← Book details Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 71

Sashe 29

Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin tafiya de tazama dole yasa tabawa kanta haquri tayi shiru har Allah yakaisu kano lafiya, Bayan sun huta sun d'anci abinci Hajiya Amina tace "baba jummai ai nayi zaton kunfasa kawo yarinyar ma, itama Kuma Hajiyan bata sake kirana akan maganar ba, Amma gaskiya Ina tunanin tariga tasamu ma, Bari de inkirata inji Yaya ake ciki"

Addu'ah Aisha take a ranta Allah yasa tariga tasamu din, ba komai ne yasa take kukan barin gida ba Sai rabuwa da Hajja dakuma tunanin yanda Shahaab zai dawo yaji labarin bata Garin.

Jin Hajiya Amina tana magana awaya yasa tamaida Hankalinta kanta, Bayan sun gaisa cikin ladabi Hajiya Amina tace "Hajiya Mama Dama akan maganar me kula dakene, nace gashi ansamu wata yarinya idan har yanzu baki samu ba"

Daga can 6angaren mama tayi magana, Sai Hajiya Amina tace "a a wallahi yarinya ce qarama baki ganta ba, Kuma babu qazanta a tareda ita, ke kanki Sai hankalin yarinyar ya birgeki, babu wani datti tsaf take, babu Wanda zaice yar aiki ce"

Mama ce tasake magana, Sai Hajiya Amina tasake cewa "to.... To shikkenan, saisun zo d'in, babu komai wallahi Nima nagode"

Aisha tanajin haka ta Lumshe idon ta, shikkenan tafaru ta qare.

Kallan su tayi tace "to Alhamdulillah tace ba'a samu ba, Aisha saiki huta yau, gobe zansa driver daga Nan yatafi dake, zai Kaiki har can insha Allah"

Jummai tace"to yanzu Amina Yaya batun kudin aikin ta?saboda idan nakoma inshaida wa mahaifinta yanda mukai dake "

Murmushi tayi tace"idan taje gidan Hajiya Mama zata fad'a mata yanda zata dinga biyanta, Nima tace zata turomin wani abu ta account dina, Baba jummai Aida kinsan gidan da Aisha zata tafi da bakiyi min maganar kudin aikinta ba, saboda duk Wanda suke aiki a gidan suna samun alkhairi sosai, bare Kuma Nata aikin special ne, bawani aikin wahala zata dinga yiba,"
Tajuya ta kalli Aisha sannan tace"Aisha idan kikaje babu ruwanki da harkar kowa kinji ko? Mahmud yanason mamansa, zai iya yin komai saboda wannan tsohuwar matar, bayason abinda zai 6ata ranta, Kuma zai iya 6atawa da kowa saboda ita"

Iya jummai tace "yawwa to ai Gara kifada mata tun yanzu kinga idan taje gidan shikkenan tahuta da bincike akan halaiyar 'Yan gidan, menene ma zai had'ata da wannan matar bare har ta 6ata mata rai?"

Hajiya Amina tace "inde ta kiyaye tsakaninta da mama to ai batada wata matsalar komai, saboda a yanda naji shine, Mahmud din yana son matarsa sosai, amma duk soyaiyar dayake mata inde ta 6atawa mama rai to sa6ani take samu dashi"

Tunda suka fara magana Aisha bata saka musu baki ba Sai yanzu, ahankali tace "yanada mata?"

Murmushi Hajiya Amina tayi tace "haba Aisha, Babban mutum kamar Mahmud Wakili ai dole ya ajiye iyali, Amma ke ai ba 6angaren matarsa zakije ba, kefa kina wajan Hajiya mama, duk ayyukan da zakiyi to abinda ya shafi mama ne"

"wanne irin aiki ne?" tasake tambaya

Hajiya Amina tace "Zaki dinga kula da'ita, zaki dinga riqe hannunta kudinga Dan tattaki a gidan saboda ciwon qafafunta, zaki dinga matsa mata qafafunta, idan angama abinci Zaki zubo mata ki kawo mata, zaki dinga yimata hira saboda karki Barta cikin tunani"

Aisha ta Jinjina kanta tayi shiru, irin wannan hidima haka saikace basarakiya?(🤔)
Iya jummai tace"saboda Allah yanzu wannan har aiki ne?ai wannan bazaka kirashi aiki ba tunda kince matar ta manyanta wannan aikin ai idan ka taimaka mata kaima zaka samu Lada,tobakada aikin fari bare na baqi kawai zama fa zakayi tareda ita,"
Tajuya ta kalli Aisha tace"me sunan Hajja,kisa aranki saboda Allah Zaki mata komai, sannan ki kalleta kamar Hajjanki, insha Allah sakamakon ki yana wajan ubangiji"
Haka suka dinga zancen gidan har dare, kasancewar akwai kayan kallo a gidan Sai Aisha tad'an saki ranta tana kallo,lokaci zuwa lokaci Hajja da Ummah suna Fado mata Arai.

