← Book details Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 71

Sashe 32

Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mama tayi shiru tana kallon ta, tayaya zata bar yarinya tana mata aiki babu ko sisi Aida shiga haqqi, dole zasuje su bude Adinga saka mata kudinta, taga har yanzu yarinyar tana fishi da'ita, duk da bata futo fili tafada mata gaskiya ba, bazai iyu tafada mata dalilin dayasa ta 6ata mata rai rannan ba, abinda ya shafi tsakaninta da Aysha Sulaiman Bompai wannan tsakanin sune, Bai shafi masu aikinta ba, tana wannan tunanin taji Aisha tace "mama kihuta lafiya"

Daga Nan tatafi daki, saboda wani irin zazza6i datake ji tunda safe,ga qirjinta ciwo yake har cikin boobs dinta Wanda takejin wani irin abu aciki me zafi, haka bayanta ma yana mata ciwo kadan kadan

(Allah karabu da rashin sanin ciwon kudin mu 😖😖😖in samu kudi na daqyar insai abu, Kuma in zauna Ina fitar dashi saboda shirme, duk wadda tasan bata biyani haqqi naba nabar ta da Allah, bazan taba yafe mata ba)

******

Yau cinema akwai wasa, Ball za'a buga me zafi, tun rana Hajja tagama harhada komai na kunun Aya, da yamma ta zauna zata Fata d'urawa acikin jarkoki, Kallan uban kunun ayar dake gabanta tayi, ta juya ta kalli Abba dayake shirin fita qofar gida tace "mamuda ai bakaga ta fita ba, zuwa zakayi ka zauna ka duramin wannan kunun ayar, tunda ka sallami Wadda take min"

Abba baiyi musu ba yadawo ya tsugunna yafara d'ura mata kunun ayar, koda wasa ba zaiyi kuskuren yin maganar Aisha da'ita ba yanzu, saboda yanzu saita fara yimasa bori tace lalle lalle Sai yaje yadawo mata da'ita

Hajja tasaki tsaki tace "tunda Wanda nake Tarawa kudin registration din yatafi makarantar ai sai infara tattara kudina inje dakaina in dawo da Mai sunan qawa, bazai iyu duk lokacin dazanyi durin kunun Aya sainaje majalissa-majalissa Ina nemanka ba"😂😂

Ummah ta ajiye tsintsiyar hannunta tawanke hannayenta, sannan tazo ta zauna itama sukaci gaba da dura mata, saida suka gama tsaf... Suka saka mata shi cikin babbar kula sannan Abba yamiqe zai fita, Hajja tace"Ai baka gama ba, jeka nemomin me mashin"😂

Bai iya cewa komai ba Sai "to Hajja"

Sannan yafice daga gidan cikin sauri.

******

Kallon Yaron dake gabansa yayi, yau Yacika sati na uku kenan a qasar Amma yaro harya fara sauya wa, fatarsa tasake fresh Sai wani irin haske yake yi, jaridar dake hannunsa ya ajiye yace "jabir ka tsaya ka nutsu kayi karatu kaji? Kaga wannan karatun shine gatanka, idan kayi karatu iyayenka ma zasuji dadi su sakama Albarka, karka sa tunanin gida a ranka, kasa karatu agaba kayi abinda yakawo ka kakoma gida lafiya"

Cikin ladabi jabir yace "to Alhaji nagode sosai, Allah yasaka da alkhairi, abunda kayi mana Allah yabiyama da gidan aljanna"

Murmushi yayi yace "jabir aiba nine nadauki nauyin zuwanka qasar nan dakuma karatun kaba, oga nane, Shima yana tare damu acikin qasar saide ayyuka dasuka yi masa yawa yasa baisamu lokaci ya ganka ba, yanzu haka Nigeria zamu wuce, wannan wayar ma shine yace akawo ma, idan yasamu lokaci zai kira layinka "

Cikin mamaki jabir ya kalli mutumin da tsananin alhini, tunda suka fara hidimar tafiyar su shida Abba wannan mutumin yake Gani, yayi tunanin shine yad'auki nauyin karatun nasa, ashe bashi bane, to waye wannan?

Murmushi mutumin yayi kamar yasan abinda yake cikin zuciyar jabir yace "nasan kanaso kasan waye yakai Abban ka Saudia,sannan kaima yakawo ka qasar nan karatu, to zaka sanshi very soon, ya tabbatar min idan yasamu lokaci zai kiraka, idan ya kiraka saika yi masa kowanne irin tambayoyi"

Jabir yace "to shikkenan Alhaji nagode, Allah yakaiku lafiya, Allah yasadamu da alkhairi"

Mutumin ya amsa masa da "Amin" sannan sukai sallama yatafi gidan da'aka kama masa, shikuma mutumin yanufi Airport.

