Sashe 39
Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kallo ta maida Hankalinta Kai, har suka gama meeting dinsu,baqin suka fita, Shima ya tattara kayansa yace mata"muje ko "
Cikin sauri ta dauki Jakarta tayi gaba, takusa zuwa kofar yasa hannu ya fuzgota, batayi wata wataba tafada cikin faffan qirjinsa, Bai tsaya jiran komai ba yasaka hannunsa ta baya ya rungume ta tsam a qirjinsa, wata irin ajiyar zuciya yake saki kamar Yaron daya dade baisha nonon uwarsa ba, tsawon minti biyu suna haka, ahankali yasakar mata kiss agoshi, sannan yace"good morning"
Murmushi tasaki, bata amsa masaba ta qwace jikinta daga nasa ta nufi kofar, babu musu Shima yabita, Dan Sandan dake waje a tsaye, shi yabawa key din sannan suka tafi shida ita, suna shirin shiga mota driver ya qaraso, cikin kulawa Shahaab yace"malam Hassan babu damuwa ka zauna, zankaita Airport ne"
Cikin girmamawa yace"to yalla6ai a dawo lafiya"
Tunda suka fara tafiya babu Wanda yayi magana, hannu yasa ya kunna karatun alqur'ani suna saurara har suka qaraso wani super Market, kallon ta yayi, yace"muga jakar taki"
Cikin alamun tambaya tabashi jakar, budewa yayi babu komai cikin jakar kamar yanda ya tsammata,hannu yasa a aljihunsa sannan yasaka rafar kudi Yan nera hamsin hamsin kimanin dubu hamsin, sannan yace"kiyi amfani dashi idan kin koma gida"
Mamaki yakama Aisha, kafin tayi magana yafice daga motar tareda shigewa cikin super market din, kayan kwalliya yad'auko mata,da ice-cream dakuma turaruka, sannan yadawo cikin motar yad'ora mata akan cinyarta yace "kiyi hakuri bazan iya kaiki wajan cin abinci ba, saboda yanayin shigar ki, zan iya fada daduk Wanda ya kalleki, haka Kuma ban'isa in Hana a kalleki ba, sannan ko agida ne kidinga saka hijab banaso ko a falon mama nadinga ganinki babu hijab saboda kowanne lokaci mama cikin baqi take maza da mata"
Cikin ladabi tace"insha Allah, Amma wannan kudin yamin yawa, ka ajiyemin awajanka to, idan zan kashe saina dinga karba"
Murmushi yayi baice mata komai ba Kuma bai Kar6a ba, yaja motar suka tafi Airport din, Allah ya temaketa akwai jirgin dazai sake tashi nanda minti arba'in, danhaka yayi parking a cikin airport din suka zauna amota, kasancewar glass din motar tinted ne babu Wanda ma yake lura da motar, ajiyar zuciya yasauke yace"akwai ice-cream aciki ki dauka Kisha kafin kuwuce"
Wani irin farinciki ne ya kamata har yana mamaki, cikin sauri ta bude ledar tadauko babbar robar ice-cream din tadebo a spoon takai masa bakinsa tace"haa"
Murmushi yayi yabude bakin babu musu, cikin ransa yana farinciki kasancewar karatun dayake dora mata yana shiga cikin kanta tun kafin tashigo cikin hannunsa, saida tabashi yasha sannan itama Tasha, saida Tasha ta qoshi ta d'ago ta kalle shi tace "nagode sosai, Allah yasaka da alkhairi"
Cikin sauri yace"wait.... Meyasa ne bakya son Kiran sunana?"
Kallan sa tayi tace"sunan Abbana gareka, bazan iya fadar sunan ba"
Murmushi yayi yace"kamar yanda kike da sunan mama nah,kinga shikkenan nahuta saiki za6amin suna Mai dadi Wanda ya dace Dani"
Murmushi tayi cikin kunya tarufe fuskarta, kallon ta yasake yi cikeda nishadi yace"meyasa baki saka zobe ko agogo a hannunkiba Amma Kuma gashi kin siya kinyi kyauta dashi?"
