← Book details Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 71

Sashe 46

Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saida sukai sallar ishsha'i sannan suka dawo gida, Abba ne yayi waya aka kawo wa securities lemuka da ruwa, sannan Shahaab yace suje hotel cikin dutse su kwana, zasuyi waya gobe, direban daya kawo su yabawa kudi masu yawa, daga Nan suka tafi gaba dayansu.

suna zuwa gida Kai tsaye d'akin Abba suka wuce, Abba yafuto yayiwa Ummah magana aka kaiwa Shahaab ruwan wanka, sannan yaje yayi masa magana, ankai ruwan wanka bandaki, shikuma yawuce Dakin Ummah, saida sukaji shigar sa bandakin sannan Abba yace"bari infita asiyo kayan shayi, idan yafuto saiki sa Aisha takai masa abinci, saiya kwanta acan, nikuma saina taho Nan mukwanta"

Ummah tace"to saika dawo, ataho mana da qwai da Dan dankalin turawa in za'a samu, Sai ahada ayi amfani dashi"

Amsa mata yayi, sannan yafuto daga d'akin, dakinsa yakoma ya futowa da Shahaab wata sabuwar jallabiya daya siyo ta tundaga Saudia a zuwansa Umarah, ya ajiye masa ita akan gadon, sannan ya ajiye masa turare da man shafawa, yafice daga gidan cikin sauri.

Yana futowa daga wanka Dama tunanin kayan sakawa yake, Sai yayi tozali da kayan akan gado, murmushi yayi, yarufe Dakin sannan yacire kayan jikinsa gaba daya, yasaka jallabiyar yafeshe jikinsa da turare,Sai a lokacin yasaki ajiyar zuciya yad'auki wayarsa yakira Ramadan yana bashi labarin komai.

Saida Ummah ta danja lokaci sosai Wanda Takeda tabbacin yagama shirya wa sannan ta zuba masa abincin da kanta, ta bude fridge din Hajja tad'auki kunun Aya masu sanya ta juye su a jug, tahada komai, tashiga Dakin Hajja, duk suna fira Aisha tana game a wayar Hajja, Ummah ta kalleta Tace"Qawar Hajja ga abinci Nan tashi kikai masa Dakin Abbanki"

Cikin nutsuwa tace"to Ummah"
tatashi tasaka hijab dinta, Tajuya zata fita.

Cikin sauri mama Tace"A a takwara, dawo ki fesa turare Sai kije, dama can danake barinki kina haduwa dashi babu shiri, bansan menene a tsakanin Kuba, yanzu Kam dole yaga canji ai"

Murmushi Ummah tayi,Cikin kunya Aisha ta fesa turaren sannan tafuto ta dauki abincin ta wuce Dakin Abba, saida tayi sallama kafin tashiga, waya yake Amma yana jin sallamar ta yakashe wayar yace"shigo mana"

Shiga Dakin tayi, ta'ajiye abincin aqasa, sannan tafara zuba masa, ko kadan taqi kallon sa, Shikuwa tun shigowar ta yakafeta da ido yana kallonta, saida tagama zubawa sannan
Ahankali tace masa"gashi"

Murmushi yayi babu musu ya kar6i abincin yafara ci, dadin abincin yasa yadan Lumshe Idonsa, sannan yabude ya kalleta yace"abincin yayi dadi "

Murmushi tayi batace komai ba, Shima bai sake magana ba, saida yagama cin abincin, yaci sosai kuwa, sannan ta tsiyaya masa kunun ayar adan qaramin cup tamiqa masa, hannu biyu yasa yakarbi cup din yahada da hannunta yariqe, sannan yakai bakinsa ya shanye,yaji kunun ayar akwai dadi, yasaki hannunta yace"qaromin"

Cikin sauri taqara masa, yasake hadawa da hannunta yashanye, sannan ya zare kofin da dayan hannunsa, hannunsa dayake riqe da'ita Kuma bai saketa, cikin sauri tafara kokarin qwace hannunta , shikuma yaqi sakinta saima gefen hijabinta daya riqe yana tsoron karta gudu, cikin faduwar gaba tace"dakin Abba nefa, kasakar min hannu karyazo, Allah idan yaganni duka zaimin"

Idonsa ya Lumshe sannan yabude, cikin sigar rad'a yace"bazai zoba fa, meyasa kike wahalar Dani?kika gudo gida bakya tsoron a sacemin ke a hanya ko?"

Cikin shagwa6a tace"toba mamace ba"

Cikin wani irin yanayi na buqata yace"metayi?"

