← Book details Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 71

Sashe 14

Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Badon yasoba haka ya yarda da shawarar Ramadan akan zai 6oye mata koshi waye yaje mata Ahaka, Amma da yayi niyyar yaje ya fuskance ta, yafada mata shine Mahmud Wakili ba Shahaab ba, kamar yanda yafada mata ranar, sannan Kuma yasa tafada masa dalilin ta na zaginsa, Kuma yabata kudin takar6a Dan dolenta (tofa😲)

******

Da daddare inusa yazo, yaturo wani yaro Akira masa Aisha, gaba dayansu suna zaune atsakar gida, Yaron yayi sallama yace "Wai Ana Kiran Aisha inji Inusa me Kanti"

Hajja tace "hmm Kaikuwa yaro daga Kai har Inusa me katin Baku iya sakaya suna bane? Aisha haka gatsau ko dadin ji babu? To daga yau karna qaraji,jekace masa gatanan zuwa"

Yaron ya amsa da "to" sannan yafita

Aisha kuwa tanajin Kiran ranta ya6aci, saboda shirin tafiya sallar Ashan take yi, batason yin fashi kullum Sai taje, Kuma hakan baya hanata anjima ma karfe daya da rabi na dare tasake komawa sallar tahajjud,Amma yarasa yaushe zaizo Sai yanzu? To kode shi baya zuwa tarawih din?

Hajja tace "ba kiranki ake bane me sunan qawa?"

Tashi tayi tad'auki hijabin Sai turo dan qaramin bakinta take gaba, tana saka takalmi Hajja tace "zoki dauki dan ruwan Sanyi a fridge kitafi masa dashi, idan kinje Kuma kifada masa karya sake cemiki Aisha, uwarki da ubanki ma me sunan qawar Hajja suke cewa, danhaka karya sake cemiki Aisha, qawata tanada daraja ba sa'ar uwarsa bace" (😅🤭)

Itade Aisha batace komai ba tad'auki ruwan tafice, da sallama ta qarasa suka gaisa, tace masa "Inusa ga ruwan Sanyi inji Hajja"

Murmushi yayi yace "Haba Aisha, Inusa Kuma? Kuma kowa yana cewa Inusa kema Inusan zakice?"

Tace "Tome zance?"

"a a, Yunus zakice, ai awajanki sunan na daban ne"

Zuciyar ta daya tace "Nima to kadena cemin Aisha, sunan qawar Hajja gareni, Kuma su Abba ma basa fadar sunan saboda irin sunan Hajja ne"

"ikon Allah, to Amma Aisha arasa sunan wadda za'a saka miki Sai sunan qawar kakarki?"

Tace "Um Haka Hajja taso, Kuma Nima duk abinda Hajja takeso to inaso, saboda inason kakata, itama tana sona"

Murmushi yayi yace "Alhamdulillah kice Nima kinasona Kenan, tunda ai Dama kafin nazo saida akamin iso awajan Hajjan, yaushe zata fara kunun Ayar tane?akwai wani sikari (Suger) Dana dade da ajiye matashi, zan kawo miki shi saiki bata, tunda kince kina qaunar Hajja, nikuma kenake so, kinga Nima dole ne naso abinda kike so "

Ahankali tace" A a mungode Amma ka barshi "

"to ai kinji abinda yake had'ani dake, aini ne nayi niyyar baki,idan kikaqi kar6a ba zanji dadi ba, yanzu de Dama zuwa nayi naganki, ko zanji Sanyi araina, nasan zakije sallah, Bari nabarki haka Naga munyi kusan minti talatin, ga wannan naki ne, ki Kai a dinka miki da sallah, kudin dinkin yana ciki "yafadi haka yana bata wata baqar leda

Girgiza Kai tayi tace"a a nagode Amma ka barshi"

Tace "meyasa? Kode kin Rena?"

Kanta ta Girgiza masa, yace "to kar6i"

Hannu biyu tasa ta kar6a sannan tayi masa godia, yace "to yimin murmushi mana"

Kunya ce ta kamata, tasa hannu biyu tarufe fuskarta, cikin sauri ta wuce gida

Tana zuwa tabawa Hajja ledar , ta wuce ta dauki buta tayi alwala, Tai shirin tafiya masallaci

Hajja ta bud'e ledar atamfa ta bayyana, da kudi nera dubu biyu, atamfar irin ledar Nan ce me sauqin kudi (labona)
Hajja tasaki guda tace "Alhamdulillah, jikata tayi goshi, Hadiza, mamuda kunga abin Arziqin daya kawo mata, harda dubu biyu, tashi daya, yabata kudin albashin ta na wata guda"

