← Book details Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 71

Sashe 13

Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda yashigo yaga munirat bata biyo shi ba, saiya kwanta agadonsa tareda d'ora Kansa akan hannayensa ya zubawa Saman Dakin ido ya fad'a duniyar tunani, tunanin sa yayi zurfi ko shewar da qawayen munirat suke yi ba yajin su.

Mamakin Kansa yake, yana jinsa kamar bashi ba, haka Nan yakeji kamar ansauya shi, Bai ta6a tunanin akwai wata yarinya dazata tsaya masa a ransa Bayan munirat ba,saboda yasan Kansa, yasan bazai ta6a son wata yarinya bayantaba.

To Amma meyasa tunanin yarinyar yakasa barin qwaqwalwar sa? Wata zuciyar tace dashi "may be Dan kanason Yara ne, Kuma ka ganta yar qarama kamar Baby shiyasa kake tunanin ta"

Wata zuciyar Kuma tace dashi "kokuma saboda maganganun data fada Maka ba"
to kuwa in hakane dole ya nemeta domin yaji dalilin dazaisa tace masa matsiyaci, Shima abun atuhume shine, shi me yayi?

But ta wacce hanya zai sake ganin ta?

Cikin jin haushin Kansa yace "Wai meyasa zan damu kainane, saboda wata qanqanuwar yarinya?

Munirat ce tashigo Dakin Bayan ta sallami qawayenta.

Jin shigowar Tata ne yasa Shima ya watsar da tunanin yarinyar, saboda shide yasan cewa ba sonta yake ba, to menene zaisa yadamu Kansa akanta?
Kwanciya tayi agefen sa ta dora kanta akan dantsan hannun sa, cikin kulawa tace "tunanin mekake my Dear?"

Kai tsaye yace "Haihuwa"

Gabanta ne yafadi, tatashi zaune tana Kallan sa tace "My Dear haihuwa ta Allah ce, nide nasan lafiya ta kalau, Kuma kaima haka, sannan sisters dina dasukai aure kowa tana haihuwa a gidanta, Kuma my dear ni banga abunda zai saka tunani ba, kanada komai na rayuwa, meyasa zaka damu saboda haihuwa, ni Bana tunani akan haihuwa, saboda nasan lafiya ta kalau, Kuma haihuwa gadon Miji takebi ba gadon mata ba, inda gadon mata takebi to da tuni na haihu,tunda Bani kadai momy na ta Haifa ba, so nasan matsalar daga kaine, tunda mama ma Kai kadai ta Haifa......"
(✋🏻)hannu kawai yadaga mata, batare daya kalleta ba yace"please Leave me alone ok?"

Babu musu tatashi tafice daga d'akin Sai mita take cikin ranta, Dame ta rageshi a rayuwa? Kullum cikin neman magunguna take saboda ta gyara kanta yasamu yaji dadi, Amma duk da haka baya Gani, yaje wajan masifaffiyar tsohuwar sa ta hure masa kunne akan haihuwa, Nima zaizo ya dameni.

Shikam tana fita runtse Idonsa yayi, me munirat take nufi? Kenan shine baya haihuwa ba'ita ba? Duk haqurin Dayayi akanta yake zaune da'ita shekara da shekaru bai ta6a yunqurin qarin aure ba shine take fada masa shi kadai mama ta Haifa? Tsaki yasaki yatashi yafita daga gidan gaba daya, ko ruwa baisha tareda su ba, a masallaci yasha, Bayan an idar da sallah ma bai dawo gidan ba Sai wajan shadayan dare,munirat tun tana jiran dawowar sa taji shirun yayi yawa saboda Bahaka yasa baba, saita zargi kanta, kanta tayi wa fada karfa taje yakoyi Zaman waje duk da tasan ayyukan sa bazasu barshi ba, Amma idan ya Koya lokaci daya zasu zigashi yafara neman aure, ita Kuma abinda bazata juraba kenan, shiyasa yana shigowa ta rungume shi tareda fashewa da kukan kissa, tun yana shareta har tayi nasarar shawo Kansa yahuce

******

Yau Aisha gajiya tayi da girkin, gashi Ummah batada lafiya, itama Kuma tagaji, ita Kuma Hajja tana kulada sana'ar qanqarar ta, Dan haka itama yau tayi fuska ta wuce Dakin Hajja tayi kwanciyar ta
Saida Hajja tagama siyar da qanqara lokacin har hud'u na yamma ta gota sannan ta nemi waje ta zauna, taleqa daki tace "me sunan qawa, futo kije ki siyo mana Dan tattasai kidafa macaroni ko jallop ce"

