← Book details Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 71

Sashe 34

Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har qarfe daya saura Idonsa biyu bai runtsa ba, Ada idan yadawo daga tafiya qarfe goma yayi yawa ya kwanta, Amma yau shine har daya saura Idonsa ko alamun bacci babu, inda Dane yadade bai kasance da matarsa ba to kwana biyu ne zuwa uku, idan tashiga hannunsa kuwa saita koka, Amma yanzu shine yayi tafiyar wata daya da 'Yan kwanaki Amma ko kadan baiji yana sha'awar munirat ba, tunanin sa gaba daya yana wajan Aisha,ya dade rabonsa da matarsa, yadawo daga doguwar tafiya Kuma mama ta tarbeshi da wadannan abubuwan na Aisha masu wuyar mantawa.

Ya tabbatar da cewa bazata taba saurarensa ba koda yaje inda take yanzu, Amma Kuma tayaya zai tunkareta yabata haquri agaban mutane da rana? Idan mama ta ganshi ta'ina zai fara yimata bayani? Ahankali yazame munirat daga jikinsa, batareda tunanin komai ba yafice daga d'akin, Kai tsaye yanufi part din mama.

Yana zuwa yaga part din shiru alamun duk sunyi bacci, saida yasake kallon ko'ina ya tabbatar babu wani mahaluqi dayake falon sannan yawuce Dakin da yaga Aisha tafuto daga ciki dazu, kama handle din Dakin yayi yatura, yashiga cikin Dakin sannan ya maida Dakin yarufe, baiyi mamakin ganin ta a zaune akan sallaya ba, kanta yana cikin cinyoyinta, qamshin turaren dataji ne yasa taqi d'ago kanta bare ta kalli inda yake.

Jin gina yayi da jikin qofar Dakin yazuba mata ido yana kallon ta, gabansa faduwa yake yarasa ta'ina zai fara yimata magana? Ahankali yasaki ajiyar zuciya sannan ya qaraso wajan ta ya tsugunna gab da'ita har tanajin yanda hannunsa yake gogar Nata, cikin muryar rad'a yace "ki... kki... kiyi hakuri"

Tana jinsa, Amma taqi d'ago kanta ta kalleshi, wani irin haushin sa takeji, ko menene yakawo shi dakinta cikin dare? Wata zuciyar tace da'ita abinda bai gamaba yazo ya qarasa, wani irin tsaki tasaki cikin ranta, tasake cusa kanta cikin cinyoyinta, ganin hakan datayi yasa yasan cewa ba bacci take ba, ajiyar zuciya yasauke yasake cewa"nasan cewa nime laifi ne awajanki, banyi komai ba saida dalili Maaamah, Dan girman Allah kiyi hakuri ki yafemin..."

Wani irin kuka me sauti tasaki, batace masa komai ba Sai hannu data daga masa. (🖐️)

Kallanta yayi, babu musu ya jijjiga Kansa tareda miqewa yafice daga d'akin, dama yasan cewa bazata saurare shi ba, haka yakoma part dinsa jikinsa a sanyaye, kan gadon yakoma ya kwanta, munirat tanajin kwanciyar sa tace "daga Ina kake? Ko yanzun ma wajan ta kakoma zaka sake taba mata nonon?"

Runtse idon sa yayi, ahankali yace "me kike nufi Danine munirat? Kina nufin zan iya neman mata awaje?"

Cikin fishi tace "idan ba neman matan kafara ba, kwanan ka nawa rabona dakai?Dakazo ka nemi wani abu awajena ne? An tura Maka tsayaiyan nono kana ta6awa yaushe zaka nemi nawa?kun cuceni wallahi, Kuma dole kasa yarinya qarama tadena ganina da qima da mutunci"

Murmushi yasaki kamar wanda baya cikin damuwa, ahankali ya fusgota jikinsa tareda tura hannunsa cikin yaluluwar rigar baccinta, yayiwa breast dinta wani irin kamu, sannan yafara kissing dinta.

