Sashe 27
Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hajja ta kalli Aisha datayi tsumu-tsumi tana zare ido tace"mesunan qawa a'ina kika siyo Biron?"
Cikin faduwar gaba tace "Hajja ni Bani akayi, Kuma Wanda yabani bashida kudin da Walida take fada bare harya'iya siyoshi"
Abba daya zubawa Walida ido yana kallon ta yace"tashi kije gida Walida, qawar Taki zatazo ta sameki"
Babu musu Walida tatashi tana cewa Aisha "to wallahi ki binciki Wanda yabaki karkije na sata ne, idan kinzo saimu qarasa rubutun"
Daga Nan tasakai tafice daga gidan
Abba ya kalli Aisha fuska babu Fara'ah yace "bani Biron"
Babu musu ta dauki biro tabashi, Kai tsaye yatafi gidan Alhaji Ali domin jin gaskiyar magana,ko kadan bai yarda da maganar da Aisha tafada akan Biron ba, Ummah datake tsoron yiwa Aisha fada Hajja Tahau kanta da masifa tace "Allah yarufa asiri"
Aikuwa cikin sauri Hajja tace "Amin, aiya dade da rufawa"
Cikin sauri Aisha tatashi ta shige dakin Hajja, gaba daya fuskarta ta sauya tunani take da kokonto akan maganar da Walida tafada mata, Ina Shahaab zai samu kudi har nera dubu Dari biyar?
Lokaci daya ranar da sukaje mall itada fati yafado mata Arai, da fad'an da masu mall din suke mata, Kuma lokaci daya suka dawo suna bata hakuri saboda wani body guard datagani da baqin glass yazo yayi magana dasu, ta tuna lokacin dasuke cewa Babban customer dinsu ne yazo Kuma bayason hayaniya.
Fadawa tayi kan gado tana Girgiza kanta, tasake tuna lokacin datake cikin adedeta ance mata Mahmud Wakili yazo shi aka sauka acikin gidajen data Gani,gabanta ne yake faduwa, meyake shirin faruwa ne?To Amma Kuma ai yace mata shi Yaron Mahmud Wakili ne bare tayi tunanin ko qarya yake mata, tasan cewa Shahaab bazai ta6a yimata qarya ba, Shahaab bazai fada mata abinda bashine ba, yanada Hankali, Kuma yanada nutsuwa, sannan babba ne yanada shekaru, bazai yi mata qarya ba, lokaci daya kanta ya d'aure, tarasa waye zai bata amsa, wayar Hajja ta d'auka cikin sauri har hannayenta na karkarwa tafara Kiran layinsa, saide Kuma wayar tasa akashe(🤦🏻♀️)
Tana daga d'akin tajiyo Abba ya dawo, kujera yar tsugunno yaja ya zauna agaban Hajja dasu Ummah, sannan yace "naje na kaiwa Alhaji Ali Biron, yace zai Kai a siyar dashi,zan jira shi inji Yaya ake ciki"
Hajja tace "nifa mamuda itama Walidan data fadi maganar kallon mahaukaciya nake mata, tsakani da Allah tayaya me sunan qawa zata samo wani biro har dubu Dari biyar?to kaima tun kafin infara yima kallon mahaukaci kawai kayi shiru"
Abba yace "Hajja kenan,bakisan abinda yarinyar Nan take qullawa bane"
Jin abinda Abba yace yasa gaban Aisha faduwa, kode Abba yasan tana kula Shahaab?
Kafin Hajja tayi magana suka jiyo sallama daga kofar gida, jabir ne yatashi yafita, Sai gashi ya dawo yace "Abba Ana sallama dakai"
Kallan jabir yayi yace "nikuma? Suwaye?"
Jabir yace "wasu baqi ne, Amma Naga tare suke da Bulama"
Abba yace "baqi tareda Bulaman Gari? to Bari naje,"
Yafadi hakan tareda nufar kofar gida.
Yana zuwa yaga baqi su hudu, tareda bulaman Garin,hannu ya basu suka gaisa, daya daga cikin baqin ya kalleshi yace "kaine mamuda?"
Abba yace "eh nine,meyake faruwa?"
