← Book details Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 71

Sashe 47

Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A 6angaren Shahaab kuwa daqyar yasamu ya runtsa, Sai juyi yake yana murqususu shi kadai, yadade rabonsa da mace, yana fuskantar matsala ta kowacce jijiya ta jikinsa, yasan duk lokacin daya kama munirat a hannu, bazai mata da sauqi ba, saboda an dade ba'a hadu ba.(🙈)
Haka ya daure, yaci gaba da yakice tunanin Aishan daga ransa, Bai yarda tunanin Nata yajanyo masa wanka ba, saboda agidan surukai da kunya katashi da asuba aji kana wanka.😎

Su mama kuwa saida sukai sallar asuba sannan suka kwanta, Alokacin Kuma Aisha bata koma bacci ba, azkar takeyi har gari yayi haske,kowa yana bacci duk basu tashi ba,tafuto tad'auki tsintsinya tafara share gidan, yana jin qaran shara yafarka, wayarsa yaduba yaga bakwai da rabi na safe, tunda suka dawo daga masallaci da asuba shida Abba ya kwanta Sai bacci yasake daukansa saboda gajiya, wayar ya ajiye yatashi yayi miqa tareda salati, sannan ahankali yazo bakin kofar Dakin ya tsaya, yadan daga labulen kadan yaga waye yake shara, karyaje yafuto Kuma yaga Ummah.

Ahankali yadan leqa,saiya ga Aisha ce, ajiyar zuciya yasauke yanda ta sunkuya tana sharar hakanne yabashi damar hango tsayaiyun boobs dinta, wani irin abu yaji ya tsirga masa tundaga Kansa har qafafunsa,ya hadiye wani irin yawu,lokaci daya yanayin sa yafara sauya wa, hannunsa yatura cikin aljihun jallabiyar jikinsa, Gara sutafi daga gidannan, inba hakaba idan sukace zasu sake wasu kwanakin to yanada tabbacin wataran bazai iya Hana hannunsa ta6a wadannan abubuwan ba.(😲🙈 )

Domin yaci gaba da kallon su sosai, saiya daga labulen yafuto ya tsaya abakin kofar Dakin, yaharde hannunsa a qirjinsa yana kallon ta, yadade a tsaye yana kallon ta, sannan yayi gyaran murya, cikin sauri ta d'ago kanta ta kalleshi, hannunsa yatura cikin aljihun jallabiyar jikinsa sannan yatako ahankali zuwa kusa da'ita yace"ina kwana?"

Kanta ta sunkuyar qasa,Babban mutum kamar wannan shine yake gaishe ta, Sai taji kunya ta kamata tace"lafiya kalau, dafatan kana lafiya"

Yace"um Gani nan de"

Kallan sa tayi da sauri, kafin tayi magana ya matso kusa da'ita, dan kwalin kanta ya janye qasa, lokaci daya dogon gashinta yafuto fili, cikin sauri tajujjuya ta kalli dakunan gidan, kar wani yafuto ya gansu, tana juyawa tana Kallan dakinsu Ummah hakanne yasa ta turo masa qeyarta, cikin sauri yasaka hannu yacire ribbon din kanta, dogon gashinta yabazu akan fuskarta, kallon sa tayi da sauri, kafin tayi magana yace"kinfi kyau ahaka"

Idonta ta furfuto dashi waje, tsoro takeji kar wani yafuto ya gansu Ahaka, cikin takunsa me aji yaqaraso wajan ta, yad'ora hannunsa akanta, yafara wasa da gashin kamar zaiyi mata kalba dashi, cikin jin dadi yace"kawo tsintsiyar na tayaki sharar...."jin takun mutum ne yasa ya tsaya cak!
Shibe cigaba da wasa da gashin ba, shibe saki gashin ba, gyaran murya Abba yayi, cikin sauri suka juya, wata irin kunya ta kama Aisha, Shahaab kuwa cikin sauri yasaki gashin Nata tareda komawa Gefe yana Dan shafa sumar Kansa, Amma ko kadan yaqi kallon Idon Abba, Dan kwalinta ta maida kanta ta tsugunna Tace"Abba Ina kwana"

Ataqaice yace"lafiya"

Cikin sauri tashige daki, Shikuwa Shahaab Kansa yana qasa,yace"barka da futowa"

Abba yayi murmushi, a ransa yana mamakin yanda Shahaab baya iya 6oye soyaiyar dayake wa Aisha, yanzu inda tabashi tsintsinyar sharar zaiyi kenan?🤔
Kansa ya Girgiza tareda bashi hannu yace"yalla6ai ya gajiya?"

