← Book details Tabarmar Kashi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 88

Sashe 69

Tabarmar Kashi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maji na zaune saman abun sallah har ya tashi ya bude mata gofar tayi masa bayani suka rankaya suka fice.

"Lafiyarki fauziyya?" Dr jarma ya tambayeta
"Yaava,plaza ta gaba daya wuta ta cinye ta" ta fada tana sakin kuka me ciwon zuciya.

Guri ya samu ya zauna yana maimaita innalillahi wa inna ilaihi raji'un shima.

Dukka shagunanta ne a ciki da ta zuba kaya iri daban daban ake saida mata,wadanda ta bada haya basufi kaso daya cikin hudu ba.

Da ayar ya samu ya lallabata ta tsaida kukan
"'Kada ki damu, za'a san abinda za'a yi in sha Allah" wannan magana tasa ta dadada mata qwarai, tasan zata rage asara sosal daga wajensa,shi yasa ma bata gaya masa babu kaya masu yawa a dukka shagunan ba,don an kammala ciniki da lissafin shekara ta maqare duk wata dukiya tata a account, tana shirin zana tayi kasafi tayo order na dukka kayayyakin shagon nata a sake sabon zubi da lissafi sai kuma ga wannan tafiyar ta Germany ta taso mata.

Awa biyar tsakani, da safe likita yana dubata dr jarma na gefe suna magana da nadeeya kira ya shigo mata wayarta.

Da daga wayar da fasa kukanta hadi da fusge hannunta duka cikin minti guda tana sake fasa kukan
"Daya plaza din tawa data ragemin yaaya wadda tafi kowacce girma,itama ta gone tun daga sama har casanta yaaya
na shiga uku,wanne irin ibtila'i ne haka?"
Dr jarma yadan rufe idonsa kadan ya bude yana kiran sunan Allah, kansa yana sara masa da wani irin ciwo,gaba daya jiya bai samu isashen bacci ba wajen rarrashin maji data tubure masa kamar bata taba gainsa ba a rayuwa yanzun kuma ga matsalolin fauziyya daya na bin daya da wanne zaiji?

"Kiyi haquri ki kwantar da hankalinki,kinga yanzun nan likita ke maganar jininki bai sauka ba duk da magungunan da suka baki,zaki iya samun matsala kowacce lokaci muddin kikaci gaba da wanann abun"
"Ya kamata na koma gida yaaya na bincika meke faruwa, manyan plazas har biyu yau babu ko daya?"
"Karkiyi sabo fauziyya,Allah yana iya jarabtar bawa a duk lokacin da yaga dama bawai sai da dalili ba".

Tsam nadeeya da haka kawai takejin takaicin yadda take sharban kuka kamar yarinya qarama ta miqe tana fita qasan ranta tana jan qaramin tsaki.

Zafafabiyar
"HUGUMA*
*_TABARMAR KASHI_*
Book 02 Page 59
*****Tunda gari ya waye ta fara maganar tafiyarsu
asibiti,yana cikin duvet yana wani almurin bacci da
ahar din tasan na neman magana ne kawai, don sau
uku tana kamashi yana binta da kallo tana kai kawon
nata shirin tafiyar.

Koda ta kammala gabansa ta
iso, idanunta a qasa a kuma shagwabe tana lanqwasa
yatsun hannunta
"Please na gama fa,kai nake jira" kallon qasan ido yakeyi mata zakayi zaton baccin yakeyi har yanzu, tayi masifar kyau,shigar da tayi ta karbeta,inda yana da hali wani abu shapeless zai samu ya lullubeta ta yadda babu me iya genta har balle yaga tudun qirjinta ko na mazaunanta
"A bani coffee to" ya fada muryarsa can gasa
"Okay" ta fadi da hanzari tana juyawa.

