← Book details Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 71

Sashe 41

Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ramadan ya kwashe da dariya yace"ikon Allah, Shahaab yau kaine da kanka kake cewa aure kakeso? To munirat dinfa?"

Dan qaramin tsaki yasaki yace"Ramadan banason wulaqanci, nide nafadama aure nakeso, karkaji ansaka rana kaitsaye kace ban fadama ba"

Cikin mamaki Ramadan yace"a a, Wai to har angama magana da iyayen yarinyar ne? Naji kana batun saka rana"

Idonsa ya Lumshe yace"no, nayi mata magana tayi tunani taga yaushe yadace naje nasamu mahaifin ta"

Ramadan yace"Saitayi tunani? Kawai ka shirya kaje ka sameshi, inde tana so kanaso menene abun tunani Kuma?"

Kafin yabashi amsa wayarsa dake ajiye agefen sa tad'auki qara, excuse ya nema awajan Ramadan sannan yad'auki daya wayar yace"Malam Auwali yakake ya kwanan iyali"

Daga d'ayan bangaren Wanda aka kira da Auwali yace"Alhamdulillah yalla6ai, nace wannan filayen Naka danake gadinsu Naga ka turo anfara gini har katanga tayi nisa Amma nikuma baka fadamin za'a ginaba shine nace Bari na kiraka naji Allah yasa de ba laifi mukai ba, kayi hakuri wannan aikin dashi nadogara Kuma dashi nake ciyar da ahlina"

Kan Shahaab ya daure, shide yasan baida wani fili da malam Auwali yake gadinsa Bayan filayen mama guda goma daya siya ya ajiye mata, baida fili ko daya a unguwar saide na wajan mama daya siya mata, shikuma yasan cewa Bayan yagama duba takardun Nan da hannunsa yasaka su acikin ma'adanar sirrin sa ya 6oye mata su, Kuma shide baisa kowa ya Gina suba, cikin mamaki yace"wai wanne filaye kake magana akai malam Auwali?"

Cikin girmama wa da ladabi malam Auwali yace"wannan filayen de daka siyesu kwanaki, to Ana gina manya manya aciki, guda biyu, Kuma gini har yayi Nisa"

Cikin sauri Shahaab yace"bansan da wannan maganar ba malam Auwali, menene amfanin ka awajan za'a fara aikin gini baka kirani kafadamin ba?"

Cikin sauri yace"wallahi tallahi yalla6ai jinake kaine ka turo ayi, shiyasa yanzu ma nakira inji ko laifi nayi"

Shahaab yace"kaje ka samesu kuyi magana, kayi musu bayani saisu fadama Wanda yaturo suyi aikin"

Yana fad'ar haka yakashe wayar, fada yafara yana sababi shi kadai, har wani Kiran yasake shigowa ya d'auka, malam Auwali yace"yalla6ai, sun fadamin wani Alhaji ne ya basu kwangilar aikin, yanzu haka yana cikin Abuja, nace su dakatar da aikin sunqi yarda sunce saka su akayi bazai iyu su daina ba, nace su Bani number Alhajin daya saka su sunce bazasu Bani ba"

Cikin 6acin rai yace"okay haka sukace? Rabu dasu kakoma wajan ka ka zauna, Alhajin zaizo da Kansa ya sameka har wajan gadinka, bazan sake nemansa ba saide shi ya nemeni "

Wayar yakashe, malam Auwali kuwa waje yasamu ya zauna cikin ransa yana fadin to fadan nasu na manya ne, yana kallon yanda masu aiki suke ta kwa6a cement suna aiki, shide ya zauna daga Gefe yana kallon ikon Allah, baifi minti goma Sha biyar da zama ba Sai ganin manyan motoci yayi sun nufo wajan gadan gadan, koda suka qaraso wajan basu saurari mutanan dasuke aiki asaman katanga ba suka nufi ginin suka fara zubar dashi, Nan da Nan masu aiki kowa yake ta ransa, nasama sukayi gaggawar saukowa qasa,anata ihu Ana hayaniya Amma masu motocin Nan kamar wanda suka saka Bluetooth akunne, ko kallon mutane basayi saida suka rushe ginin Nan gaba daya, malam Auwali dayake Gefe yana kallon ikon Allah ya tuntsire da dariya yace"shegiya nera..."

Kamar wanda akai ruwa aka dauke, suna gama baje ginin suka kada kan motocinsu sukayi gaba, masu aiki cikin sauri suka nufi malam Auwali suka bashi waya, yana sallama Wanda yasa ayi masa aikin filin yadinga roqonsa akan yafada masa waye uban gidansa, babu 6oye 6oye yafada masa MAHMUD WAKILI ne.