******

Nnamdi Azikiwe International Airport Abuja.

Tsaye yake yana jiran motoci su qaraso daga gida,kasancewar babu wanda yasan da zuwansa, saida ya sauka sannan ya kirasu, Sanye yake cikin Riga da wando, baqin wando, da Riga Ruwan toka me ratsin baqi, Sai glass din Idonsa baqi, dakuma agogo baqi,Wanda yasake haska farar fatarsa, Sai takalmin qafarsa kambos fari, gashin kannan nasa yasha gyara Sai sheqi yake,Bai 6alle botir din gaban rigar tasa duka ba, yabar guda uku a bude, hakan ne yasa ake iya hango lallausan gashin daya kwanta akan faffad'an qirjinsa, hannuwansa zube cikin aljihun wandon sa, Dan qaramin tsaki yasaki Bayan yasake kallon agogon hannunsa, yadubi Alhaji Ibrahim Wanda suka dawo tare yace"Alhaji zaka iya tafiya, gasunan sun qaraso"

Alhaji Ibrahim yabashi wani Kati tareda cewa"to oga, ga wannan katin, number wannan Yaron ne jabir"

Katin ya Kar6a, tareda turashi cikin aljihunsa yayi gaba batareda yasake cewa komai ba, wajan da aka Parker motocinsa ya qarasa, cikin sauri aka bude masa motar yashiga, sannan suka dauki hanyar gida, Kansa ya jinginar a jikin kujera yana jin yanda bugun zuciyarsa yake sauya wa Zuwa faduwar gaba matsananciya.

Bai dauki hakan a matsayin komai ba, tunda yasan mama tana lafiya, munirat ma haka, saide Aisha ce bai saniba, itama Kuma so yake ya qarasa gida yabude wayarsa datake kiransa da'ita Yakirata yaji muryarta ko zai samu ya'iya runtsa wa a Daren yau din.(😇)

Suna qarasa wa gidan Kai tsaye yawuce part din mama, tana zaune afalon ita kadai, abinci ne a gabanta tana kokarin hadawa, cikin jin dadi dakuma shagwa6ar daya saba ya rungume ta tabaya yace"mamaaaa.....I miss you"

Mama da batasan da zuwansa ba cikin farinciki da jin dadi tajuyo tace"mahmud?''

Murmushi yake saki kamar bashi ba dayake daure fuska kowanne lokaci, kwanciya yayi akan kujerar tareda dora Kansa akan cinyarta yace"mama nayi kewarki dayawa, nayi kewar cinyarki "

Dogon hancinsa taja, cikin farinciki tace"ai gashinan kadawo, Bari inzuba Maka abinci Dama yanzu nake shirin cin abincin Nima"

Cikin sauri yatashi zaune yana fuskantarta, cikin 6acin rai yace "mama bangane ba? Kece Zaki zuba abincin da kanki? Ina masu aikin suke?"

"masu aiki suna Nan Shahaab, sukam ai sungama aikinsu sabuwar yarinyar datake kula Dani wadda na dauka itace de batazo tabani ba,Kai ni rabona da'ita ma tun Daren jiya, kwata kwata yau bansata a'idona ba, fishi take Dani na babu gaira babu dalili, datage ala dole saita dinga kula Dani ta qarfi da yaji kamar likita ta, yanda kasan kudi ake biyanta idan tanamin fada akan matsa qafafun Nan nawa"

Cikin 6acin rai yace "what...?, fada Kuma? To idan qafar tana miki ciwo sosai fa?"

Ganin yanda ya rikice yasa mama Tace"A a tanada gaskiya ai,yanda take kulawar Dani yasa ma yanzu banajin ciwon qafar sosai "
Badan ya gamsu da maganar tataba yace"to waye yayi miki ayyukanki na yau kenan?"

"waye zaimin tunda d'an Dana Haifa baya Nan bare yamin?" cewar mama

Ransa ne yasake 6aci,yanzu idan me kula da mama batayi mata komai ba hakan yana nufin munirat bazata zo tadinga temaka mataba? Kenan ko Bayan ransa munirat bazata ci gaba da Kula masa da maman saba?
Wayarsa ya d'auka yakira number munirat, bugu uku ta d'auka, tayi tunanin baizo qasar ba, saboda acan dinma da number sa yake kiranta, cikin 6acin rai yace "yau kinje kinga mama ne kinji ko tana buqatar wani abu?"

