← Book details Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 71

Sashe 37

Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin sauri ta d'ago ta Kalle shi, jijjiga Kansa yayi yace"yes.... Saboda wani dalilin su Wanda nikaina banga amfanin saba, Sai Bayan nahadu dake ne Naga amfanin hakan tunda gashi nagane kina sona da gaskiya, ba kudina kikeso ba, bakisan waye niba Ina dashi banida shi Amma ahakan kika saurareni, maaamah...Ramadan koda yaushe bashida burin yaga naqara aure, mama kuwa tayi maganar tayi maganar harta gaji,kiduba shekaru na maaamah har yanzu banda yaro ko daya, mama kullum burinta shine taga naqara aure ko Allah zaisa na haihu, Amma naqi yarda saboda inason matata munirat banason nayi abinda zaisa hankalin ta yatashi har tayi tunanin nadena sonta, naje Asbiti andubani, doctor's dayawa sun tabbatar min qwayoyin halittana lafiya suke, zan iya haihuwa a kowanne lokaci, Amma munirat bataje ba, koda yaushe tana fadamin haihuwa ta Allah ce,yafimu sanin halin damuke ciki, Kuma ita gidansu sunada gadon haihuwa tunda ba'ita kadai mamarta tahaifa ba, muma idan mukai haquri Allah zai bamu watarana, tafi tunanin rashin lafiyar daga nine, hakanne yasa na shirya har qasar waje naje akan hakan suma sun tabbatar min lafiya ta kalau, hakan Dana fadawa mama da Ramadan shine yabasu damar da suka sake damuna akan maganar aure.

Bayan haduwa ta dake, ban 6oyewa Ramadan komai ba, saboda a ranar ma dashi muka fara zuwa garinku, har fadan mu saida nafada masa, daga lokacin da nabar garinku ban sake tunanin komawa ba, saida tunanin ki yamin yawa sannan, tunda Ramadan ya lura da tunanin danake nakuma fada masa komai daga Nan yafara cusa min ra'ayin ki araina daga qarshe harna gane Ina sonki, kullum Ramadan fadamin yake karna kuskura nafada miki koni waye, yakamata ace nagama sanin halin ki, shin zamuyi abota dake ta Amana kokuwa? Banta6a tunanin akwai soyaiyar gaskiya a duniya ba Sai ranar dakika Bani kyauta kika fadamin kudin karatun qaninki ne da kike Tarawa kika siyomin agogo dashi, kin sake shiga raina a ranar, kin birgeni yanda bakya zato, na fadawa Ramadan komai, shine yasake Bani qwarin gwiwar dazan tunkareki da maganar soyaiya, inba hakaba to shi zaizo har gidanku yace yana sonki, hakan ne yasa nafada miki Ina sonki, Sai Bayan kin amince da soyaiya ta shine Zaki gujeni?"

Sauran Hawayen idonta ta share, sannan tace"kaine kaje super market akano koba kai hane? "

Ahankali yace"nine, kuma tun a ranar nayi DANA SANI akan rufe miki koni waye danayi, inda kinsan cewa nine Mahmud Wakili da tuni na bayyana a gabanki na tambayeki waye wannan Yaron dayake tare dake?"

Cikin shagwa6a ta turo bakinta gaba tace"niba saurayi na bane, saurayin fati ne"

Cikin kishi yace"koma waye maamah banason kisake sauraren kowanne namiji, Rasa control din kaina nake, Bana son sake ganinki da kowanne namiji this is the first and last kinji ko?"

Cikeda yarinta tace"um"

Wayarsa yadauko dake gefe, yayi Dialing wata number, yasaka ta a hands-free, ringing hudu aka amsa cikeda nutsuwa, kallansa tayi tarasa bakin magana, ahankali ya jijjiga mata Kai yace"your brother..."
tareda bata wayar.

Cikin mamaki ta kar6i wayar tace"jabir...."
Saita Fashe da Kuka

Shahaab ya Girgiza Kansa, cikin ransa yace"Yarinyar Nan batada damuwa, abu kadan kuka na farinciki Dana baqinciki"

Daga d'ayan bangaren cikin wani irin farinciki jabir yace"takwarar Hajja,Wai kece?"

Cikin sauri Kuma tasaki dariya tace"Dalla nice"

Cikin mamaki tace"amma Yaya akai Naga kin kirani da number Yaya Mahmud?"

Cikin sauri tace"yaya akai kasan shi?"

Yace"muna waya dashi sosai, amma ban fada masa yayata tana aiki a gidansa ba, yacemin ogansa ne yad'auki nauyin karatu na"

Hararar wayar tayi, sannan ta juya ta harari Shahaab, cikin sauri tace"bawani ogansa, shine, Kuma idan nakoma gida ma saina fadawa Abba da Hajja da Umm...."