Abba yace "Allah yasaka masa da alkhairi"

Ummah tace "ya kyauta, Allah yasa ayi damu, ai inusa bashida laifi, yana ganin girman manya duk inda yaganni saiya tsugunna yake gaisheni"

******

Yaso ace yanzu haka yana jigawa, yanaso yasake Sakata acikin Idonsa yaji dalilin dayasa take zaginsa, to Ramadan ya hanashi tafiya yace yabari su shirya sutafi tare.
Shikuma Ramadan dalilin dayasa yayi haka yanaso ne sutafi tare dashi danya dinga cusa masa ra'ayin yarinyar ahankali, harga Allah so yake Shahaab yayi aure ko Shima zai samu magaji

Mama ta kallashi, tunda ya dawo daga wajan aiki take lura dashi acikin tunani yake, kuma yakasa tashi yaje yayi wanka yacire wannan suit din ta jikinsa, hannu bibbiyu yayi tagumi yana kallo, Amma hankalin sa ba akan kallon yake ba,sau uku tana sauya Tasha Amma tana lura dashi ko motsi ba yayi Idonsa yana waje daya

Ahankali tace "Shahaab"

Cikin damuwa yajuyo ya kalleta yace "na'am mama"

Tace "har yanzu baka nemomin mekula Dani ba, koka manta ne?"

Maimakon yabata amsa saiya miqe tsaye, cikin damuwa yace "mama abubuwa sunmin yawa, kisa a duba miki kawai"

Daga yanayin yanda yake magana kad'ai zaisa kagane yana cikin matsananciyar damuwa
Ahankali tasake cewa "Shahaab"

Yajuyo yace "na'am"

"zonan"
Abinda tace dashi kenan, babu musu ya dawo gabanta zai zauna aqasan kafet din, cikin sauri tataroshi, ya dawo kan kujera, ahankali tajashi jikinta ta rungume shi, wata irin ajiyar zuciya yasauke, yasake qanqameta, sumar Kansa ta dinga shafa masa, ahankali har wani bacci me dadi ya dauke shi

Jin yasaki jikinsa yana bacci yasa tata6e baki, cikin zuciyar ta tace "banga amfanin munirat ba, mijinki yana cikin damuwa Amma ko ajikinki, yanzu haka damuwar akan office dinsu ne, tariga tasan inde akan wannan aikin nasu ne to baya kula da cikinsa ma kamar yanda yake kula da wannan office din"

Kusan awarsa d'aya yana bacci, mama da Hankalinta yakoma kan kallo can qasa-qasa taji Shahaab yana cewa " 'yar qarama...., 'yar qarama...."

Mamaki yakama mama, batasan lokacin data Kai dubanta gareshi ba, cikin zuciyar ta take cewa "wacece Kuma 'yar qarama?"

SHAHAAB littafin kudi ne,naira 300 ne kacal 👌🏻yar'uwa siyan nagari maida kudi gida, ki biya naira 300 ki karanta abinki Hankali kwance

Zaki tura 300 ta wannan account din

0164549488
Amina muhammad
GTbank

Zaki tura shedar biya ta wannan number 08033300034

Amnah El Yaqoub✍🏻
[10/09, 22:14] +234 803 697 8511: 🌸SHAHAAB🌸
(Romance)

Writing By Amnah El Yaqoub

Dedicated to Aisha's Name

Like my Page On Facebook👇🏻

https://www.facebook.com/amnahel

15&16

Kallan sa tasake yi, itade tasan cewa Shahaab baya kula mata, yanda yad'auki son duniya ya d'orawa munirat batajin wannan 'yar qaramar dayake fad'a da mace yake, takai shekara da shekaru tana fad'a masa yanemo yarinya ya aura, Amma har Zuwa yanzu saide yace mata shida munirat Sai Allah, tarasa Yaya zatayi dashi, shiyasa ta tattara shi ta watsa.
Ta6e bakinta tayi tad'auki remote tasake sauya Tasha

Sai yanzu ne yayi wani juyi, yaci gaba da baccinsa, yad'ad'e yana baccin sa me dad'i cikeda mafarkin Aisha, sannan ahankali yabud'e Idonsa,mama ta Kalle shi tace "katashi?"