Mini coffee maker ta kunna ta hada masa irin wanda yakeso har two cups, duk abinda takeyi din yana kallonta yana dariya qasan ransa, tare da tuno abinda ta jiyar dashi daren jiya wanda shi kam bai taba sanin akwai wannan abun ba.

Gabansa ta iso ta tsaya da mini tray tana cewa
"Ga coffee din" dan Jim yayi kamar bai jita ba,sai kuma ya miqe yana yaye duvet din,ya zauna sosai saman gadon ya miga mata hannu yana kallonta.

Tray din duka ta miga masa, hannu yasa ya karba,da hanzari ya ajjiye shi saman bedside table dai dai sanda ta juya ya saka hannunsa ya kamota,fincikota yayi a tausashe sai gata gaba daya cikin jikinsa
"Me yasa baki da wayo kullum,ni da nace ki bani hot coffee saiki bani cold coffee?" Ya fada yana riqe da fuskarta yana kallon cikin idanunta.

Zare masa manyan fararen idanunta tayi tana cewa
"Sai dava tafasa fa sosai,ka duba ka gani"
It was not hotter than you,and ba wani hot coffee da ya fiki,i like hot shower,a regular shower but with me in it"
"Don Allah,na yiwa fadeela alqawari zamu iso da wuri"
Tsayawa yayi da abinda yake shirin yi, yana dubanta da jirkitattun idanunsa
"'Me yasa zaki hukunci bayan kinsan idan baban fadeela yana guri rayuwarki da lokacinki duka nasa ne?" A yadda ta hangi fitina fal idanunsa tasan muddin bata lallabashi ba tsaf zai iya soke fitar ma
"Sorry i make a mistake but bazan sake ba" ta fada tana hada hannuwanta guri daya tana dan boye murmushin. fuskarta saboda yadda ta fahimci tayi masifar yi masa yankan hanzari.

Kansa yadan juyar gefe guda
"Na fahimci idan akan fadeela ne zaki iya komai shine kikemin wannan 'var murvar don kawai a cuceni ko? yayi
.. na yarda,but i need a kiss please"
"Tashin hankali" ta fadi qasa qasa,tasan kiss a gurinsa kamar wani mabudi ne na bude shi
"Eheen, baki shirya fita asibiti ba?" Ya tambayeta yana taba lips nashi da yatsansa.

Yana gama fadi ta hade bakunansu ta fara masa yadda yakeso din, saidai daga garshe shi ya karba ragamar.

Yadda ta zata din kuwa fara wuce gona da iri yayi, ta kama hannunsa ta riqe tsam don ba damar yin magana da baki, ya fahimci me takeson fada ya daga kansa yana dubanta
"Am sorry for being too forward but your lips make me wonder what the rest of you would taste like da safen nan".

Bai bata dama ba ya warware shirinta tsaf yayi yadda yadda ransa yakeso .

Bayan ya kammala ya sauka ya sauka ya barta yana mata dariyar cewar da takeyi
"Ka karya algawari " cikin kukan kissa da shagwaba
"Eh ai dama indai nine ta wannan fannin na dade da zama rules breaker, but duk da haka am sorry my
MOONBEAM" sai yayi kissing nata a tausashe ya wuce toilet.

Har ya fito tana kwance, ya zaci zai samu ta shiga daya daya toilet din dake parlor ta shirya, qarasowa yayi gabanta fuskarta na rufe cikin pillow
"Hello ko kina son gari ne?" Hararar wasa ta jefa masa
sannan ta sake qunshe kanta,can qasa tace
"Marata ce takemin ciwo*
"Ya salam* ya fada vana tayar da ita.

Da gasken take don sosai ta rigeshi tana cije lips
"Let me help you kiyi wankan mu wuce asibitin sai kiga
likita ko?".

