Sashe 26
Tabarmar Kashi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hannunta a qirjinta tana duban tukunyar da ta fara tafasa,qamshin cardamom na 'ana'ana da madara da flavour yana tashi kadan kadan yana cika kitchen din.
Zuciyarta nason fadawa tunani amma tana turewa daga ranta, don batason yau kwata kwata ta kwana da wani ciwon kai bare a gobe ta rasa karsashin fita office a goben kamar yadda Dr jarma ya umarta
Tun kafin ya qarasa shiga qamshin yayi masa maraba,ya lumshe ido yana sanya kai a kitchen din, bakinsa dauke da sallama gasa qasa.
Bata waiwayo ba ta amsa sallamar tana sake gyara yafen dankwalinta,kadan kadan yake dora idanunsa akan fuskarta,da gaske baiga alamun komai saman fuskartata ba.
Ya garasa shigowa yana dauke kansa,ta qasan idonsa kuma vana satar kallon coffee pot dinta dake shirin fara tafasa wadda va tabbatar a nan gamshin da ya game sassan yake fita.
"'Ina kwana" ta fada ciki ciki tana murza yatsunta wadanda ke da sauran shatin jan lallen biki a jiki
"'Idan mutum vace bakisan daraiar ilkinki ba fitsarrun bakin nan naki yace zai qaryata right?" Ya fada yana kafeta da shanyayyun idanunsa.
A bazata maganar tazo mata,sai ta daga fararen idanunta ta zubesu a fuskarsa wani abu me gyalli daga tsakiyarsu ya fusgeshi da qarfi ya maida nasa idanun ya lumshe, abinda dama yaketa son gani kenan, tsakiyar qwayar idanunta
"Ya kamata Jacob ya ganki a haka?" Yayi mata tambayar da wani yanayi da ya tunzurata
"Ya kamata Jacob ya zama yana shiga kitchen dinan?, Kai
ka damu dashi,ni dukkanku ban damu da wanzuwarku ba" shine abinda takeson gaya masa,amma sai wani sashe na zuciyarta ya kwabeta,uwa uba kuma a yau batason bashi damar da zai shanye mata tea ya barta da zafin lebe don haka sai ta kauda kanta kamar ba da ita yake ba.
Hakan da tayi sai yaji abun ya zafafeshi
"Am talking to you" ya fada adan kausashe,har ta dago kamar zata kalleshi sai ta fasa, ta sauka daga kan stool din tana nufar tukunyarta sannan tace
"To" ta dauki garamin rariya ta fara tace ruwan madarar da ya tafasa yasha kayan qamshi.
A nutse ta gama juyewa,ta ajiye kayan ta juya tana barin kitchen din.
Tukunyar data bari a wajen ya kalla,ya danja tsaki yana tambayar kansa tsoron yace ta dafa masa yakeji ko kuwa?.
Kai ya girgiza
"No, bayason raini ne kawai" dole qanwar naqi ya jona coffee maker din yana hada kayan tare da addu'ar Allah yasa yayi dadi.
K'arfe sha biyu da rabi na rana suna zaune a falon, ranar farko kuma karon farko da ta taba zama a falon bawai wucewa ba,hakan ya faru ne saboda nacin da fadeelan ta dinga yi mata
"Please anty N mu zauna kawai a nan,nan din yafi dadi, kuma sai nafi sanin abby ya dawo,daxun yayimin alqawarin kawomin cookies" kumatunta ta kama taja tana murmushi
"Bakin kwadayi,shi yasa kike qara kumatu" hirar da suke ne ta tsaya cak, fara'ar fuskarta kuma tayi gaura duka lokaci guda.
A nutse ta tashi daga durquson da tayi tana duban fuskar IG celebrity MEENAL YA'AQOUB AJI,wadda ta shahara da dora mabanbanta hotuna da fuskokin MT JARMA da Instagram basa gajiya da recommending mata ita tamkar ta buqaci haka daga garesu.
Ta bangaren MEENAL itama sanda take takowa nata idanun suna kan fuskar s
ahar din, wani irin abu me girma yana zarta mata tun daga tsakiyar kanta har zuwa tafin qafarta.