******

Hajja ta kalli Ummah da Abba tace"yanzu mamuda abinda ka aikata kayi daidai kenan? Yarka guda daya jal 'ya mace ka dauketa ka rabamu da'ita? Mamuda kodan yanda na shaqu da mesunan qawa ashe bazaka Gani ba?bansan cewa bakada mutunci ba Sai yau, Ina kuka yarinyar Nan tana kuka haka ka rabani da'ita, ai shikkenan babu komai, yau ka nunamin kafini iko akan AISHA"
Tana qarasa fadar haka ta Fashe da Kuka, cikin sauri Ummah ta kalleta jin sunan AISHA data fada Kai tsaye, abinda bazaka ta6aji Hajja tafada ba, ahankali tace"Hajja kiyi hakuri, abinda yasa bansaka baki ba akan maganar yarinyar Nan, Hajja ke kanki sheda ce munbawa Aisha tarbiya, kema kin bata, Aisha tana da Hankali, Barta de da rashin kunya wani lokacin, Amma abun mamaki da tsoro shine yanda ta'iya kallon idon mahaifin ta tace ita Shahaab take so, yana Dukan ta Amma yarinyar Nan haka take sake fada ita Shahaab take so, Sai abun Nata yabani tsoro, lokacin da akazo da maganar inusa ko musu batayi da mu ba, Amma zuwan wannan yaro Shahaab cikin rayuwar ta gaba daya ya sauya mana tunanin Aisha, yanzu dasuke shiga mota suna zance bamu San yaushe take zuwa wajan sa ba, inda ciki nema haka zaiyi amfani da qananun shekarun ta yayi mata, Amma Kuma saida tatafi nake jin kamar mun aikata kuskare, Ina tsoron kar Yaron Nan Shahaab yabita can Abujan suci gaba da abinda suke" tana fadar haka tafara share hawaye

Hajja datake kuka tace"kul Hadiza, banaso na qara ji kince mesunan qawa zata aikata wannan mummunan aikin, inde halin takwararta ta'iyo babu abinda zata aikata, kuskure de ubanta gashinan yariga yayi, duk abinda yabiyo baya, saiya kuka da Kansa"
Tana fadar haka, ta share Hawayen idonta tatashi tashige dakinta tanajin kamar zataga Aisha tana game a wayarta.
Ajiyar zuciya Abba ya sauke yana sake gaskata wa zuciyar sa cewa dade ace yabar Aisha anan, Gara tatafi Abujan yafi masa kwanciyar Hankali, ko banza idan Yaron yazo yagaji da zuwa zai haqura yabar masa yarsa

******

Washe gari karfe Goma nasafe suka tafi, jummai bata tafi ba saida taga tashin su Aisha sannan itama tafara haramar tafiya gida.

Sai Bayan la'asar suka Isa Abuja, Aisha tun tana bacci tana farkawa harta daina,bata ta6a tafiya me Nisa irin wannan ba, Sai abun yazame mata Sabo, tunda suka shigo cikin Garin kuwa tabaza ido tana kallo, sunyi tafiya me Nisa sosai acikin Garin sannan suka qaraso wani tanfatsetsen gida, baki bude take ganin tsaruwar gidan, yanayin unguwar babu hayaniya, Babban titin daya kawoka har bakin get din gidan ta kalla babu wasu mutane dasuke zama awaje kamar yanda akeyi a garinsu, Lema ce a kwance akoi'na alamun ruwa aka gama yimusu, Sai yanayin Garin yasake yin kyau, bata gama mamaki ba taga sojoji sun bude musu get din gidan, saida direban ya basu wani I'd card suka Gani sannan suka barsu suka shiga, batasan dalili ba haka Nan ta tsinci kanta da faduwar gaba har Sai tafara karanta "hasbunallahu wani'imal wakeel" acikin ranta.