Sosai yayi Nisa wajan nuna mata yanda yayi kewar ta, soyake ya mantar da'ita abunda tagani dazu, saide shi Kansa kawai yanayin Hakanne Amma kokadan bayajin sha'awar, saboda tashin hankalin dayake ciki,daga Nata bangaren itama Qin bashi hadin Kai tayi, Dan dole yarabu da'ita tareda juya mata baya yayi kwanciyar rub da ciki, itama kwanciyar ta ta gyara tarabu dashi, saide ko minti goma batayi ba taji Hankalinta yaqi kwanciya, yariga yata6o mata inda yake mata qaiqayi, ahankali ta juya ta rungume shi tabaya, yanajinta yarabu da'ita, sake Matsowa jikinsa tayi tana goga masa qirjinta a bayansa, saide hakan datake masa ma ba komai tatuna masa ba Sai Wanda yata6a dazu, ahankali yasaka hannunsa ya janye ta daga jikinsa, sannan yaja fillo ya rungume a qirjinsa.

Mamaki ne yakamata, yau itace take neman Mahmud Amma yana janye ta da hannunsa? Babu yanda ta'ita duk yanda take jin sha'awar sa haka ta qyaleshi.

Washe gari da safe tsaf ya shirya cikin suit dinsa, baisaka jacket dinba Sai zuba uban qamshi yake,soyake yafita domin shirye shiryen sabon company dazai bude, Wanda yayi alqawari zai Bawa matar datake da muhimmanci awajansa wato munirat ,tun qarfe takwas na safe suke masa waya, already har sun gama tsara komai, kawai jiransa ake yazo yasaka ranar daza'a bude companyn, baisan daliliba, haka kawai yake jin wani irin farinciki acikin ransa, Kuma yasan cewa hakan baya Rasa nasaba da kasancewar Aisha acikin gidansa,yarasa menene yakawo ta gidan a matsayin maiyiwa mama hidima, tayaya tazo? Dole itace zata bashi labari Kuma tana fishi, inda Dane ba lalle ya tsaya yin break fast ba saboda jiransa da ake, Amma yau Kam dole zai tsaya yaci abinci kodan yaganta ma.

Munirat tana wanka danhaka yafice shi kadai, Kai tsaye part din maman yanufa, yana zuwa kuwa yaga ma'aikatan sun gama shirya komai akan dinning, mama tana zaune, yayinda Aisha take tsaye tana qoqarin hada mata tea, yau taji jikin Nata dadan qarfi, babu zazza6in ya sauka tun Bayan datasha magani cikin dare, wani irin dadi yaji, cikin takunsa me aji ya qarasa dinning din tareda sallama, mama ta kalleshi tace "nayi tunanin zaka huta ne bazaka fita ba?"

Saida yadan kalli Aisha yaga tahade girar sama data qasa, yasaki murmushi sannan yace "akwai mutanan dasuke jirana ne dangane da bude wannan sabon companyn, shiyasa zan fita, Amma bazan dade ba zan dawo"

Kafin mama tabashi amsa, qasa-qasa Aisha tace "Ina kwana"

Murmushi yasaki, yasan cewa Dan kada mama taji taqi gaida shi ne, shiyasa tayi masa wannan gaisuwar, Amma Badon hakaba Shima yasan bazai samu gaisuwa agareta ba

Maimakon ya amsa Sai yayi shiru tareda zuba mata ido yana Binta da wani irin mayen kallo,har zuwa wannan lokacin bai zauna ba, yanda Aisha take a tsaye tana qoqarin hada tea din, haka shima yakama daya daga cikin kujerar dinning din yariqe, wani irin nishadi yake ji a ransa harma ya manta cewa mama tana wajan.

Mama ta d'ago zata masa magana taji Aisha ta gaishe shi Amma yaqi amsawa saita kamashi yana kallon ta, cikin mamaki tace "menene kake kallon ta,kokuma yanda kake tuhumar 6arayin Gwamnati itama tuhumar ta kake?,to wannan de Batada abun dazaka tuhumeta akansa"

Murmushi yasaki, dimples dinsa suka futo, yaja kujerar yana qoqarin zama, Hips dinta ya kalla yanda suka sake bajewa fiyeda ranar daya fara ganin ta, ya tuna tsayaiyun breast dinta yanda yake matsa su cikin nishadi kamar karya daina, cikin qasa-qasa da murya yace "tana dashi mana"

Mama tace "au tanada abun tuhumar kace?"