Cikin shagwa6a tace "wallahi Hajja nagaji sosai, jinake kamar na fadi"

Hajja ta Jinjina kanta tace "ai shikkenan Naga alama yau iskanci kikeji tonima nazama yar'iska, kowa ya zauna da yunwar sa" (🤭)

Aisha tace "A a Hajja, abun bekai nanba,ni Bana fada da Azumi, saide in qarshe aka kaini" daga Nan tafuto daga d'akin tasaka hannu acikin cinikin Hajja tad'auki kudin tattasan,sannan tafita taje tasiyo tadawo ta dora musu abincin

******

Kwana daya Shahaab yayi yana yaqi akan tunanin Aisha, daqyar ya'iya yin wuni daya, da yaji zuciyar sa tana so ta kawo masa tunanin yarinyar, Sai yayi sauri yad'auki wani abun dazai dauke masa Hankali,acikin kwana dayan Nan wuni yayi da jarida a hannunsa,har munirat tana mamakin sa, to Amma Kuma karatun jaridar ma daya fara zata Fado masa, baisan lokacin Dayayi wulli da jaridar ba aikuwa tayi d'aid'ai a falon nasu (😅)

Yau tunda sassafe ya shirya yafita office, yanaso ya tsiri aiyuka dayawa ko hakan zaisa ya yakiceta a ransa, saide yana zuwa ma aikata suka shaida masa cewa yaune ranar dayasa zasuyi meeting akan sabbabin masu bada horo daya gayyato daga qasar Germany domin su sake wayar wa da sabbabin ma'aikatan su dasuka dauka wannan watan Kai.

Hamdala yayi a ransa, yaji dadin hakan sosai saboda shaf Yama manta da wannan batun, shadaya daidai na safe suka fara meeting din.

Qwararrun masu bada horon ne suke bayani cikin salon birgewa dakuma sanin makamar aiki dangane da yaqi dacin hanci da rashawa, Dafarko Kam a nutse yake, yana kallon komai daki-daki yanda yakamata, Amma basufi minti talatin ba da fara meeting din ya Lula duniyar tunanin ta....,wata zuciyar tace dashi "kotayi dinkin sallah?"

Magana masu bada horon suke masa Amma inaaaa... Hankalinsa yariga yatafi, Ramadan dake gefensa yata6ashi, firgigit yayi ya dawo cikin hayyacinsa, Kansa yadafe ya kallesu yace "am.. Idan babu damuwa Dan Allah kuyi hakuri kuci gaba da metting d'in, inada wani Babban uzuri agabana"

Daya daga cikin ma'aikatan efcc din yace "Amma Boss maganar dasuke fa tanada muhimmanci, yakamata ka tsaya..."

Agogon hannunsa ya kalla yace "kuyi hakuri please, Babban uzuri gareni" yajuya ya kalli baqin nasu yace "mr Jone next time ok?"

Kafin wani yasake magana yad'auki jacket dinsa, tareda zira hannunsa guda daya cikin aljihun wandonsa, cikin sauri yafice.

Gaba d'ayansu da Kallan mamaki suka bishi, Bai ta6a yin hakan ba, kowa yasan inde akan aiki ne yana tsayawa ayi komai a gabansa, su kansu baqin basu so yatafi ba, saboda sun so ace yana Nan suka gama bayanin komai, koba komai zasu samu Jinjina daga gareshi.
Ramadan ne yasake basu haquri yace "may be baida lafiya ne, Bari in bishi"

Sun yarda da abunda Ramadan din yafada, tabbas Mahmud Wakili ba qalau yake ba yau.

Tunda yabar Dakin meeting din nasu, Kai tsaye office dinsa yawuce yafara dube-dube cikin loka yana tunani a ransa, ba lalle ne yar qarama tayi dinkin sallah ba, wata loka yabude yafuto da kudi bandir biyu, Yan dubu dubu, aqalla zasu Kai nera dubu Dari biyu,Adede lokacin Ramadan yashigo, yayi mamakin ganin kudi ahannunsa, cikin damuwa yace "meyake faruwa ne Abokina?"

Bai iya qarya ba, haka Kuma bayason yakoya yanzu, danhaka batare dawani 6oye-6oye ba yace "wata yarinya zanje nakaiwa"

Ramadan Kam baisan lokacin daya kwashe da wata irin dariya ba, kujera ya gyara ya zauna yadinga dariya harda Tari.