Shahaab bai bashi hannun ba, ganin yanda yake jin kunya yasa abban yakama hannunsa sukayi hanyar waje, yana fada masa akwai yan'uwan mahaifinsa, yakamata suje su gaisa dasu.

Aisha kuwa saida taji fitarsu sannan tafuto tana qarasa sharar, hararar inda suka tsaya itada Shahaab tayi, cikin ranta tace"bashida kunya, gashinan yaja Abba yaganmu"

Saida tagama sharar, sannan taje ta tambayi Ummah abinda za'a dora, Sai umman tafuto suka fara harhada abun Karin kummallon tare,har zuwa lokacin Hajja da mama,Sunata bacci, basu tashi ba.

Sai wajan karfe goma su mama suka tashi, basu zauna Zaman cin abinci ba Sai wajan shadaya na safe, Alokacin harsu Abba sun dawo shida Shahaab, yakaishi yaga dangi, yaga iyayensa, sun kuma yi maganar neman auren Aisha da Shahaab yakeyi, anan suka tabbatar masa zasuzo har gida Sai ayi maganar agaban Hajja, Bayan sun dawo gida wanka yayi, ya maida kayansa na jiya, Amma baisaka babbar rigar ba, ta cikin kawai yabari Sai hularsa daya dora, Sai hakan yaqara yimasa kyau yakoma tamkar saurayi, anan tsakar gida sukaci abinci shida Abba, Aisha tana cikin daki bata futo wajan su ba, Shahaab Kansa na qasa yana danna wayarsa,Mama ta kalli Hajja tace"to Aysha ai sai kuyi shiri mutafi ko?"

Cikin sauri Hajja tace"ina zamuje?"

Mama tace"Abuja mana, kina tunanin zan Barku kuci gaba da rayuwa anan ne?"

Hajja Tace"A a, banfada miki ba, dade Ina cewa duk lokacin Dana ganki to wajanki zan koma kodan in rabu da jarabar mesunanki ,Amma Kuma yanzu tunda akwai alaqa, akwai dalili, bazan biki ba, zan jinkirta idan aka daura auren takwarar ki, sainabi Yan kaiwa amarya mutaho tare, kude turo motoci masu yawa, Dan inada jama'ah, kinga jummai ma nasan itama zatayi gayya,tunda ta dalilin ta ne har Allah ya hadani dake koba haka ba"(😂)

Mama tayi dariya tace"to uwar gayya,har yanzu de kina Nan da jama'arki kamar baya,to aini banice meturo muku motoci ba, kin ganshi Nan, kifada masa"

Hajja ta juya ta kalli Shahaab tace"Kai Shahaabu, kanajina nida uwarka aiko?"

Murmushi yayi yace"Hajja hanya fa babu tsaro yanzu, za'a iya saceku acikin daji,kigama lissafin mutanan ki tsaf, saiki fadawa amaryar,duk yanda kukayi da'ita saita fadamin ta waya, inyaso saikubi jirgi, Amma kude bazaku dawo ba idan kunje, saboda haka kuyi sallama da kowa kafin kutafin"

Abba ya Girgiza Kansa yace"haba yalla6ai, a a baza'a yi hakaba, zamu dorama nauyi yalla6ai"

Batare daya hada ido da abban ba yace"Babu damuwa,koba Dan Aisha ba, dole zaku bimu kodan amintar mama da Hajja"

Ummah ce tafashe da Kuka tace"mungode Allah yasaka da alkhairi, Allah yaji qan mahaifin ka"

Gaba dayansu suka amsa da "Amin"

Hajja Tace"A a to tunda jirgi zamubi, bazanyi gayya ba, tun Ana abu na Hankali karkuma a koma na rashin Hankali, saboda haka duk Wanda yake min mutunci dashi za'ayi tafiyar Nan, lalla6a jummai zanyi inyi shiruuuu, tanamin abu komin qanqantar sa zan cireta daga list..."(😂😲)

Dariya suka saki gaba dayansu, mama tace"ni bakima kiramin ita mun gaisa ba"

Kafin Hajja tayi magana yan'uwan mijin Hajja suka shigo gidan susu uku, Hajja Tace"A a malam baqori kune a gidan? Sannunku da zuwa"

Ummah ce tasake shinfida musu wata tabarmar suka zauna, Bayan sunyi gaishe gaishe dakuma bayanin juna, anan aka tsaida lokacin biki sati uku masu zuwa, shi Shahaab asan ransa ma a saka sati biyu, saboda shi kadai yasan meyake ji, jiyake kamar ya hadiye Aishan kowama ya huta, Amma Hajja ta daddage tace saide a saka sati uku, kafin Nan sungama kintsawa.