Motar su tana tsayawa aharabar gidan taga sojoji ta ko'ina suna shawagi, Sai yanzu tasake ganin kyan gidan, tashin Hankali ne ya wanzu akan fuskar ta, yanzu wannan gidan mutane ne suke rayuwa aciki gida kamar aljannar duniya?
Sai yanzu ne tasake tabbatar wa Mahmud Wakili ba qaramin mutum bane, duk yanda ake bata labarinsa ashe yawuce haka, wannan shi ake kira jinka yafi ganinka.

Direban ne yafuto yabude mata motar yace "futo muje" yanda yabata girma harda su bude mata mota yasa Shahaab yafado mata Arai, duk yanda yake da kyau dakuma shekaru bude mata mota yake kamar itace shugabar sa, kawar da tunanin tayi daga cikin ranta suka qarasa cikin part din Hajiya Mama.

Tsaruwar falon Nata ne yasa Aisha tasake daga kanta ta kalli falon sosai, batace komai ba face Jinjina kanta datayi, wata mata ce zaune acikin daya daga cikin kujerun falon ta dora kafarta daya Kan daya,banana ce a hannunta tana karya kamar bata son ci, hankalin ta nakan abinda ake yi a TV.

duk da daga nesa ta hangeta saita ga batafi Hajja shekaru da tsufa ba, daya daga cikin masu aikinta dake tsaye abakin kofar itace tace dasu "sannunku da zuwa, ku qaraso"

Direban ne ya amsa da "yawwa" sannan tayi musu jagora zuwa wajan mama, qasa ta tsugunna tayi wa mama magana sannan ta juya zuwa kitchen

Cikin farinciki mama ta juyo ta Kalle su tace "sannunku da zuwa,mutanan kano ne?"

Aisha batayi magana ba Sai kallon matar take, haka kawai taji matar ta kwanta a ranta,kwata kwata a shekaru batafi Hajja ba, saide kana ganin ta kaga hutu da jin dadi daram ajikinta, tayi tunanin zata yi musu kallon wulaqanci a yanda ake bada labarin izzarta.

Zama sukai har suna hada baki wajan gaida ta, cikin murmushi tace"sannunku da zuwa," ta maida kallonta ga Aisha tace"yar kyakykyawa kece Mai aikin?"

Cikin sauri Aisha ta kalleta sannan tayi qasa da kanta, cikin ladabi tace "eh nice MAMA"

Jin yanda ta kirata da mama Sai hakan yayi mata dad'i, duk yanda akai yarinyar tanada nutsuwa, cikin jin dadi tace "masha Allah, kema daga kano kike?"

Kanta aqasa tace "A a Jigawa"

Gaban mama ne yafadi,jin sunan Garin yasa ta tuna da qawarta Aysha Sulaiman Bompai, Sai taji a ranta koda batada ra'ayin yarinyar to dole zata sake riqeta saboda tafuto daga jihar da qawarta tayi aure, dalilin Garin dole zata dauketa, cikin murmushi tace "menene sunanki?"

"AISHA" tafadi hakan kanta tsaye.
Mama tace "masha Allah,kice tsohuwa ce"

Murmushi su Aisha sukayi, Adede lokacin Mai aikin takawo musu abun motsa baki, mama tace "kikai masa Dakin baki saiki dawo kitafi da Aisha"

Cikin ladabi tace "to mama"

Tashi Direban yayi yabi Bayan me aikin, Bayan sun tafi mama tasake kallon Aisha tace "Aisha kisaki jikinki kinji? Maganar gaskiya Ada maiyi min hidima nace akawo min, to Amma kasancewar kinfuto daga jihar datake da dumbun tarihi awajena, saina ji bazan iya sakaki aiki ba, idan babu damuwa zan dauke ki kamar jikata, Nan gidanku ne, kidaukeni kamar mahaifiyar ki, ni banida matsala inde anyi min abinda nakeso, abu daya nakeso kikula dashi shine banaso idan Dana yazo inda nake Inga wani mahaluqi awajena, inde Mahmud yana tare Dani inaso inganni nida shi mu biyu"

Cikin ladabi Aisha tace"insha Allah zan kiyaye mama"

Mama tace"kinada account ne Wanda za'a dinga tura miki kudin aikinki aciki?"
Chapter 29 · 0% Book details