Sashe 23
Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Aisha ta kalleta kawai ta girgiza Kai batare da tayi magana ba
Bayan ankira sallar magrib Aisha Tasha ruwa sosai tayi wa Shahaab addu'ah, Amma addu'ar Tata tafi karkata ne akan Allah yabashi haihuwa idan yayi aure, kasancewar ya6oye mata cewa yana da aure, shiyasa koda wasa batace Allah yabawa matarsa ciki ba, fatan ta idan yayi auren Allah yabashi haihuwa Mai Albarka.
Washegari Hajja ta dauki azumin sitta shawwal, babu Wanda ta fadawa tana azumi, da azahar Ummah takawo mata abinci saitace Sai anjima zata ci, kunun Ayane a gabanta tana hadawa, saida ta zubasu acikin jarkoki sannan tasaka su a fridge da rufe.
Wani yaro ne yayi sallama yace "Wai abani kunun Aya na Dari bakwai"
Cikin murna Hajja tatashi, tadauko leda babba, ta zuba masa Yan Dari-Dari guda bakwai tabawa Yaron, shikuma yabata dubu daya, tad'auki canji tabashi tana cewa "idan sun shanye kadawo min da jarkokin kaji"
Yaron ya amsa, sannan yafice daga gidan.
Baifi minti ashirin da tafiya ba ya dawo yace "Wai abani pure water na nera ashirin"
Hajja tace "babu pure water yaqare, Ina jarkokin da'aka Sai kunun Ayar?"
Yaron yace "sun tafi dasu"
Cikin sauri jabir dayake zaune agefe yace "Alhamdulillah... inda nine ma Yan hamsin-hamsin zan siya yanda zaki Rasa jarkokin dayawa, haba Adinga maganar jarka de, kasai abu ai shikkenan jarka tazama taka"
Kafin Hajja tayi magana wani Almajiri yashigo da wasu jarkoki a hannunsa yace "Hajja ga jarka inzaki siya"
Jarkokin ta karba tafara dubasu, saida tagama dubasu tas sannan tace "wannan ai duk irin jarkokina ne dasuke 6ata, waye yabaka?" (🙆🏻♀️😂)
Yaron yafara rantsuwa yace "wallahi abakin kasuwa na tsinto su, banaki bane"
Cikin masifa tace "Kai jeka da abunka, sunyi qazanta dayawa, bazan siya ba, a tsinto jarkoki abakin kasuwa a kawowa Hajja mahaukaciya tasiya, debe su daga gabana bazan siya ba"
Aisha ta futo daga d'aki kanta babu dankwali, Sai qyalli gashin Nata yake kasancewar tashiga rana, ta kalli Hajja tace "keda kikace duk irin jarkokin kine?"
Hajja tace "mesunan qawa Ina kika samu wannan abun daure gashin? Sai daukan ido yake daga Gani yanada tsada"
Cikin ko'in kula tace "Walida ce tabani"
Hajja tace "tunda babanta yanada Hali zata Iya baki wannan Kam, jeki kar6omin wayata a gidan Jummai, dazu nabayar takaimin maqotansu naji sun kunna inji, 95 ne Dani shine nakeso subatse min ita"
Jabir yace "Hajja waya a 95 kika Kai wajan caji?"
Cikin masifa tace "to Ina ruwanka? Wayar nan fa saboda mesunan qawa nake kaiwa caji, idan tafara waya da inusa Kai kace akansu aka fara soyaiya"
Jabir bai sake magana ba, yaga yau Hajja masifa takeji, komai akayi mata Sai masifa, baisan azumi take ba (🤣)
Aisha kuwa hijabi tasaka, sannan taje ta kar6o wayar tabawa Hajja, Hajja tana Gani tace "ya haka? Menake Gani kamar 50 percent?"