Mama ce tad'auki kudin komai tabayar kamar yanda al'adar Garin take,daga Nan Kuma Shahaab yayiwa securities dinsa waya suzo su tafi, daga Nan shida Abba suka raka tsofaffin gida.

mama da Hajja suna zaune arumfa suna qulla Goro, Wanda za'a rabawa mutane, nasaka ranar Aisha,mama ta kalli Hajja tace"oh bakiga idon Shahaab ba da'aka saka sati ukun Nan, inajin da Kuka zai saki"

Hajja tayi dariya tace"naganshi,Dan qaniyarsa ai gata nake masa, a wannan lokacin nefa zan Dan samu Tasha magungunan Sanyi,muda muke neman haihuwa ai dole mu nemi maganin Sanyi, Shima idan kun koma akwai maganin dazan baki kitafi dashi saiki bashi yadinga Sha,idan akwai sanyin ma to zai rabu dashi insha Allah"

Mama yace"aikuwa zan bashi, zan dinga zaunar dashi Ina bashi yanasha,har komai ma bashi zanyi, ai ba ita kadai yakamata Tasha maganin matan ba, Shima saiya Sha irin Wanda yadace"

Haka suka dinga zancen su har mamakinsu Ummah takeyi, ko gajiya basayi da zance.
karfe biyu daidai sukayi shirin tafiya,Aisha tana daki tanaso ta ganshi Amma Kuma tana kunyar futowa, mama da Hajja sukayi gaba, Abba ya kalli Ummah yace"kira masa ita suyi sallama"

Daga Nan Shima yafice daga gidan, Ummah ta kalli Shahaab dayake tafiya kamar bayaso Dama Kuma Shima abinda yake ransa kenan, jira yake ko Yaya ne yadan kalleta kafin yatafi, Ummah tace"bari Akira ta"

Babu musu kuwa yaja ya tsaya, a gabansa tashiga d'akin Hajja sannan tafuto itama tafice daga gidan, yana tsaye tafuto daga daki tana Sanye cikin hijab, Kallan ta yayi yace"Maa-mah, banda yawo, banaso kina fita kowa yana kallon ki kinji ko?"

Daga masa Kai tayi sannan tace"insha Allah, Allah yakaiku lafiya"

Yace"Amin,saiki fara shirin tar6ata nanda sati uku, ni banso ma akasa lokacin har haka ba, kefa?"

Cikin kunya tace"jinake ma wata uku za'a saka"

Girgiza Kansa yayi, ya matso kusa da'ita yayi kissing goshinta yace"ki kulamin da kanki, banda kula maza, Sai munyi waya"

Tace"to insha Allah"

Daga Nan yafuto daga gidan cikin sauri, saida yagama sallama da mutanan dasuka zazzo Yan Garin yayi musu ihsani , sannan yashiga motar suka tafi, har lokacin Hajja da mama labari suke, saida mota taja, sannan suka juyo cikin gida, tundaga Nan Kuma mutane suke zuwa gidan Ana yiwa Hajja Allah yasanya alkhairi, jikar ta takusa aure.

(littafin kudi ne, idan kika karanta min baki biyaba nabarki da Allah)

******

Wannan Karon kawai Airport suka wuce sukabi jirgi shida mama, suna sauka a Abuja Kai tsaye gida suka wuce shida mama, munirat tana part dinta batasan sun dawo ba, zama yayi akan kujera cikeda gajiya, mama ta wuce wajan ma'aikatan gidan tana sanar dasu auren me gidansu nanda sati uku, yana zaune Idonsa a Lumshe aka masa waya, daukar wayar yayi tareda sallama"ranka yadade mungama tracking din number Nan daka turo mana,angama bincike akan number, yanzu haka yarinyar tana hannun mu, Amma tafada mana ba'ita kadai bace, itada qawarta ne, zamu turo Maka pictures dinsu da sauran information din damuka dauka awajansu ta Email dinka, sauran bayanin Kuma sai abinda kace"

Cikin sauri yace"babu damuwa,Sai munyi waya"

Kai tsaye Email din yaduba

Yana ganin fuskar su yarasa Ina yasan su, mama data dawo falon tayi magana taji shiru, tasake yimasa magana taji shiru, mamaki ya kamata, yazuba wa waya ido yana kallo kome yake kallo? Hannu tasa ta ta6oshi, cikin sauri ya kalleta, tace"tunanin me kakeyi haka?"
Chapter 47 · 0% Book details