Sashe 31
Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Munirat ta kalli Aisha, taga Sai wani qara yin fresh take, cikin kwanakin datayi a gidan yarinyar gaba daya sauya wa take kamar wanda ake mata wankan inji, haushinta takeji musanman wannan dogon gashin Nata dayake tsokale mata ido, kwata kwata yarinyar bata kwanta mata ba, tacika rawar Kai da fi'ili dakuma cusa Kai, jide yanda ta shige wa mama daga baqunta kamar wanda suka shekara tare.
Tashi munirat tayi tatafi Part dinta, mama ta kalleta tace"munirat bazata sauya ba, yanzu kiduba kigani ko sallama batamin ba tatafi, tun lokacin da Mahmud zai aure ta naqi yarda, to kinsan sha'anin Dan yau, bazan iya hanashi ba saboda shi kadai Allah yabani, dole in so abinda yake so, dayake sonta yake kamar ransa, saina bashi Dama ya aure ta, tunda akai auren nide banji wani dadi ba, Amma shi Ahaka yake son abarsa"
Aisha cikin ranta tace"Allah yaqara, ai Shima dannaki bawani mutunci ne dashi ba, Gara daya auri daidai dashi, nida zan ganshi ba Dana tambayeshi Ina Yaronsa SHAHAAB? (tofa😂)
Amma a fili saitace "kiyi hakuri mama, watarana Sai labari"
Mama tayi shiru batace komai ba, domin kuwa inda Sabo yaci ace tasaba da halin munirat.
(idan kinsan baki biya kudin littafin nanba kika karanta to nabarki da futowar rana da faduwarta, harga Allah banyafe ba)
Yau satinta biyu a gidan, Kuma yau Abbanta ya dawo daga Saudia, saide ita Kam batasani ba, har Zuwa wannan lokacin batayi waya da kowa ba, Amma takai maqura wajan kewar Yan gidansu, yau jitake kamar ta qwaci waya takira Hajja, batason kar6ar wayar mama saboda kartace mata tana mata shishshigi, haka ta daure tafita wajan mama domin yimata aikin data saba.
Yau mama tashi tayi da son ganin qawarta Aysha Sulaiman Bompai, tayi nisa a tunani, tana tunanin irin rayuwar da sukai itada Aysha Sulaiman, yanzu sun kusa shekara saba'in, Amma da alama basuda Rabon haduwa da juna, shi Shahaab yayi mata alqawarin yin aikin gidan marayun ta akan lokaci, to yatafi Australia har yanzu shiru bai dawo ba, waya Sani ma ko tunda yatafi baya yiwa masu aikin waya?yakamata ya dawo haka, domin ayi sauri a qarasa a saka marayun aciki.
Tana wannan tunanin batasan har Aisha tazo wajan ta ba, tasan yanzu lokacin matsa mata qafafu yayi, danhaka ta zauna tafara matsa mata qafafun
Cikin damuwa mama tafara Girgiza qafafunta, ga damuwar rashin qawarta, ga Kuma shi Shahaab yatafi yayi zamansa, ta dade Rabon Dayayi tafiya yad'auki tsawon lokaci haka batareda sun kasance tare ba, taqi jinin ganinsa nesa da'ita, Aisha ta jijjiga kanta, ganin tana matsa mata qafafun Amma ita Sai jijjiga qafa take, ahankali tace "mama ki tsaya inyi miki tausar, kada qafafunki su kumbura,"
Ciki-ciki ta amsa mata dacewa"Yaya kike so inyi ne? Haka zan tsaida qafata niba itace ba, ba katako ba?tashi kije idan kingaji"
Cikin fishi Aisha ta kalleta tace"babu inda zanje... Rikitacciyar tsohuwa kawai, Ana kokarin nema miki lafiya Amma bakya Gani,"(🙆🏻♀️🙆🏻♀️😳😲)
Mama tayi shiruuu tana kallon Aisha da mamaki, da alama da gaske de yarinyar Nan daukar ta take a matsayin kakarta kamar yanda tafada.
Aisha tasake kallon mama cikin fishi tace"sai kallo na kike kamar baki sanni ba, bazan Dena matsa miki qafafun ba tunda lafiyarki ake nema"
Tana fadar haka tad'auki qafar Tata ta dora akan cinyarta, sannan taci gaba da matsa mata qafafun
(tofa..... 🤔😇, Hali zanen dutse, me Hali...... )
Mutara zuwa yamma insha Allah 🙏🏻
Littafin Shahaab na kudi ne, ki biya naira 300 kacal ki karanta,idan baki biyaba kika karanta wallahi banyafe ba.
