← Book details Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 71

Sashe 30

Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin mamaki tace "kibarshi mama, ba saboda kudi Abbana yaturo ni aiki ba saidon laifi Dana aikata masa Kuma yake hukuntani ta wannan Fannin, koba Dan haka Bama Ina ganinkine kamar Hajja ta, saboda haka zan yi miki komai tsakani na da Allah Kuma saboda Allah"

Cikin mamaki mama ta kalleta, awannna zamanin har za'a samu yarinya wadda abun duniya bai rufe mata ido ba kamar wannan yarinyar? Jitayi yarinyar tasake birgeta, tun farko irinta taso Allah yabawa Mahmud dinta,Amma Allah baiyi ba.

murmushi tayi tace"Aisha ai ba'awa iyaye laifi, biyaiya ake musu sosai, yanda Mahmud yake kyautata min yakemin biyaiya inda yaji cewa kinyi wa iyayenki laifi har suke hukuntaki toda saiya zaneki"(😄)

Murmushi Aisha tayi tafara wasa da yatsun hannunta, (nikam nace me zanewa ai shine maqasudin me laifi mama 😂)

Adede lokacin yar aikin tadawo, mama ta kalli Aisha tace"za'a bude miki account Sai Adinga saka miki kudinki aciki, wannan haqqin ki ne, bazan tauye miki haqqi ba, tashi kuje zata nuna miki d'akin ki, kiyi wanka kici abinci kihuta, zuwa gobe"
Tajuya ta kalli Mai aikinta tace"Mansura baquwa ta ce wannan, takawo min ziyara ne daga jigawa, a kaita daki na musamman"
Cikin ladabi mansura ta amsawa mama, itama Aisha tayi wa mama godia tana tunani fal ranta, wacce irin mata ce wannan? Ita datazo aiki meyasa ta 6oyewa yar aikinta tace ita din ziyara ta kawo mata? To menene na jihar Jigawan tayi mata dahar take ganin qimarta saboda kawai tace daga jigawa take? Haka ta dinga yiwa kanta tambaya har suka bar wajan maman.

Acikin falon maman Dakin yake daga can Gefe, tsaruwar Dakin ne yasa Aisha ta shagala da kallon komai, daki saikace baza'a mutu ba, akwai komai na more rayuwa aciki, nuna mata komai tayi, sannan ta juya ta fita domin kawo mata abinci, tana fita Aisha ta zauna jagwab akan gadon Dakin, cikin zuciyar ta tace"duk wannan daular gidan saboda wannan tsohuwar? Aikuwa yanda na'iya zama da Hajja Toda kowama zan zauna"

Har dare tana daki bata sake gigin futowa falon ba, tunda taji mama tayi mata kashedi akan idan danta yana Nan tana buqatar kebewa, saita rufawa kanta asiri tayi zamanta adaki, bata fatan ace ma ta ganshi, menene ma hadinta dawani danta bare har zaizo tazo tasasu agaba?

Haka ta dinga tunani, daga qarshe Takoma tunanin gida, gashi de tana cikin gida har gida, Amma Kuma tana tunanin su Hajja, Sai yau taji taqaicin rashin waya, da yanzu kiransu zatayi taji muryar su, ko Hajja tayi kunun Aya yau? Haka ta dinga tunani har bacci ya dauketa Bayan tayi sallolin dake kanta

Washe gari tunda tayi sallar asuba bata koma bacci ba, kitchen tashiga tana taya masu aikin yin wasu ayyukan, anan suka Dan saba da'ita ganin tanada budadden baki har suka sake wayar mata da kai akan yanayin gidan,yanda tasake dasu sosai ta basu mamaki, saboda Hajiya Mama bata ta6a yin baquwa wadda tashiga ransu kamar Aisha ba, gashi ita ba yar aiki ba Amma tashiga cikin su kamar wasu yan'uwanta, basu gama aikin ba Sai karfe bakwai da rabi, sukam kowa daki Takoma, tunda sungama aikinsu, saide idan mutanan gidan sungama bacci sun futo shine zasuzo su zuba musu, Aisha Kam bata koma ba, afalo ta zauna tana kallo har mama tafuto, less ne ajikinta wuyanta da hannunta d'aukeda sarqa da zoben gold,kana ganin ta kasan kudi, hutu, Dajin dadi ya zauna mata, cikin sauri Aisha ta gaishe ta, sannan tace "akawo miki abincin yanzu?"

