← Book details Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 71

Sashe 15

Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajja tace"Gaskiya hakane Kam, idan takwarar ta taji Natura ta wata uwa duniya Abuja ma nasan bazata yafeni ba, Nasan halin Aysha Yakubu sagagi, cewa zatayi inrasa wazan tura aiki Sai takwarar ta? Nasan halin abata tsaf zata aikata, danhaka jummai ayi hakuri da wannan batu, me sunan qawa kawai zamu hadata da inusa"

Jummai tace "to shikkenan Hajja, Amma Dan kunqi ne, nikam naso Aisha taje komuma wataran maje Abujan mu dandani Arziqi"

Haka tadinga mita harta fice daga gidan, Sai Alokacin Aisha tasaki wata irin ajiyar zuciya, saboda harga Allah batajin zata Iya yiwa uwar wani bauta, itama Tata uwar tana buqatar kulawar ta, haka kawai saita tsallake mahaifiyar ta da Hajja tatafi tana yiwa wata mata aiki? Matar ma uwar mutumin daba birgeta yake ba, mutumin da taqi jinin taji sunansa, mutumin da saboda shi tadena jin redionta kwata kwata, bazai iyu ba

(tofa🥺)

******

Yau makara sukai a sahur, saura minti shida Akira sallah Sannan suka tashi, Ahankali Aisha ta bude idonta, taga babu Wanda yatashi sahur, Kuma wani lokacin bacci yana cikin dad'i za'a tasheta ace lokacin sahur yayi, Amma yau Kuma taga ta danyi baccin sosai, hannunta ta miqa tad'auki wayar Hajja, tana ganin lokaci tazaro idonta, durowa tayi daga gadon tace "Hajja....kunyi sahur ne nice Baku tasheni ba?"

Hajja tace "innalillahi wa inna ilaihirraji'un....ankira sallah ko?"

Aisha tace "A a, ankusa de, waidama babu Wanda yatashi kenan?"

Cikin sauri tafita taje tatashi Ummah da jabir, tasake tashin Abba, ai kowa a gurguje yatashi, Aisha yau babu batun brush, kawai bakinta ta kuskure tadauko musu kular dasuka zuba taliya aciki, da Ummah, da Hajja, da Aisha, da Jabir, gaba dayansu kowa hannu yasaka yafara ci, babu batun zubawa kowa, Abba yayi murmushi yaga yanda suka hade Kai kowa tura abincin yake, Ummah ta Kalle shi tace "kaidama ba sahur kake ba, duba mana saura minti nawa Akira sallah?"

Agogonsa ya kalla yace "saura minti biyu"

Cikin sauri suka qarasa cin abincin, ruwa kuwa kowa tashi yayi yake nema yanasha, kowa sauri yake inbakayi ban waje....

Suna gama shan ruwa kuwa aka kira sallah, Sai Alokacin Hajja tayi magana (😂)
"Oni Aishatu... Da yanzu yau munyi shige, wannan azumin na Bana Inkayi sahur ma Yaya aka qare bare Kuma bakayi ba"

Jabir ya kalleta yace "Hajja keda kikace sahur ba damunki yayi ba?"

"Kai da Allah Ina nufin Alokacin danake Aysha Sulaiman Bompai kenan, yanzu kuwa Hajja A'i nake"

Dariya Aisha tasaki tace "Hajja nifa jinake kun tasheni naqi tashi ne, shine kukai abunku kuka rabu Dani, ashe duka gidan yau makara mukayi"

Hajja tace "aini Gara hakan ma,nasan da yanzu kina Nan kina d'ora abincin a harshanki"

Cikin shagwa6a tace "kaii Hajja, aike nabiyo, kece kike cin abinci kamar bakya so"

Hajja tace "wa?.... Lalle yau na yarda bakisan wacece takwararki ba, ai Aysha Yakubu sagagi, idan tanacin abinci ke kyace yar sarki ce, Aysha inda ace me kudi ce ita bansan wanne irin mulki zatayi ba, Ada canma damuna boarding school dinmu ta Goron dutse idan aka zomin visiting mukaje muka kar6i abincin da aka kawomin, wato idan muka koma daki tafara cin abincin Nan saiki dauka yar wani gwamnan ce, saboda Aysha Yakubu sagagi akwai yanga, gashi batada 6oye 6oye, saide kaji haushin ta, Amma tana fadar gaskiya komin dacinta "