Aisha tace "Wai data cikane shine jikan iya jummai yake kallo kafin kizo ki Kar6a"
Hajja ta Jinjina kanta tace "Amma kuwa jummai anyi marar zuciya da bazata iya futo na futo da jikokin ta akaina ba"
Ta juya ta kalli jabir tace "ga wayar inzaka siya kawo dubu biyun kawai"
Jabir yace "banaso akai kasuwa"
Cikin jin haushi tace "ai shikkenan"
Tajuya ta kalli Aisha tace "me sunan qawa ki shirya kije kano gobe, kisiyomin kayan hadin kunun Aya a singa, idan kikai wa su Malam kwana biyu saiki dawo" (malam mahaifin Hajja)
Tace "to Hajja Allah yakaimu"
******
Washe gari da yamma Aisha tatafi kano, dayake sun dan kwana biyu ba suje Garin ba Sai take murna da tafiyar Tata, gab da magrib ta qarasa kano, kasancewar a yankaba baban Hajja yake, kawai napep tashiga aka kaita har gida, malam da matarsa guda daya kishiyar mahaifiyar Hajja, dayake mahaifiyar Hajja ta rasu, Sai kishiyar ta, sunyi murna da zuwan Aisha, Fati jikar qanin Hajja datake zama a gidan tana tayasu Dan aikace aikace Nan da Nan ta janye Aisha da surutu, dayake Dama akwai Sabo a tsakanin su, Bayan sunci abinci Nan suka shige daki suka fara zancen samari, Fati tace "Aisha Ina samarin ki, nasan yanzu ankusa aurenki, tunda ku ba'a barin yarinya ta girma sosai kamar Nan"
Aisha tace "samari suna Nan, ni besan ma nataho ba, saide Hajja tafada masa idan yaje gida"
Faty takama ha6arta tace "tafiya babu yiwa saurayi sallama? Anya kwa dashi za'ayi?"
Dariya Aisha tayi tace "ke Ina naki saurayin?"
"Auwal yana Nan Shima, ai Yanzu tunda kinzo, zan kirashi yazo ku gaisa,"
Aisha tace "to Allah yakawo shi lafiya, yawwa Fati nikam in tambayeki mana, wata qawata ce tanada saurayi, to agida ansan shi, Kuma tana sonsa da farko, to Kuma Sai wani mutum yazo, batasan ko waye ba, Amma shi Dan maiduguri ne, duk Bayan kwanaki saiya kawo mata ziyara, Kuma har kudi yake bata, to seta fara tunanin sa, Kuma fa bece yana sonta ba, Wai yafi so kawai su zauna tare yadinga kallon ta, to dan Allah me hakan yake nufi"
Fati tayi fari da idonta cikeda yarinta kasancewar batafi Aishan shekaru ba tace"toshi meyasa ba zaije gidansu yace yana sonta ba?ai babu zumunci tsakanin mace da namiji, inde namiji yanason yarinya da gaske to zakiga wajan mahaifin yarinyar yake fara zuwa, saboda haka Ita qawar Taki, tace masa tanason wancen Wanda Yan gidansu suka sanshi, Shima tace masa inde yana sonta yafuto"
Cikin sauri Aisha tace"to ai bece yana sonta ba, itace take sonsa "
Fati tace" rainin wayo ma, Kuma baya sonta yake zuwa wajan ta? kawai idan ita tana sonsa zata Iya auren sa, tayi wuff dashi kawai "
Dariya sukasa, Aisha tace"ke babba nefa"
Fati kuwa cikin rashin kulawa tace"Babban,ai anfi yimusu shagwa6a, kiga sunata siyo Maka abinda kakeso"
Aisha tace"to shikkenan zan fada mata"
Fati tace"kifada mata wallahi"
haka suka kwanta bacci gaba dayansu daga ita har Aishan babu me hankalin da zaiyi tunanin meyasa to namiji zai dinga zuwa wajan ka kawai yana 6ata Maka lokaci shibece yana sonka ba, shibe futo fili yabari iyayen yarinyar sunsan dashi ba, itama fatin dayake yarinya ce kwata kwata bata gane cewa Labarin da Aishan tabata ba'akan qawatar Aishan ne ba.
******
Tsaye yake ahabar gidan nasa, tunda ya dawo daga sallar la'asar baifi ta ko'ina ba kasancewar yau juma'ah, Sanye yake da wando three quarter Sai Riga yar qarama wadda tasa farar fatarsa futowa sosai,sojoji Sai zagaya gidan suke suna zare ido, Bluetooth ne amaqale a kunnan sa yana magana da Ramadan, ahankali cikin qasa qasa da murya yace "ok saika qaraso"
Ajiyar zuciya yasauke yazira hannayensa cikin aljihun wandon nasa, sannan ya qarasa wajan wata yar qaramar tumfa da aka qawata ta da kujeru masu kyau, lemuka ne a ajiye awajan da ruwa dakuma fruit, Sai wata wayar tasa datake ajiye awajan, zama yayi tareda Dialing number Aisha, yadade baiji shirmanta ba, yanaso ya ganta yajita akusa dashi, fiyeda yanda yake son jin muryarta, yaga alama idan bashine Yakirata ba, ita bazata kirashi ba, yana kira Alokacin wayar tana hannun me ita, Hajja ta d'auka tareda sallama, jin ba muryar Aisha bace yasa yayi sauri yakashe wayar, yana d'ago wa yaga Ramadan ya qaraso, hannu yabashi suka gaisa, sannan yace "nasamu saqo ta Email dina Gwamnatin kano tana gayyata taron daza'a yi na Yan kasuwa, sannan akwai Daurin auren wata yarinya da mahaifin ta yake aiki a qarqashin hukumar mu dake jihar kano, mahaifin yarinyar ya turomin saqo cewa yanaso inyi masa waliyin yarinyar, so Naga duk rana daya za'a yi, shine nakeso ka rakani"
Ramadan yace "ok babu damuwa ai, yaushe ne tafiyar?"