Mama tayi murmushi tace"nace kisaki jikinki tsohuwa, kidinga yin abunda yadace kawai basai kin tambayeni ba, saide idan kinyi idan Bana buqata zan sanar miki"

Aisha tayi murmushi jin sunan da mama ta kirata tace "to insha Allah" sannan tanufi dinning tafara zuba mata abincin.

Abincin takawo mata, maimakon ta zauna aqasan kujera, saita zauna akan kujera kusa da mama(😳🤭)

Mama ta kalleta cikin mamaki, saboda ba'a ta6a yimata hakan ba, koda yaushe masu mutanan gidan girmamata suke, kafin tagama tunanin Aisha ta debo abincin a spoon tace "mama bude bakinki dakaina zan baki abincin"

Wani irin shock ne yakama mama,lokaci daya Mahmud yafado mata Arai, inda ace tayi masa aure da wuri, da yanzu tanada Jika kamar wannan yarinyar, inama yanda halayen yarinyar yake, haka halin munirat yake? Da menene zaisa ta dinga Yiwa Shahaab maganar qarin aure? Murmushi tayi tace "Aisha Anya kuwa baki ta6a aiki awani gida ba kafin Nan?"

Cikin sauri tace"a a mama,banta6a yiba,inajin ki araina ne kamar kakata Hajja, kiyi hakuri Bana daukar ki a matsayin uwar gidana, Ina daukar ki ne a matsayin kakata Hajja, inda Hajja ce take matsayin ki, Tozan iya goyata ma, saboda Hajja tana sona"

Murmushi mama tayi, tarasa meyasa yarinyar ta kwanta mata fiyeda sauran Wanda take dauka aiki, ganin ta take kamar jikar ta, wani lokacin Kuma Sai halaiyarta ta dinga birgeta taji Dama ace Mahmud da'ita yafara haduwa, babu musu ta bude mata bakin, ahankali cikin kulawa Aisha tafara bata abincin, harta kammala munirat bata shigo part din na mama ba, dama Kuma Aisha batasan cewa akwai Wanda suke zuwa cin abinci part din maman ba

******

Tun karfe takwas munirat ta shirya cikin dinkin shadda Wanda aka kashewa kudi wajan dinki, mayafi ta yafa, tad'auki hand bag dinta tareda takardun filayen mama Wanda ta dauke batareda Shahaab din yasani ba, fita tayi tasa driver yakaita wajan wasu mutane, yana daga cikin mota ita kadai ce tafita, sun dade a tsaye da mutanan sannan ta basu takardun filayen, aka dauki kudi acikin wata jaka aka bata, kudin ta karba Takoma cikin mota, daga Nan banki suka wuce tabayar a saka mata kudin acikin asusun ta, bata dawo gidaba Sai wajan karfe goma Sha daya, Kai tsaye Part din mama ta wuce.

Adede lokacin Aisha tana qasan kujera, mama tana zaune a kujera tana kallo, Aisha Kuma tana matsa mata qafafunta, hira suke kad'an kad'an mama tana sake yabawa da yarinyar acikin ranta, kodan irin sunanta Dana qawarta Aysha Sulaiman Bompai gareta?
Ahankali tace"Takwara ta akwai kayan danayi miki order na sakawa, Naga bakizo da Kaya ba, idan aka kawo miki saiki dinga amfani dashi, Amma ai bazai iyu ace yanmata babu kwalliya ba"

Aisha tayi murmushi kafin tayi magana munirat tayi sallama falon, daga Aisha har mama, kallon su suka Kai gareta, Aisha tana ganin ta haka kawai taji matar bata mataba, saide Kuma kallo daya zaka mata kasan cewa yar Gayu ce, tanaji da ado da wayewa ta Yan birni, qasa tayi da kanta, munirat ta qaraso kusa da mama ta zauna, tace "barka da safiya mama, nafita unguwa ne bansamu Dama nazo munyi break ba"

Babu yabo babu fallasa Aisha tace mata "Ina kwana"