Jikinta dukka ya fara fidda gumi tana jin wani rudani yana shigarta.
Addu'a takeyi qasan ranta.
Ya Allah ya sanya ba wannan bace matar yaa moha, Allah ya taqaita wahalarta ya sanya ba ita bace,muddin hakan ta kasance tasan babu ta inda zatakai labari wajen hada kyanta da take taqama dashi dana s
ahar din.
Duba daya tal ta yiwa meenal din ta dauke idanunta daga kanta,saboda cikin qasa da minti daya sautin muryarta ya tabbatar mata itace haseenar hajiya qarama.
Yadda ta debeta ta watsar itama ya bata amsar cewa ita dince, itace matar da tasha gaban burinta takeson kawowa cikar burinta barazana,wannan tunanin ya sanya ta sake tsuke fuska itama
"Ukhtie....abby dinki yana ciki?" Ta tambaya don gudun karya tsarinsa, kamar yadda a dazun ya gargadeta kan bayason irin wannan zuwan
"Ya fita" fadeelan ta amsa mata a taqaice don ba wani sabo ko shaquwa bane me yawa a tsakaninsu,don meenal din na hannun mahaifinta tun tana da shekara goma sha biyar, kawai lokaci lokaci ne take zuwa musu hutu,tunda kuma ta shiga university ma bata sake zuwa ba sai yanzu data kammala
"Okay" meenal din ta fada, cikin satar kallon sahar ta samu waje ta zauna, ta kuma dora qafa daya saman daya ta fidda tsadajiyar wayarta ta fara dannawa.
Tamkar batasan Allah yayi ruwanta a gurin ba sukaci gaba da hirarsu da fadeela, nadeeya duka yau din bata nan, don haka sai su biyu.
Har zuwa lokacin sallar azahar yayi ta janye fadeela suka wuce dakinta suka bada farali, sannan suka fice daga sashen don komawa sashensu,saboda yau tana da sha'awar yi musu abincin dare abinda tunda ta dawo gidan batayi ba.
Bayan s
ahar din meenal tabi da kallo, tana da izza fiye da tata tana kuma da miskilanci da jin kai da yafi nata yawa yanzun ta ina zata fara quntata mata? ta wanne bangaren ya kamata ta fara ajiyewa rayuwarta bacin rai?, sai kawai ta gyara kwanciyarta cikin qayatattun kujerun falon tayi kwanciyarta hankali kwance,ta dauki. waya ta turawa hajiya qarama tex don kada tayita bulayin nemanta cikin gidan.
"HUGUMA*
"TABARMAR KASHI'
Book 02 Page 23
*****Tsaye take cikin kitchen din tana qoqarin rufe lunch bag din fadeela dake dauke da tarkacen kavan beak dinta na makaranta.
Sanye take da wata lafiyayyar tattausar abaya sagar dubai, da aka sagata da zare da kuma yadi me tsananin kyau da tsada.
Maroon color ce wadda aka yiwa ado da bagi da kuma zaiba a jiki.
Daga ciki kuma wani lallausan cotton lace ne maras nauyi wanda aka yiwa dinkin riga me dogon hannu da straight skirt.
Daurin kanta ya zauna das sakamakon yadda ta yiwa gashin kanta gammo daga baya ta kuma daura dankwalinta ya zauna mata dass da samfurin daurin dankwalin nan da ake kira zahra buhari.
Wani irin tattausan gamshi take fitarwa,wanda ya zame mata al'ada ya kuma kama suturunta da kyau.
Turaren wuta na kaya me asalin tsada wanda take samu takanas daga masu abun wato garin mahaifinta BORNO.
Wani irin sassanyan kyau tayi a safiyar kyau me ratsa idanu da shiga zuciya,ba tun yau ba shigar laffaya na daya daga cikin shigar dake matuqar qara mata kyau da matuqar da kwarjini, takan koma kamar balarabiya tare da fita a ainihin yarenta na SHUWA-ARAB.