Baqin ciki ne yakama Shahaab, yazubar da kudin akan table din gabansa, sannan ya zauna a kujera ya jinginar da Kansa a jikin kujerar yana Kallan rufin office din, saida yagama dariyar sa son ransa, sannan yajuya ya kalli Shahaab, baya buqatar yayi wani bincike yasan cewa abokin nasa yagama kamuwa cikin tarkon wata yarinyar, ahankali cikin nutsuwa ta sigar lallashi yace"Shahaab kode kafara son wata yarinya ne?"

Ransa ne ya6aci, cikin fishi yace" wacce irin banzar magana ce wannan Ramadan? Dama tunanin dakake akaina kenan? Yarinya qarama cefa, 'yar cikina, nama haifi wannan yarinyar, sannan Kuma.... Ba data kunya ma.... "

ya qarasa maganar qasa-qasa kamar baison Ramadan din yaji, fuskar Nan yahade ta kamar sabon hadari

Ramadan da yaga Shahaab bai gama yarda son yarinyar yake ba, Sai yayi haquri ya bishi a yanda yake so din, cikin hikima yace" okay,naji, kadena cewa yar cikinka, tunda ba kaine ka haifeta ba, ai Dafarko nayi tunanin budurwa kayi mana, but koma de menene kada ka nuna mata cewa Kaidin kanada Hali "

"menene danna nuna mata inada kudi Ramadan?saboda me zanyi mata qarya Bayan ba sonta nake ba? Idan tagano nayi mata qarya mutunci na zubewa zaiyi a'idonta, yanzun ma abinda yasa kaga na dauki kudin Nan Ina tunanin ba lalle ne tayi dinkin sallah ba, shine zan Kai mata tayi "

Ramadan yace"A'ina yarinyar take ne? Tasan Kai waye?"

Girgiza Kansa yayi yace "no, bata sanni ba, tana jigawa, qauyen damuka raba kayan Azumi, harni take cewa ni abun atuhume ni ne?sainaje nasaka tafadi abinda yake ranta da bakinta"

Mamaki yakama Ramadan, gashi babu damar tambaya kar abokin nasa ya harbo jirginsa,yanzu awannan qauyen Kuma cikin dare har yaga yarinyar datasa yake wannan rawar jikin? Cikin kwantar da Hankali yace "Abokina, inde wannan qauyen ne wallahi kana bata wannan kudin, guduwa zatayi, zatayi tunanin saceta kazo yi, kokuma kaidin Dan yankan kaine, tayaya zaka dauki kudi haka a fili kawai kabawa yarinya Bayan kace bata sanka ba?aikuwa kana bata wannan kudin yanzu nema zatace tabbas kaidin abun atuhumeka ne, Kayi hakuri ka dauki ko dubu biyar ne kabata, ahankali ahankali zata saba dakai harka bata kudaden masu yawa, Amma bade lokacin farko ba, tunda Naga kanaso ka taimaka mata ai nasan ganin ta kake kamar 'yarka, shiyasa kake tausayin ta, Amma Kuma yanada kyau koda abota zakayi da'ita to kasan halaiyarta kafin kufara, yakamata kasamu Mai sonka da abota ta tsakani da Allah bawai don kudinka ba "

Cikin damuwa yace
"Ramadan tayaya zan'iya mata kyautan dubu biyar? Kamar Almajira? Banason qarya, bazan zo daga baya tasan koni waye qarshe tamin rashin kunya ba, Gara infada mata gaskiyar koni waye, sannan inji dalilin dazaisa tacemin matsayaci, idan taqi fada Kuma sainasa ankama ta na zaneta dakyau yanda zata Dena rashin kunya"

Ramadan da jikinsa yayi yayi Sanyi akan maganganun Shahaab saiya tafi duniyar tunani, tabbas Shahaab yanason wannan yarinyar koma wacece,to da alama akwai abinda yahadasu har tayi masa rashin kunya, Wanda 6acin ran hakan yasa yakasa gane sonta yake.
bazai iyu yanaji yana Gani yabarshi yasake aure irinna munirat ba, Gara yafara gwada yarinyar yaga hankalin ta, to Amma shi Shahaab yadage baison qarya, ahankali yasaki ajiyar zuciya yace "zaka iya Abokina, mu gwada hakan"
Chapter 13 · 0% Book details