Sashe 74
Tabarmar Kashi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Irin nau'in kulawar da ta sanya ta dinga hango tsananin wauta da sokonci da take kallon abinda adam ke mata a baya da sunan KULAWA,sam sam babu hadi tsakaninta da wanna kulawar ta ainihi da toufeeq yake nuna mata.
Sassanyar soyayya me tafiya da imanin diya mace, duk kuwa da cewa bashi da damar shiga gonarsa yayi ban ruwa,amma a hakan daga ita har shi cikin wani irin aminci suke.
Baisan lya adadin sau nawa bakinsa ya furta godiya ga ubangiji ba,wato inda Ubangly bai cire ameesha daga rayuwarsa ba haka zai tabbata cikin quncin kurkuku da sunan AURE?,haka zai dawwama cikin mayaudariyar soyayyarta wadda bata da ma'ana ko gardi ko kadan?,cikin kwanakin KHADIJATU SAAHAR ta zame masa ALJANNARSA TA DUNIYA kamar yadda taci alwashi.
Komai nata a nutse yake da want inn tsari me tsayawa a zuciyar namiji,tana da want irin Kula da takatsantsan a komai nata da sanya farincikinsa a gaban nata.
Sun hadu sun kulle sun dinke sun zama cikakken abu guda.
_RAMIN KARYA kurarre ne_*
karfe uku na rana jirginsu ya sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na mallam aminu kano dake garin kano.
Jirgin da yayo dakon iyalin DR MAHMUD JARMA da kuma surukansa.
Toufeeq da sahar,dr din da kansa
da sarautar mata maji, afifa da hayatee dinta sajjad, sal kuma sister nadeeya da shalelensu fadeela, daga gefe kuma hajya qarama ce dake ankare da takun kowa,cikin ranta da zuciyarta kuma tana jin duk wannan scenes din ya qare tun a Germany,dukkansu sun gama cin gaajiyar soyayyarsu, a yanzu lokaci ne da kowa zai girbe hukuncin data tanadar masa.
Duk da haka babu abinda ta tsana irin idanunta su sauka akan maji da Dr, ko kuma s
ahar da toufeeq,basu ba hatta nadeeya ta sakawa ranta wannan karon ba zata sassauta mata ba,ita kanta afifa saita fita daga da'irar danginsu tunda ta silar saahar ta shiga family din.
lauranin masoyan guda biyu,zaka rantse da Allah saboda hutunsu da jin dadinsu yasa aka shirya tafiya garmany, daga toufeeq din har saahar sunyi wani irin kyau sunyi fresh cikin sati biyun da suka qara akan kwanakin da suka shirya tahowar.
Saahar ya hade mata da yanayin cikinta wanda ya samu cikakkiyar kulawa da tabbacin zamansa dai dai bisa mahaifarta, ya kuma sake zuba mata wani irin kyau kamar 'yar sarkin aljannu.
Toufeeq kuwa zai iya cewa kafff!
Tsahon rayuwarsa bai taba samun nutsuwa makamancin wannan a rayuwarsa ba,nutsuwa ta ainihi tun daga gangar jiki zuwa ruhi.
Ko da soyayya bata burgeka kana kallonsu zasu baka sha'awa ta kowacce fuska,sai nan nan yakeyi da sahar din tamkar sarauniyar matan duniya, o yaya ta motsa sar ya tambayeta
"Me kikeso ne moonbeam?" A sannan dumin jikinsa kadai take bugata,amma tana jin kunya da nauyin nuna masa,ta tsinci kanta a wani yanay na tsananin son kasancewa dashi.
Sanda ta fahimci hakan hankalinta ya tashi,ba da wanda zata iya maganar dashi sai bestie dinta.
Dariya afifa tayi sosai kamar zata kifa akan dan matashin cikinta,har sai da saahar da zuciyarta yanzu yanzu zakaga tazo kusa tace da ita
"'Ki yarfani yadda kikaso,dama aini na kawo kaina ko?"
Rigo hannunta afifa tayi tana qoqarin saita kanta
"Ki yafemin Bestie, Allah bazan ya riqe dariyata bane, nasan wannan yanayin zar yiwa moha dadi qwaral,ashe akwai wanann lokacin zaizo?"