Yace "karka damu babu komai, munzo ne daga National Hajj commission,ma'aikatar aikin Hajji, muna farincikin sanar dakai sunanka yafuto acikin jerin Wanda zasuje Umara cikin wannan satin, sannan danka yasamu gurbin karatu a qasar Australia, zamu wuce daku dutse domin yimuku international passport"
Abba yayi shiruu kamar baiji abinda suka fada daidai ba, cikin tsananin mamaki yace"ranka yadade Saudia de Dana Sani?Kai inaga de kuskuren adreshi kuka samu"
Daya daga cikinsu yace"Muma Umarni ne muka Kar6a daga sama,kashiga kasanar agida muje mucika umarnin da'aka bamu"
Cikin mutuwar jiki Abba yajuya cikin gida tunani fal ransa, dama mutum yana samun karatu ne batareda yanema ba?jabir din dasuke fafutuka yasamu ko legal Ringim ne yatafi yayi diploma shine yanzu yasamu gurbin karatu a qasar waje? Tayaya? Yanzu a wannan zamanin har akwai mutumin dazai biyama Saudia ne batare da yasankaba? Kuma sunce umarni aka basu daga sama, hakan na nufin koma wanene yasaka su to wani Babban ne a qasar, Kuma yayi bincike sosai akansa tunda gashi har yasan yanada d'a namiji
Yana qarasawa cikin gidan yafadawa Ummah da Hajja abinda yake faruwa, Hajja tace "to mamuda, dayake Saudia de Kiran Allah ne bazan hanaka zuwa ba, Amma abun da mamaki ace an dauki nauyin karatun jabir, kaikuma anbi Yama Umara, to waye ne wannan?"
Ummah tace "Hajja koma wanene ba qaramin masoyinmu bane, wataqila lokacin da zamuji dadi ne yazo, Allah yasaka masa da alkhairi, yasa ladan abunda yayi yadinga binsa har qabarinsa"
Abba ya jijjiga Kai yace "hakane, Amin ya Allah"
Cikin sauri Aisha tafuto daga daki tace "Abba Allah yasanya alkhairi"
Baice da'ita uffan ba, Sai kallon jabir da yayi yace "Kai taso muje"
Cikin sauri jabir yatashi suka fita, Kai tsaye dutse sukaje kamar yanda mutanan suka fada, anyi musu passport duka su biyun,Wanda sukaje gida suka Dauko su sune suka kar6i passport din, sannan suka dubi Abba, daya daga cikinsu yace "Zaku iya komawa gida, yanzu zamu Kai passport din Abuja, za'a yi muku visa"
Abba de da yaga abun nasu da gaske ne, saiya tsugunna yafara yimusu godia, cikin sauri suka tarbeshi yatashi tsaye, sannan sukace babu komai, Abba har hawaye yake yana qara yimusu godia, daqyar suka samu yayi shiru, sannan sukai sallama dasu
Basu koma gida ba Sai dare, agida ma magana daya aketa maimaita wa, mata Sai sallama suke yi a gidan anayiwa Hajja Allah yasanya alkhairi mamuda zai tafi Umara, Abba yarasa Ina Yan gari suka samu labari, Amma daya tuna da Bulama saiya Dena tunani akan hakan.
(Shahaab littafin kudi ne, ki biya naira 300 kacal ki karanta abinki, duk wadda ta karanta batare data biyani haqqina ba nabarta itada mahaliccinta,
0164549488
Amina muhammad
GTbank)
******
Cikin dare hadari yahadu sosai, Nan da Nan aka tsinke da ruwan sama, acikin wannan ruwa Aisha tatashi tafuto tayi alwala, kafin Takoma daki duk ta jiqe, Dakin Takoma ta kunna wayar Hajja ta shimfida sallaya, sannan ta kashe hasken wayar tacire kayan jikinta, ta dauki wani kayan tafara sakawa, cikin rashin Sani tad'an bigi breast dinta,cikin sauri ta runtse idonta saboda zafin dataji, tarasa meyasa wani lokacin suke mata ciwo, sannan Kuma kullum cikin qaruwa suke, hijabi tasaka sannan tatada sallah, Bayan ta idar haka ta dinga addu'ah Allah ya dawo da Shahaab lafiya domin ya wanketa akan wannan biro, yazo yafada musu Bahaka bane, sannan tayi wa Allah godia akan abun farincikin daya samu Abban ta da jabir, tayi musu addu'oi sosai, sannan ta kwanta awajan tana istigfari, batasan lokacin da bacci ya dauketa ba, saiji tayi Hajja tana tashin ta sallar asuba.