(littafin kudine,ki karanta abinki yafiya Kuma ban yafeba, nabarki da Allah, zai isar min"

******

Tana daukan wayarta afalo Kai tsaye ta nufi Dakin Aisha tana so ta lalla6a yarinyar ko zata fada mata gaskiyar abinda yake faruwa, saide tana shiga Dakin taga babu ita, babu dalilin ta, Sai wasu takardu data Gani azube akan gado, dauka tayi ta duba takardun, faduwar da gabanta yayi ne yasa cikin sauri ta dafe qirjinta tareda zama akan gadon, takardun tasake kalla cikin sauri tace"wannan ai takardun sabon companyn da Mahmud yabude ne, Yaya akai Aisha tasamu? (tun farko akwai wadda nayi niyyar mallakawa, ita din mace ce mai mutuqar muhimmanci a gareni,zan'iya sadaukar da rayuwa ta domin ta,dalilin hakane yasa na mallaka mata wannan company,ba kowa bace face AISHA).

maganganun Mahmud suka Fado mata acikin rai lokacin daya bude company, ta tuna kallon dayake bin yarinyar dashi washe Garin ranar lokacin da Aishan take hada mata tea, cikin tsananin mamaki tace"kaiii tayaya? Yaushe har suka hadu acikin gidan Nan suka fara soyaiya bansani ba?hakan yana nufin wannan Aishan yake nufi kenan? Idan ba ita yake nufi ba tayaya zata ga takardun acikin Dakin Aishan?.

Cikin sauri tafara qwala mata kira, saide duk inda yakamata ta duba, ta duba babu Aisha kwata kwata, cikin sauri ta doka wa Shahaab kira, Yana d'auka tace"yaushe zaka dawo?"

Cikin mamaki yace"mama meyafaru?"

Cikin tashin hankali tace"komai ma yafaru, narasa Aisha, kazo ka Nemo min ita, duk inda yarinyar Nan take kaine silar 6acewar ta, na nuna mata vedion da kukayi, daga Nan na nemeta narasa"

Cikin mamaki yace"vedio Kuma mama? Wanne irin vedio?"

Cikin sauri tace"kome kake a lagos kabari kazo gida yanzu-yanzu"

Cikin sauri ya amsa mata, domin kuwa Shima Kansa Hankalinsa atashe yake, yanaso yasan waye yasa agina masa filayen mama, sannan yanaso yasan wanne irin vedio ne mama take magana akai, babu 6ata lokaci ya shirya yanufi Airport.

Awa daya da wani abu ce takawo shi gida, a compound ya hango munirat ranta a6ace, tana ganin zuwansa Ana bude masa kofar mota tayi sauri Takoma daki, idan a Kwai Wanda batason Gani bai wuce Shidin ba.

Kai tsaye part din mama yanufa, yana zuwa bata barshi ya zauna ba tamiqa masa takardun company tace"yaya akai wadannan takardun sukaje wajan Aisha?"

Ta qarasa maganar tana tsare shi da idonta.

Gabansa ne yafadi, ya hadiye wani irin yawu sannan yace"mama ki zauna nayi Miki bayani, please zauna"

Babu musu ta zauna, tad'auki wayarta ta bude vedio tace"shikuma wannan vedion mezaka ce akansa? Shahaab Ina Hankalinka yake? Abinda kakeyi da yarinyar Nan kenan shiyasa kake mata 6arin kudi kayi mata siyaiya, ka dauki company kabata, menene ribar irin wannan rayuwar daka jefa Aisha aciki? Yanzu gashi tagudu, na nemeta narasa, shikkenan tashiga duniya kaji dadi" ta qarasa maganar tana fashewa da Kuka...

Kansa yadafe yace"innalillahi wa'inna ilaihirraji'un...."
Yazubawa vedio ido yana kallo,saida yagama Gani sannan yabude breafcase dinsa, yadauko computer sa aciki,sannan yatura vedio yayi Yan danne danne tsawon lokaci, sannan yatura mata computer gabanta yace"mama, idan kikaga irin wannan vedion nutsuwa yakamata kiyi ki kalla dakyau mama, yanzu duba kigani Bani bane, ba Kuma Aisha bane, dora fuskar mu akayi akan vedio,kiduba jikinsu kigani, mama wannan yarinyar tafi Aisha girma, ki kalli surar jikinta dakyau, sannan ki kalli ta namijin Shima kigani, ga zahiri nan computer ta nuna miki, duba kigani mama"

Ajiyar zuciya tayi, ta share Hawayen idonta sannan tafara kallo, lokaci daya tasaki salati tace"yanzu Dama anayin haka Mahmud?"

