← Book details Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 71

Sashe 12

Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aisha da takaici ya cikata tataba sauran gashin taji saura guda biyu agama,batason jin takaicin firar Hajja da jummai Wai labanu...

Can Kuma Sai jummai tace "oh nikam Hajja ya mukaji da labarin taliya, har yanzu tana nan muna Jan dafaduka da'ita, wannan yaro Allah de yabiya shi,masu kudi dazasu dinga haka dasun samu Lada awajan Allah"

Hajja tace "masu kudi sunada kudi infada miki, Amma Kuma suna qara son kudin su, kiduba kiga Yan siyasa sunada kudin, wani ma har jikokin sa bazasu taba talauci ba, Amma a hakan nema suke susake Hawa kan mulki, mukuma talakawa muna Nan Sai godiar Allah, ni yanzu ko dubu talatin aka Bani ai jikinane zai fara karkarwa, wallahi zazza6i zai sakani "

Jummai tace"aikuwa in hakane Hajja A'i kakarki ta yanke saqa, Ina Yaron Nan inusa me kanti na qofar gidana?"

Hajja tace "wai inusa wannan me shago?"

Jummai tace "shide, jiya jiyan Nan yazo ya sameni yace tunda ke aminiyata ce inyi masa hanya mana yazo wajan mesunan qawarki, Kuma Hajja A'i inde Aisha ta amince ba abunda bazai muku ba, yanada sakin hannu"

Aisha tanajin haka kunya ta kamata, tatashi da gudu tatafi daki
Jummai tace "laaa Hajja A'i kode harta amince ne, Naga tatafi daki cikin kunya"

Hajja tace "ai mungama amincewa jummai"

"to Alhamdulillah zan sameshi nafada masa, saiki fada mata idan zaizo ta dinga kwalliya, 'Dan janbakin Nan ta dinga shafawa, taci kwalliyarta da mayafi"

Hajja tace "Ina me sunan qawa zata saka miki mayafi? Dan qirgen dangin take 6oyewa, Kuma kinsan Yara inde suna wannan matakin Tofa ko yayan limamai Albarka, Amma inda tana kwalliya ai samari Sai mun kori wasu,tun yanzu ma gashi anfara aike, kinsan Kuma farinjinina ta Dauko da alama, Saboda Nima alokacina saida aka kawomin Goro d'aid'ai har guda sittin"(😳)

Jummai tace "to aikuwa zan fada masa dangin farinjini yake so, tun kafin wani yazo yatureshi Gara yadage, 'Dan man Nan ya dinga siyo mata tana shafawa duk Dama Naga jikar Taki fara ce sol ga hanci har baka inni mayya ce incinye kaina" (😂)

Hajja tace "fada masa Kam gaskiya"

Jummai tasake Kallan Hajja tace "Hajja Kuma Yaya kikayi da Goron da aka kawo miki?"(🤔)
Hajja tace "ai inafada miki a makaranta ma malamai fada suke akaina, da sukaga Bana kulasu kawai saide kiga sun shirya sun Kai Goro gidanmu, Ahaka Ahaka har guda sittin kinji zancen gaskiya, Amma dayake aure rabo ne duk masu son Nan nawa babu wanda na za6a Sai uban mamuda Allah yaji qan rai "

Jummai tace" ikon Allah, banta6ajin irin wannan labari nakiba ko a hikaya"

Hajja takauda kanta Gefe tace"to yanzu kinji"

******

Yau Shahaab da munirat sun Lula qasar Saudia umara, munirat kamar ta zuba ruwa aqasa Tasha Dan murna, saboda tarabu da jarabar mama, yau itama de take6e itada mijinta.

A hotel suka sauka, kwanansu biyar da zuwa qasar Amma munirat har wata qiba tayi, jikinta yayi wani irin fresh, kasancewar bata tafi da kayan magungunan ta Wanda ta siya awajan qawayenta ba, Sai jikinta yake sauya wa, ita akaran kanta tasan ni'ima ta saukar mata, tunda kullum cikin hutu take babu tunanin mama, saide taita cin fruit masu kyau tana kwanciya, shiyasa a kwanansu na shida tarasa gane kan Shahaab, tunda ya ratsata yaji ta sauya Nan da Nan ya rikice mata, kamar mahaukaci haka ya dinga abu daya.
Yanda take samun hutu a qasar Sai take jin Dama su dauwama Ahaka,ga Kuma uwa uba Mahmud dinta yana tare da'ita, shiyasa gaba daya addu'ar ta taqare 6angare daya, wato Allah yabar mata Mahmud, ya mallaka mata zuciyar sa ya kasance ita kadai yake Gani acikin mata, duk wata mace dazata mata shamaki da mijinta to Allah yasa Shahaab ya dinga kallon ta a namiji