Dai dai lokacin da dukka motocinsa da suke fita zuwa kamfani suka gama komai, fitowarta kadai suke jira, harda toufeeq din dake zaune cikin motar.
Sanye yake da wasu kurtas charcoal color da suka dace da farar fatarsa,hankalinsa duka suna kan system din dake cinyarsa yana shigar da wasu bayanai akan meeting din da sukayi a daren jiya shida board members na sabon kamfaninsa da zai fara aiki wata me kamawa, dai dai lokacin da yake sanya ran ya kammala da kamfanin MT JARMA.
Ta cikin eye glasses dinsa ya daga agogon hannunsa daya kwanta luf cikin gargasar data zama tamkar rumfa wa fatarsa vana duba lokaci.
A galla sunyi zaman jiran mintuna goma kenan zuwa sha biyar,baya cikin tsarinsa bata lokaci da saba lokacin zuwa aiki,gashi tana son zama silar haka a ranar farko.
Qaramin tsaki yaja yana ajiye system din, sannan ya buda gofar side dinsa a hankali yana zura gafafunsa waje.
Da sauri elyas ya matso,sai ya daga masa hannu,ya fahimci me yake nufi don haka ya koma da baya yaci gaba da tsaiwa a gurbinsa.
Har ya sako daya qafar ya hangi tahowarsu,fuskokinsu gaba daya cike da wani irin walwala da annuri ita da fadeelan, tana riqe da lunch box din fadeelan,ta kuma rataya school bag din nata still a daya kafadar, daya hannun kuma na riqe da hannun yarinyar.
Sak suka fito a 'YA da UWA,wani abu ya taba zuciyarsa ya kuma tuno masa shekarun baya,a lokacin da yake da shekaru kwatankwacin na fadeelan,lokaci da maji ke riqe hannuwansa kamar haka ta kaishi makaranta sannan ta wuce gurin nata aikin.
Anutse ya zare idanunsa daga kansu,ya maida qafafunsa cikin motar tare da jan murfin motar.
Karo na biyu idanunsa suka sake sauka a kansu.
Dai dai sanda ta zame hannunta daga na fadeela tana gyara yafen lafayar jikin nata,zara zaran yatsunta da aka sakawa lalle a jiya suka bayyana hakan sai ya tuna masa da wani lokaci can baya, ranar farko data mige cikin taron ma'aikata kamfani don ta gabatar da nata aikin.
A ranar dukkan wanda ya kalla cikin mazan dake hall din idanunsa vana kanta, daya bayan daya ya dinga bin fuskokinsu da kallo ba tare da sun sani ba,haushi da takaicin da ya sanya yace ta hada file din kenan zai duba a gida ko office ba tare data garasa cinye mintuna goman da suka rage ba.
A yau ma sal ya samu kansa da sauke dubansa saman fuskokin guards din nasa dake tsaye suna dakon fitowarta.
Daya bayan daya yake nazartarsu,sai ya janye idonsa yana furzar da iska daga bakinsa.
Kusan mutum biyar a cikinsu idan idanunsa sun gaya masa dai dai kamar ita yaga suna kalla.
Jamal daya daga cikinsu ya hanga yana gyara tsaiwarsa tare da gyara zaman glasses dinsa.
Haka kawai yaji wani abu me nauyi yana sauka a hankali saman qirjinsa.
Jamal na daya daga cikin mazan da Allah ya jarabta da son mata,mutum ne me yawan kule kule, abinda ya sanya tasu sam batazo daya da toufeeq ba.
Kusan sau biyu yana dakatar dashi kafin ya samu ya maida hankalinsa ya kuma dai daita kamar yadda tsarin duka yaransa suke.
"Madam
madam" muryar adama daya daga cikin
masu aikin dake aiki a sassan hajiya qarama ta ziyarci kunnenta.
Cak ta tsaya tadan juya kadan har adama ta
qaraso
"Abincin makarantar fadeela ne......inji hajiya qarama" ta fadi a ladabce.
Sosai ta kalli qawatacciyar lunch bag din dake rige a hannun adama, mamaki yana sauka a ranta.