Cikin sauri Aisha tabar wajan, domin kuwa Dama mama tace inde danta yana waje toka Barta tagana da danta,qasa-qasa yabi bayanta da kallo, cikin zuciyar sa yace "wannan ai itace yakamata a tuhumeta, tunda harta mallaki wad'annan abubuwan Kuma ta sace Min zuciya ai dole na tuhumeta, kamata yayi ma nasaka ta adaki na kulle kofar nafara tuhumar ta tayaya akai ta mallaki wannan kayan alatun?(😍)

Mama dataji yayi shiru itama saita share shi tafara cin abincinta, sun kusa gamawa kenan sannan munirat tafuto itama taja kujera ta zauna tafara cin abinci Bayan ta gaida mama.

******

Da yamma Bayan yadawo yana zaune a part dinsa yanashan Lemo, ya kalli munirat yayi mata magana, ciki ciki ta amsa masa, ahankali yasake ce mata "ki shirya jibi zamuyi taron bude sabon company, kece nafara fadawa, idan da wadanda Zaki gayyata saiki sanar dasu"

Wani irin farinciki ne yakama munirat, batasan lokacin data rungume Shiba, nuna masa tayi batasan cewa ita zai mallaka wa kamfanin ba, cikin kissa tace "Congratulation my Dear, Ina tayaka murnar bude sabon company, Allah yasa mu mora"

Mamaki ya kamashi,tabbas yasan yamata laifi saboda abinda tagani jiya yana yiwa Aisha, Amma Kuma yanda tad'auki zafi da fishi akan hakan kawai lokaci daya yanzu daga jin maganar company harta manta abinda yafaru? Cikin mamakin sauyinta na lokaci daya yace "Amin ya Allah"

Tashi yayi yatafi wajan mama domin itama ya sanar da'ita, yana fita munirat tad'auki wayarta tafara Kiran Yan gidansu tana sanar dasu jibi akwai taro, Shahaab zai mallaka mata sabon company, Bayan takira yan'uwanta, saita koma kan qawayenta, babu Wanda bata kiraba, acikin danginta ma wanda ta dade bata kirashi ba yau ta kirashi, saboda tana so ta kankarowa kanta daraja a'idon duniya.

Murmushi take ta saki ita kadai tana lissafa irin mutanan dazata dauka aiki a qarqashin companynta.

Tun daga ranar dasuka hadu a dinning bai sake ganin Aisha ba, yasan kuma Sarai fishi take dashi, shi Kansa idan ya tuna da yawan qaryaiyakin Dayayi mata saiya ji tabbas duk hukuncin data masa din hakan yayi, koda yazo wajan mama baya ganin ta, gaba daya a kwana dayan dabai ganta ba, duk Sai Idonsa suka fada.
anar bude company Shahaab tun sassafe yafita, Aisha kuwa tana d'akin mama, yau tasaki ranta ganin yanda maman take janta ajiki, itace ta fesa mata turare sannan ta kalleta tace "mama kinyi kyau sosai, nasan idan kikaje wajan Nan Sai kowa yace mama nah tafi ta kowa kyau"

Murmushi tayi tace "ki shirya muje"

Cikin sauri tace"a a mama, zan zauna agida inyi miki girki me dadi kafin ki dawo"
Bakomai ne yasa tafadi hakan ba Sai Shahaab da batason Gani, sosai ranta yabaci saboda abunda yamata, Sanadin sa tafara ja'inja da mahaifinta, duk yanda take da kunya saboda Shahaab tafuto fili ta fadawa Abban ta cewa itade Shahaab take so.

Cikin farinciki mama tace "to shikkenan"

Hannunta Aisha ta kama suma futo har compound din gidan, driver yad'auki mama, sannan ita Kuma tajuyo cikin gida.

Wajan taro yayi tsari da kyau yanda yakamata, manyan mutane Yan kasuwa da sauran abokan huldarsa sun halarci taron, Bayan anbude taro da addu'ah anyi Yan jawabai, daya daga cikin masu ruwa da tsaki akan aikin companyn yatashi yafara bayanin yanda sukayi aikin companyn cikeda inganci dakuma ingantattun kayan aiki daga qasar waje.

Munirat tana hakimce agefe guda ita da bataliyar mutanan ta, taci Gayu harta gaji, ta matsu a kirata a matsayin mamallakiyar company, momynta Sai zungurinta take alamun itama ta matsu Akira munirat din.
Chapter 34 · 0% Book details