Saida ta turo bakinta gaba sannan tace"video fa ta nunamin, Wai nice dakai"

Hannunsa dake riqeda ita yasa ya shafa dogon hancinta, cikin sauri ta Lumshe idonta, yayi kasa da bakinsa yad'ora lips dinsa daidai kunnanta yace"kinga videon?"

Cikin sauri ta daga masa Kai alamun tagani, murmushi yayi yace"saiki shirya, dannima saikinmin irinsa"

Wata irin kunya ce ta kamata, cikin sauri tarufe idonta da hannunta,yanayinsa yaji yana sauya wa, cikin rad'a yasake ce mata"me kika Sakamin acikin kunun Aya?"

Cikin sauri ta Girgiza kanta, yadage mata girarsa guda yace"really? To meyasa nake jina wani irin?"

Kallan sa tayi tace"menene wani iri?"

Yace"bakisan wani iri ba?"

Cikin rashin Sani tace"ni bansani ba"

Murmushi yayi yace"to infada miki yanda yake?"

Cikin sauri Tace"A a "

cikin yanayin rad'a yace mata "why?"

Kanta ta Girgiza masa tace"dakin Abba nefa, tsoro nakeji, Nika denamin wannan maganar cikin rad'a, wani iri nakeji "

Dariya ce ta kamashi, babu musu yasake ta sannan yace"yanzu kinsan wani iri kenan ko?Maaama na lura bakya tausayi na,kinfi tausayin mama akaina,shiyasa kika zama tauraruwa awajanta,dakika taho haka ta dinga tambayata naduba Naga inda kike? Ajima tasake cewa anga Aishan kuwa?saida nakawo ta har gida, sannan nasamawa kaina , da zuciyata lafiya, Amma Kuma gashi ke Sai wahalar mata Dani kike...."

Yaya labarin Anty munirat ne? 🤔

Mutara zuwa anjima 🙏

Idan kika karanta baki biyaba nabarki keda mahaliccinki, littafin kudi ne, 300 ne kacal, ki biya ki karanta karki karanta haqqin wani

0164549488
Amina muhammad
GTbank

Number
08033300034

Amnah El Yaqoub ✍

BASAJA TAKU NA UKU

"momy wallahi bazan iyaba,nariga nagama yanke hukunci akan zamana dashi, bazan ta6a bude idona a gidannan Inga Mahmud yana tareda wata matar Bayan niba, mahaifiyar sa itace matsala ta, Kuma yanzu nagama da wannan matsalar, saikuma yarinyar, agabana fa yarinyar tazo gidannan Amma saboda qiyaiyar da mahaifiyar sa take nunamin harta cusa masa ra'ayin yarinyar, wallahi anayin kuskuren daura musu aure wallahi saide yayi biyu babu.... Babu nidin, babu itan..."
taqarasa maganar cikin matsanancin kuka.

Saida tayi kukan ta sosai, sannan momynta tasaki ajiyar zuciya tace"mekike shirin aikata wa munirat?,kifadamin menene shirin ki nagaba? Ni tunda kika fadamin maganar abunda nakawo raina shine kawai muje wajan malamai ayi roqon Allah akan Allah ya watsa lamarin, ya fitar masa da yarinyar daga Kansa, a cireta acikin zuciyar sa, Amma ita mahaifiyar sa menene Nata aciki? Shifa shine me auren, duk tsiya shine yakai mata maganar zaiyi auren harta samu take fada miki magana akan haka, Amma yanzu de fadamin shirin ki nagaba, idan naji yayi daidai da nawa shikkenan"

Cikin kuka tace"momy kamar ni? Ai abun kunya ne ace mijina zai qara aure, momy kishiya fa zaimin, qawayena dariya zasumin suce Dama Bana kula dashi yanda ya kamata,momy dame na ragi Mahmud? Kullum cikin gyara nake, ita mahaifiyar tasa ai itace take kitsa masa komai, idan tace yau ya auri mata uku, to adaran zai aura saboda yana jin maganar ta"

Cikin sauri momy ta katseta tace"yanzu mekika yanke akan hakan?"

Cikin 6acin rai tace"zaki Gani momy" daga Nan takashe wayarta.

Zagaya Dakin taci gaba dayi, idonta yayi jajir saboda kuka da 6acin rai, ahankali tasake Kai hannu ta share Hawayen daya sake zubo mata, tunda taga har dare yayi basu dawo ba, hakan yana nufin acan zasu kwana kenan, bata kirashi ba, haka Shima bai nemeta ba, abunda yaqara qona mata rai kenan, yanzu haka yana can tareda wannan yarinyar me cusa kan masifa, kokuma yanzu ma yana can tana bashi abinda tafara bashi anan hartaja Hankalinsa akanta.