"lafiya," munirat ta amsa a daqile

Mama tace "Munirat munyi baquwa Baku haduba jiya, daga Jigawa State take, sunanta AISHA,nafada miki ne saboda ki kiyaye fadar irin sunan surukar ki,ga abinci can a dinning Zaki iya tashi"

Munirat tayi shiru kanta aqasa, idan ta fahimci mama tana nufin karta kira sunan wannan bafulatanar yarinyar kenan, saboda irin sunanta gareta, to yanzu sotake ta kirata da ANTY AISHA kokuma MOMY AISHA? cikin danne fishin ta tamiqe tana cewa "wallahi na qoshi mama, saide ko anjima inyi lunch, a hanya Naga Goro har zan siyo miki Kuma wani abu ya dauki Hankali na bansiyo miki ba"

Mama batace da'ita uffan ba, Aisha tayi tunanin zata tanka, Sai taji maman tayi shiru, anan tasake tabbatar wa mama akwai cikakken iko, Bayan munirat tafita Aisha tayi ajiyar zuciya tace "idan anyi niyar siyo miki ai saide kawai kigani mama"(😲)

Mama tace "Aisha kenan,Allah yayi miki Albarka, Sai hakuri al'amarin, wannan itace surukata matar Dana MAHMUD WAKILI"

Haka Nan Aisha taji gabanta yafadi, Amma bata kawo komai a ranta ba, saita kama addu'ah cikin zuciyar ta

******

Washagari jirgin Abba da jabir yatashi, Abba yatafi Saudia, jabir Kuma yawuce Australia, tunda aka fara musu hidimar tafiyar babu wata hanya da'aka Bari har su kasan ga sahihin mutumin daya dauki nauyin tafiyar tasu,tundaga ranar da sukaje dutse Abba Kam Yama manta da batun su, saboda kawai ganin abun yake kamar wasa, Amma haka mutanan suka sake dawowa tareda Mai Garin Garin, aka gama musu komai har suka tafi.

gidansu Hajja shiru babu wani dadi saboda Abba baya Nan, jabir baya Nan, Aisha bata Nan, daga Ummah Sai Hajja, kullum jummai tana zuwa wajan Hajja domin Sudan zanta, Amma Hajja bata kulata, haushinta takeji saboda da'ita mamuda yahada Kai suka tura mesunan qawarta Abuja.

Tunda Abba yatafi kullum saiya kira su ta wayar Hajja sun gaisa, har yau daya cika kwana takwas, yana shirin cika sati biyu sannan ya dawo gida.

A bangaren Aisha kuwa yau tacika kwana goma a gidan, batada damuwar komai, tana zaune lafiya a gidan, Kuma har zuwa yanzun bata ta6a saka Mahmud Wakili a idonta ba, damuwar ta de guda daya ce rashin jin muryar Hajja dasu Ummah, saikuma tunanin Shahaab, tana tunanin ranar dazaije gidansu bai sameta ba.

Yauma munirat da mama suna zaune afalo, munirat da wayarta a hannunta tana tura kudade tana order kayaiyaki da kudin filin mama data siyar (🙆🏻‍♀️)

Mama tana mata kallon gefen ido tana mamakin shegen danne dannen waya irinna munirat, Aisha ce tafuto falon tayi kyau sosai cikin doguwar Riga irin kayan da mama ta siya mata, cikin ladabi tace "mama nagama gyara miki Dakin, yanzu saukowa qasa zakiyi, kokuma ki kwanta in tsefe miki kanki, kitsonki ya tsufa mama"

Mama tayi murmushi tace "Bani abinci de infara ci tukunna, nagode da qoqari, Allah yasaka miki da alkhairi"

Murmushi tayi ta nufi dinning tazubo mata abincin, sannan tadawo ta zauna tafara bata abincin abaki, munirat ta Kalle su, wani irin baqin ciki ya to kare mata maqoshi, ta maida Hankalinta kan wayar ta.

saida tagama bata abincin sannan tafara tsefe mata kanta, cikin kulawa tace "mama idan kinajin zafi fa kifadamin saina dinga yi miki ahankali"

Mama tayi murmushi tace "babu zafi Aisha, inda nake zuwa kitso ma suma kamar hakan suke min, Allah yayi miki Albarka"

Cikin jin dadi tace "Amin mama"
Chapter 30 · 0% Book details