ya tura baba ramatu gurin abokiyar zaman mahaiffyar sajjad, gidan ya rage daga hajiya garama sai masu aiki.
*******Cikin nasara fadeela ta kammala kwanakin da suka diba mata kafin aikin, duka gwaje gwaje sun kammala,hakama shirin aikin nata,aka sanya mata rana da kuma lokaci.

Zuwan ba zata sajjad da afifa sukayi mata ana ya gobe za'a yi aikin,batasan cewa tana da rauni ba sai da taga bestie dinta,ashe dai tana bugatar wani a kusa,ta rige hannun afifa da kvau hawave nason sauko mata
"C'mon bestie meye haka? u are strong woman,kinyi abinda ba kowa ne zai iya ba, kici gaba da addu'a,it will be successful surgery in sha Allah".

A ranar babu wani wadataccen bacci da tayi,kamar ko yaushe ta kwana tana sallah tare da addu'a me tarin yawa.
***K'arfe takwas na safe afifa ta shigo musu da lafiyayyen breakfast da sajjad yayi musu order.

A tsaye gaban madubi ta samu s
ahar cikin black laffaya me adon silver a jiki.

Agogon hannunta silver color take daurawa, komai nata cikin sanyi take yinsa,saidai tayi wani irin mugun sassanyan kyau,kayan sun haskata sosai tare da gara mata wani irin kwarjini, Wayarta ta jawo ta sake duba sagon toufeeq na daren jiya,wasu irin sagonni yake aike mata masu taushi da narkar da zuciya cikin kwanakin saboda koda ya kirata bata dagawa,haka kawai takeii a ranta kamar tayi masa wani babban laifi da bazai gogu ba,ta dinga jin kamar ta shaida masa abinda sukeyi a Germany.

Idanun afifa a kanta har ta garaso, dai dai sanda fa ajjiye wayar ta maida dubanta kan afifa
"Afifa, am afraid" a nutse ta tako ta dafa kafadarta tana murmushi
"Karki saare bestie,khairan in sha Allah" sai ta miqa hannu ta dauko cup na tea data hada mata da plate dindake dauke da tarkacen chips dasu ketchup
"Kici wani abu kafin mu fita" kai ta girgiza
"'Bazan iya ba bestie, tunda nazo garin nan sau daya
nake iya cin abinci" ido ta fiddo
"Saboda me?" Kafada ta dage
"Ban sani ba afifa, kawai inajin cushewar ciki ne,sannannayi loosing apatite gaba dayaa, bakina bashi da taste"
"Kuma a hakan sai a duka yawon shaqatawa
kikazo fatarki tayi wani mugun fresh da haske kamar
wadda ke wanka da madara" wani marayan murmushi tasaki tana kaiwa afifan duka
"Ke har yanzu baki girma ba wai?,ga baby kina shirin ajemana,mutumin da bai iya cin abinci yaushe zai samu irinwannan nutsuwar da kike fada?"
"Eh kika sani ko babies din namu tare sukeson isowa" afifa ta fada tana murmushin tsokana.

Dan tsuke fuska tayi tana harararta
Zafafa biyar
"HUGUMA*
_ TABARMAR KASHI_
Book 02 Page 50
"An gaya miki kowana ayu ne irinki?, besides mani ba auren zama nayi ba wannan shine last aikina da zanyi na gama zama a wajen" dariya sosai afifa ta saki harda kama ciki, sanann kuma daga bisani ta samu guri ta zauna.

Dariyar ta qular da s
ahar
"Waye kikema dariya haka?"
"Astagfirullah,da wanda ya tsargu nake" ta fadi tana fuskewa.

Bata taba gain wauta zalla irinta s
ahar din ba,da gasken gaske autar ce ta gaske, duk yawan buda sagonnin toufeeq da yadda fuskarta kan saki a duk sanda ta gama karanta sagon afifan na karance da shi daga jiya zuwa yau din,amma duka wanna ta tattara ta ture,
itakam zataso taga ya wanna drama zata kaya.
_muma zamu so mu gani ni da jama'ar zafafa_
Sai s
ahar din bata sake cewa komai ba don vau
din bata jin kowanne wasa da afifan zata yi mata zaiyi tasiri, amma hakanan maganar baby din data fada saita tsaya mata a rai.

Ta yaya zata samu wani baby?, bayan ko kafin ta taho tayi period, kuma zuwa next week take sanya ran zuwan next period dinta,sannan ko a yanzun tana jin cramps a mararta, amma idan ya tabbata fa baby dinne? ta yiwa kanta da kanta tambayar,sai kawai ta samu kanta da subucewar murmushi a fuskarta wanda ita kanta batasan dalilinsa ba.

Kurba uku kacal ta yiwa tea din taji ya cika mata ciki fal, qamshin madarar dana Lipton din ciki yana son hautsina mata ciki,sai ta ajjiye tana duban afifa dake cin abincinta tuquru kan jiki kan qarfi.

Kaman zatace wani abu sai kuma ta janye idanunta, tuni afifan ta ganta, murmushi ta saki
"Bestie wannan dan naki acici ne Allah"
Sai da dukkansu suka jira afifan na kusan minti
ashirin ta gama lodin abincinta sannan suka fita farfajiyar hotel din,inda taxi din da zata garasa dasu asibitin su ukun take jiransu.

Ko a hanya ma shuru ne nata,tayi nisa a duniyar
tunanin me ranar ta vau zata haifar musu? farinciki ko
akasin haka?, abinda ke qara sanyaya mata gwiwa daya ne,dukkan sakamakon da zai biyo baya ITACE SILA ALKHAIRI KO AKASINSA.

Da gudu fadeela ta sauko daga saman gadon ta
rungumeta tana kiran sunanta
"I missed you anty N" sosai s
ahar ta rigeta hawaye
nason zuba a idanunta amma tana danneshi, ta tsugunna a hankali ta rungume fadeelan cikin jikinta hawayen na zartowa.

Har an aske area din da za'a yi mata surgery din.

Tsanar hajiya garama ta sake cika a zuciyarta sanda fadeelan ke fadin
"Abby bazaizo na ganshi ba?" Banda gudun sharrinta, ta yaya za'a yiwa fadeela aiki irin wannan toufeeq baya gurin? baima sani ba?.

"'Zaizo in sha Allah my fadee, kada ki damu"
"Yaushe anty?" Ta sake tambayarta tana rungume a jikinta
"Yau in sha Allah" taji afifa ta fada tana riqe hannun fadeelan a tausashe.

Ajiyar zuciya s
ahar din ta saki, har a ranta taji dadin yadda afifan ta kubutar da ita, don batason viwa fadeelan qarya.
Chapter 58 · 0% Book details