Ta6e baki tayi tace"babu komai"
Batare da damuwa ba yabude wani waje cikin motar yadauko wani agogo Dan qarami na mata Mai kyau, daga Bayan agogon yaduba yasake gyara na'urar datake jikin agogon, sannan yakama hannunta ya daura mata agogon, cikin jin dadi tace"nagode"
Cikin rashin damuwa yace"ban yarda ba, banason godiar ki, idan kinji dadin kyautar Dana miki yakamata ki nuna min nagani"
Tace"tayaya?"
Kafada yadaga yace"lokacin dakika Bani kyautar naki agogon menayi?"
Idonsa ta sunkuyar qasa sannan tace"kiss"
Murmushi yayi sannan yace "uhm bissimillah"
Babu musu ta dora Dan qaramin bakinta akan agogon tayi kissing dinsa, cikin wani irin kallon soyaiya yace"bahaka zakiyi ba"
yamiqa hannu yakamo hannunta me agogon yad'ora bakinsa yasakar wa agogon wani irin kiss Mai tsayawa Arai, sannan ya maida bakinsa kan Bayan tafin hannunta yafara tsotsar sa ahankali, gabanta ne yafadi, tarasa wanne irin d'a mama ta Haifa, ko kadan baya gajiya da kiss, tanajin sa yanda yake tsotsar Bayan hannun Nata ahankali, salon yanda yake Sha ne yasa taji yanayin ta yana sauya wa, cikin sauri ta qwace hannunta, cikin qanqan da ido yace"why?"
Dan qaramin bakinta ta turo gaba tace"ni.... Nifa wani iri nakeji"
Murmushi yayi yace"Nima haka nakeji, gashi Nima kimin"
Yafadi hakan tareda miqo mata hannunsa
Cikin shagwa6a tace"nide a a, haka kawai daga kawo takardu Kuma mama ta gane abinda nayi, nide tsoro nakeji"
Kansa ya maida kan kujerar dayake zaune yace"Aisha"
Yakirata da wata irin murya cikin rad'a.
Kallonsa tayi tace"na'am"
"inason ki sosai, please karki rabu Dani Dan Allah, kiyi tunani kisa min lokaci inaso inje Inga Abbanki"
Jikinta ne yayi Sanyi, ahankali ta daga masa Kai, tace"insha Allah zanyi tunanin, Kuma zanci gaba da sonka har qarshen rayuwata"
cikin jin dadi yace"kinyi alqawari?"
Cikin sauri tace"eh"
Agogon hannunsa ya kalla yace"nagode, muje na rakaki, lokacin tashin ku yayi"
Mutara zuwa gobe insha Allah 🙏🏻
SHAHAAB, littafin kudi ne, idan kika karanta batareda Kin biyani haqqi naba, to ban yafe ba, nabarki keda mahaliccinki
Nera 300 kacal, zaki turo ta account dina kokuma katin MTN ta wannan number
0164549488
Amina muhammad
GTbank
Number 08033300034
Mrs Usman ce✍🏻
Bata sake tabbatar da cewa Mahmud Wakili Babban mutum bane saida yariqo hannunta suka qarasa cikin Airport din,mutanan dasuke bashi girma awajan kadai ya'isa ya tabbatar Maka da cewa shi din Mai fada aji ne acikin qasar, yanda yake riqeda hannun Nata hakanne zaisa kagane cewa kode budurwarsa ce, kokuma masoyiyar 'yarsa da yakeji da'ita, mayafin kanta ne yadan zame kadan, gashin gaban goshin ta yadan futo, Dakatawa yayi da tafiya ya fuskanceta ya tsaya ya danja mata mayafin abayar har kan goshinta, yanda gashin zai rufu, sannan sukaci gaba da tafiya, Hauwi dake Gefe itada ikee suka saki wani irin murmushin kissa, cikin sauri batareda Shahaab yasani ba, suka dauki photonsa shida Aisha,ko minti biyar baiyi ba ma'aikatan wajan suka qwace Aisha daga hannunsa acewarsu tunda suna Nan ai babu amfanin zuwan sa wajan da Kansa,😚
hannu ya basu sukai musabaha daga Nan yajuya cikin sauri da wannan takun nasa na jarumai Kuma jajurtattun mazaje.
Wani ke6an tattacen waje aka kaita, tana zaune tana tunani kode takira Hajja da wayar mama su gaisa dasu Ummah kafin tabawa mama wayarta?