Munirat tafara kame kame, cikin borin kunya tace "yanzun Nan nake shirin zuwa ingano ta, Allah yasa de bacemaka tayi nayi mata laifi ba"

Baice mata komai ba kawai kashe wayar yayi, yadaga murya cikin fishi da 6acin rai ya kwalawa daya daga cikin masu aiki kira, jin muryar Mahmud Wakili yau da Kansa yana kiran me aiki yasa jikin masu aikin yakama karkarwa

Saboda ba kulasu yake ba,baya shiga shirginsu, idan yazo falon kowa nemansa kake karasa saide dagashi Sai mama, Amma yau gashi yana kira Kuma da alama akusa yake, ransa a6ace yake, cikin sassarfa wata yarinya ta qaraso, ya kalleta yace "jeki kiramin me kula da mama"(🙆🏻‍♀️)

Cikin sauri ta juya zuwa Dakin Aisha.

Mama ta kalleshi tace "Aida karabu da'ita, yanzu kana 6ata mata rai zata dinga daure min fuska tana shamin qamshi, nagama lura haushi na takeji saboda Dan sabanin da muka samu rannan,nikuma hakan damuna yake narasa dalili"

'Yar aikin tana zuwa ta ganta cikin blanket, yaye bargon tayi,jikinta na karkarwa muryarta na rawa tace "Aisha kizo inji yalla6ai , yanason ganinki"

Aisha ko bude idonta batayi ba, saboda bayanta dayake mata mugun ciwo, ga ciwon qirji ko dogon numfashi takasa ja, ahankali ta bude Dan qaramin bakinta tace "banda lafiya..., kije kice masa banida lafiya bazan iya tashi ba"

Gaban yarinyar ne yafadi, yaushe zata Iya Kallan idon yalla6ai da Hajiya Mama tace musu Aisha tace bazata iya zuwa ba? To Amma ganin yanayin datake cikin yasa ta juya tafice daga d'akin cikin sanyin jiki, tana zuwa falon ta tsugunna qasa, kanta qasa tace "yalla6ai tana kwance, batada lafiya ne"

Cikin sauri mama tace "subhanallah.... Ashe shiyasa batazo ba"
Duk yanda mama takai da rashin kirki, tana tsoron jinya, bare Kuma Aisha datake bata kulawa yanda ya dace, ta juya ta kalli Shahaab tace"muje kadubamin ita Dan Allah, idan Kuma Asbiti zamuje saimu tafi yanzu"

Tsananin mamaki yakama Shahaab, Wai wacce irin yarinya mama tasamu haka? Yaga fuskar maman ta sauya alamun tausayawa, wacce yarinya ce me sa'ah haka?
Kallan me aikin yayi, har yanzu fuskarsa a daure take, yace"kije kice nace tazo"

Juyawa me aikin tayi cikin sauri Takoma Dakin Aisha, Badon ranta yasoba haka ta daure tatashi, Riga da siket ne ajikinta na atamfa,kayan sunyi mata daidai, hips dinta yayi dass acikin siket din, rigar yar qarama daidai da'ita,dan kwalin kayan yadan Zame alamun kawai dorashi tayi bai gama dauruwa ba, gashin kanta me santsi yafara futowa tagaban goshinta, futowa sukai zuwa falon, Bayan ciwon baya da qirji da takeji harda wata irin faduwar gaba da takeji tun safe.

Kanta yana qasa har suka qaraso kusa da mama, me aikin data kirata ta kalleshi tace "yalla6ai gata" sannan ta juya cikin sauri tabar falon

Hankalinsa yana kan wayarsa yana dannawa, Mama ta kalleta tace "sannu AISHA"

Jin sunan Aisha da'aka kira yasa yadago Kansa cikin sauri, Adede lokacin itama ta d'ago kanta ta kalleshi,(🙆🏻‍♀️)

Idonsu ne yasarqe cikin na juna, cikin wata irin faduwar gaba Aisha ta bude bakinta, cikin zuciyarta tace "Shahaab...."
cikin sauri yatashi tsaye haryana wullar da wayar hannunsa.

Mama ta kallashi da tsananin mamaki tace "MAHMUD lafiya?"
Chapter 32 · 0% Book details