Sashe 53
Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ango kuwa yana tareda manyan mutane Bayan Daurin aure anata gaggaisa wa,dayawa daga cikin mutanan suit ce ajikinsu hancinsu manne da takunkumi, Wanda hakan zai baka tabbacin cewa Yan hukumar efcc ne,kawai ruwan pictures ake ta d'auka tareda shi,yayi masifar kyau cikin shadda fara sol, iri daya data Abba, Ramadan dayake Fama da wasu mutanan shima farar shaddar yasaka Sai sukai kyau susu ukun kamar Dama can har Abban abokinsu ne.
Ana Rabon Goro Abba yatashi yafuto yanufi gida wannan babbar riga Sai tashi sama take(😄)
Cikin sauri jabir ya bishi ya rungume shi tabaya, Abba yana juyowa yaga jabir, cikin tsananin murna yace"jabir?,Wai Kai dinne da gaske?"
Cikin murna yace"nine Abba, angon ne yace Nima in shirya inzo Daurin aure"
Abba ya Girgiza Kansa cikin farinciki yaruqoshi tareda fadin"ikon Allah, to muje, muqarasa cikin gidan"
Adede lokacin su Aisha suka dawo daga wajan kwalliya, anyi mata kwalliya daidai misali bamai yawa ba, tana Sanye cikin farin leshi Riga da zani, dinkin rigar anyi mata bubu,ta daura zanin akan rigar, da farin mayafi me girma, qafar ta taci wani takalmi me tsinin gaske, wuyan ta da hannayenta yasha Adon gold, Sai Jan lallen da aka mata da zanen fulawa na baqin lalle Wanda farar fatarta tasake haska lallen, sosai ta dauki hankalin mutane, jabir yana ganin ta yace"qawar Hajja amarya"
Tanajin muryarsa ta yaye mayafin kanta tatafi da sauri ta rungume shi, gaba daya mutanan wajan Sai dariya suke musu, Abba kuwa bai kulasu ba samari yake kira suka shiga cikin gidan suna futowa da furar da aka Dama wadda taji qanqara tayi Sanyi sosai, Kai tsaye wajan Daurin auren suke kaita, yayinda gidan Jummai Kuma aketa futowa da take aways na abinci Wanda Abba yasa aka kira masa masu girkin hotel's takanas tundaga dutse, sukazo tun asuba suka fara aikin girkin Yan Daurin aure, girki me dadi da tsafta Wanda kowa yaci saiya so yaqara.
Su Aisha suna shiga cikin gidan aka fara amarya, amarya, amarya Ansha kyau, kowa da irin abunda yake fada, mutane da Yara Yan unguwa Sai Binta suke duk inda tayi, yayinda jabir yayi wajan Ummah yashige jikinta, cikin farinciki tajashi sukayi wajan Hajja.
Anan tsakar gidansu aka fara yimata photuna da mutane, kowa soyake yayi photon da'ita, ita kuwa magana take Ina Hajja, Amma Hajja tana can Kai yadau zafi tana Fama da mutane, daqyar fatin kano taje ta janyota, itama leshi ne ajikin ta Wanda Hajiya Mama ta aiko matashi da wasu kayaiyakin Wanda zata saka ranar auren, photon aka fara yimusu itada Aisha, anyi musu yafi a dadi, mutane Sai jira suke Hajja tafita sunaso ayi musu da amaryar, Amma Hajja ta kame Sai style take sauya wa, ango ne yashigo tareda abokan su, Sai Alokacin Hajja tayi can tana musu sannu da zuwa, a tsatstsaye aka kawo musu fura basu Sha Bama, suka gaggaisa da iyayen dakuma sauran dangi, wanda basu ganshi ba suka ganshi, sannan Ramadan yajashi yahade su da Aisha ya kalli me daukar photo yace"yimusu da sauri kafin muwuce"
Shahaab de kunya ce ta kama shi ganin yanda dangin Aishan gaba daya hankalin su yadawo Kansa, shiyasa tunda yashigo bai yarda ya Kalle taba, Amma yanzu da Ramadan yahada su, sosai ya shagala akallonta, harma ya manta inda suke, ya manta da akwai mutane awajan, ya rungume ta tabaya, tundaga Nan masu waya suka fara sana'ah, hannunsa yad'ora akan hips dinta, sannan yazuba mata ido, aka fara daukar photon, Hajja ta Girgiza kanta, cikin qasa da murya tace"fitsararre Dama yasa ba, ni nayi mamakin wannan kunyar"(😂)
Yayi tunanin angama photon, yasaketa yayi hanyar fita, me camera yasake cewa a a ya dakata Sud'an sauya style tukunna, dole haka yadawo yariqe hannayenta aka sake yimusu, sannan cikin dabara ya mintsine ta ahannun suka fice shida Ramadan, da sauran mutanan dasuka shigo.