Kafin taqarasa maganar Shahaab yayi sauri zai qwace wayar, itama tafara kokarin hanashi,basusan sun kashe wayar ba Garin kokawa kowa yanaso ya kar6i wayar, saida ya Kar6a sannan yace"miye haka? Meyasa Zaki fada masa?"

Hawaye ne yasilalo daga idonta, cikin kuka tace"to meyasa Shima zaka masa irin nawa?"

Wayar yasakar mata, sannan yariqe fuskarta da hannu biyu yace"sokike nafada masa nine na dauki nauyin karatun sa? Menene abun birgewa to? Nayi ne Dan Allah,sannan Kuma danke, dakika dauke kudinsa da kike Tarawa zai tafi makaranta kika min kyauta dashi, to gashinan nahutar dake, Saudia Kuma Dama ai kece Zaki kaimu ko...?"
Yaqarasa maganar cikin sigar tsokana, cikin farinciki takai masa Dukan wasa a hannunsa, sakinta yayi yana murmushi, sannan yadauko abincin sa ya ajiye akan cinyarta yace"dazu kinbawa mama, nikuma kika hanani, yanzu saiki Bani Nima"

Cikin sauri tace"kaje Kaci afalo, kaga yanzu goma da kwata, dare yayi, baka tsoron matarka tasan kana zuwa dakina?"

Fuskarsa yadan daure yace"kinaso na kwana da yunwa?"

Cikin sauri ta Girgiza masa Kai, yace"to bani"

Kallan abincin tayi tace"to ai babu spoon"

Cikin shagwa6a yace"da hannu"
Cikin ranta tace"nashiga uku"

Afili kuwa saita Girgiza masa Kai tace"um um ni bazan iyabb....."

Kafin ta qarasa maganar cikin sigar rad'a yace"please"

Badon tasoba tasaka hannunta tafara bashi abincin, duk lokacin dazata saka masa a bakinsa saiya Lumshe Idonsa sannan zai fara ci, mamaki ne ya kamata ganin yanda yakecin abinci kamar bayaso, har qaguwa tayi yagama saboda ita Bahaka mama take cin Nata ba, wanne irin cin abinci ne wannan saikace mace.

Saida yaci yaqoshi, sannan yariqe tsintsiyar hannunta, yafara tsotsar Yan yatsun data bashi abincin, Idonsa a Lumshe suke yana tsotsar yatsun kamar wanda yake shan sweet, kallansa tayi tanajin gabanta yana faduwa, wani irin yanayi yana shiga jikinta, ahankali tazame hannunta daga bakinsa, babu musu yasaki, cikin wata irin murya yace"Albishirin ki"

Cikin sauri tace"goro"

"to menene Goron albashir dina?"

Fari tayi da idonta tace"duk abinda kake so"

Yace"kinyi alqawari?"

Tace"inde baifi qarfi naba"

Briefcase dinsa yabude, yad'auko wasu takardu yad'ora mata akan cinyarta yace"kyauta ce daga masoyi zuwa masoyiyarsa, kyautar amsa tayin soyaiya ta dakikai, fatana ki kasance tare dake da dadi ba dadi,da kudi ba kudi,kici gaba da sona fiyeda kowa a duniyar Nan Bayan iyayenki, kibani kulawa fiyeda wadda Zaki Bawa 'ya'yanki,kijani ajikinki, muyi rayuwa tare har abada, kyautar sabon company n Dana bude yau ne"
Yad'ora hannunsa akan takardun tareda bude wani shafi, can qasan page din ya nuna mata yace"kinga sign dinki daga yau, a ko'ina haka Zaki dinga yi,Ash-hab sunan yamiki dadi ko?"

Yaqarasa maganar tareda Dagowa yana kallon ta, tunda yafara maganar Aisha take kallon sa, wanne irin mutum ne Shahaab? Dama haka halaiyarsa take? Duk wannan abun dayake saboda kawai tana sonsa ne? Yakai mahaifin ta umara, yakai qaninta karatu qasar waje, duk wannan abubuwan da wannan facaka da kudin dayake bashida d'a nashi na Kansa, tausayin sane ya kamata,itakam Dame zata sakawa wannan mutumin a rayuwa? batasan lokacin da hawaye ya wanke mata fuska ba, dama ita Aishan yake nufi? Ashe sunanta yasaka Bana matarsa ba, Bana mahaifiyar saba, wacce irin soyaiya ce wannan?