To ni made bansaniba munirat, bari muje mugani idan hakane ko bashin ake😂🙈🏃🏻‍♀️

(littafin kudi ne, idan kika karanta baki biyaba nabarki keda ALLAH)

******

Harararsa tayi,cikin qasa qasa da murya tace"ni ban wahalar dakai ba"

Cikin sauri yace"gashinan kuwa,Bayan abunda nakoya miki ma yau ko tayani bakiyi ba,Amma last time saboda mugunta haka kike ta tsotsar bakina, ko tausayamin bakiyi ba,bakiyi tunanin zan iya fita daga dakinki nahadu dawani afalo yaga yanayi na, yayi tunanin wani abu a tsakanin muba"

Cikin sauri ta kalleshi tace"bakaine Kamin ba"

Cikin sauri Shima yace"yawwa to tunda hakane meyasa ni yau din bazakimin ba?"

Kafin tabashi amsa, suka jiyo muryar mama akusa da qofar Dakin tace"Aisha taso mutafi zamu rufe qofa, lokacin bacci yayi"😂😳

Cikin sauri ta matsa daga kusa dashi tareda zare hannunta daga cikin nashi hannun, Shima murmushi yayi ya shafa sumar Kansa, yasan mama saboda shi takeso Aisha tatafi, kafin tafuto daga d'akin suka jiyo muryar Hajja tana cewa mama"harsun gama zancen ne? Dakin rabu dasu tunda yau din basu samu waje sun zanta ba"

Cikin sauri mama Tace"A a,bakisan Shahaab bane, saurin bacci gareshi, yanzu haka idan agida ne datuni yayi bacci"🙊

Tasake daga murya tace"Aisha!"

Cikin sauri Aisha dasukai shiru sunajin surutun mama da Hajja tatashi tsaye zata fice, ahankali Shima yamiqe tsaye yabiyo bayanta, zata bude labulan Dakin kenan yayi saurin fuzgota tafada jikinsa, wata irin wawuyar runguma yayi mata tareda d'ora Kansa akan kafadar ta, kamar jaririn da uwarsa ta dade bata bashi nono ba, haka yake sakin ajiyar zuciya, yanda yake jin tudun dukiyar fulaninta akan qirjinsa, hakan ne yasa yasake matseta sosai ajikinsa yanda zaifi jin abun sosai a qirjinsa, shiru tayi ko kadan batayi gigin hanashi ba, Idonsa a Lumshe, yad'ora bakinsa akan kunanta,cikin rad'a yace"ina sonki,kici gaba da sonah please"

Daga masa Kai tayi alamun to, saide itama kanta tarasa meyasa taqi raba jikinta da nashi,yanda tayi luf akan faffadan qirjinsa jitayi kamar su dauwama Ahaka, Adede lokacin Kuma Hajja tace"kode basa cikin Dakin ne? Naji shiru...."(😂)

Sai Alokacin taraba jikinta da nashi, tafice ahankali,mama tana ganin futowar ta tasaki ajiyar zuciya, tasan halin danta, akan idonta ma Yaya aka kare da wannan shegen kallon nasa dayake yiwa yarinyar, har Mahmud din za'a cewa a barshi da Aisha su zanta?🤔
Kuma acikin daki su biyu?🤔

Hannun Aishan takama suka wuce Dakin Hajja,yanda taji qamshin turaren yarinyar ya sauya akan Wanda tafita dashi, shine ya tabbatar mata da cewa Mahmud ba ido yazuba mata ba, Amma taji dadi tunda taga Hajja bata fahimci komai ba, Gara ayi magana guda daya gobe Dasafe, abawa Mahmud yarinyar Nan tun kafin azo ayi abun kunya.

Suna zuwa daki Aisha tahaye gadon Hajja ta kwanta tareda Lumshe idonta, sukan sabuwar hira suka dasa, yanayin yanda ya rungume tane yafado mata Arai,tasake tuna yanda ya furta mata cewa yana sonta ,wani irin yanayi take jinta aciki, cikin zuciyar ta tace"nima Ina sonka..."

Tun tana tunanin sa, har batasan bacci ya dauketa ba, Sai cikin dare ta farka taji su mama sunata zance itada Hajja, mamaki ya kamata, lalle an dade ba'a hadu ba, ita Kam juyi tasake yi taci gaba da baccinta.
Chapter 46 · 0% Book details