Duk yadda taso dojewa bai fita ya barta ba,sai da tayi wankan ta fito ta shirya duka a gabansa,ga kunya ga ciwo,shi kuwa ya murje idanunsa,saima wani mayen kallo da yake bin ko ina na jikinta dashi har ta gama shiryawa
"Ko na sake warming maka coffee din,bakasha ba" kai
ya girgiza yana murmushi
"'Nooo,I got the better ai sukutun da guda daga wajenki
kunyarsa ta sakata kau da kai, bayajin kunyat baro zance baro baro, sai sun fita kuma waje kaga ya kame kamar ba shine me b'arin zancan nan ba.

Sun samu an gama yiwa fadeela komai daya
Kamata, tasha magani an gyara mata jikinta,sai zaman jiransu.

Sanda suka shigo kamar zata koma cikinsu,sosai farinciki ya cikata,ga abby dinta ga aunty N,duk inda ta waiwaya sune.

Basu wuce awa dava da isowa ba afifa da sajjad
suka iso.

Sanda suka shigo sahar na saman gadon daga gefan fadeela tana bata fruit yayin da ogan yake zaune saman kujera a gaban gadon hannunsa goye a qirji ya tsaresu da kallo.

Migewa yayi ya bawa sajad hannu sukayi musabaha,afifa ta matsa kusa dasu bayan sun gaisa da toufeeq tana duba jikin fadeelan,shima sajjad din ya dubata,sai suka juya suka fice suna magana a tsakaninsu.

Ba jimawa suka dawo,a lokacin ta gama batan tana zaune daga gefanta tana tayata karanta wasu abubuwa da likitan dake kula da sashen magana na qwaqwalwa ya bata.

A tausashe yake jifanta da wani irin kallo har ya qaraso daf dasu.

Afifa ta kula,sai taja jikinta baya tana boye dariya qasan ranta.

"Moonbeam" ya furta gasa gasa yana dubanta.

Kunya ta kamata jin ya maimaita sunan da ya sanya matan a gabansu afifa, ta daga idonta a hankali ta dubeshi, hakan yakeso sai ya marairaice mata
"Ki barwa su sajjad din ita kizo muje kiga likitan" kai ta jinjina, ta sakarwa fadeela dan qaramin littafin tana zamowa daga saman gadon.

Kafin ta qaraso ya sanya hannu ya saita mata takalmanta, kunya da nauyinsu. sajjad ta sake kamata,ta zira takalman a nutse tana dawurwura na abinda zatace da afifa
"A dawo lafiya" kawai taji afifan tace sai bata ce komai ba tayi gaba kamar yadda toufeeq ya bugata.

"Dan tsaya" yace da ita bayan sun fito, ta tsaya cak ya qaraso kusa da ita, sai ya lalubi hannunta ya saka a nasa
"Yauwa to muna iya tafiya,naga alaman turawannan suma mayun mata ne" ya fadi yana wani tsare gida,abinda ya sanya qaramin murmushi ya kubce mata,sai taji dadi gasan ranta, karon farko kenan da taga haka daga wajen mijinta.

Abinda adam bai taba damuwa yayi ba kenan, hasalima shi duk inda zasu shiga qoqari yakeyi aga kyanta,yana alfahari sosai da kyan da take dashi.

Ko cikin office din yana tsaye daga bayan kujerarta kamar wani bodyguard ita kuma tana a zaune.

Qwararriyar gynecologist ce da take a wani department daban a asibitin cikakkiyar musulma ce, abinda ya qara masa nutsuwa kenan,s
ahar tayi mata bayani dalla dalla da harshen turanci
"Ina zargin wani abu" likitar mai yawan fara'a da kirki ta fada bayan ta gama yi mata tambayoyi tare da duba report nata.

Scanning ta fara dayi mata cikin nutsuwa, kai kawai take gyadawa murmushi na fita a fuskarta,sai ta sanya hannu ta kirayi toufeeq tana tsaida na'urar kan wasu abubuwa guda biyu masu suffar wake ko gananun ayaba
"Kalli babies dinka" ta fada tana masa nuni da allon computer din da hannu.
Chapter 69 · 0% Book details