Jabir yasako musu baki cikin firar tasu yace"to Hajja ita qawar Taki ba'a zuwa mata visiting dinne ita? "

Tace"Ana zuwa mata mana, Yan gidansu suna zuwa, idan sukazo tare muke zuwa, kawai de Alokacin ne tafi yimin rakiya gaskiya, saboda kaga a wancen lokacin iyayena sunada kudi, ita Kuma nata iyayen basuda qarfi sosai, to saiya kasance Ana zuwamin visiting din sosai, da Azumi kullum Sai ankawo min abinci daga gida, Kuma idan natashi komawa makaranta Bayan motar Sai ancika min shi taf da Kaya, harnaje nadawo Bana iya cin wani abun, direban dayake kaini makaranta idan ya saukeni har dauke min wasu kayan yake yanamin wayo yana cewa ai wannan ma ba lalle kici ba, nikuma babu wayo, Sai ince eh, to haka mukai karatun mu babu abinda yake rabani da'ita, mutane dayawa suna tunanin ma gidanmu daya, saboda Bama fada, koda munyi fada to a ranar zamu shirya, ita babu rufi, idan na 6ata mata rai fadamin take, nikuma da masifa, inhauta da fada, anan de Sai mutane sun shiga tsakani sun raba mu, Amma kabamu awa uku, saide kaga mun shirya, ko ban kulata ba, to ita Kam saita kulani, tundaga Nan da mutane suka gane halin mu, ko sunga suna fadan saisu qyalemu saboda sunsan zamu shirya"

Aisha tace"to Hajja bakida photon tane kinuna mana? "

Tace"inada shi mana, yana cikin adaka ta aqasan gado na, zan nuna miki takwararki, har saurayinta na makaranta ma duk inada photon sa, Shima zan nuna miki "

Cikin sauri Aisha tace"au Hajja har soyaiya kuke a makaranta? "

Hajja tace" emana, kafin muyi candy kowacce tanada saurayi, mudinga rubuta wasiqa muna aika musu, suma suna aiko mana, Bayan munyi candy ne Kuma muka rabu da samarin kowa tafara tunanin aure, ni muka dawo jigawa, ita Kuma suna kano "

Jin ankira sallar asuba yasa firar tasu ta tsaya, Abba yatafi masallaci, sukuma kowa yafara kokarin daura Alwala.

******

Yau saura kwana uku sallah, tunda sassafe yatashi yayi wanka, yadauko suit takai Kala biyar, duk wadda yad'aga saiya ga batayi ba, daga qarshe yasaka wata ruwan toka wadda ta qarfi fatar jikinsa

Yayi mutuqar kyau shi Kansa daya kalli Kansa a mirror yasan yayi kyau, murmushi yayi yad'auki turarensa yafara feshi dashi ajikinsa
Munirat data shigo Dakin saita zubawa sarautar Allah ido tana kallo

Cikin mamaki tace "my Dear yanaga ka zubar da kayaiyaki akan gado, lafiya?"

Batare daya kalleta ba yace "naza6i Wanda zan saka ne"

"to yanzu duk wannan daka zubar akan gadon basu Maka ba? Dubafa kagani harda suit din Dana siyoma a Cairo"

Yatsina fuska yayi sannan ya kalleta yace "wannan naza6a"

Hannu tasa a qirjinta ta hardesu, sannan ta fuskance shi sosai tace "zakaje wajan Mr President ne?"

Gabansa ne yafadi, Sai alokacin yadago Kansa ya kalleta "no, zamuje jigawa nida Ramadan,ganin aikin gidan marayun Nan"

Wata wawuyar ajiyar zuciya tasaki sannan tace "Alhamdulillah....na yi tunanin wajan wata zakaje wallahi, yanda kake zuba kwalliyar Nan ai sai kasa jinina yahau, nasan inde kafita saiwata ta kallemin Kai, Amma tunda qauye zakaje, nasan banda damuwa,nasan Babu wadda tayi daidai da kalar mijina a wannan baqauyen Garin, babu ita, ba Kuma za'a yitaba"

Kansa ya girgiza yace"hakane"

Bakinsa yad'ora akan goshinta yasakar mata kiss, sannan yafice daga d'akin cikin sauri

Kai tsaye wajan mama yatafi, ganin ta yayi tana matsa qafafunta da kanta, cikin sauri ya qaraso ya tsugunna yaci gaba da matsa mata qafa fun, Kallan sa tayi tace "masha Allah,Dan mama yau Kuma Sai Ina? Ko qasar zaka Bari Amma baka sanar Dani ba?"