Sa6anin Shahaab daya duqufa wajan yin addu'ah Allah yabashi 'Ya'ya nagari idan yanada rabo,saikuma mama datace masa yadinga yimata adduah Allah yasa kafin ta mutu tahadu da qawarta Aysha Sulaiman Bompai, wuni yake a masallaci yana wannan addu'ar, idan tare suka tafi da munirat gajiya take da jiransa Takoma masauqin su, shikuma daga baya Bayan yagama addu'ar sa saiya dawo shi kadai.

******

Yau gaba d'ayansu atsakar gida sukai sahur, Abba yana Gefe yana karatun alqur'ani, Ummah da jabir da Hajja suna zaune atsakar gida, Aisha kuwa adaki taci Nata abincin, saida tagama tafuto,ta bude fridge din Hajja dayake cike da qanqarar sayarwa, tad'auki ruwan Sanyi ta tsugunna tanasha, Hajja ta bita da kallo tace "kaga shafaffiya damai, inajin bata mayi sahur dinba"

Jabir yace "aikuwa kamar kinsani Hajja batayiba"
Hajja tace "Ahaf! Aini tabiyo, Nima fa wannan sahur din bawani damuna yayi ba, Amma jiya duk da nayi sahur azumin Nan yabani wahala, ko yaya na sunkuya kawai duhu nake Gani, duk jijiyoyin jikina saki sukayi, sallar la'asar ma a zaune nayi ta"
Gaba dayansu dariya suka sa, harda Abba, Hajja kenan me abun mamaki, tace sahur bai dameta ba Amma Kuma mutumin da sahur bai dameshi ba shine yake sallah a zaune tsabar wahalar azumi, Kuma sude asaninsu da Hajja kullum Saitayi sahur, wannan ladan baya wuce ta.

Ta kalli Aisha data gama shan ruwa tace "debomin ruwa a kafara na qulla nasaka a fridge, babu pure water yaqare, harna fara kewar azumi wallahi, tunda muka shiga goman qarshan Nan"

Aisha tatashi zata bata ruwan tace "ai dole kiyi kewar azumi, tunda kina cafkar kudin qanqara"

Sarai taji abunda Aishan tace Amma Saitayi shiru, saboda tasan tabbas tana samun kudin qanqarar, Kuma tsaf me sunan qawa zata fadawa mamuda abinda take samu kullum, danhaka Saitayi shiru taqi ta tanka mata, saima cewa da tayi "Bani ruwan sanyi a fridge Nasha jabir, wadannan masu gaggawar yanzu zakaji sun fara Kiran sallah, idan shan ruwa ne Sai sun gama Jan ajinsu sannan su kiramana sallah, Amma idan lokacin sahur ne abincin ma baya tsirga musu suke tafiya masallaci sukira sallah "

Jabir yayi murmushi yad'auki ruwan yabata

******

Ana azumi na Ashirin da d'aya, sannan su Shahaab sukai shirin tafiya, munirat tasashi agaba tana so tayi wa yan'uwan ta da qawayenta tsaraba, dole yad'auki maqudan kudade yabata, tasashi ya shirya domin suje super market da boutique tayi siyaiyar acan, haka badon yasoba ya shirya suka tafi.

Kai tsaye BIN DAWOOD HYPERMARKET sukaje, shide babu abunda zai siya, kawai Kallan ta yake tana za6ar duk abinda taga yayi mata.

Ajiyar zuciya yasauke, yarasa meyasa yake tunanin ta, tun Bayan tahowar su daga Garin yake nema ya yakice tunanin ta a ransa Amma yakasa, gaba daya taqi barinsa ya huta, yarasa Yaya zaiyi da ransa.(🤦🏻‍♂️)

Kayan yaci gaba da kalla, anan yaga wani ribbon dark green Mai masifar kyau, babu Wanda yasake fad'o masa Arai face ita, ya tuna yanda dogon gashinta yake ko ribbon babu, cikin ransa yafara magana "marar kunya 'yar qarama...."

hannu yasa yad'auki ribbon din yaga ansaka shi cikin wani gida, kana Gani kasan yanada tsada, price dinsa yagani,kudin ribbon din kadai yafi kudin daya Bawa munirat tayi siyaiya dashi.(🙆🏻‍♀️)

Batare da tunanin komai ba yadauka matashi.