Cikin shagwa6a yace "um"

Tace "to sannu da mafarki, d'agamin cinyata"

Gabansa ne yayi wata irin faduwa "karde mafarkin Dayayi yanzu mama tajishi" shiru yayi yakasa cewa komai, yasan cewa Saitayi masa tatas saboda yanda yaqi jinin a had'ashi da wata yarinyar, Amma yau gashi shine da mafarkin wata qanqanuwar yarinya, haushin Kansa ne ya kamashi, to Shima miye na mafarkin Nata? Daga kwanciya bacci, cikin baccin ma bazata barshi ya sarara ba?

Mama tace "karufawa kanka Asiri Shahaab, kar aikin ku yasaka ka koma qaramin mahaukaci, toma 'yar qaramar me kake kira?"

Cikin qaramar murya kamar baison magana yace "no mama kawai mafarki ne, akwai wata yar qaramar flower ne dana dad'e Ina nema" (🤭)

"toshi fure har wani muhimmanci ne dashi dakuke neman sa yanzu? Wasa kakeji dashi, kaga tashi kaje kayi wanka,babu abinda munirat take Sai riqe waya, saika sata ta duba ma furen"

Hamdala yayi cikin ransa ganin bata ganoshi ba,daga mata Kai yayi sannan yatashi yatafi

Yana tafiya tad'auki wayarta tasa wata mata akano ta bincika mata yarinya wadda zata dinga kula da ita, Amma anan arewa takeson yarinyar, saboda ta gwada na kudu dayawa Amma babu abun Arziqi

Matar kuwa cikin ladabi ta amsa mata, sannan sukai sallama

******

Yau jummai ce tazo musu gidan tunda sanyin safiya, dukansu kuwa suna gida babu Wanda yafita, Abba ma yana kwance yana jin taskar labarai a redion Aisha.

Bayan sun gaisa ta nemi waje ta zauna sannan tace "Hajja A'i gulma ajali inba'ayi ba amutu, wani zance ne nazo muku dashi keda mamuda Da Hadiza, Amma kafin Nan kunada Dan magi kubani? Saboda yau dafaduka zanyi"

Hajja tace "bamudashi jummai, fad'amin meyafaru?"

Jummai Tace "Ina wannan bawan Allah mejin tausayi da jinqan al'uma? To dazu dazu yayata Datake kano tamin magana tace itama maqociyarta ce wata Mai kudi, tace Dan Allah ayi mata ciki yar aiki, zata turawa wata Hajiya datake zaune a Abuja yarinyar, to Amma hajiyar Abujan ance tanada mugun kudi sosai, Dan da yan kudu take dauka aiki Kuma kasancewar anga tana bada kudi kamar ruwa, Sai mutane suka fara asiri, kowa so yake dansa yaje yayi aiki a gidanta "

Hajja tace" ikon Allah na kwance yafadi..., to ita kwa wannan wanne irin kudi ne da'ita haka kamar yayi?wacece? "

Jummai tace"ai hajiyar Kanon tace wadda take neman yar aikin Mahaifiyar shugaban EFCC ce wannan Yaron de MAHMUD WAKILI, Wanda yamana Rabon kayan Azumi, Amma fa Ana bala'i sosai idan mutum zaiyi aiki a gidan, sannan Kuma akwai kudi sosai,Kuma ance matar tanada izzah sosai, saide Kuma duk masu aikin gidan ma kadai, suna cikin kulawa saboda akwai tsaro a gidan na sojoji da yan sanda, sannan masu aikin ma inde a gidan suke to sun riga sunyi kudi, sainake ganin ko Zaku tura mesunan qawarki, tunda zataci Tasha, ta dinga aiko muku da kudade Kuma"

Hajja tayi ajiyar zuciya tace"ai jummai kin 6ata zance tunda kikace Ana bala'i sosai idan mutum zaiyi aiki a gidan, menene abun bala'i a neman aiki duk dade itama mesunan qawartawa yar bala'i ce?"(🤭🤣)

Jummai ta kalli Abba da Ummah tace"mamuda bakace komai ba, Hadiza kiyi magana mana"

Ummah tace "nikam duk abinda Hajja tace ai ya zauna, Hajja ai itace komai na mesunan qawarta, nikam ai kawai haifarta nayi"

Abba yace"gaskiya hakane Kam, saboda haka iya jummai da anyi hakuri da maganar aikin Nan, tunda de yanzu gashi inusa yafuto Kuma naga alama da gaske yake, to kawai babu damuwa zan hadata aure dashi, Nima Hankali na zaifi kwanciya, koba hakaba Hajja?"

ya qarasa maganar yajuya yana Kallan Hajja
Chapter 14 · 0% Book details