0164549488
Amina muhammad
GTbank
Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034
Mrs Usman ce✍🏻
Page 22
Banda kallo babu abinda mama take wa Aisha, Wai yau itace wata yar yarinya take fada mata wadannan maganganun, Kuma abun mamakin da d'aure Kai ko kadan bataga laifin yarinyar ba, ta lura tsakani da Allah yarinyar take zaune da'ita, tunda duk abinda tafada mata made akan lafiyar ta take fadan, Dan qaramin tsaki tasaki, Aisha ta kalleta, ahankali ta ajiye mata qafar ta, sannan ta wuce Dakin maman tad'auko wani Mai datake mata amfani dashi, tadawo falon ta zauna tasake daukan qafar Tata ta dora akan cinyarta ta dinga shafa mata man, saida tagama sannan ta ajiye mata qafar ta ko sallama bata mata ba ta wuce dakinta
Mama ta bita da kallo harta shige daki, wayarta ta d'auka takira Shahaab, yana dauka cikin damuwa tace "yaushe zaka dawo?"
Murmushi yasaki dimple dinsa suka futo, shi Kansa yanaso yadawo kodan Aishan sa, yace "mama nakusa dawowa kiyi hakuri, Ina fatan de babu wata matsala ko?"
"yakamata kadawo saboda aikin gidan marayun Nan"
"mama komai yana tafiya daidai, duk wasu ayyukan Dana Bari Ramadan yana kula da komai, Kuma yana sanar Dani halin da ake ciki, kiyi hakuri nakusa dawowa kinji?"
Tace "yaushe?"
"nanda ten day's insha Allah"
"kwana goma ai yayi yawa Shahaab, please kadawo dawuri"
Yace "to mama insha Allah, ki kula da kanki" dif yakashe wayarsa.
******
Ruwan zam-zam ne a gabanta cikin wata babbar gora tana qulla shi a leda, Jikan iya jummai ne a tsugunne a gabanta, saida tagama qullawa sannan ta kalli Ummah datake kakkarya bagaruwa tace "kawo idan kingama"
Ummah tabata, Kar6a tayi ta kalli Yaron tace "kanajina ko ididi, kakai duk gidajen Dana lissafa Maka, kace inji Hajja A'i tsarabar mamuda ce ta Saudia , kaji nafada Maka karka Bawa jummai ruwan zam-zam dina, har yanzu a hanci na take, kadan nake jira in fato ta" (😂)
Ummah tace "Hajja da kinyi hakuri anbata Shima baisan zaije Saudian Nan bafa, Kuma mu aiki jikanta Amma muhanata ko ladan ganin ido?"
Cikin masifa hajja ta kalli Ummah tace "to Hadiza fadamin abinda yakamata inyi, waini tare kika ganni da jummai ne kokuma kece kika hadani da'ita? Nan tazo har gida ta samfe min jikata tayi gaba da'ita, har yanzu ko d'uriyar yarinyar banqara jiba, ai wallahi tsakanina da jummai saide kallo, da Hankali na ba zanje har gida in dauki jikar ta in kaita uwa duniya aikatau ba, ci muka Rasa ko Sha?"
Ummah tace"kiyi hakuri"
Hajja tace "haka de"
Yaron ne yad'auki robar yafita, Hajja tatashi tafara tace niqan kunun ayarta da'aka kawo mata yanzu
******
Kamar kullum Yauma da safe tatashi tafada kitchen kamar yanda tasaba, suna cikin aiki ta kalli daya daga cikin masu aikin tace "mansura Dan Allah Aron wayarki Zaki Bani inaso nakira mamanah"
Mansura tace "wayata tana d'akin mu, jeki dauka"
Cikin murna tatafi Dakin,wayar tana caji, ta cireta takira Hajja, a lokacin tashin su kenan daga bacci Ummah tana kokarin dora musu abincin Kari, Abba yana Gefe yana jin redio yayi fresh dashi har wata yar qiba yaqara, Hajja tanajin qaran wayar ta, ta d'auka tareda cewa "wannan kira da sanyin safiya kode mutuwa akayi?"