"Ban sani ba,sakeni"
"Zauna kiji" ta fada tana daidaita dariyarta,sannan ta zauna tana fuskantar saahar din.
"Akwai yanayi irin wanann dake iya samun mace me ciki dama, saboda qaruwar hormones dake jikinta, amma karki damu,tunda kwanakin da zaki wake ki koma mu'amalarku yayi,ba wani matsala, kibar toufeed yaci karensa kawai babu babbaka,nayi imanin zai sake haukace miki ne kawai, saboda a yanzun jikinki na sakin sinadaran da suke sake maida mace cikakkiya qwarai,kada ki damu,zan fahimtar da hayatee,ya daukawa yaa toufeeq hutu a kowanne branches na Kamfaninsa dake kowacce qasa har sal ya gama biyan bashin dake kansa" dariya wannan karon bestie din nata ta bata, sal kawai ta dungure mata kai,amma qasan ranta kunyar aritan takeji,itama ta fahimci haka sai tace
"No boundaries between us bestie, komal nawa ya shafeki, kamar yadda komai naki ya shafeni".
"Tunanin me kikeyi moonbeam?" Ya tambayeta yana dan Jan hancinta,kanta yana kwance akafadarsa
"'Ba komai" muryarsa ya sassauta yana yin qasa da muryarsa
"Na gane komai fa, kuma zan biya duka basussuka,ina
tsoron qetare ryaka ne maji tace nayi wani abu da ba dai dai ba ta daukemin Kai,shi yasa nayi kawaici na qara wadan nan kwanakin akai, amma definitely am craving for you" sunne fuskarta kawai tayi ta rasa amsar bashi.
Madubi hajya mansura ta dauka tana sake kallon fuskarta da kyau, kamar yadda labiba ta kasa zaune ta Kasa tsaye,duk bayan mintuna saita duba make-up din Tuskarta.
Dukkaninsu ita da mahaitiyar tata sun shirya tarbar uba da dansa, bayan cikakken shiri da kuma tabbacin da suka samu daga bakin sabon boka na musamman da mansura ta canza saboda gain bayan hajiya qarama.
A yau din kacokam ta sauka gidan toufeeq don tarbar mijinta, labiba kuma ta tarbi touteeq ta Kuma ci gaba da zama a gidan tana farautar zuciyarsa kamar yadda tayi imanin hajya qaraman na cusa haseena cikin lamuransa ta qarfi da yaji don samun shiga a wajensa.
Taci alwashin wannan Karon babu gudu babu ja da baya, kanta tsaye zatayi fito na fito da hajiya qaraman,ta kuma gama shirya duk wata hujja akan hajiya garaman koda zata nemi kawo mata wargi ko ta Kawowa shirinta tarnaqi.
Manya manyan hujjoji ne da ake tanada saboda rana irin wanann,manyan hujjojin da kake ajjiyewa saboda tarwatsa maqiyi kuma abokin adawa a duk sanda yakejin zai tsallake lyaka da kuma gonarka.
Karo na uku hajiya mansura ta sake leqawa da
Kanta farfajiyar gidan ta window din sashen Dr jarma wanda bazai iya tuna yaushe rabonsa da shi ba.
Da kanta ta sanya akayi masa gyara na musamman saboda zamanta a nan dinne kadai zai iya bata damar aiwatar da burinsu hankali kwance.
Duk da ta fara qaguwa da jiran isowarsu amma zuciyarta fes take saboda albishir din data samu daga mutumin da take Kira da malam.
"Akwai nasara a goben guda d'aya,akwai faduwa da asara guda biyu" bayanan da yayi mata kenan, bayan ya sake bata tabbacin hajya qarama na daya daga cikin faduwa da asara guda daya cikin biyun da ya lissata
"Nike da nasara!, tabbas nike da nasara!!" Abinda ta maimaitawa kanta kenan,saboda tako ina idan ta juya tunanita nasarar take hangowa kanta,cikakken shirt ta yiwa kanta da take da yaqinin babu faduwar!!, nasarar dal!...