Murmushi yayi, dimples dinsa suka futo, yace "Wai nayi kyau ne mama?"

Tace "sosai ma kuwa, kamar Ango"

Murmushi yayi tare dayin qasa da Kansa, yad'ora hannunsa akan sumar Kansa ya Dan Sosa qeyarsa, sannan yace "haka munirat ma tace Wai nayi kyau, babu inda zanje mama, jigawa kawai nakeson zuwa saboda ganin aikin gidan marayun dakika sakani"

Cikin farinciki mama tace "Allahu akbar, Allah yayi Maka Albarka Mahmud, yanda kakemin biyaiya kaima Allah yabaka Wanda zasuma fiyeda haka, Allah yasa kafin nabar doron duniyar Nan Inga jikokina Kuma Inga Qawata Aysha Sulaiman Bompai"

Cikin sanyin jiki yace "Amin mama, Bari intafi, Ramadan yana jirana a Airport"

Tace "to Allah ya dawo daku lafiya, ABINDA KAJE YI ALLAH YABAKA NASARA AKANSA"

Ahankali yace "Amin mama" sannan yakama hannunta yayi kissing Bayan hannun, yafice daga falon cikin sauri, binsa tayi da kallo tana jin dadi a ranta, cikin zuciyar ta tace "Allah ka qara aramin lokacin dazanga yayan Mahmud dina...."

Motoci biyu ne suka rakashi Airport, daya yana ciki, dayar Kuma sojoji ne, suna zuwa Ramadan yazo da sauri yatareshi, sannan suka qarasa cikin Airport din.

Bayan sun sauka a dutse, wani direban ne yasake daukar su, Kai tsaye wajan aikin gidan marayu suka wuce, komai yayi, suna aikinsu yanda ya kamata, saida sukai sallar la'asar awajan, Shahaab ya dubi Ramadan yace "muje ko?"

Ramadan yace "Ina?"

Kai tsaye yace "Abinda yakawo mu"

Wayarsa ce tafara ringing Kiran munirat, Bayan sun gaisa tana masa qorafi bai ta6a tafiya yaqi kiranta ba, Sai wannan tafiyar, goshinsa yadan shafa yayi shiru, shi Kansa yasan gaskiya ta fad'a masa, baisan menene yake damunsa ba yau din, haquri kawai yabata, sannan yafada mata aiki ne yamasa yawa, zasuyi waya anjima, daga Nan yakashe wayar

Kallan sa Ramadan yake lokacin dayake waya da Munirat, gaskiya Shahaab ya sauya sosai, Kuma yasan cewa duk a dalilin wannan yarinyar ne, kowacce irin yarinya ce haka data sauya masa tunani lokaci daya? Shikam zai so yaga wannan yar baiwa, to matsalar Kuma shine shi yaqi yarda son yarinyar yake, Amma babu damuwa ai lokaci zai nuna komai.

Shahaab yace "Ramadan bakajini bane?"

Ramadan yace "najika Sarai, kaine de kunnanka yadena aiki, idonka yarufe, kwata kwata ka manta waye Kai, ka manta cewa kaine MAHMUD WAKILI...."

cikin rashin fahimta yace "mekake nufi?"

"Abokina kaine kace min yarinyar Nan batasan waye kaiba, asalima ce mata kayi kaidin Yaron Mahmud Wakili ne, Kuma Sarai ta ganka, Kuma yanzu Sai muje garinsu da yamma, mu parker mota aqofar gidansu, muyi magana da'ita, karka manta ita kadai ce batasan waye kaiba, bawai mutanan Garin ba, itama nayi mamaki dakacemin bata sanka ba, to yanzu kuwa muna zuwa, idan wani yaganka ya ganeka, zai fadawa na kusa dashi, Shima ya fadawa wani, dahaka mutanan qauye su taru azo wajan Mahmud Wakili ayi masa godia saboda kwanaki ya aiko musu kayan abinci, Shahaab kana buqatar privacy, karka manta a Abuja ba Kai kadai kake yawo ba, Nan dinma kwanciyar hankalin jihar ne yasa kake yawo ko'ina haka "
Chapter 15 · 0% Book details