Wata zuciyar tace meyakaiki? Kina yar aiki meyasa bazaki karbi wayar masu aiki yan'uwanki ba? Saita sake tunanin cewa tana gama wayar Kuma ai zata goge number, cikin sauri tad'auki shawarar zuciyar ta, ta danna number Hajja aikuwa waya tashiga, saide harta katse, Hajja bata dauka ba, tsaki tasaki, tana kewar Yan gidansu sosai, tunda tazo saudaya sukai waya, jitake kamar tayi tsuntsu taganta acikin gidansu.
Sake Kiran tayi, Shima harta gama ba'a dauka ba, wasa wasa har saida takira Hajja sau hudu, bata dauka ba, daga qarshe Sai hakura tayi tadena Kiran, tayi saurin goge number Hajja din, d'ago kanta tayi tana kallon ma'aikatan wajan yanda kowa yake abun gabansa, wani irin haske tagani kamar na camera anyi mata photo, tajujjuya taga bataga komai ba, saita daga kafadunta alamun shikkenan, Adede lokacin Kuma wani ma'aikacin yazo yace tatashi suje, jirginsu zai tashi.
Hauwi ta kalli ikee tace"kinga abinda muke fada ko? Wannan yarinyar ba itace munirat tace mana baquwar mama ceba?"
Ikee tace"ai gashinan tana zaune yarinya qarama zata qwace mata mijin, Dan Allah kiga yanda yawani riqo ta harda gyara mata mayafi saikace wata matarsa, waya San ma daga Ina suke? Idan kika bincika ma may be yarinyar tasaba zuwa suna sheqe ayarsu anan, inba hakaba Ina baquwa ina Hawa jirgi?"
Hauwi tace"nima tunanin danayi kenan, yariqe hannunta qam yaki saki ko kunyar mutane bayaji, ai daga Gani ma Dama can kinsan tasaba dashi, aini tundaga lokacin da munirat tacemin mahaifiyar sa tariqe yarinyar shikuma yana ta6a mata nono, nasan da walakin Goro amiya, ai uwarsa ce ta daure masa gindi"
Ikee tace"bakiga suma ma'aikatan wajan yanda jikinsu yake rawa ba? Suna wani bata girma saikace yar gwamna, basusan baquwa ce tazo cin Arziqi ba, kiduba kigafa ko kayan hannunta basu dubaba suka Barta tashige dashi"
Hauwi tasaki ajiyar zuciya tace"yanzu Yaya zamuyi da wannan pictures din? Muturawa munirat kawai, taga abinda mijinta yakeyi da baquwar datake cewa tasan mijinta baya kula mata Dan haka bazai kula wannan yarinyar ba"
Ikee tasaki dariya tace"bakida Hankali, tunda kikaga yana rawar jiki yana Bawa yarinyar Nan kulawa daga qarshe aure ta zaiyi mu muna zaune, uwarsa bazata hanashi ba tunda Dama so take yayi auren, ga shawara, mezai Hana muyi amfani da fuskokin su, mudora fuskar akan wani vedio din kawai sai mu turawa uwarsa da Kuma munirat din, suna Gani kinga mun tada fitina, daga qarshe mu ziga munirat yanda zata daga Hankalinta hartasa yasake ta, shikuma uwarsa ta hanashi mu'amula da wannan yarinyar, kinga daga qarshe mu saimuyi wuf dashi"
Dariya suka saka harda tafi, suna wannan dariyar sukaji sanarwar jirgin rivers zai tashi, cikin zumudi suka tashi, dama kowacce ta gaqu ta ganta awajan Nata Alhajin.
Suna sauka taga driver daya kawo ta yana jiranta, da alama Shahaab yafada musu sun taso ne,wajan sa ta nufa tashiga motar suka tafi gida, suna zuwa gida ta wuce part din mama, cikin murna mama ta kalleta tace"um um kaga yanmata, yau anhau jirgi Sai Fara'ah kike kamar gonar auduga"
Cikin murna ta zauna aqasan kujerar da mama take zaune tace"wallahi mama naji tsoro sosai,amma daga baya sainaga abun ma babu wahala Kuma Nan da Nan Naga har munje"
Mama tace"to Alhamdulillah, ya hanya?, nasan halinsa,inji de baiyi miki fada ba?"