Yace"gashi kuwa kingani mama?, bani number da'aka turo miki vedion, zansa ayimin tracking dinta"

Babu musu mama tabashi number, murmushi yayi har dimple dinsa suka futo yace"yanzu shikkenan Hankalinki ya kwanta?"

Sake goge idonta tayi tace"AISHA"

Murmushin yayi, sannan ya shafa sumar Kansa yace"mama nida Aisha mun dade muna tare"

Cikin sauri ta Kalleshi, Shima ya Girgiza mata Kai sannan yace"qwarai kuwa mama,nahadu da Aisha tun cikin azumi,Kuma kece silar haduwa ta da Aisha mama, tun lokacin dakika umarceni naje Jigawa State in bude miki gidan marayu saboda qawar ki, tun Alokacin nahadu da'ita, idan Zaki tuna mama Alokacin banda magana saide ince zanje jigawa, ki gafarceni mama, Amma wani lokacin ba wajan wannan aikin nake zuwa ba, wajan Aisha nake zuwa, nadauki shawarar ki data Ramadan cewa in6oyewa budurwar danakeso kaina, hakan nayi akan Aisha, ban nuna mata inada kudi ba naje mata a matsayin Yaron Mahmud Wakili, ahakan ta amince Dani take soyaiya Dani, iyayen Aisha talakawane mama, suna rayuwa cikin kwanciyar Hankali zuwana cikin rayuwar ta saida hakan yata6a wannan farincikin na ahlinsu, duk abinda nasaka ta shi take min,kudin dan'uwan ta datake aiki take Tarawa tana so Yaron yakoma makaranta shita dauka tamin kyauta dashi mama, A'ina zan samu irin wannan soyaiyar mama?akwai Wanda akeso abata agida tace ita Shahaab take so,dalilin hakane yasa babanta yaturo ta aiki Abuja, baisan cewa gidana yasake turo taba, ranar Dana dawo daga Australia a ranar na ganta a gidan Nan idan zaki tuna Alokacin nashiga cikin wani irin yanayi, kiyi hakuri mama, Amma inason Aisha, bantaba son kowacce yarinya kamar son danake mata ba Bayan ke, inaso Dan girman Allah mama kinemomin Aurenta please"

Ya qarasa maganar yana hade hannayensa waje daya, mama data zuba masa ido tana kallon sa tasaki ajiyar zuciya tace"amma kukan anyi munafukai, daga Kai har Aishan ba qananun munafukai bane, ni Ina zaune ashe ku soyaiya kuke shiyasa kake wa yarinyar mutane ihu saboda tace tadena son Wanda ya yaudare ta? Yanzu ashe Dama dakai take? Yanzu fisabilillahi ka kyauta abinda Kamin Shahaab? Kasan Sarai kanason yarinyar Nan Amma shine lokacin da batada lafiya na riqeta kadinga ta6awa yarinya nonuwa kod'an musu babu? Yarinyar Nan bata so Amma haka nasa ta tsaya saida kagama abinda kaga Dama sannan karabu da'ita,meyasa lokacin ko dukanka zanyi bazaka cemin bazaka ta6aba?"

Wata irin matsananciyar kunya ce ta kamashi, yayi sauri ya sunkuyar da Kansa qasa tareda Sosa qeyarsa yace"mama saida nace Miki a a...fa"

Cikin sauri tayi masa daquwa tace"qarya kake Shahaab,cemin kayi dubawa de kake,nasan hakane yaushe zanyi wannan danyan aiki?"

Kansa yana qasa yayi Dan qaramin murmushi, sannan yadan kalleta cikin kunya yace"mama to Zaki nemamin auren Nata?"

Fillon dake gefenta ta d'auka takai masa duka dashi tace"Wato Aisha ta maida Kai marar kunya, aini babu abinda zance, idan kaga zaka iya yiwa munirat kishiya shikkenan, dama kaine kake cewa kaida munirat Sai Allah, yanzu Yaya za'ai Naga Aisha?"

Cikin nutsuwa yace"za'a ganta mama,ki kwantar da Hankalinki,mutuqar agogon Dana daura mata yana hannunta, to dole zansan inda take"
Chapter 41 · 0% Book details