-tofa jama'a, maji ma gani wai an binne tsohuwa da ranta,maga wake da nasarar,wake da asarar da kuma faduwa_
Zafafabiyar
"HUGUMA*
*_TABARMAR KASHI_*
Book 02 Page 64
Dukkansu suka mige sanda sukaj| qarar bude gate din gidan tare da qarara shigowar ayarin motocinsu su
MT JARMA.
Kallo sosal hajiya mansura ta mayar kan labiba
"Wannan karon babu sauqi babu sassauci,babu kuma daga qata,fatatawa ce ta gaske,yaqin sunquru za'a yi tsakaninmu da duk wanda zai hana mana cikar burinmu,ni dake kowa yayi amtani da damarsa ya samawa zuciyarsa abinda takeso" kai labiba ta jinjina cike da gamsuwa
"In sha Allah mama" tare suka fara takawa suna fita zuwa harabar ajjiye motoci na gidan, don zuwa yanzun sunsan duka motocin sun isa can.
Lissatinsu ya basu dal dal, sanda suka isa din duka suna qoqarin fitowa daga motocin, banda toufeeq, da s
ahar dake zaune cikin tasu motar kamar basu shirya fitowar ba,ya tsareta da fararen idanunsa yana Kalionta bayan ya dauke kallonsa daga duk jama' ar dake farfajiyar gurin, kama daga ma'aikatan gidan da haseena dake riqe da hannun hajiya qarama dake qogarin fitowa da mota,har labiba da ke isowa gurin.
"SAHR
...bana buqatar.....
"Shshshsh" tace dashi tana dora yatsantsa kan labbansa fararen idanunta masu wani irin haske ta zubesu a cikin nasa
"Kada kace komai,duk wadan nan tarkace nima bana bugatarsu,for now ya kamata su nisanci rayuwar mijina ko? idan ba haka ba zasuy nadaman cusa kansu ga rayuwarka,am new version of saahar, ba tsohon version din da suka sani bane" a hankali ya kama yatsanta dake kan labbansa ya tura bakinsa yadan tsotse kadan.
Da sauri ta fuse hannun tsigar jikinta na tashi tana masa nuni da fadeela dake zaune gaban motar, kafadunsa duka biyun ya daga sannan ya rausayar da idanunsa ya maidasu waje shi da ita duka suna ci gaba da kallon wajen.
Cikin takun kissa da jan hankali hajiya mansura ke takowa zuwa gurin har ta iso bakin motar dr jarma
"'Barka isowa,marhaban da......." Qafewa kalaman bakinta sukayi suka tsaya mata a wuyanta,su basu fita ba su basu koma ba,wani irin abu ya tsarga mata wanda ya haifar da tsatstsafowar gumi daga kowacce kafa ta jikinta sakamakon ganin maji da tay na fitowa a motar mazauni daya da Dr din.
Duk wata walwala tata ta janye kaff!.
Bata taba zaman kishi da maji ba, amma tayi imani zaman kishi da matar bazai taba yi ma kowacce macce dadi ba,duk wadda kuma tayi gangancin aikata hakan tabbas zata iya kwasar kashinta a hannu.
Da boka da malam cakude da tuggu da makirci amma tsahon shekarun da tayi da Dr din basuyi nasarar cire maji dari bisa dari daga zuciyarsa ba,ta wahala ta wannan fannin da tsantsar baqin kishi, wanda ta dinga ji inda tare suka rayu da maji babu abinda zai hana zuciyarta bugawa fes.
Murmushi hajiya qarama ta saukewa fuskar hajya mansura,ta tabbatar a yau boom na farko da zai fara tayar mata da kan mansura batun maida auren mijinta ne da tsohuwar matarsa da tayr imanin mansura din bata sani ba,kuma tasan itace mutum ta farko da zata fara aje zarginta a kanta,to ko hakan ma yayi mata,wannan zai qara mata tsoronta cikin zuciyarta hadi da shakkarta,zai kuma sake dasa mata cewa ita din ta isa da yayanta kuma kome tace ya aikata zaiyi din,duk da lamuran sun fara sauyawa.
Murmushin da ta gani a fuskar fauziyya shi ya sanyata hanzarin maida nata murmushin saman tata fuskar itama,ta sani murmushin fauziyya irin wannan ga abokin takun saqa ba alkhairi bane,sai ta sake matsawa tana yi masa maraba,fiye da rabin hankalinta nakan maji.