Cikin kuka tafara Girgiza masa Kai Tace"A a, ban cancanci haka daga gareka ba, matsayi na baikai Nan ba, abun yayi yawa, ka barshi Dan Allah"

Matsowa yayi jikinta, kamar wanda zai rungume ta, Cikin sigar rad'a yace "haba kekuwa,menene abun kuka Kuma? Kinaso kimin asarar Hawayen ki kooo?" yaqare maganar cikin wata irin murya me cikeda fitina,
Matsowa yasake, ahankali yad'ora hannayensa a fuskarta, yariqe fuskar, sannan ya matso da bakinsa dab da fuskarta yad'ora harshansa akan kumatunta, yafara lashe Hawayen datake zubar wa, jin abinda yake ne yasa tarufe idonta ruf..., ta nemi kukan datake tarasa, saida yaji tadena kuka, sannan yahade bakinsu waje daya,al'amarin daya saka duka zukatan masoyan cikin wani Hali na shauqi da begen juna, hakan yasa wannan Karon batasan lokacin data bashi hadin kaiba,Dan qaramin lips dinsa take Sha ahankali, hakan datayi ne yasake gigita Shahaab, cikin fitar wani irin numfashi da tsantsar soyaiya, yake yimata wani irin kiss,gaba daya ya manta acikin dakinta yake, zuciyar sace take zigashi akan yata6a abubuwan Nan guda biyu masu dadin shafawa, wata zuciyar Kuma tana hanashi, daqyar ya'iya zare bakinsa, gudun kada ya aikata abun kunya acikin gidansa yasa cikin mutuwar jiki, yasakar mata kiss a goshinta, tareda miqewa ya fice daga d'akin cikin sauri.

Haka yakoma part dinsu Idonsa cikeda jaraba, yayi mamakin ganin munirat zaune afalo ta dora qafa daya Kan daya, yana sallama ko d'ago kanta batayi ba bare ta amsa, cikin mamaki ya qaraso wajan ta ya tsaya yace"munirat bakiji Ina sallama bane?"

Kamar da dutsi yake magana haka munirat tayi masa banza, ajiyar zuciya yayi, yarasa dalilin yin fishin ta, yace"meyafaru kike fishi?"

Nanma batace masa komai ba tayi shiru, Kansa ya Girgiza kawai yawuce dakinsa, idan ma akan rade radin dayake ji ne matarsa tana fishi saboda yabawa mama company ai yana ganin hakan ba zaisa tayi fishi ba, tunda shide bai futo fili yace budurwarsa yabawa ba, Yan kalamai yayi sannan Kuma yabayar da company, yanzu inda maman yabawa ma kenan haka zata yi fishi? Hakan na nufin idan mama yabawa munirat tana daga cikin Wanda zasuyi fishi akan yayiwa mahaifiyar sa kyauta, maimakon itama tayi kokari tasamu abinda yafi company awajansa, Girgiza Kansa yayi yashige toilet ya watsa ruwa,domin yanayin da yakeji ajikinsa Sai ahankali, Bayan yayi wanka yafuto ya shirya sannan ya kwanta tareda rungume fillo tsam a qirjinsa ya Lumshe Idonsa.

Bayan ya idar da sallar asuba yana dawowa part dinsu yakoma ya kwanta, Bai dade da kwanciya ba akayi masa Kiran gaggawa daga kamfanin su dake lagos, cikin sauri ya shirya ko sallama baiyi da munirat ba yafita yayi part din mama, itama yaga bata tashi ba Sai ma'aikata dasuke aiki a falon, Bai kula gaisuwar dasuke masa ba yajuya cikin sauri yafita, Kai tsaye Airport yawuce daga Nan yawuce lagos.

Meeting suke akan wani tallafi dayake son yiwa mata Wadanda basuda sana'ah.

Saida meeting yayi Nisa aka tambayeshi takardun dasuka fara tsara komai aciki a last Zaman da sukai yadafe Kansa sannan yace"wallahi na manta, Bari nakira Sai abayar akawo"

Munirat yakira, Amma yayi mata missed call kusan hudu bata dauka ba, tunawa yayi tana fishi dashi, saiya Girgiza Kansa kawai yakira wayar mama, mama tana dauka yace"mama barka da safiya"

"barka Mahmud, nafuto yin break Yara suke fadamin kazo"

"eh mama nazo, Ina sauri ne anyi min Kiran gaggawa daga office dinmu na lagos, gashi Ina sauri ma namanta da wasu takardu agida"

"to yanzu Yaya za'ayi? Katuro Ramadan ya dauka"
Chapter 37 · 0% Book details