Sauran mutane Yan Daurin aure sukai ta masa Allah yasanya alkhairi yayinda wayarsa datake cikin aljihunsa alert yake ta shigowa na mutane daban daban babu qaqqautawa, banda masu turo masa message na Allah ya sanya Alkhairi
Saida yagama da jama'arsa, sannan sukayi shirin tafiya, inda yayi magana da Abba agefe, sannan yashige mota suka dauki hanya, daga Nan sauran mutane Yan Daurin aure kowa yafara tafiya, Sai mutanan Garin kawai.
(nabarki da Allah inde kika krnta baki biyaba)
******
Mutanene a zazzaune acikin Babban falon Hajiya Mama, duk Wanda ka kalla kasan gogaggun masu kudi ne sukazo, kowa takama kujera ta hakimce daga masu danna waya Sai masu fira, Sai masu daukar pictures a falon, Sai yanmata masu Hawa tiktok Ana vedio, yayinda ma'aikatan gidan suke kawowa kowa abinci Wanda yaji nama da ganyaiyaki, yanda ciki da wajan gidan yatara Jama'ah hakanne zaisa kasan cewa Ana gagarumin biki a gidan.
Hajiya zaliha dake Gefe a zaune itada mama wadda take Sanye da leshi irinna Hajja sak, tace"gaskiya Hajiya Aisha tsarin gidan naki yasake kyau, sainaga baki ta6a gyaran gida yayi kyau sosai kamar wannan lokacin ba,ansake fenti ansake komai duk acikin wannan qanqanin lokacin"
Mama tayi ajiyar zuciya tace"duk aikin Dan gidanki ne, shifa tunda wannan aure yazo, yakasa zaune yakasa tsaye,ko zumudin Dayayi a aurensa na farko,bakai wannan ba,abun har mamaki da tsoro yake bani"
Hajiya zaliha tayi murmushi tace"nikam Hajiya Aisha, gulma ajali inba'ayi ba amutu, tun tafiyar mu Dubai hado lefen Nan nakeso na tambayeki meyasa yasaki munirat ne?karfa mutane su zagemu ace Dan zai qara aure ne"
Mama tasaki ajiyar zuciya tace"Hajiya Zaliha munirat rabuwa da'ita ai shine yafi, idan bai rabu da'ita Bama to muddin yakawo wannan amaryar cikin gidannan to tashin Hankali za'a yi, bazasu zauna lafiya ba, sofa tayi ta kasheni"
Hajiya zaliha ta zaro idonta waje(😳) sannan tace"kisa?"
Mama tace"kisa fa, shine da yaji tana wayar tana fadawa masu zuwa su kashenin yanda zasu shigo har dakina, saiya saketa, bnda sata datake qunduma masa a wannan Zaman nasu, infada miki, Nan sukazo itada uwarta suka gama borin kunyar su, daga qarshe da sukaga babu Riba suka qarewa Mahmud Gorin haihuwa suka tashi suka tafi"
Hajiya Zaliha tasaki ajiyar zuciya tace"tabdi, lalle munirat anyi butulu, menene Shahaab baiyi mata ba? Kullum suna yawo qasa qasa saikace tsuntsaye, banji dadi ba wallahi, Amma dakika min maganar Gorin haihuwa, saiki tunamin da wani magani da aka kawowa wata yarinya saqo ta hannu na, shekararta Tara babu haihuwa,Amma tana shan wannan magani, wallahi saiga ciki, sauran sa yana Nan agidana, idan ankawo amaryar,zanzo har gida inbata Tasha,in Allah ya yarda Shima zai haihu, haihuwa lokaci ce ai"
Mama tace"to Allah yasa adace Hajiya zaliha"
Haka suka dinga firarsu Sai yamma masu kidan qwarya suka zo, mama ta sauya Kaya suka fita compound aka sake shagalin biki anan, Sai wajan magrib masu kidan suka tashi, daga Nan Kuma Yan yinin biki kowa yayi haramar tafiya, Hajiya zaliha ta dinga bin kowa tana fada masa akwai dinner da za'ayi Bayan ankawo amarya.