(😲🤔tabdi sorry Munirat😥)

SHAHAAB littafin kudi ne,naira 300 ne kacal 👌🏻yar'uwa siyan nagari maida kudi gida, ki biya naira 300 ki karanta abinki Hankali kwance

Zaki tura 300 ta wannan account din

0164549488
Amina muhammad
GTbank

Zaki tura shedar biya ta wannan number 08033300034

Amnah El Yaqoub ✍🏻

[10/09, 22:14] +234 803 697 8511: 🌸SHAHAAB🌸
(Romance)

Writing By Amnah El Yaqoub

Dedicated to Aisha's Name
https://www.facebook.com/amnahel

13&14

'Boyeshi yayi a Bayan hannunsa, Karo na farko kenan daya fara 6oyewa matarsa wani abu, Kallan ta yayi yace "munirat idan kin gama kisameni awaje,I'm tired"

Juyowa tayi tace "okay my dear five minutes"

daga Nan taci gaba da tafiya tana za6ar abinda takeso tana sakawa acikin kwando.

Juyawa yayi cikin sauri, yaje ya basu atm dinsa suka dauki kudin ta dollar account d'insa, sannan ya 6oye abun acikin aljihunsa, yakoma cikin mota yana jiranta.

Bayan tagama siyaiyar tafuto,hotel suka koma, saida yaga tashiga wanka sannan yasaka ribbon din cikin jakar kayansa data had'a masa tun Daren jiya.

Cikin dare jirginsu yatashi zuwa qasar Nigeria,Bayan sun sauka munirat Kam bacci ta kwanta, shikuma yatafi wajan mama, saida ya ganta tana bacci sannan ya dawo part dinsa.

Ganin baccin munirat din yayi Nisa yasa ahankali yatashi, yabude cikin jakarsa ya dauke abun kama gashin daya siyo, yasaka shi cikin wata akwati, sannan ya danna wasu numbobi security din jikin akwatin yakoma yarufe, sannan ya ra6a gefen munirat din shima ya kwanta tareda sakin wata irin ajiyar zuciya ya Lumshe Idonsa Sai bacci.

Dasafe baije wajan aiki ba, tun safe da suka tafi wajan mama bai dawo ba, munirat ce tadawo ita kadai saboda tana shirin kar6ar baqin qawayenta Wanda zasu zo mata sannu da zuwa.

Sai yamma yakoma part dinsu, anan yaci Karo da baqin munirat da basu dade da zuwa ba,har hada baki suke suna gaida shi, ya amsa musu fuskarsa adan daure, sannan yawuce daki

'Daya daga cikin su mesuna meji (maijidda) tayi qasa-qasa da muryarta cikin sigar rad'a tace "tabdi, lalle munirat kina qoqari, irin wannan ingarman mijin naki yaushe wasu matan zasu iya dashi, kema fa Dan kina dagewa ne da shan magungunan damuke baki, Amma wallahi da idan ya riqeki, Sai kinyi kuka da idonki"

Murmushi tayi tace"Meji kenan, to waya fada miki baya sakani kukan? Ai ranar dakuka aikomin da magungunan kasa gane Kansa nayi, Nasha wahala ranar harda kuka, har mukaje Saudia a haukace yake "

Dariya suka saki harda shewa, ikee (iklima) data cika bakinta da naman kaza kasancewar tana period bata azumi, tace" ahh waya fada miki mudin na wasa ne? Ai inde kinbi wannan magungunan kina shansu akai akai, wallahi keda kishiya saide kiji anayi a maqota"

Munirat tace "hmm kude kubari kawai, Bari inje insame shi, kunsan shi da shagwa6a yanzu saiya fara min rigima nabarshi shi kad'ai"

Hauwi (Hauwa) tace "A a jeki Kam, adeyi ahankali kar akaryawa megida azumi, Amma fara sallamar mu dadan abun ta6awa saboda shan ruwa, saimu tafi"

Tace "karki damu Hauwi, harda tsarabar ku ta Saudia zan kawo muku yanzu yanzu"
tana fadar haka tajuya zuwa dakinta, sukuma suka hada ido tareda ta6e baki, kowaccensu haushi takeji Dama itace a matsayin da munirat din take.
Chapter 12 · 0% Book details