Wani irin farinciki ne yakama Aisha jin muryar Hajja, muryarta ta bude tayi magana cikin sigar tsoratar wa tace "Aljana manuba ceeee"
Hajja tasaki dariya tace "tazo takamamu nida ke, yar bantan uba"
Dariya Aisha tasaki tace "waisaida kika ganeni? Ke Hajja"
Cikin farinciki Hajja tace "haba mesunan qawa, ko a mafarki kika sauya murya kika min magana ai dole nagane,mesunan qawa shikkenan jummai ta rabani dake, mamuda yashiga tsakanin mu, kina samun abinci de kinaci Kina qoshi ko?"
Cikin sauri tace "Hajja inacin duk abinda nakeso, bakiga gidan ba, qaaaaato, ga abun dadi sunaci kullum wani abun ma bansan sunan saba, Kuma ko Hajja har bread ake rabawa duk juma'ah baki gansu ba manya manya fulawa zirrr"
Hajja ta zaro ido tace "kice daqyar kike iya daukan guda daya?"
Zaro ido tayi tace "Biredin?"
Hajja tace "emana, naji kince fulawa zirrr..." haushi ne yakama Aisha tace "Kai Hajja Dan Allah, kinfara ko?"
Cikin sauri tace "Allah yabaki hakuri me sunan qawa, kullum inata kewarki, inji de matar gidan tabaki madubi babba?"😂😂
Fari tayi da idonta, sarai tasan Inda maganar Hajja ta dosa, murmushi tasaki tace "akwai,kuma kullum saina kalla abuna, tunda banaki bane nawane"
Hajja tasa dariya tace "toga Hadiza, Amma bazan baki mamuda ba, har yanzu a wuyana suke shida jummai"
Murmushi tayi tace "tobata"
Ummah ta kar6i wayar suka gaisa, tayi qasa da murya yanda su Hajja bazasu jitaba tace "ki kama kanki de aduk inda kika tsinci kanki, banda shiririta, banda kula maza, ki tsare mutuncin ki, Kuma bance kiyi musu rashin kunyar Nan Taki ba"
Cikin sanyin jiki tace "insha Allah Ummah"
Hajja ce ta qwace wayar tace "zan ajiye number, idan inaso inyi magana dake saina dinga kiranki tanan ko?"
Cikin farinciki tace "to Hajja, Sai anjima"
Bayanta ta jinginar a jikin gadon Dakin tatafi tunani, rayuwa kenan, yau itace take rayuwa awani waje daban, su Hajja suna wani waje daban, Allah yaso tama tariqe number su.
Kitchen din Takoma suka qarasa aikin, bata koma dakinta ba afalo ta zauna ta jira mama tafuto, daga Nan tafara yimata aikin data saba, saide fuskarta adan daure take, ta lura gigin tsufa ne yake damun mama kamar de Hajja idan ta rikice musu wata Rana.
Haka taci gaba da Kula da mama, bata fasa kyautata mata ba, koda tayi niyyar yimata tsiya idan ta tuna nasihar da Ummah ta yi mata saita fasa, mama tanajin dadin yanda Aisha take bata kulawa, yarinya qarama da'ita Amma tasan yanda take kula daduk wasu al'amuranta, da alama Dama can tana aiki a gidansu, ta lura kwata kwata yarinyar tadena sakin jiki da'ita kodan saboda Dan Sa6anin dasuka samu kwanaki ne? Toyaya zatayi? Tunanin qawarta ne ya janyo hakan, duk lokacin data tuna Aysha Sulaiman Bompai tanajin ranta yana 6aci, Gani take kawai mutuwa zatayi batare data ganta ba, burinsu na hada 'ya'yansu Aure, bazai tabbata ba, duk lokacin datake cikin wannan yanayin shi Kansa Shahaab dinnata uzuri yake mata, saboda ta dinga 6acin rai kenan.
Yau satin Aisha hudu daidai a gidan,Kuma yau ne Shahaab yayi wata daya da kwana biyar da tafiyar sa,yau Aisha tana matsa wa mama qafafu mama tace "Aisha yau yakamatakuje ki bude account kema,Amma Naga Sai fishi kike Dani har yanzu"
Cikin ladabi tace "kiyi hakuri mama, Bana fishi dake, Amma maganar kudin Nan kibar ta"