Su Shahaab kuwa basu dawo gidaba Sai dare,baima nemi mama ba, kwanciya yayi cikeda gajiya batareda 6ata lokaci ba bacci yayi awon gaba dashi.
******
Kwana biyu Bayan biki, su Hajja sukai shirin tafiya Abuja Bayan sun gama sallamar kowa, fridge dinta tabawa jummai shi, anyi Rabon robobi da dubulan da alkaki na biki, Abba Kam har kuka saida yayi lokacin dayake sallama da mutanan Arziqi Wanda akai Zaman mutunci dasu, gaba dayansu mutum goma ne masu tafiyar, Ummah, Abba, Hajja, Aisha, jabir, jummai, Walida, fati, da mutum daya dangin baban Abba, da mutum daya dangin Ummah, shatar mota suka dauka aka kaisu kano, saboda tacan zasu tashi,Aisha tana Sanye cikin material fuskarta tayi kyau sosai duk da ba kwalliya tayi ba, Amma kana ganin ta kaga amarya, karfe goma shadaya jirginsu yatashi, Sai shabiyu dawani abu suka gama komai Bayan saukarsu, motoci guda biyu sukazo suka dauke su Sai gidan Hajiya Mama.
Aisha dayake tasan gidan tad'an zauna agarin nadan lokaci, batayi wani Kalle Kalle ba, Amma Hajja Kam hanci ta bude da ido tana kallo, Sai surutu suke itada jummai, gashi sun riqe Aisha sun sata atsakiya su Ala dole awajansu amarya zata zauna.
Suna zuwa gida Hajja taga ruwan sojoji
Ta kalli jummai tace"jummai irin wannan sojojin Ina mutum zai iya watayawa yanda yakeso, kinga Dadin qauye fa kenan"
Jummai tace"um ai Hajja A'i wannan dinma wata sabuwar duniyar ce, kiduba kiga gida fa kamar baza'a mutu ba"
Aisha de tana jinsu kanta yana lullu6e cikin mayafi, driver yana tsayawa Hajja takamo hannunta tace"futo da qafar Dama, ki karanta addu'oi aranki harmu shiga"
Haka akayi kuwa, hannunta cikin na Hajja suka qarasa falon bakinta d'aukeda addu'ah, suna zuwa Hajiya Mama tareda Hajiya zaliha suka tashi suka tar6esu cikin farinciki, zama sukai a falon nanfa fira ta 6arke yayinda baqi suka zama Yan kallo Sai kallon aljannar duniyar gidan suke, Hajja ta kalli Mama tace"Aysha Yakubu Wai Dama anan kike rayuwa?"
Mama tayi murmushi Tace"Anan nake, kema yanzu ai kinzo kenan"
Hajja tayi ajiyar zuciya tace"to irin wannan gida inji de bakya mantawa da sallah ko?"(🤣)
Dariya tabawa mutanan falon gaba dayansu, Hajiya zaliha tamiqe taja hannun Aisha Suka wuce Dakin mama, suna zuwa Aisha tasake gaishe ta, cikin jin dadi tace"ke bude idonki Kisha iska, wadancen tsofaffin babu me cewa bude mayafinki ta firarsu suke"
Cikin murmushi tacire mayafin Nata, Hajiya zaliha tace"masha Allah" ganin yanda amaryar tasu Takeda kyau kamar ita tayi kanta.
Waya Hajiya zaliha tayi, Mai gyaran Kai tazo har gida, Kai tsaye d'akin mama tashigo suka wuce toilet itada Aisha,kanta dayasha wanki aka sake warware wa, aka wanke shi, sannan tabarta a toilet din, Hajiya zaliha takai mata ruwan dafaffan lalle Wanda yaji humra yar ubansu, tace ta daure kanta sannan tayi wanka dashi, wankan tashiga tana tunani a ranta wanne irin so mutanan Nan sukewa Shahaab ne? Kowa kokari yake yaga yayi mata abu duk de Dan saboda shi, tana gama wankan tafuto, matar tasake gyara mata kanta, tashafa mata mayuka masu qamshi, sannan tayi musu sallama tatafi, wata hadaddiyar shadda dataji aiki tabata tace"saka wannan kayan, Bari inje kitchen in dawo"
Aisha tace"to nagode"