Tunda suka tashi da safe ta gaida Abban ta taga ya amsa mata daqyar, jikinta yayi sanyi, haka Takoma Dakin Hajja ta kwanta batareda kowa ya lura da yanayin datake ciki ba, da yamma Alhaji Ali yazo gidan yayi sallama da Abba, Abba na fita suka gaisa da Alhaji Ali, anan Alhaji Alin yaqara tayashi murna saboda samun labarin Dayayi Abba yasamu kujerar umara, sannan yaqara da cewa "Mamuda ga wannan kudin, jiya nakira wayar ka akashe, dama inaso in fadama ne Wanda yake siyan Biron baya Nan, Sai yaransa nasamu, sukuma sunce bazasu siyeshi haka ba saboda babu kwalin Biron, danhaka zasu iya siya dubu Dari hudu da hamsin, ga kudin Naka"
Jikin Abba ne yafara rawa ganin wannan uban kudi, ,qafafunsa suka fara karkarwa yana neman faduwa, ahankali yasaka hannu ya kar6i kudin sannan yace "nagode Alhaji Ali, zanzo gidanka anjima"
Alhaji Ali yayi godia yajuya yatafi, Abba kuwa duhu duhu yake Gani daqyar yakai Kansa gida,yana zuwa ya zauna akan tabarmar da Hajja da Ummah dakuma jabir suke zaune, ya ajiye kudi agaban Hajja, tsorata sukai da yawan kudin, cikin 6arin jiki Hajja tace" mamuda Ina kasamu wannan uban kudin?"
Baice da'ita komai ba, ya kalli jabir yace"kiramin yayarka"
Jabir yaje Dakin Hajja yace "qawar Hajja kizo inji Abba"
Haka kawai taji faduwar gaba ta ziyarceta, cikin sanyin jiki tafuto ta zauna akusa da Hajja, ahankali tace "Abba Gani"
Abba yajuya ya kalli Hajja yace "to Hajja gatanan, wannan kudi da kike Gani kudin biro ne, saboda haka ta bude baki tafada mana waye yabata Biron? Saboda ni kwata kwata ban yarda da yarinyar Nan ba"
Yajuya yasake kallon Aisha da kanta yake qasa, idonta Yacika taf da hawaye, sannan yace "AISHA...., fadamin waye yabaki wannan Biron? Sannan Ina kike zuwa da daddare?"
Cikin sauri Hajja tace "bangane Aisha haka Kai tsaye ba mamuda, sunan qawar tawa kake kira haka? Ashe zaka iya kirana Kai tsaye Nima? To Bari kaji idan baka yarda da wannan yarinyar ba mamuda Nina yarda da'ita,tayaya za'ace biro qwaya daya jal nera dubu Dari hudu da hamsin? To shi Biron baya qarewa ne?"(🤔)
Abba yace"Hajja wannan biro haka kudinsa yake, kuma qarya take tasan inda taje ta Nemo shi, saboda ban yarda da ita ba, ta bude baki ta fadamin gaskiya kokuma yanzun Nan inyi mata dan'iskan duka wallahi"
Hawaye ne ya zubo daga idonta, ahankali tafara shashshekar kuka, cikin wata irin murya tace "Abba Dan Allah kayi hakuri"
Cikin 6acin rai Abba yace "ta tabbata kenan abinda malam Manu ya fadamin gaskiya ne ko? Irin tarbiyar Dana baki kenan ko?"
Hajja ta kalli Aisha tafara tafa hannu tana salati, tace "Nina Rasa abun damuwa anan mamuda, waime kake nufi da wannan maganar taka ne? Memakon kayi murna yarinya tafara samo mana kudi Amma Naga Kai tuhumar ta ma kake, ni idan hakane ai jummai rufata tayi, inusa ba mijin aure bane, duk Wanda yabawa mesunan qawa wannan biro ai shine mijin aure "(🙄😂🙆🏻♀️)
Ummah ta zubawa Aisha ido tana kallonta, Sarai tasan akwai abinda take 6oye musu, yanayin ta kawai zaka kalla kasan batada gaskiya,tsoronta daya kartaje wani marar tsoron Allah yayi amfani da rashin wayon 'yartata yana amfani da'ita awani waje, saboda babu Wanda zaiga qirar Aisha yaji bai kwadaitu akanta ba,share Hawayen idonta tayi,cikin muryar kuka Ummah tace"waye yabaki Biron? Sannan Ina kike fita da daddare?"
Cikin kuka tace" Ummah ni gidansu Walida nake zuwa"