"gobe insha Allah"
Ramadan yace "Allah yakaimu"
Fork ya dauka yad'auki yankakkiyar pineapple din dake gabansa, cikin aji yake taunawa kamar bayaso, sannan ya kalli Ramadan dake tsiyaya ruwa a cup yace "Naje Jigawa"
Ramadan batareda daya kalli Shahaab ba yace "eh aika fadamin kaje saboda kaji sunan yarinyar Nan ko?"
Shahaab yace "nakoma" (😍)
Cikin mamaki Ramadan yace "Tofa, yaushe?"
Kafadarsa yadaga alamun rashin damuwa yace "kaide tunda nacema naje, ai shikkenan, dole Sai kaji ranar?"
Murmushi Ramadan yayi yace "a a babu dole, amma wannan Karon zuwa kayi domin kaji shekarun ta nawa ko?" (🤣)
"no, tacemin tanason biro, shine naje nakai mata"
Cikin sauri Ramadan yace "yanzu saboda biro ka6ata kudin jirgi kawai kaje kakai mata kadawo?"
"to ai tana sone, Dame zatayi rubutu idan bankai mata ba?"
Ramadan ya jinjina Kansa, tsananin mamaki ya hanashi magana, shikam zai so ganin wannan yarinya, gaba daya tatafi da hankalin Shahaab, ya tabbatar inda ace bai bashi shawara ya6oye mata Kansa ba, da tuni iyayen yarinyar da'ita kanta yarinyar sun dade a Abuja, idan kayi masa magana ko sonta yake saiyace shi temakon ta yake, koma wacece ba qaramin so yake mataba, idan kuwa ya aure ta,Toya tabbatar Sai abinda tace, saboda ko lokacin dayake neman munirat, baiyi wannan haukan ba, fisabilillahi saboda biro?(🤔)
Ajiyar zuciya yasauke sannan yace "gaskiya Abokina kanason yarinyar Nan"
Cikin sauri yace "no, kawai de birgeni takeyi, tana birgeni sosai gata yar qarama, Amma tanada abubuwan more rayuwa najin dadin aure"
Ramadan ya katse shi da cewa "to tunda hakane mezai Hana ka aureta? Abubuwan dakake fada tana dasu saika more abunka Kai kadai?"
Kai tsaye yace "munirat fa?"
Haushi ne yakama Ramadan, baisake ce masa komai ba, saiya Dauko masa wata hirar, wadda ta danganci aikinsu(😂)
******
Washe gari asabat fati tatafi islamiya, Kuma basa tashi da wuri Sai karfe hudu da rabi, Aisha datake San tafiya jibi ta kalli malam shida matarsa tace "Baba malam nikam zanje insiyowa Hajja saqonta, jibi nakeso natafi"
Malam yace "to ai Zaki de gane ko?"
Murmushi tayi tace "zan gane mana, ai wajan bashida wahala"
Kudi yadauka yabata yace "to ga kudin adedeta, saikin dawo"
Sallama tayi musu, sannan ta shirya cikin wata doguwar Riga ta atamfa, tasaka hijabi sannan tatafi, tun kafin tafiyar su tayi nisa taga Garin Yacika da goslow, gashi de tafiyar bawata me Nisa bace Amma sun kusa awa daya a hanya, Dan adedetan ne yasaki tsaki yace "wannan hanyar akwai go slow sosai Bari mu sauya hanya"
Cikin damuwa Aisha tace"ni banaso ma karfe shida tamin a waje wallahi, da nasan haka Garin yake da go slow da tun safe nafuto nayi abinda yakawo ni"